JAGORANCIN IMAM SADIK (a.s)
 

Ayatullahi Uzma Sayyid Ali Alkhamena'i
Fassarar: Malam Umar Kumo
Dubawa: Hafiz Muhammad Sa’id

Gabatarwar Cibiyar Ahlul-bait (a.s)
Rayuwar Ahlulbaiti (a.s) ta banbanta da ta waninsu domin ita wata silsila ce kwakkwara, mara yankewa, sai dai yanayin zangon tarihin da kowane imami yake rayuwa a cikinsa, ya kan sa ya dauki wani matsayi wanda a zahiri ka ce yana sabawa da wanda imamin da ya gabace shi ko ya biyo bayan sa ya dauka, sabani mai tsanani. Muna iya ganin wannan a matsayin da Imam Hassan (a.s) da Imam Hussain (a.s) suka dauka. Amma bisa hakika wannan ba sabani ba ne, aiki ne daidai da abin da yanayi ya nema, ta yanda matsayin kowane daya daga cikinsu yana cikata aikin imamin da ya gabata ne ko ya yi shimfida ga aikin da wanda zai gaje shi zai gudanar.
Sakamakon rashin fayyacewar nazari a tattare da sashen masu bahasi kan rayuwar imamai, an sami nazariyya da ra’ayoyi daban-daban wajen kokarin bayyana yanayin aikin da wani Imami ya zartar.wanda sun kasance bisa kuskure, bincike-bincike kuwa ba a zurfafa mahangarsu ba kuma ba su dogara kan tushe na imamanci da isma ba domin ba su ginu kan ingantacciyar fahimta mai iya riskar hakikanin yanayin ba.
Asalin wadannan nazarce-nazarce mara tushe ne mai cin karo, ta kowace fuska da imani da ma’asumin jagoranci wanda kowane imami yake tafiya a kai bisa abin da ya fahimta daga yanayi ko kuma dabai’ar zangon da ya sami kansa a ciki, da kuma kasancewar matsayinsa ba matsayi ne wanda son rai ko amfanin kai ko mai da martani a makance suke rinjaya ba. Matsayi ne wanda yake tattare da hikima da hangen nesa da dacewa da taimako daga ludufin ubangiji.
Irin wancan karkatacciyar fassara ta shafi rayuwar dukkan imamai. Sai ka ga wani lokaci ana sifanta su da daukar matakin dauki ba dadi, kamar matakin juyin juya halin da Imam Hussain(a.s) ya dauka, ko kuma a ce sun karkata zuwa rayuwar tsanaki da nisantar fagen siyasa kamar yanda Imam Sajjad (a.s) ya yi. Ko kuma a buga masu tambarin masu daidatawa da azzaluman mahukunta kamar matsayin Imam Sadik (a.s).
Wannan littafin da ke gabanmu ya kunshi wata laccar da mai girma shugaban musulmi Sayyid Ali Khamene’i (Allah ya ja zamaninsa) ya yi kafin juyin Islama mai albarka da aka aiwatar a kasar Iran. A cikinta ya bijiro da wadancan karkatattun nazarce-nazarce tare da rusa su ta hanyar karfafan hujjojin ilmi da tarihi.
Daga bisani, Sayyid ya gabatar da ingantaccen nazari mai fassara matsayin da kowane imami ya ba da himma a kan shi domin ya yi shimfida ga imamin da zai biyo bayan shi, har al’amari ya iso hannun imam Sadik (a.s). jagorancin wannan imami bai kasance mai mika wuya ga son rai ko amfanin kai ko kuma tsoron azzalumai ba. Wannan jagorancin wani ma’sumin matsayi ne mai bin ka’idar da Allah subhanahu wa ta’ala ya bayyana, ma’asuman gabanin Imam (a.s) kuma suka shimfida masa. Imam Sadik a nasa bangaren aiwatar da wannan tafarkin ne ya yi, yana mai amfani da kwarewarsa ta siyasa da saninda Allah (s.w.t) ya karfafa shi da shi, domin ya jagoranci jirgin musulunci zuwa gabar tsira da aminci, domin kuma ya tsare wa musulmi addininsu da akidarsu bisa dacewa da ingantaccen asalinsu wanda Annabi Muhammadu (s.a.w) ya kawo, tushen da azzalumai suka yi kokarin shafe almominsa da bice haskensa, tsawon tarihi.
Cibiyar Ahlulbaiti (a.s) ta kasa da kasa, saboda sauke nauyin da ya rataya a wuyarta, ta dauki nauyin buga wannan littafi tare da watsa shi don ya kasance wata haskakawa ce kan tunanin musulunci da ingantaccen tarihi, domin kuma ya bayyana wa masu bincike kan Ahlubaiti fuska mafi tsabta da za’a fahimci hanyarsu mai albarka.
Cibiyar Ahlulbaiti (A.S) Ta Kasa Da Kasa


Gabatarwar Mai Tarjama
Wani dan labari dangane da wannan lacca:- Wannan labari yana nuna abinda rayuwa a kasar Iran gabanin Juyin Islama take tattare da shi, na aiyukan tabbatar da musulunci da kuma kalubale da karfen kafa daga bangaren masu adawa da kiran .
Wata rana cikin watan Shawwal shekara ta 1394 H. kararrawar tarho ta buga a gidan malami mai laccan a birnin Mashhad, mai magana a wayar shi ne Shahid Dokta Muhammad Mufattih daga Tehran.
Bayan gaisuwa, Sheikh Mufattih sai ya nemi Sidi da ya taho Tehran.ran 25 ga Shawwal (watau ranar wafatin Imam Jaafar bin Muhammad Assadik (a.s) domin ya gabatar da wata lacca kan Imam Sadik .
Halin da ma’abocin laccar yake ciki ya kasance mai kunci a wancan lokacin saboda yawan aiyuka da karantarwa da yawan jama’a masu zuwa daga nahiyoyi daban-daban na Iran. Yana ba da laccoci a masallacin Imam Hassan da masallacin Alkarama a Mashhad, birnin da ke gabashin Iran, sannan ya tafi yammacin kasar domin gabatar da lacca a Hamadan da Kermanshah. A cikin Mashhad din kansa yana koyar da tafsiri da Nahjul balaga da hadisi ga kuma darusan kwarewa a fikihu da usulu.
Duk wadannan aiyuka Sidi yana gabatar da su ne a cikin wani hali mai tsananin matsi, ga wahalar rashin kudi ga ta kuntatawar yanayin siyasa. Ya kasance yana rayuwa cikin matsanancin talauci ba tare kowa ya sani ba. Sannan masu mulki suna matsa masa lamba suna sa ido ainun bisa duk abin da yake yi. A wannan shekaran ne suka rufe Masallacin Alkarama, abin da ya sanya Sidi ya takaita da karamin masallacinsa, watau masallacin Imam Hassan ya ci gaba da aiyukansa. A cikin hunturun wanna shekarar ne masu mulki suka sake kama shi, abin da ya kai shi kurkuku a karo na biyar ke nan.
To a cikin irin wannan yanayin ne Sheikh Mufattih ya bukaci Sidi Khamene’i da ya gabatar da lacca a kan Imam Sadik (a.s) a Tehran a Masallacin Javid inda shi Sheikh Mufattih yake ba da salla. Ma’abocin laccar sai ya ba da hanzari saboda dalilan da muka ambata da kuma saninsa cewa akwai malaman da za su cike gurbinsa a can Tehran, kamar su Sheikh Mufattih kansa. Amma Sheikh ya matsa, saboda haka malamin ya yarda. Bayan kwanaki Sheikh Mufattih sai ya sake buga waya yana cewa:-
“Yan sanda sun hana taron laccar” Sidi ya yi ajiyar zuciya, yana mai jin ya huta da wannan nauyin, ya kuma yi hamdala. Ba’a dade ba sai ga Sheikh ya sake bugo waya yana mai cewa:- “ Alhamdu lillahi an dauke hanin. Muna nan muna sauraronka a ranar da muka ajiye”.
Sidi ya yi iya kokarinsa domin a karbi uzurinsa amma ina Sheikh Mufattih bai gamsu ba, sai ya amsa da cewa:- “Mun riga da mun sanar da batun laccan nan cikin jami’o’ i” Sidi ya ba da dalilin cewa samun tikitin jirgi yana da wahala. Amma Sheikh sai ya ce a shirye yake ya saya masa tikitin, saboda haka ba makawa ga halartar Sidi!
A ranar laccar ya baro Mashhad ya kuma iso Tehran yan sa’ o’ i kafin lokacin farawa, sai ya wuce zuwa masallacin kai tsaye. Yayin da mai masaukinsa ya gan shi, ya yi farin ciki matuka, a lokacin kuwa yana tare da matasa kamar dari biyu suna jiran a ta da salla. Ana cikin salla matasa sai zuwa suke yi har adadinsu ya kai dururuwa da dama. Bayan’yan mintoci sai ga dalibai gungu gungu suna ta shigowa, wannan bayan an tashi daga darasi a jami ‘o’ i kenan.
Masallacin da farfajiyarsa da loko-lokon da ke daura dashi duk suka cika makil da mutane. Sidi ya fara lacca yana rike da takardu guda arba’in wadanda suke kunshe da muhimman batutuwa kan laccar. Ya ci gaba da bayani wanda ya dauki hankalin masu sauraro, kai ka ce tsuntsaye ke bisa kawukansu saboda tsananin natsuwa. Laccar ta dauki tsawon sa’a uku amma sashen takardun nan kawai Sidi ya sami damar sharhinsu. Da ya zo rufewa sai ya daga wadancan takardu arba’in yana mai ishara da cewa lokaci bai ba shi damar gabatar da dukkanin abin da ya yi niyya ba.
Bayan wannan zama ba a dade ba sai aka kama Sheikh Mufattih aka hana shi salla a masallacin Javid. Bayan an sako shi sai ya koma masallacin Kuba. A nan, ya zama wajibi mu yi nuni da wani muhimmin al’amari, shi ne : Sidi Khamene’i (Allah ya kiyaye shi ) ya gabatar da laccan nan ne shekara ashirin da suka wuce. Kuma babu shakka ya yi nazari da bincike mai yawa kan rayuwar Imaman Ahlulbaiti (a.s) saboda haka ta yiwu yana da wadansu sababbin ra’ayoyi ko kuma ya canja ra’ayi, kan wata mas’ala daga cikin mas’alolin da ya gabatar cikin jawabin. Hakika mun so mu san ra’ayinsa kan wadannan mas’aloli domin mu cimma ra’ayoyinsa na baya-bayan nan kafin mu soma tarjamar wannan jawabin zuwa harshen larabci. Amma nauye-nauye da tarin ayyuka da cushewarsu ya hana hakan. Saboda haka za mu gabatar da ita kamar yanda take. A cikinta akwai sabon ilmi mai yawa da kuma gadon tunane-tunanen musulunci kamar yanda ake tattauna shi a Iran gabanin nasarar Juyin Islama, abubuwanda suke da muhinmanci ga duk wani mai bincike.
Ana iya lura da cewa Sidi ya yi fito-na-fito da ra’ayoyi guda biyu wadanda yake yawan sukar su a laccocinsa da darussansa. Wadannan kuwa su ne: Ra’ayin gurguzu mai sukan musulunci da alamominsa, yana sifanta mazajen musulunci da cewa ba su tabuka komai ba wajen kare hakkin matalauta da wadanda aka zalunta, dadin dadawa ma sun kasance madogarar azzalumai da masu hanu da shuni! Na biyunsu shi ne ra’ayin wanda suka yarda an rinjaye su. Saboda rinjayarsu da aka yi sai suka kasance ba su da katabus, kokari suke su sami abin da wai zai zame musu hujjar rashin motsawa, a cikin tarihin rayuwar Imaman musulunci. Wadannan ra’ayoyi sun yi tasiri a kasar Iran kafin habakar Juyin Islama, sun kuma zamo karfen kafa ga masu kiran al’umma zuwa hanyar musulunci.
Dokta Muhammad Ali Azarshab


Ubangiji Madaukaki yana Cewa:
Daga muminai akwai wandansu mazaje da suka gaskata abin da suka yi wa Allah Alkawari a kansa, sa'annan a cikinsu, akwai wanda ya biya bukatarsa, kuma basu musanya ba, musanyawa. Ahzab 23
Kuma muka sanya su shugabanni suna shiryarwa da umurninmu. Kuma muka yi wahayi zuwa gare su da ayyukan alheri da tsayar da sallah da bayar da zakka. Kuma sun kasance masu bauta garemu. Anbiya 73.

Dubi Biyu Karkatattu
Godiya tabatta ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah da alayesa da wadanda suka yi koyi da shiriyarsu.
Akwai karkatattun dubi guda biyu kan al’amrin Imam Sadik (a.s) wadanda suka samo asali daga nau’i biyu na tunani. Abin mamaki a nan shi ne duk da sabawarsu da juna suna da kusaci wajen kamanni da abin da suka kunsa da kuma tushe, kai ana ma iya cewa wadannan dubi biyu suna da cikakkar tarayya a sashen ginshikansu.

Dubi Na Farko
Ra’ayi ko kuma kallo irin na masu karewa watau masoya, wannan ra’ayin wasu masu zaton su mabiyan Imam Sadik (a.s) ne amma shi’arsa ne da fatar baki kawai banda aiki. Ra’ayin a takaice shi ne:-
Cewa Imam Sadik (a.s) ya sami yanayin da imaman da suka gabace shi ko suka biyo bayan shi basu samu ba, yanayin da ya ba shi damar yada hukunce-hukuncen addini da kuma bude wa dalibai kofofin majlisinsa. Ya zauna gidansa yana karbar masu zuwa, ya rungumi karantarwa da yada ilmomi, duk dalibi ko mai bidar gaskiyan da ya zake masa yana kashe kishinsa na ilmi. Mutum dubu hudu suka yi karatu a gabansa, kuma ta hanyar wadannan dalibai ilmomin Imam Sadik sun watsu a ko ina. Daga cikinsu akwai ilmomin addini kamar su fikihu da hadisi da tafsiri, akwai kuma ilmomin dan’adamtaka kamar su tarihi da kyawawan dabi’u da ilmin zamantakewar al’umma.
Imamu ya yi mukabala da ma’abota sababbin ra’ayoyi, ya yi raddi kan zindikai da yan maddiyya da mulhidai, ko dai kai tsaye ko kuma ta hanyar dalibansa. Ya yi yaki da mazowa karkatattun addinai matuka. A ko wani fagen addini Imam ya tarbiyantar da wasu fitattun dalibai da kwararru.
Ma’abota wannan mahanga suna karawa da cewa: domin burin Imam a kan ci gaban wannan gagarumin aikin ilmantarwa, dole ta sa ya guji sa baki cikin al’amuran siyasa, saboda haka bai gabatar da kowani aikin siyasa ba, bugu da kari ya ma zabi hanyar daidaitawa da irin siyasar halifofin zamaninsa domin dadada musu da nisantar duk wata rikitarwa da ka iya kusantar aikinsa. Don haka bai yi fito-na-fito da halifofin ba, ya kuma hana kowa yin hakan. Wani zubin ma yanayi yana sawa Imam ya je gaisuwa ya kuma sami kyaututtuka da goyon bayansu. Idan shugaba ya yi masa mummunan zato sakamakon faruwar wata harkar tawaye ko kuma tsegunta masa wata tuhuma, Imam ya kan je gaban shugaban domin ba da baki.
Ma’abotan wannan dubin su kan jero hujjojin tarihi domin karfafa ra’ayinsu. Hujjojin sun hada da riwayar Rabi’u Alhajib da makamantansa, wadanda suke siffanta Imam da baiyana kuskure da nadamarsa a gaban Halifa Mansur. Wannan riwaya tana dangantawa Imam kalmomin yabon Mansur, wanda ko shaka babu karya ce a ce sun fito daga Imam Sadik (a.s.) dangane da azzalumai irinsu Mansur. Wadannan kalmomin suna sifanta Mansur cewa kamar Yusuf da Sulaiman da Ayyuba ya ke, suna neman ya dauki hakuri kan munana masa da Imam ko ‘ya’yan Hassan suke masa: “Hakika an baiwa Sulaiman (mulki) kuma ya yi godiya, an jarrabi Ayyuba, ya yi hakuri, kuma an zalunci Yusufu, ya yi gafara, kai kuma irinsu ne……”[2]
Wannan ra’ayi yana sifanta Imam da cewa shi masani ne mai bincike, Abu Hanifa da malik sun sha daga kogin ilminsa, sai dai ya yi matukar nisantar yaki da zaluntar addini da masu mulki ke yi, ya kuma nisanci bukatun umurni da kyakkyawan aiki da hana munkari yayin da sarki ya zama ja’iri. Imam ba shi da wata dangantaka da masu tawaye wa zalunci ire-iren su Zaid ibn Ali da Muhammad bn Abdullah da Hassan bn Ali shahidin Fakh ko kuma rundunonin wadannan mutane. Bai kasance yana mai da martani kan abin da yake aukawa jama’ar musulmi, ko nuna damuwa kan dimbin dukiyar da Mansur yake tarawa, ko yunwar da ‘ya’yan Annabi (s.a.w.a) suke fama da ita a cikin tsaunukan Tabaristan da Mazandaran da garuruwan Irak da Iran ba, ta yanda basu da abinda zasu sa a baka ko abinda zai rufe musu al’aura idan suna son salla a jam’i !! Kuma ba ruwansa da kisa da azabtarwa da tarwatsa mabiyansa alhali suna hannu rabbana basu samun ko da kwatankwancin abin da marasa galihun wancan lokaci suke mora!!!
A zaton ma’abota wannan dubin Imam Sadik sam bai nuna wata damuwa kan wannan yanayi ba, a maimakon hakan ya gamsu da yin mukabala da ire-iren su Ibn Abi Awja, ya rufe masa baki da hujjoji ya kuma rinjaye shi duk da cewa ba zai ba da gaskiya ba. Wannan shi ne siffanta Imam Sadik da mazowa ra’ayin farko sukayi.

Dubi Na Biyu
Masu dauke da irin wannan dubin ba su yarda da imamancin Imam Sadik ba. Ita wannan mahanga tana ganin cewa ya nuna halin ko oho bisa zaluncin da yake aukawa al’umma. A zamamaninsa al’umma na kukan zaluncin yanayin zaman jama’a mai hawa-hawa da dagawar siyasa da babakere kan dukiyoyin jama’a [3] da hadarin da ya shafi rayuka da mutuncinsu. Dadin dadawa sarauta ta rinjayi hankula da rayuka da tunani da kuma zukatan mutane. Lamarin ya kai ga al’umma ta rasa mafi kankantan hakkokin bil Adama wanda ya hada da ikon zabe. A gefe guda kuma azzalumai suna ta wasa da makomar mutane yanda suka so, suna gina katafaran soraye kamar soron Al-hamra wanda ke makwabtaka da dubban kangwayen da matalautan al’umma ke zaune a ciki. Cikin wannan jama’ar da take dandana nau’i daban-daban na rashin adalci da danniya wai Imam Sadik ba abin da ya yi sai fuskantar bahasinsa da bincike da tarbiyyar dalibai, yana karkata dukkan kokarinsa kan samarda fukaha’u da masana ilmul kalam!!
Hakika dukkan mahanga biyun nan sun bi son zuciya wajen hukunci kuma basu ginu kan wani tushe ba, basu kuma dogara kan wani dalili na gaskiya ba. Sai dai ra’ayin farko ya fi tsanani wajen bin son zuciya da zaluntar Imam Sadik (a.s) tun da yake ya fito ne daga masu da’awar wai su shi’arsa ne kuma mabiyansa.
A nan ban yi niyar daukan salon bahasin ilmin nan da aka saba bi wajen bincike-bincike, wanda a kan bijiro da dukkanin nassoshin da suka yi magana kan rayuwar Imam Sadik (a.s) sannan a auna wannan da wancan wajen matani da isnadi har a fitar da sakamako ba. Abin da nake nufi shi ne gabatar da nazari na uku wanda ya sha bam-bam da wadancan biyun. Sannan in auna shi da hujjojin da zan tsamo daga littattafan da suke hannunku’ domin, a matsayinku na alkalai ‘yan ba-ruwan mu, ku iya hango fuskar Imam ta hakika.
Kafin in shiga cikin bahasin ya zama wajibi in yi nuni da cewa dukkanin nazariyyan na biyu basu dogara kan sahihin tushe abin amincewa ba. Kamar yanda na ambata, ra’ayin farko yana dogara kan wasu riwayoyi(na bayyana yanayin isnadinsu a kasa). Wadannan riwayoyi bisa dabi’a sun dace da bukatar masu neman hutu da gudun tsangwama suna fakewa da su a matsayin yankakken hujja.Lallai kam sun isa hujja ga raunanan zukata masu saukin girgizuwa!
Wadannan riwayoyi sun sifanta Imam da cewa yana mai lallamin Mansur domin kare rayuwarsa duk da cewa yana iya magance yanayin da ya sami kansa ta hanyar hikima. Idan dai haka jagora yake, me zaton ka da mabiyi? Mun yi imani cewa yanayin nassin wanna riwaya ya wadatar wajen tabbatar da cewa kirkirarta aka yi. Ai Imam yana da damar tunkude sharrin Mansur ta wadansu hanyoyin daban kamar yanda amintattun riwayoyi suka nakalto abin da ya faru a wurare mayaiwata. Ashe babu dalilin da zai sa Imam ya koma wa lalama mara tushe ko yabon da ba na gaskiya ba, har ma ya baiwa Mansur halayen da ba shi da su da matsayin da bai cancance shi ba. Babu shakka matsayin imamanci ya daukaka sama da wannan, daukaka mai girma, darajarsa kuwa ta wuce irin wannan kaskanci ya gurbata ta.
Ta bangaren isnadi kuwa, idan aka zurfafa bin diddigin masu ruwaya abubuwa da yawa za su baiyana a gare mu. Isnadin wasu daga cikinsu yana karewa ne kan Rabi’u Alhajib sarkin kofa.Sarkin kofan Mansur! Wannan kuwa akwai adali! Littattafai sun nuna cewa Rabi’u ya fi kowa kusanci da Mansur, ya fi kowa fada. Mansur ya yi masa waziri a shekara ta dari da hamsin da uku hijiraya watau shekaru biyar bayan wafatin Imam Sadik. Hakika Rab’u ya sami daukaka a matsayin ladan karairayin da ya kirkira ya kuma danganta su ga Imam.
Irin wannan mutum wanda kusancinsa da alkawarinsa ga halifa ya tabbata ba abin mamaki ba ne ya kirkiri karairayi ya kuma jingina wa Imam Sadik lalama ko ya sake kalami mai zafi da Imam ya yi furuci da shi, ya mai da shi na kankan da kai da lallami. Wannan ba bakon abu ba ne wajen irin wannan bafaje, amma abin al’ajabin shi ne yanda mai hankali zai gaskata abokin sirrin halifa a kan abin da ya shafi abokan gabarsa, har ma a ce wai shi ma shi’a ne. Wannan kaulin shi ma wani yanki ne daga kule-kullen da kaskanci ne musabbabinsu.
Shi ma ra’ayi na biyun fonko ne kwatankwacin na farkon, kuma bai kafu bisa ilmi ba. Ra’ayin yana kama da irin hukuncin da mustashrikai suke yi wanda ya samo asali daga jahilci da kulli, da kuma ruhi irin na tsagwarar maddiyya wacce ba ta tafiya daidai da dabi’ar abin da yake gudana a musulunci. Mun ga irin wancan hukunci na rasar kunya da bashi da kanshin gaskiya wanda sashen mustashrikai suke yanke wa musulunci da Imaman Ahlulbaiti (a.s). Ga abin da daya daga cikin su [4] ya fada kan Imam Hassan Mujtaba: cewa ya sai da halifanci ya karbi kudi! Ya gama rayuwarsa tare da turare da mata da walwala. Wani [5] kuma ya ce: Musulunci ya cirato al’umma daga matakin bauta zuwa na tsarin akda’(watau tsarinda talakawa basa mallakar filayen noma sai dai su yi aiki a filayen masu iko kana su raba amfanin)! Mahanga ta biyun tana tarayya da zantuttukan wadannan mustashrikai wajen biri-boko da garaje da kuma madogara ta maddiyya. Abin sha’awa a nan shi ne hujjojin da ma’abota ra‘ayi na biyu, watau ra’ayin ‘yan gurguzu, suka dogara da su ba komai ba ne face hukunce-hukuncen da ma’abota ra’ayin farko suka kirkiro!

Sahihin Dubi: Na Uku
Bari mu fara bayanin mahanga ta uku kan lamarin Imam Sadik, ra’ayi da ko wani kaifin basira yana iya tsinkayar shi idan ya koma ga littafan riwaya. Wannan hukuncin ba ya takaita da rayuwar Imam Sadik kadai, a’a yana game dukkan Imaman Ahlulbaiti, bambancin kawai shi ne abin da aikin kowannensu ya kebanta da shi gwargwadon abin da yanayin zamani da wuri ya hukunta. Wannan sabawar kebantattun sifofin aikin ba ta cin karo da haduwar ruhin aiki da hakikaninsa ko kuma haduwar manufa da hanya.
Idan muna son fahimtar yanayin rayuwar Imamai ya wajaba da farko mu fahimci falsafar Imamanci. Tafiyar da aka san ta a mazhabar Ahlulbaiti da sunan Imamanci, wacce ginshikanta mutum goma sha biyu ne daya na bin daya kuma ta dauki kusan tsawon karni biyu da rabi, bisa hakika ci gaban aikin annabci ne. Shi annabi, Allah (s.w.t) yana aiko shi ne da wata sabuwar manhajar rayuwa, da sabuwar akida da wani sabon shirin alakokin dan Adam da kuma sako wanda aka dora masa, gwargwadon shekarun da aka ba shi a wannan takaitacciyar rayuwa.
Wajibi ne kira ta ci gaba a bayan Annabi domin sakon ya cimma mafi daukakan matsayin da ake bukata wajen tabbatar da manufofinsa. Kazalika dole ne mutumin da ya fi kusaci da ma’abocin sakon ta dukkanin fuskoki ya dauki nauye-nauyen ci gaba da kira, domin sakon ya kai amintaccen matsayi, ya sami turke mai karfi, tabbatacce mara yankewa. Wannan aiki, babu shakka yana bukatar amintattun mutane. Wadannan sune Imamai, wasiyyan Annabi. Kuma dukkanin Imamai madaukaka kuma ma’abota sako suna da wasiyyai da halifofi. Ba za mu san nauyin al’amarin Imamai ba sai mun san na Annanbi, wanda Alkur,ani mai girma ya bayyana da cewa: “Hakika, lalle, mun aiko manzanninmu da hujjoji bayyanannu, kuma muka saukar da littafi da sikeli tare da su domin mutane su tsayu da adalci……..” [6] Wannan daya daga cikin ayoyi masu baiyana dalilin aiko annabawa da kuma nauyin da aka dora masu ne. An aiko su ne saboda gina wata sabuwar al’umma da tuge ginshikan fasadi da sanarwa kan aiwatar da sauyi ga jahiliyyar zamaninsu da kuma sake wa al’ummarsa fasali. Wannan shiri na kawo sauyi Imam Ali (a.s) ya bayyana shi a farkon karbar ragamar shugabancinsa da cewa :-. “ …..har sai na kasanku sun zamo su ne a sama na samanku kuwa sun zamo su ne a kasa….”[7] Wannan aiki ne na gina al’umma bisa asasin tauhidi da adalcin zamamtakewa da martaba dan Adam da yanta shi da tabbatar da daidaiton hakkoki da dokoki a tsakanin jama’u da dai-daiku da yarfar da kangi da zalunci da boye kayan masarufi; da bude kofa ga karfi da kokarin dan Adam; da kwadaitarwa kan neman ilmi, da ba da shi, da kwadaitarwa kan tunani da sauransu. Shi aiki ne na kafa wata jama’a wacce a cikinta, ake habaka ilahirin hanyoyin daukakar dan Adam ta dukkanin muhimman fuskoki da kuma zaburar da shi don ya fuskanci tafiyan nan ta neman kamala a tsawon tarihinsa.
Saboda wannan nauyin ne Allah ya aiko annabawa.A matsayin Imamanci na ci gaba da daukar nauye-nauyen annabci, muna iya cewa yana daukar wadancan aiyuka. Da a ce Manzon Allah (s.a.w.a) ya rayu shekara 250 da wadanne ayyuka zai gabatar? Yanda ya aikata wajen kira haka nan Imamai suka aikata. Manufar Imamanci ita ce ta annabci hanyar daya ce watau samar da al’umma ta musulunci adila da kokarin kare ingantaccer tafarkin musulunci. Sai dai abin da zamani yake hukuntawa yana bambanta, kuma gwargwadon wannan bambancin dabaru da solon aiki na sabawa. Annabi (s.a.w.a)da kansa ya yi aiki da wani salo a farkon kira wajen tabbatar da manufofinsa bayan an kai wani zango kuma ya yi amfani da wani salon dabam.
Yayin da kirar take farkonta, tana kewaye da barazana da kalubale tana bukatar wani shiri na musamman domin gudanar da aikin ida sako. Yayin da kuma ginshikan tsarin musulunci suka kafu, musulunci ya sami kafuwa a Tsibirin Larabawa sai dabaru da salo suka sake.Tabbataccen al’amari na dindindin shi ne madaukakiyar manufar da sakon ya sauko saboda ita. Shi ne kuma kokarin samar da al’ummar da a cikinta dan Adam yake iya tafiyarsa ta bidan kamala ta dukkanin fuskoki, a ciki ne kuma kwazo da karfin da ke boye cikin halittar dan Adam za su bubbugo. A nan fa kariyar wannan al’umma da tsarinta na musulunci suke.
Imaman shi’a, kamar yanda Annabi ya yi, suna faskantar ainihin wannan manufar ne watau kafa adalin tsari na musulunci mai wadannan sifofi kuma bisa wannan tafarki. A dai dai lokacin da ake kafa wannan tsarin ana kuma ba da karfi wajen kariya da tabbatar da dogewarsa.
Me kafa tsarin zaman jama’a da ci gaban gudanarsa yake bukata?. Da farko yana bukatar wata manufa ko akida (aidiyolojiyya) mai shiryarwa wacce daga gare ta ne wancan tsarin yake bubbugowa kuma ita take zayyana shi. Na biyu yana bukatar karfin zartarwa mai iya kutsawa cikin wahalhalu da matsaloli da kangiya domin tabbatar da manufar tsarin. Mun san cewa aidiyolojiyyar (ko kuma akida) Imamai ita ce musulunci. Shi kuwa musulunci sako ne madawwami ga dan Adam, watau sakon da ke tattare da sinadarin wanzuwa da tabbatarsa.[8]
Idan muka lura da wadannan mas’aloli, cikin sauki za mu iya fahimtar manhajar Imamai na Ahlulbaiti kuma wasiyyan Annabin rahama (s.a.w.a). Wannan manhajar tana da sassa biyu malizimta juna: na farkon yana dangantaka da akida, na biyun kuma yana da alaka da samar da karfin zartarwa da zamantakewa. A sashen farko, Imaman suna fuskantarda kokarinsu da himomminsu ne wajen yada manufofin sako da kafa su, da tono duk wani kaucewa gaskiya da karkata wadanda masu bin son rai suke sabbabawa; da bayyana ra’ayin musulunci kan sababbin mas’aloli da raya alamomi wadanda suka rushe, sakamakon karo da amfanin ma’abota iko da masu fada a ji; da faiyace abin da ya boyu wa hankula na daga littafin Allah mai girma da sunnar Ma’aiki. Ana iya takaita zance kan nauyin sashen farko da cewa kare rayayyen sakon musulunci ne mai ginuwa, tsawon zamani.
A sashen na biyu kuwa gwargwadon abin da yanayin siyasa da zamantakewar al’ummar musulunci suke hukuntawa, suna kokarin samar da shimfida da ake bukata wajen karbar ragamar shugabancin al’umma da kansu a kusa, ko kuma shimfida domin imamin da zai ci gaba da tafiyar tasu a nan gaba ya kuma karbi shugabanci bayan zango mai tsawo.
Wannan a takaice shi ne manufar rayuwar tsarkakan Imamai, kuma wadannan su ne tsarin manufofinsu a game, saboda su suka rayu kuma dominsu suka yi shahada. Idan tarihin rayuwar Imamai wanda ya zo mana ba ya tabbatar da ra’ayin da muka tafi a kai, to akidarmu kan Imamai ta isa ta sauwara mana rayuwarsu ta wannan fuskar kadai. Mene ne zatonka idan tarihi yana ba da shaida da take gamsar da ko wane mai bincike cewa rayuwar Imaman Ahlulbaiti tana kan wannan mafuskantar?.

Zango-zango na Tafiyar Imamanci
Tafiyar Imamanci ta fara ranar da Manzon Allah (s.a.w.a) ya bar duniya cikin watan Safar, shekara ta goma sha daya bayan hijira har zuwa wafatin Imam Hassan Askari (a.s) a watan Rabi’ul Awwal, shekara ta dari biyu da sittin bayan hijira. Cikin wadannan shekaru, tafiyar Imamaci ta ci zango hudu, wanda a kowanne Imamai sun dauki matsayi fitacce gaba ga mahukuntan al’ummar musulmi.

Zango na Farko
Wannan ya kunshi matakin kame baki ko mu ce matakin taimakawa mahukunta. A wannan zango jinjirar al’ummar musulunci ta yi fama da hadarin magabta wanda ya yi mata kawanya. Yayin da wadannan magabta suka ji barazanar da sakon musulunci yake masu, sai suka dana tarkon su daga wajen daular musulunci suna dakon wata dama domin su aukawa wannan sabuwar al’umma. A wani janibin kuwa akwai adadi mai yawa na sabon-shiga musulunci wadanda hankalinsu ba zai iya daukar halin rarraba cikin al’ummar musulunci ba, saboda haka duk wata tsagar da ka iya faruwa za ta zama barazana ga tushen al’ummar da ma samuwarta. Na uku, karkatar da ta sami al’umma ba ta yi tsananin da har mutum kamar Amirul Muminina Aliyu ibn Abi Talib(a.s) wanda ya fi kowa kaunar kubutar sakon musulunci da al’ummarsa, ba zai iya jure mata ba. La’alla wanna halin da ya sami jama’ar musulmi shi ne abin da Manzon tsira Muhammadu (s.a.w.a) ya yi ishara da shi lokacin da ya yi wasici ga wannan dalibinsa wanda yake farda, da ya yi juriya idan ya auku.
Wannan zangon ya dauki tsawon rayuwar Imam Ali (a.s) fara daga wafatin Manzon Allah ( s.a.w.a) har zuwa karbarsa halifanci. Imam ya yi sharhin matsayin da ya dauka cikin takardar da ya rubuta wa mutanen kasar Masar yayin da ya nada masu Malik Ashtar hakimi. Ya ce:- “Sai na kame hannuna yayin da na ga masu juyawa sun juyawa musulunci baya, suna kira zuwa shafe addinin Muhamamdu (s.a.w.a). Sai na ji tsoron idan ban taimaka wa musulunci da ahlinsa ba, zan ga tsagewa da rugujewa tattare da shi. Da haka zai faru, to da musibar da za ta sami musulunci ta fi tsanani a gare ni bisa ga kubucewar shugabancin ku.……sai na bayar da gudumowata a abubuwan da suka faru”(1)
Yayin da shugabanci ya kauce masa sai ya hakura domin musulunci, lokacin da al’umma ta fuskanci hadura masu girma sai ya mike domin kare musulunci da al’ummarsa, yana mai shiryarwa da aiki a fagagen siyasa da soji da zamantakewa. Cikin Nahjul Balaga da sirar Imam Ali, akwai bayanai masu tabbatar da irin nau’in kokarinsa a zamanin shugabancinsa.