GUDUMMUWAR MACE WAJAN GINA AL'UMMA
 

Wallafar: Mu'assasar Al-balag
Fassarar: Yakubu Ningi

Gabatarwa
"Muminai maza da Muminai mata kuwa masoya juna ne; suna horo da aikata alheri suna kuma hani da mummunan aiki.."Surar Taubati, 9:71.
"Ya ku mutane, hakika Mu Muka halicce ku daga namiji da mace, muka kuma sanya ku al'ummu da kabilu (dabam-dabam) don ku san juna, hakika mafi girmanku a wurin Allah shi ne wanda ya fi ku tsoron Allah..."Surar Hujarati, 49:13.
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai.Tsira da aminci su tabbata ga shugabanmu Muhammadu da tsarkaka daga lyalansa da zababbu daga Sahabbansa.
Zamantakewar dan Adam ba ta taba zama a wata rana cikin wadatuwa daga mace ba, alhali kuwa ita ke matsayin rabin samuwarsa ko ma fiye da haka. Duk wanda ya nutsa cikin zurfin tarihin dan Adam, zai ga cewa, hatta a lokutan da suka fi koyaushe ci baya, mace na da wata babbar gudummawa, duk kuwa da cewa wannan gudummawa ta faku daga gannai.
Idan har wayewar zamani ta fuskanci yin ta'akidi a kan gudummawar mace (a rayuwa) da ta da yekuwar kiyaye hakkokinta, duk da cewa na bayyane ne kawai, to Musulunci tun farkon bayyanarsa, ya yi kira kan cewa mace ta taka rawarta a rayuwa, kuma ta dauki nauyin da ya hau kanta wajen ginin wayewar bil-Adama. Allah Madaukaki Ya ce:
"Sai Ubangijinsu Ya amsa musu (cewa): `Hakika Ni ba zan tozarta aikin wani mai aiki ba daga cikinsu, namiji ne ko mace', sashinku daga sashi yake..." Surar AIi-Imrana, 3:165. Idan har mace a lokacin jahiliyya ta kasance wani kashi da aka yi watsi da shi wanda kuma ya fada karkashin tsiraici da kaskancin matsayi, to a cikin zamantakewar Musulunci ta dawo ta zama mutum wadda ke da abin koyi ga sauran muminai. Tarihin Musulunci ya shaida wasu lokuta masu muhimmanci na wasu fitattun mata, kamar Uwar Muminai Khadija, da shugabar matan duniya Fadimatu (a.s.).
Wata kila karnonin karshe-karshen nan, saboda jahilcin da ya bayyana cikin wasu garuruwan Musulmi kamar sauran garuruwan duniya, sun shaida wani nau'i na kangiya ga mace daga irin tasirin ta na dabi'a, da hardiya ga tafiyarta na cika; abin da ke sanya tilascin yunkurar wa da tunatar da tunane-tunanen Musulunci da suka ta'allaka da ita, domin kuwa sanya mace a fagen da ya dace da ita cikin rayuwa, yana da babbar gudummawa cikin yunkurin al'umma da bunkasarta.
Babu shakka kan cewa wannan gudummawa ya saba da hakikanin yadda mace ke rayuwa a al'ummun da ke bin abin duniya na zahiri, wandanda suka janye wa mace karamarta da mutuncinta, suka so ta zama na'urar tallace-tallace a kafafan watsa labarai, kuma kayan wasa wadda masu kudi ke amfani da ita bisa son zuciyoyinsu; a karshe sai mace ta rasa matancinta, uwartakarta, daukakar tunaninta da taushin ranta, ba ta girbe komai daga hakan ma face ta'addanci, yin watsi da ita a gefe, yanke kauna, wahalhalu da shigar iyali cikin halin kaico da wastewa.
Binciken da ke hannunka, ya kai mai karatu, wata 'yar sassarfa ce a kan gudummawar mace da ayyukanta cikin al'umma bisa tunanin Musulunci. Muna fatan zai sami lura da muhimmanci daga gare ka.
Dukka godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.

Ma'anar Al'umma
AI'umma: na nufin tawagar nan ta mutane da ta hadu daga daidaiku, wadanda alakokina akida da amfanonin rayuwa iyakantattu suka hada su. Idan har wannan ne gamammiyar ma'anar al'umma, to al'ummar Musulmi ita ce wannan al'umma wadda ake gina alakokin kuma ake tsara amfanoni a cikinta bisa asasin Musulunci. Za mu iya ta'arifin al'ummar Musulmi da cewa:
"Taron Jama'ar da a siyasance suke zaune a wani lungu na kasa, wadanda suka yi imani da Musulunci, kuma ake tsayar da alakokinsu da tsarin rayuwarsu a bisa asasin Musulunci".[1]
Don haka al'ummar Musulmi al'umma ce ta akida, wadda ke da abubuwan da suka kebanta da ita da siffofinta da ke bambanta ta da wasunta na daga al'ummu. Ita al'umma ce da ta kebanta da tunane-tunanenta, halayenta, dokokinta, tsarin rayuwarta, dabi'unta da sannanta. Hakika AIkur'ani mai girma ya takaita wadannan siffofi da cewa: "Rinin Allah, ba kuwa wanda ya fi Allah iya rini, kuma mu Shi muke bautawa". Surar Bakara, 2:138.

Mafarin AI'umma
Daga cikin al'amura na asasi da babu makawa a kan karanta su, binciken su da bin diddiginsu a ilmance, akwai mas'alar nan ta tashin al'umma da rayuwar zamantakewa, da sanin dalilai da musababbin shi (tashin); saboda abin da ke cikin na murdewa da haduwa da alakoki.
Don bayyana ra'ayin Musulunci game da tashin al'umma da haduwar rayuwar zamantakewa, bari mu karanta abin da ya zo daga ayoyin AIkur'ani wadanda ke magana game da sha'anin zamantakewa, kuma suke kira zuwa ga ginin al'ummar dan Adam, da rina rayuwar mutum ta hanyar hada gamammen zaman tare bisa asasai karfafa da akidu tabbatattu; ga wasu daga cikin ayoyin kamar haka:
"Ya ku mutane, hakika Mu Muka halicce ku daga namiji da mace, muka kuma sanya ku al'ummu da kabilu (daban-daban) don ku san juna, hakika mafi girmanku a wurin Allah shi ne wanda ya fi ku tsoron Allah..." Surar Hujarati, 49:13. "Akwai daga ayoyinSa Ya halittar muku mata daga kanku, don ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya kauna da tausayi a tsakaninku, lalle cikin wannan akwai ayoyi ga mutanen da ke tunani." Surar Rumu 33:21. "Shin su ne za su raba rahamar Ubangijinka? Mu ne muke raba musu arzikinsu a rayuwar duniya, kuma muka daukaka darajojin sashinsu a kan wani sashi don wani sashin ya riki wani mai yi mishi hidima; rahamar Ubangijinka kuwa, ita ta fi abin da suke tarawa (na duniya)." Surar Zukhrufi, 43:32.
Darasi da bin diddigin wadannan ayoyi zai fitar mana da sabubba da dalilan tashin al'umma, wadannan sabubba kuwa su ne:
1-Tubalin asali na ginin zamantakewa shi ne gamammun dokokin dabi'a na auratayya, wadanda suka hadu daga saduwar jima'i ga mace da namiji; ke nan su ne tubalin asasi na ginin rayayyen zamantakewa ta fuskoki biyu: Abin da zai auku a gaba da halayya.
Wannan alaka wadda ke nufin kariyar nau'i, kuma take tunkudawa zuwa jima'i don nufin jin dadi; ta dukkan bangarorinta biyu na halayya da `yan Adamtaka tana tsayawa ne a bisa asasin kauna, jin kai da samar da natsuwa.
Da wannan AIkur'ani ya dauki mace a matsayin tushen natsuwa ta hanyar tabbacin hankali da na zamantakewa ga namiji da rayuwar zamantakewa baki dayanta; wannan kuwa saboda kosar da rai daga son wani jinsi da jaraba ta jiki daga gare shi, suna haifar da kawar da damuwar rai da na zuciya, da cika irin faragar da rai din ke da shi, da sarrafa karfin bukatar jima'i da halayya don tabbatar da daidaici ga jinsosin biyu da ke tsaye a kan asasin cika ta hanyar gamammiyar dokar auratayya ta halitta.
Daga nan nauyin da ya rataya a wuyan mace wajen gina rayuwar al'umma mikakkiya kuma mai lafiya ta jiki da zamantakewa ke iyakantuwa; saboda ita ce mabubbugar natsuwa, kauna, tausayi da jin kai cikin rayuwar zamantakewa.
2-Sanayya: Abu na biyu da ke sa mutum hada rayuwar zamantakewa, shi ne ka'idar nan ta sanayya tsakanin mutane, abin da ke tsaye a bisa asasin nan na jin son zaman tare wanda masana falsafa ke nunawa da cewa: 'Mutum mai zaman tare ne bisa dabi'a". Jarabce-jarabce na halayya da zamantakewa sun tabbatar da cewa mutum ba ya jin tabbas da kwanciyar hankali, kuma mutuntakarsa ba ta cika sai da zamantakewa da rayuwa tare da wasu. domin shi yana da matsananicyar bukata ta rai kuma mai Zurfi zuwa ga wasu, saboda haka ne ma Allah Ya fad'i cewa: ".-don ku san juna"; kalmar sanin juna na nuni ne ga boyayyen abin da ke tura mutum zuwa zamantakewa da hada al'ummar dan Adam.
3-Musayar amfanoni: Sababi na uku daga sabubban gina al'umma shi ne musayar amfanoni na abin duniya dabam-dabarn. Hakika Allah Ya so daidaikun mutane su sami cika da irin karfi da kwarewarsu ta tunani, jiki da hankali, kuma wannan cika na tabbata ne ta hanyar musayar amfanoni tsakanin daidaiku. Kowane mutum -shi kadai- yana da bukatu da wasu abubuwa da yake nema masu yawa, kuma ba ya iya samar wa kansa da su duka; don haka yana bukatar wasu, su ma suna da bukata da shi, wannan sabani cikin kwarewa wanda daga gare shi ne ake samun sabani cikin nau'o'in abubuwan da ake samarwa da hidimomin da mutum ke iya yi ga wasu, da musayar wadannan abubuwa da amfanoni da hidimomi don biyan bukatu, shi ne wanda AIkur'ani mai girma ya yi maganarsa da cewa:
"..kuma muka daukaka darajojin sashinsu a kan wani sashi don wani sashin ya riki wani mai yi mishi hidima..." Surar Zukhrufi, 43:32.
A bisa wannan asasi ne ayyukan zamantakewa ke faruwa, kuma (haka) ya fassara tubalin faruwar ayyuka a cikin al'umma don rayuwa ta sami cika kamar yadda gabubban jiki ke cika wajen cika ayyukansu.
Haka nan AlKur'ani ke yi mana bayanin abubuwan da ke haifar da al'umma, mutuntaka da abin duniya. Kuma cikin dukkan wadannan tubaloli da asasai, gudummawar mace na bayyana karara tun daga tushe, sawa'un ta bangaren abin duniya ne ko ta halayya ko aiki cikin rayuwar zamantakewa, ita babbar sashi ce ta al'umma. Hakika alkaluman mutanen duniya baki daya na nuna cewa adadin mata a duniyar dan Adam ya wuce adadin maza.
Ta wannan hange na cikan aiki da AIkur'ani ya bayyana a baya, za a iya ginin gudummawar mace kamar yadda ake ginin gudummawar namiji daidai-wa-daida cikin tsaikon manufofi da halayyar Musulunci, mace ba asasi ta biyu ba ce, ba kuma karin halitta ba ce, duk kuwa da cewa jarabce-jarabcen dan Adam sun tabbatar da cewa gudummawar namiji wajen gina ilimi da tattalin arziki ya fi gudummawar mace zurfi da yawa kuwa, amma nata gudummawar wajen hada shika-shikan ruhi don gina iyali ya fi gudummawar namiji girma nesa ba kusa ba kuwa. wannan shi ne abin da AIkur'ani ya nuna da cewarsa:
"..Ya kuma halicci matarsa daga jikinsa don ya sami natsuwa da ita". Surar A'arafi, 7:189. Ke nan namiji shi ne yake natsuwa zuwa ga mata, ya sami tabbaci da rayuwa tare da ita, ita ce cibiyar haduwa kuma tsaikon aminci, kauna da soyayya. AIkur'ani na magana a kan 'natsuwa' a wurare da yawa, ta nan za mu iya fahimtar ma'ana irin wadda mace kan samar ga mijinta, za mu fahimce shi ta hanyar fadarSa Madaukaki:
"Akwai daga ayoyinSa Ya halittar muku mata daga kanku, don ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya kauna da tausayi a tsakaninku.." Surar Rumu 33:21. Da fadarSa: "..Ya kuma halicci matarsa daga jikinsa don ya sami natsuwa da ita". Surar A'arafi, 7:189.
Za mu fahimci kimar kalmar `Natsuwa' a zaman tare ne yayin da muka san cewa AIKur'ani ya siffanta alaka tsakanin miji da mata da cewa alaka ce ta (Natsuwa, kauna da soyayya).Ke nan bari mu karanto kalmar `natsuwa' a wurare da dama cikin AIkur'ani, don mu san ma'anarta a zamantakewa da iyali. Allah Madaukaki ya fadi cewa:"(Allah) Ya sanya muku dare a natse" wato mutane na nastuwa a cikin shi natsuwa na hutawa. Haka nan Allah Ya fadi cewa: "Ka yi salla gare su lalle sallarka natsuwa ce garesu". wato suna natsuwa da addu'arka, kuma hankalinsu na kwanciya da ita. A wani wuri kuma Ya ce: "Shi ne wanda ya saukar da natsuwa a zukatan Muminai"
Ya samar da tabbas da kwanciyar hankali.Malaman harshen larabci sun yi wadataccen sharhi a kan kalmar, tare da bayar da misalai, inda duk suka fassara `Natsuwa' da: Kwanciyar hankali, rashin jin kadaici da duk abin da ka sami tabbas tare da zama da shi kuma ka huta da rayuwa tare da shi.[2]
Da haka za mu iya fahimtar natsuwar da mace ke samarwa ga mijinta da iyalinta, wato shi ne: hutawa, aminci, dauke kadaici, tausayi, albarka da tabbaci, kamar yadda za mu iya fahimtar sirrin zabar wannan kalma mai ma'anoni da yawa, da AIKur'ani ya yi.
Hakika darussa na ilimi sun tabbatar da irin tasiri da yanayin rai da halin mutum ke da shi a kan daukacin harkokinshi cikin rayuwa; saboda a tabbace yake a ilmance cewa ayyukan zamantakewa, alhakin aiki da neman abin duniya, na daga noma, sana'a, hada-hadar siyasa, zamantakewa da hidima ga al'umma kamar ayyukan gudanarwa, aikin injinya, karantarwa, aikin likita, kasuwanci, fannoni da sauran irinsu wadanda kowane daya daga namiji da mace ke yi; duk suna da tasiri kai tsaye daga yanayinsu na halayya. Namijin da ke raye a tsakiyar matsalolin iyali da damuwar zuci da bacin rai, samun shi ga abin duniya kadan ne, haka nan nashadinshi wajen aiki da tunanin kirkiran wani abu cikin ayyukan shi su ma suna tasirantuwa, kuma matsalarsa na karuwa wajen alakarsa tare da abokan aikinsa da wadanda yake da alaka da su.
Da haka dabi'ar alakokin auratayya tsakanin namiji da mace ke taimakawa wajen kyautata matsayin nema da samun, ta hanyar bayyanar tasirinsu na rai da zuciya a kan iyawar mutum da harkokinsa na yau da kullum, da alakarsa da neman abinci da abokan aikinsa.
Ba ma kawai wannan ba, Uwa na taimakawa wajen bunkasa al'umma da gina ta a tunani, abin duniya, da dabi'u ta hanyar tarbiyyantarwa da fuskantar da su; domin yaron da ya tashi nesa daga kunci da damuwar rai da matsalolin iyali, zai tashi mai mikakkiyar mutuntaka, mai kyakkaywar alaka da mu'amala da wasu, haka mai bayar da gudummawa mai kyau ga al'umma. Sabanin yaron da ya tashi cikin yanayin iyali da ke cike da matsaloli da tashe-tashen hankula da mummunar mu'amala ga yaro, irin wannan zai tashi ne birkitaccen mutum, mai adawa cikin dabi'u da alakokinsa; don haka ne ma mafi yawan halayen laifuka da mujirimanci cikin al'ummu na samo asali ne daga mummunar tarbiyya.
Akwai kuma wani fage daga fagagen ginin al'umma da Uwa ke taka rawa a cikin shi kamar yadda uba ke takawa, wannan kuwa shi ne fagen tarbiyya mai kyau. Yaron da ke tashi a bisa son aiki da kiyaye lokaci, ake fuskantar da shi fuskantarwa ta karantarwa mikakkiya ta hanyar iyali, kuma yake ci gaba da karatunshi, kuma yana gina iyawarsa na kirkire-kirkire, zai zama wani da ake amfana da shi ta hanyar abubuwan da yake samarwa na kwarewa da sannai na ilimi. Sabanin malalacin yaron da iyayenshi ba sa kwadayin fuskantar da shi ga aiki da samar da wani abu, domin shi zai zama na'ura ga wasu, kuma irin wadannan na haifar da ci baya mai yawa da ta6ar6arewar samar da abubuwa da daskarewar rayuwar zamantakewa, tattalin arziki da ilimi.
Haka fagagen gini ke kulluwa tsakanin tarbiyya, samarwa da bunkasar tattalin arziki, halayya da zaman lafiyar al'umma, kuma irin gudummawar mace wajen ginin zamantakewa na bayyana a dukkan wadannan fagage.

Tubalin Ginin Al'umma
Alaka tsakanin daidaikun mutane a rayuwar zamantakewa kamar alaka ce tsakanin haruffan (wani) harshe, matukar wadannan haruffa ba su hadu ba kuma an tsara alakokin da ke tsakaninsu ba, gamammen ginin harshen ba zai samu ta yadda zai dauki tunanin mutum ya suranta jiyayyar rayuwar mutum gaba dayanta ba.
Haka ma daidaikun mutane, ba sa daukar siga ta mutuntaka da hada al'umma da ke da samuwarta da tushenta da ya bambanceta daga samuwa da tushen daidaiku sai sun shaje da wasu alakoki, sun tsaru da alakokin da ke tsara harkokinsu da halayensu, wadannan alakoki su muka sammata da Tubalan ginin al'umma, wadannan kuwa su ne:
1-Akida: Alakar akida na daga mafi girman alakokin dan Adam wadanda ke hada daidaikun mutane ta mayar da su abu daya da ke hade kamar jiki daya; kamar yadda hadisin Annabi ya nuna haka da nassinshi: "Za ka ga Muminai cikin tausayin junansu da kaunar junansu da jinkan junansu kamar jiki ne, idan wata gaba daga gare shi ta koka, sai sauran sassan jiki ya dauki zazzabi da hana barci".[3]
Akida na da tasirorinta da abubuwan da take haifarwa na halayya da jiyayya a aikace cikin alakokin mutane baki dayansu, kuma tasirorinta na fadada daga gini zuwa kyautatuwa da kiyaye ginin zamantakewa; don haka za mu sami AIkur'ani mai girma yana bayyana wannan alaka da cewa:
"Muminai maza da Muminai mata kuwa masoya juna ne; suna horo da aikata alheri suna kuma hani da mummunan alkl.." Surar Taubati, 9:71. Wannan aya mai albarka tana tabbatar da akidar kauna tsakanin maza da matan da suka yi imani da Allah Madaukaki da sakonSa, haka nan tana tabbatar da ka'idar tunani da halayya da suka fi kowace ka'idar ginin zamantakewa karfi. Mace na shiga cikin wannan alaka a matsayin wani tubali na asasi, kamar yadda ya zo cikin nassin AIkur'ani, tana shiga cikin da'irar soyayya, kuma tana daukar alhakin gini, sauyi da kawo gyara ga zamantakewa kamar yadda namiji ke daukar na shi daidai wa daida; wannan na bayyana karara cikin nassin AIkur'ani da ambaton shi ya gabata a baya.
Da wannan mace ke samun wannan matsayi na shakalin ginin zamantakewa, take kuma da nauyin da ya hau kanta ta hanyar alakar kauna ga daidaiku da al'umma da dukkan jinsosin biyu namiji da mace.
2-Dokoki da tsare-tsare: Ana ta'arifin doka da cewa ita ce: "Wasu gungun ka'idoji da aka tsara don halayyar daidaiku a cikin al'umma, wadanda kuma hukuma ke tilasta mutane a kan mutuntasu ko da kuwa ta hanyar yin amfani da Rarfi ne a lokacin da haka ya zama dole. "[4]
Don haka dokar zamantakewa ita ce hanyar da ke tsara harkokin al'umma, take kuma hada daid'aikunta, kuma take fuskantar da su da sha'anoninsu, kamar yadda dokokin dabi'a (na halitta) ke tsara motsin rana da wata da sauran irinsu. In ba tare da doka ba ba, za a iya gina surar zamantakewa ko bunkasata ba.
Dokokin Musulunci kuwa, su ne dokokin da aka ciro daga AIKur'ani mai girma da Sunna mai tsarki don tsara al'ummar Musulmi daidai da tunani da manufofin Musulunci, don su suna magance matsaloli a kan asasin ilimi; don haka ne ma (dokokin) suka yi la'akari da dabi'ar rai da jiki ga kowane daya daga namiji da mace. Bayan an gina su a kan kai'doji na ilimi, ana kasa dokokin Musulunci zuwa kashi uku kamar haka:
a-Dokoki da hukunce-hukunce da suka kebanci mace. b-Dokoki da hukunce-hukunce da suka kebanci namiji. c-Dokoki da hukunce-hukunce gamammu da ke hawa kan namiji da mace baki daya, wadannan su ke da fadi a fagagen dokoki da hukunce-hukuncen Musulunci. Wannan nau'i na tsari mai la'akari da jinsi, yana kallafa wa mace, kamar yadda yake kallafa wa namiji, wanda kowannensu ke motsawa a fagage biyu, na farko a fagen da ya ke6anta da jinsinsa kuma da yanayinsa na jiki; na biyu kuma ya hado dukkan al'umma da duk gininshi da haduwarsa.
3-AI'adun Musulunci: AI'ummar Musulmi na da al'adunta wadanda ke matsayin wani tubali na asasi daga tubalan gininta wadanda suka kebanta da ita, wadanda kuma ya wajaba a kwadaitar a kansu a kuma tabbatar da su don kiyaye ka'idojinta.
4-Hidima da musayar amfanoni: Ta bayyana gare mu ta hanyar ayar nan mai girma: "..kuma muka daukaka darajojin sashinsu a kan wani sashi don wani sashin ya riki wani mai yi mishi hidima..." Surar Zukhrufi, 43:32. Cewa bukatar zuwa ga wasu shi ne sababin asasi na shigar mutum cikin taron mutane da hada ginin Zamantakewa; don su shiga aikin musayar amfanoni, kamar yadda rayayyun abubuwa da dabi'a ke musayar amfanoni tsakaninsu a fagensu na dabi'a da ya kebanta da su. Ta haka mutum zai sami biyan bukatarsa, kuma ya taimaka wajen cikar rayuwar dan Adam.
A sakamakon bunkasar bukatun mutum da al'umma, da sabanin daidaikun mutane daga maza da mata wajen kudura da iyawa ta hankali da jiki da rai; da karfin irada, sai kebance aikin kowa ya faru a cikin al'umma a hankali a hankali ta wata fuska, ta wata fuskar kuma tare da zabin mutum ga aikinsa na zamantakewa, wato nau'in aikin da zai yi cikin al'umma, kamar noma ko aikin likita ko kasuwanci ko karantarwa da wasun su, ko wani mai tsare-tsare daga gwamnatin Musulunci, ta fuska ta uku, wato wanda nauyin tsara al'umma da fuskantar da kudurarta ke wuyansa, don biyan bukatun daidaiku da magance matsalolin da ke samo asali daga bukatu daban-daban. Cikin abin da zai zo za mu yi nazari gudummawar mace a wadannan fagage, mu dan yi bayani a kansu ko da kuwa a takaice ne.

Bambance-bambancen Yanayin Halitta Da Ke Tsakanin Namiji Da Mace
Daya daga cikin mas'alolin ilimi da kowa ya mika wuya garesu a tsakanin masana halayyar dan Adam da likitanci, shi ne cewa kowane daya daga namiji da mace na da yanayin halittarsa ta kebanta da shi, da cewa a dabi'ance dole a sakamakon haka ayyukan mace a cikin rayuwar zamantakewa ya saba da na namiji. don haka daidaitar rayuwar zamantakewa na bukatar kowane daya daga namiji da mace ya kiyaye bangare da yake ciki na jinsi, namiji ya kiyaye mazantarsa mace kuma ta kiyaye matancinta.
Hakika AIkur'ani mai girma ya yi bayanin bambanci halitta da ke tsakanin jinsosin nan biyu, abin da ya haifar da bambancin ayyuka, haka nan ya bayyana inda jinsosin biyu suka dace, Allah Madaukakin ya ce:
"Kuma kar ku yi burin abin da Allah Ya fifita wasunku da shi a kan wasu. Maza na da sakamakon abin da suka aikata, haka ma mata suna da sakamakon abin da suka aikata. Kuma ku roki Allah daga falalarSa, hakika Allah Ya kasance Masani ne da dukkan komai". Surar Nisa'i, 4:32.
Haka nan hadisai sun yi ta'akidi a kan cewa mabayyanar kamala cikin mutuntakar kowane daya daga namiji da mace, suna da alaka da irin kebance-kebancen nau'i ga kowane daya daga cikinsu, da kiyayewarsa a kan su da daukakarsa da su, don haka hadisai suka hana kamantuwar mata da maza, kamar yadda suka hana maza ma hakan. Darussan halayyar dan Adam da gwaje-gwajen da aka gndanar A cikin hadisai akwai hani da tsawatarwa masu tsanani a kan irin wannan hali, kai! har ma sun la'anci irin mutane masu wannan hali.
Babban malamin hadisin nan kuma masanin furu'a Hurrul Amili (Allah Ya rahamshe shi) ya kawo hadisai masu yawa karkashin babin `Rashin halaccin kamantuwar mata da maza da maza da mata'.
An ruwaito daga Imam Sadik (a.s.) da Imam Ridha (a.s.) cewa: - "Lalle ni ina kin namiji ya kamantu da mace'. [5]Ma'anar `ki' a nan shi ne haramci da rashin halalci, kamar yadda ya zo a sunan babin. Haka nan an ruwaito daga Imam Sadik (a.s.) daga Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa:
"Manzon Allah (s.a.w.a) ya kasance yana tsawatar da maza kar su kamantu da mata, yana kuma hana mata kamantuwa da maza cikin suturarta".[6]
An karbo daga Ibin Abbas ya ce: 'Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana tsinewa mazan da ke kamantuwa da mata, da matan da ke kamantuwa da maza.[7] Fayyace wadannan bambance-bambance zai haifar da amincewa a ilmance da bambance-bambancen ayyuka a wasu fagage da wajiban da aka kallafawa kowane daya daga namiji da mace. Daga wannan asasi ne bambance-bambance da inda ake tare cikin ayyukan zamantakewa ke iyakantuwa.

Mace Da Wayewar Duniyanci
Karanta tarihin al'ummu da kasashe a tsawon zamunansu, yanafito mana da wahalhalun mace, kuntata mata da takura mata. Babu wani tsari ko akida da ya yaye wa mace mayafin zalunci da kuntatawa in ba ka'idojin Allah da suka hadu da mafi kyawun surarsu a sakon Musulunci madawwami ba.
Kafin mu bayar da bayani game da kimar mace, hakkokinta da matsayinta mai ban sha'awa a Musulunci, yana da kyau mu kawo wasu alkaluman kididdiga wadanda ke magana a kan wahalhalun mace da masifun da ta sha a karkashin wayewar duniyanci na zamani karkashin jagorancin Amirka da kasashen Turai, wadanda ke daga taken 'hakkokin mace'.
Alkaluman kididdiga na ta'akidi a kan cewa, dan Adam din da ya ji jiki a karkashin wannan wayewa, kuma ya zama bawa da na'urar jin dadi shi ne: Mace. Ga wasu daga cikin alkaluman kiddidiga na cewa:
"Wani rahoto da kamfanin dillacin labaran kasar Faransa ya kawo ya bayyana cewa: kashi 70 bisa dari na mutane biliyan 1.3 da ke raye a cikin halin mugun talauci a duniya su ne mata, kuma akwai kimanin mata biliyan 2.3 da ba su iya karatu da rubutu ba a duniya. Haka nan kashi uku bisa hudu na daukacin matan kasashen Norway, Amirka, Holland da Newzaland na fuskantar hare-haren fyade. AAmirka kuwa, cikin kowadanne dakikoRi 8 mace daya na fuskantar mummunar mu'amala; haka cikin kowadanne dakikolti 6 ana sace mace daya"[8]
Rahoton ya kara da cewa: Kimanin mata rabin miliyan daya ke mutuwa a kowace shekara saboda ciki da suka dauka da cutukan shi, kuma kimanin kashi 40 bisa dari na wannan adadi yan mata matasa ne. Kuma albashin mata miliyan 828 da ke aiki a fagagen tattalin arziki ya fcaranta daga albashin maza da abin da ya kai tsakanin kashi 30 zuwa kashi 40 bisa dari, kuma irin dan tagazawar nan na bankuna da ake ba ma'aikata a duniya ba sa samun fiye da kashi 10 bisa dari na wadannan agaje-agaje".[9] Haka nan ya zo cikin wani rahoton cewa:
"A bisa wani bincike da ma'aikatar adalci ta kasar Amirka ta aiwatar, an gano cewa adadin sace mutane ko yunkurin sace mata na faruwa a Amirka har sau 310 a kowace shekara, wannan kuwa ya ninka alkaluman da hukumar 'yan sandan cikin Amirka ta F.B.I. ta bayar."[10]
Kuma kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labaran kasar Faransa daga Washigton ya bayar, a kowace shekara akwai halin yi wa mata fyade har sau rabin miliyan a Amirka; alhali kuwa hukumar 'yan sanda ba ta bayar da sanarwar adadin samuwar sace (mata) ko yunkurin sace su a Amirka ba face dubu 140, kamar yadda alkaluman kididdigar hukumar F.B.I. ya bayyana.
Haka nan ya zo cikin wani rahoto da jaridar kasar Iran mai suna lddila'at ta bayar a adadinta na 20,401 daga kamfanin dillancin labaran Iran da ke birnin Rom na kasar Italiya, cewa: "Matsalar halayyar rashin tausayi na kara matufcar tsananta a tsakanin iyalan Italiyawa, domin halin kashe iyaye a hannun `ya'ya da kashe 'ya`ya a hannun iyaye ya karu fiye da yadda ya kasance a da can. Haka wata jaridar Kasar Italiya, a adadinta na baya-bayan nan, ta dauko wani rahoton Kididdigar shekara-shekara na kungiyar Eruospas cewa: cikin watanni goman farkon na shekara ta 1994, an rubuta halin rashin tausayi har 192 a cikin iyalan Rasar Italiya, wadanda 129 daga wannan adadi suka Kare da kisa. Kamar yadda wannan rahoto ya nuna, irin wannan nau'i narashin tausayi a shekara ta 1993 adadin shi ya kai 112, wanda kusan wannan adadin ya kare da halin kashe-kashe. wani abu, da ya zama dole a nuna shi ne cewa kimanin kashi 40 bisa dari na laifuffukan iyali ya faru ne a arewacin Italiya, kuma kashi 40.8 bisa dari daga cikinsu sun faru ne a kudancin kasar, alhali kashi 16.1 bisa dari ya faru a tsakiyar kasar. Kuma mafi yawan kashe-kashen iyali da aka yi a shekara ta 1994 sun faru ne a lardin Lombardi da ke arewacin Italiya".
Haka nan jaridar 'Jumhuri Islami', a adadinta na 4,485, fitowarta shekara ta 1994, ta bayar da rohoton cewa:'MujallarEpidemiology (ilimin annoba) da ke Karkashin hukumar lafiya ta duniya (WHO), a adadinta na 11, na shekara ta 1993 ta rubuta alkaluman Kididdiga na karshe da ya Kunshi adadin wadanda suka kamu da cutar kan jiki (AIDS) a duniya baki daya, inda aka rarraba alkaluman daidai da yankunan duniya dabam-dabam. Alkaluman na nuna cewa adadin wadanda suka kamu da cutar kan jiki da suka tabbata ga wannan hukuma har zuwa shekara ta 1993, ya kai kimanin 718,893. Kimanin 371,086 na wannan adadi na wadanda suka kamu da cutar Kan jiki sun fito ne daga nahiyar Amirka, yayin da kimanin 247,577 suka fito daga nahiyar Afrika, kimanin 92,482 kuwa sun fito ne daga nahiyar Turai, adadin da ya kai 4,188 sun fito ne daga Australiya, 3,561 kuwa daga nahiyar Asiya. Wan aka bi kasa-Kasa kuwa, Kasar da ta fi kwasan adadi mai yawa ita ce Amirka, wadda ta kwashe adadin wadanda suka kamu da wannan mummunan cuta kimanin 289,320, sai kuma kasar Tanzaniya da ke biye mata da kimanin 38,719, sai Kasar Birazil mai 36,481, sai Kenya da 31,185, sai Uganda mai 34,611, sai kuma Biritaniya mai 26,955, sai Faransa mai 24,226, sai kuma kasar Zaire mai 21,008, sai Spain mai 18,347, sai Italiya mai 16,860, sai Congo (Brazavill) mai 14,655, daga nan sai sauran kasashe su biyo baya. Kamar yadda za a iya lura, ba kawai kasar Amirka namatsayi na daya ba ne ta fuskar adadin wadanda suka kamu da cuta mai karya garkuwa jiki, a'a har ma akwai sabani mai yawan gaske tsakanin ta da Kasashen da ke biye mata. Kuma idan muka dauki wadannan alkaluma na adadin dari, za mu sami wadanda suka kamu da wannan mummunan cuta a kasar Amirka sun kai kashi 40 bisa dari na dukkan wadanda suka kamu da ita a kasashen duniya 150, wannan kuwa duk da cewa adadin mazauna Amirka bai wuce kashi 5 bisa dari na dukkan al'ummar duniya ba'.