Hakkokin Ibadoji
Hakkin Salla: "Kuma hakkin salla shi ne ka san cewa ita halartowa ce zuwa ga Allah madaukaki, kuma kai mai tsayuwa ne a cikinta a gaban ubangiji mai girma da daukaka, to idan ka san haka, sai tsaya matsayin bawa mai kaskanci, wulakantacce; mai kwadayi, mai razana; mai kauna, mai jin tsoro; miskini, mai kaskan da kai. Mai girmamawa ga wanda yake gabansa da nutsuwa da kawaici; Ka fuskanto ta da zuciyarka, ka tsayar da (kiyaye) iyakokinta (dokokinta), da hakkokinta".
Hakkin Hajji: "Kuma hakkin hajji shi ne ka san cewa shi zuwa ne ga ubangijinka, kuma gudu ne daga zunubanka zuwa gareshi, kuma da shi ne za a karbi tubanka, da sauke nauyin wajibi da Allah ya wajabata maka shi a kanka". (Hakkin Hajji bai zo ba cikin ruwayar sama, sai dai ya zo a ruwayar da muke kawowa nan kasa).
Hakkin Azumi: "Kuma hakkin azumi shi ne ka san cewa shi wani hijabi ne da Allah ya sanya shi a kan harshenka, da jinka, da ganinka, da cikinka, da farjinka, domin ya kare ka daga wuta da shi, idan kuwa ka bar azumi, to ka keta suturar (katangar) da Allah ya yi maka".
Hakkin Sadaka: "Kuma hakkin sadaka (zakka) shi ne ka san cewa ita ajiyarka ce gun ubangijinka, kuma ajiyarka ce wacce ba ka bukatar sanya sheda a kanta, idan ka san haka sai ka kasance mafi amintuwa da abin da ka ajiye shi a sirrance fiye da abin da ka bayar da ajiyarsa a fili, kuma ka sani cewa ita tana kare maka bala'o'i da cututtuka daga gareka a duniya, kuma tana kare maka wuta a lahira. Sannan kada ka yi wa wani gori da ita domin taka ce, idan kuwa ka yi gori ga wani da ita, to ba ka amintuwa ka kasance gareta kamar wulakanta kanka ne gareta da abin da ka yi gori da ita kan wani, domin wannan yana nuna cewa ba kanka kake nufi da ita ba, domin da kanka kake nufi da ba ka yi wa wani gori da ita ba".
Hakkin Hadaya: "Amma hakkin hadaya shi ne ka nufi Allah mai girma da daukaka da shi kawai (don Allah), ba ka nufin halittunsa da shi, kuma ba sa son komai da shi sai rahamar Allah da tsiran ranka ranar da zaka gamu da shi".
Hakkin Shugaba: "Amma hakkin jagora shi ne ka san cewa shi jarrabawa ce gareka, kuma shi abin jarraba ne game da kai saboda abin da aka sanya a hannunsa a kanka na iko, kuma kai kada ka jawo wa kanka fushinsa sai ka jefa kanka cikin halaka, sai ka zama wanda ya hada hannu da shi a kan duk abin da ya same ka na cutarwa".
Hakkin Ilimi: "Kuma hakkin mai tarbiyyantar da kai da ilimi shi ne ka girmama shi, ka kuma karrama majalisinsa da kyautata sauraronsa da fuskantowa zuwa gareshi, kuma kada ka daga masa muryarka, kada ka amsa wa wani mutum wani abu da yake amsa masa sai dai ya kasance shi ne wanda yake amsawa, kada ka yi wa wani magana a majalisinsa, kada ka yi gibarsa, kuma ka yi kariya gareshi idan aka ambace shi da mummuna, kuma ka suturta aibinsa ka bayyanar da darajojinsa, kada ka zauna da mikiyinsa, kuma kada ka yi gaba da masoyinsa. Idan ka yi haka, to mala'ikun Allah zasu yi maka sheda cewa ka nufe shi kuma ka san iliminsa saboda Allah madaukaki ne ba don mutane ba".

Hakkokin Al'umma
Hakkin Jama'a: "Amma hakkin jama'ar kasa da kake jagoranta shi ne ka sani cewa sun zama jama'arka ce saboda rauninsu da kuma karfinka, don haka wajibi ne ka yi adalci a cikinsu, ka zama garesu tamkar uba mai tausayi ne, ka yafe musu jahilcinsu, kada ka gaggauta musu da ukuba, kuma ka gode wa Allah a kan abin da ya ba ka na karfi kansu".
Hakkin Ilimin Jama'a: "Amma hakkin jama'arka na ilimi shi ne; Ka san cewa Allah mai girma da daukaka ya sanya ka ne mai daukarsu darasi da abin da ya ba ka na ilimin da ya bude maka shi na taskokinsa, to idan ka kyautata koyar da mutane, ba ka wulakanta su ba, ba ka kyare su ba, sai Allah ya dada maka daga falalarsa, amma idan ka hana mutane iliminka, ka wulakanta su yayin da suka nemi ilimi gunka, to Allah mai girma da daukaka yana da hakkin ya kwace maka ilimi da kwarjininsa, kuma ya zubar da matsayinka daga zukata.

Hakkokin Makusanta
Hakkin Matar Aure: "Amma hakkin mata shi ne ka san cewa Allah madaukaki ya sanya ta mazauni da wurin nutsuwa gareka, sai ka san cewa wannan ni'ima ce da Allah madaukaki ya yi maka ita, sai ka girmama ta, ka tausaya mata, duk da kuwa hakkinka a kanta ya fi wajaba, amma tana da hakki a kanka na ka tausaya mata domin ita ribacewarka ce, kuma ka ciyar da ita, ka tufatar da ita, sannan idan ta yi rashin sani da wauta sai ka yafe mata".
Hakkin Bawa: "Kuma hakkin wanda kake mallaka shi ne ka sani cewa shi halittar ubangijinka ne, kuma dan uwanka na uba da uwa, kuma tsokarka da jininka ne, ba ka mallake shi domin kai ne ka halicce shi ba Allah ba!, kuma ba ka halicci wani abu na daga gabobinsa ba, ba ka fitar masa da wani arziki ba. Sai dai Allah madaukaki ne ya isar maka da wannan sannan ya hore shi gareka, ya sanya shi amana a hannunka, ya ba ka ajiyarsa, domin ya kiyaye maka abin da kake zo masa da shi na alheri. Don haka ka kyautata masa kamar yadda Allah ya kyautata maka, idan kuwa ka ki shi, to sai ka canja wani da shi, amma kada ka azabtar da halittar Allah madaukaki da buwaya, kuma (ka sani) babu karfi sai ga Allah".
Hakkin Mai Bawa: "Amma hakkin mai jagorantarka da mallaka, shi ne ka yi biyayya gareshi kada ka saba masa sai dai cikin abin da ya saba wa Allah mai girma da daukaka, to (ka sani) babu biyayya ga abin halitta cikin sabon mahallicci".
Hakkin Ubangida: (Amma hakkin mai mulki da kai yana kama da na mai mulki da kai a jagoranci, sai dai wannan -jagora- ba ya mallakar abin da wancan -mai bawa- yake mallaka. Don haka haka biyayyarsa ta zama wajibi a kanka a cikin komai karami da babba, sai dai idan wani abu ne da zai fitar da kai daga biyayyar hakkin Allah, wanda zai hana ka biyan hakkinsa (ubangiji), da hakkokin sauran halittu, idan ka gama da hakkinsa (ubangiji) sannan sai ka shagaltu da hakkinsa (ubangida), kuma babu karfi sai da Allah).
Hakkin Uwa: "Ka sani hakkin babarka cewa ta dauki cikinka a inda babu wani mutum mai iya daukar wani, ta ciyar da kai daga cikin zuciyarta da abin da babu wani mutum mai ciyar da irinsa ga wani, ta zama lokacinka da dukkan gabobinta; ba ta damu ba ita ta ji yunwa, ta tufatar da kai ita kuwa ta tsaraita, ta kosar da kai, ta ji kishirwa ta shayar da kai, ta yi tsaraici ta tufatar da kai, ta ji rana ta inuwantar da kai, da rasa bacci saboda kai, ita ce lokacinka zafi da sanyi, don kawai ka zama nata, to kai ba zaka iya gode mata ba sai dai da taimakon Allah da dacewarsa.
Hakkin Uba: "Kuma hakkin babanka ka sani cewa shi ne asalinka, kuma ba don shi ba, da babu kai, kuma duk wani abu da kake gani gareka da yake kayatar da kai, to ka sani babanka ne mafarin wannan ni'imar gareka, sai ka gode wa Allah, ka gode masa gwargwadon wannan. Babu karfi sai da Allah".
Hakkin Da ('ya'ya): "Kuma hakkin danka shi ne ka san cewa shi daga gareka yake kuma abin rabawa zuwa gareka a wannan duniya da alheirnsa da sharrinsa, kuma kai abin tambaya ne kan abin da ka koya masa na kyakkyawan ladabi da shiryarwa ga ubangijinsa mai girma da buwaya, da kuma taimaka masa kan biyayyarsa, sai ka yi aiki cikin umarninsa da aikin wanda ya san za a saka masa da kyautata masa, wanda kuma za a yi wa azaba kan musguna masa".
Hakkin Dan'uwa: "Kuma hakkin dan'uwanka shi ne ka sani cewa shi hannunka ne da daukakarka da karfinka, don haka kada ka rike shi makami a kan sabon Allah, ko tanadi don zalunci ga halittar Allah, kuma kada ka gaza taimakonsa a kan makiyinsa, da yi masa nasiha, to idan ya bi Allah, in ba haka ba to Allah ya kasance shi ne mafi girma gareka fiye da shi, kuma babu karfi sai da Allah".

Hakkokin Mutane
Hakkin Mai 'Yantawa: "Amma hakkin mai 'yantaka mai ni'imata maka shi ne ka sani cewa shi ne ya ciyar da dukiyarsa kanka, ya fitar da kai daga kaskanci bauta da dimuwarsa zuwa ga izzar 'yanci da nutsuwarta, sai ya sake ka daga ribacewar mallaka, ya kwance ka daga kaidin bauta, ya fitar da kai daga gidan sarkar (bauta), ya mallaka maka kanka, ya ba ka damar bautar ubangijinka, kuma ka sani shi ne mafi cancantar mutane da kai a rayuwarka da mutuwarka, kuma taimakonsa wajibi ne a kanka da dukkan abin da yake bukata daga gareka, kuma babu karfi sai da da Allah".
Hakkin 'Yantacce: "Amma hakkin wanda aka 'yanta shi ne ka sani cewa wanda ka yi wa ni'ima, sai ka sani cewa Allah mai girma da daukaka ya sanya 'yancin da ka yi masa wata hanya ce zuwa gareshi, kuma tsari ce gareka daga wuta, kuma ladanka a duniya shi ne gadonsa idan ba shi da wasu dangi magada sakamakon abin da ka ciyar na dukiyarka (a kansa), kuma a lahira kana da aljanna".
Hakkin Mai Yin Alheri: "Amma hakkin wanda ya yi maka alheri shi ne ka gode masa, ka kuma ambace shi da alheri, ka samar masa da maganar (mutane) ta alheri (a kansa), ka tsarkake yi masa addu'a a tsakaninka da Allah, mai girma da buwaya. Idan ka yi haka zai zama ka gode masa a boye da a sarari, sannan idan ka samu dama wata rana kai ma ka rama masa (alherin da ya yi maka).
Hakkin Ladani: "Amma hakkim mai kiran sallah shi ne ka sani cewa shi mai tuna maka ubangijinka mai girma da daukaka ne, kuma mai kiran ka zuwa ga rabautarka, mai taimakonka kan sauke wajibin Allah da yake kanka, sai ka gode masa a kan haka irin godiyar da kake yi wa masu kyautatawa".
Hakkin Limami: "Amma hakkin limaminka a sallarka, shi ne ka sani cewa kai kana dora masa nauyin jakadancin tsakaninka da ubangijinka mai girma da buwaya ne, ya yi magana maimakonka kai ba ka yi magana mai makonsa ba, ya yi maka addu'a kai ba ka yi addu'a gareshi ba, kuma ya isar maka da tsoron tsayuwa gaban Allah mai girma da daukaka. Idan an samu wata tawaya tana kansa ban da kai, idan an samu wata kamala to kai kana tarayya da shi, kuma ba shi da wani fifiko a kanka (cikin alherin da ake samu), sai ya kare maka kanka da kansa, sallarka da sallarsa, to sai ka gode masa a kan hakan".
Hakkin Abokin Zama: "Amma hakkin abokin zamanka sai ka tausasa masa dabi'arka, ka yi masa adalci a yin magana, kada ka tashi daga majalisinka sai da izininsa, amma wanda yake zama gunka shi yana da hakkin ya tashi daga gunka ba tare da izini ba, ka manta da munanansa, ka kiyaye alherinsa, kuma kada ka jiyar da shi komai sai alheri".
Hakkin Makoci: "Amma hakkin makocinka shi ne ka kiyaye shi idan ba ya nan, ka girmama shi idan yana nan, ka taimaka masa idan ana zaluntarsa, kada ka bibiyi sirrinsa, kuma idan ka san wani mummuna nasa sai ka boye masa shi (kada ka yada shi), idan ka san yana karbar nasiharksa sai ka yi masa ita tsakaninka da shi, kada ka rabu da shi gun tsanani, ka yafe masa kurakuransa, ka yafe masa laifinsa, ka zauna da shi zaman mutunci, kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Aboki: "Amma hakkin aboki shi ne ka yi abota shi da fifita (shi) da yin adalci, ka girmama shi kamar yadda yake girmama ka, kada ka bar shi ya riga (ka) gaggawa zuwa ga wani alheri, idan kuwa ya riga (ka yin alheri) to sai ka saka masa, ka so shi kamar yadda yake son ka, ka kare shi daga abin da yake nufinsa na wani sabo, ka kasance rahama gareshi kada ka zama azaba a kansa, kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Abokin Tarayya: "Amma hakkin abokin tarayya (wanda kuka hada hannun cinikayya) shi ne idan ba ya nan sai ka kare shi, idan yana nan sai ka kiyaye shi, kada ka yi wani hukunci sai da nasa hukuncin, kada ka yi aiki da ra'ayinka ba tare da tasa mahangar ba, ka kiyaye masa dukiyarsa, kada ka ha'ince shi cikin abin da yake babba ne ko karami na lamarinsa, ka sani hannun Allah yana tare da hannayen masu tarayyar (hada hannun jari) matukar ba su ha'inci juna ba, kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Dukiya: "Amma hakkin dukiyarka shi ne kada ka dauke ta sai ta hanyar halal dinta, kada ka ciyar da ita sai ta inda ta dace, kuma kada ka zabi kanka da ita a kan wanda ba ya yabonka, to sai ka yi aiki da ita wurin biyayyar ubangijinka, kuma kada ka yi rowa da ita sai ka koma da hasara da nadama tare da jama'ar (tababbu), kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Mai bin Bashi: "Amma hakkin mai bin ka bashi da yake neman ka biya, to idan kana da yalwa sai ka ba shi, kuma idan ka kasance maras yalwa, to sai ka nemi yardar da shi da kyautata magana, ka mayar da shi daga kanka mayarwa mai taushi".
Hakkin Abokin Cudanya: "Amma hakkin Abokin cudanya shi ne kada ka yi masa 'yar rufe, kada ka yi maza zambo, kada ka yi masa yaudara, ka ji tsoron Allah madaukaki da girmama a kan lamarinsa".
Hakkin Mai Kara: "Amma hakkin abokin shari'a wanda ya yi da'awar wani abu a kanka, shi ne idan abin da yake da'awarsa a kanka gaskiya ne to sai ka yarda da shi yana kanka, kada ka zalunce shi, ka biya shi hakkinsa, idan kuwa abin da yake da'awarsa a kanka ya kasance karya ne, to sai ka tausasa masa, kada ka zo da wani abu kan lamarinsa sai tausasawa, kuma kada ka fusata ubangijinka game da lamarinsa, kuma babu karfi sai da Allah.
Hakkin Wanda ake Kara: "Amma hakkin abokin shari'a da ka kai shi kara, (ka sani) idan ka kasance mai gaskiya a kararka to sai ka kyautata maganarsa, kada ka yi musun nasa hakkin, idan kuwa ka kasance mai karya ne a kararka, to sai ka ji tsoron Allah mai girma da daukaka, ka tuba zuwa gareshi, ka janye wannan karar".
Hakkin Mai neman Shawara: "Amma hakkin mai neman shawara shi ne; idan ka san yana da wani ra'ayi (mai kyau ne) sai ka yi masa nuni da shi, amma idan ba ka sani ba, to sai ka shiryar da shi zuwa ga wanda ya sani".
Hakkin Mai bayar da Shawara: "Amma hakkin mai ba ka shawara shi ne kada ka tuhume shi idan ra'ayinsa cikin abin da bai yi muwafaka da kai ba na ra'ayinsa, idan kuwa ya yi muwafaka da kai to sai ka gode wa Allah mai girma da daukaka".
Hakkin Mai neman Nasiha: "Amma hakkim mai neman nasiha shi ne ka ba shi nasihar, kuma ya kasance kai abin da kake nufi shi ne tausayi gareshi da tausasa masa".
Hakkin Mai yin Nasiha: "Amma hakkin mai yin nasiha shi ne ka tausasa masa dabi'arka, ka saurara zuwa gareshi da jinka, to idan ya zo maka da dacewa sai ka gode wa Allah mai girma da daukaka, amma idan bai dace ba, sai ka mantar kada kuma ka tuhume shi, ka sani shi ya yi kuskure ne kawai kuma kada ka rike shi da wannan sai dai idan ya cancanci tuhumar ne, kowane hali dai to kada ka damu da lamarinsa, kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Babba: "Amma hakkin babba shi ne ka girmama shi saboda shekarunsa, da daukaka shi saboda rigon da ya yi maka a musulunci kafin ka zo duniya, da barin jayayya da shi yayin husuma, kuma kada ka riga shi kan hanya, kada ka shiga gabansa, kada ka nuna jahilcinsa, idan kuwa ya yi maka wauta to sai ka jure ka daure, ka girmama shi saboda hakkin musulunci da alfarmarsa".
Hakkin Karami: "Amma hakkin karami shi ne ka tausaya masa cikin koyar da shi, da yin rangwame gareshi, da suturta masa, da tausasa masa, da taimaka masa".
Hakkin Mai Roko: "Amma hakkin mai roko shi ne ka ba shi daidai gwargwadon bukatarsa".
Hakkin Wanda ake Roka: "Amma hakkin wanda ake roka shi ne idan ya bayar to sai ka karba daga gareshi da godiya da sanin kyautatawa, amma idan ya hana sai ka karbi uzurinsa".
Hakkin Mai Farantawa: "Amma hakkin wanda ya faranta maka rai shi ne ka godewa Allah madaukaki sannan sai ka gode masa".
Hakkin Mai Batawa: "Amma hakkin mai munana maka shi ne ka yi masa afuwa, amma idan ka san yin afuwa zai cutar to sai ka nemi taimako (kansa). Allah madaukaki yana cewa: "Kuma duk wanda ya nemi taimako bayan zaluntarsa, to wadannan babu wani laifi a kansau". (Shura: 40)".
Hakkin Al'umma: "Amma hakkin al'ummarka shi ne ka sanya aminci garesu, da tausaya musu, da tausasawa ga mai sabawarsu, da sabo da su, da neman gyaransu, da godiya ga mai kyautatawarsu, da kame cutar da su, da so musu abin da kake so wa kansa, da ki musu abin da kake ki wa kanka. Tsofaffinsu su kasance tamkar baba ne gareka, samarinsu su kasance kamar 'yan'uwa ne gareka, gyatumominsu su kasance kamar uwa ce gareka, kanana su kasance tamkar 'ya'ya".
Hakkin 'Yan Amana: "Amma hakkin 'yan amana (wadanda ba musulmi ba da suke rayuwa tare da musulmi bisa yarjejeniyar rayuwa tare), shi ne ka karba daga garesu abin da Allah ya karba daga garesu (na su yi nasu addinin da rayuwarsu), kada ka zalunce su matukar sun cika wa Allah alkawarinsa (ba su zalunce ka ba suna masu karya yarjejeniya".

Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Saturday, June 04, 2011