Sakon Hakkoki (Risalatul Hukuk)
 

Imam Aliyyu Zainul-abidin (a.s)
Tarjamar: Hafiz Muhammad Sa'id

Kur'ani Mai Daraja:
Kuma sama ya daukaka ta, kuma ya sanya sikeli. Kuma ku daidaita awo da adalci, kada ku rage sikelin. Kuma kasa ya sanya ta domin talikai ne.[1].

Gabatarwar Mafassari
Kamalar dan Adam wani abu ne mai wahalar isa zuwa gareshi domin hanyoyin suna da surkukiya mai wahalar gaske, sai dai akwai ma'aunai da suke nuna cewa mutum yana samun ci gaba. Wadannan ma'aunan suna iya kasancewa na tunani ko na aiki, ta yadda kyawawan halayen mutum su ne suke iya nuna cewa shi salihi ne ko fasidi ba yawan ibadojinsa ba, sau da yawa wani yake bauta amma babu inda take zuwa, imma dai don bai riki imamin zamaninsa ba, ko ya riki masoya Allah makiya, ko halayensa sun munana, don haka a cikin kyawawan halaye ne masu rige zasu yi rige domin kai wa ga kamala.
A cikin littafin alKafi na sheikh Kulaini ya zo daga gareshi daga Usman dan Isa, daga Ishak dan Ammar da waninsu, daga Abu Abdullah Imam Ja'afar Sadik (a.s) ya ce: Kada ku rudu da sallarsu, ko da azuminsu, domin sau da yawa ta yiwu mutum ya riki yin salla da azumi ta yadda da ya bar su sai ya samu jin babu dadi, amma ku jarraba su gun gaskiyar magana, da bayar da amana .
A wata ruwayar Imam Ja'afar Sadik yana cewa ne: Duk wanda harshensa ya gaskata, to aikinsa zai tsarkaka .
Lamarin kiyaye hakkin mutane ya kai ga hatta cikin abin da ya shafi mutum ya hau kansa ya kiyaye hakkin mutane a cikinsa. Lamarin ya kai ga manzon Allah (s.a.w) yana la'anar mai cin guzurinsa (a tafiya) shi kadai ya bar sauran mutane.
Jarabawar da take gaban mutum tana da girma da wahala matuka, kuma kowacce ana son ya kiyaye cikinta don ya kasance mutum mai kamala wurin Allah madaukaki. Muna iya duba wannan ruwaya don muga santsin wannan hanya kamar haka:
Daga littafin Ihtijaj na dabarasi, Mansur Ahmad dan Abi dalib Addabrasi , da sanadinsa zuwa Imam Hasan al'Askari (a.s) daga Imam Ridha (a.s) ya ce: Aliyyu dan Husain (a.s) ya ce:
(Yaudara da nuna Salihanci) Idan kuka ga mutum yanayinsa da basirarsa sun kyautata, yana kaikaice maganarsa, da nuna kaskantar da motsinsa, to ku yi a hankali kada ya rude ku, sau da yawa a kan samu wanda samun duniya da hawa kan haram yake yi masa wahala saboda raunin niyyarsa, da wulakantuwarsa da tsoron zuciyarsa, sai ya nuna addini a matsayin tarkonsa, shi ba ya gushewa yana yaudarar mutane da zahirinsa, idan kuma ya samu damar aikata yin haram sai ya fada masa.
(Dukiya da Mata) Idan kuwa kuka same shi yana kamewa daga haram to (har yanzu dai) ku yi a hankali kada ya rude ku, domin lallai sha'awowin halittu suna sassabawa, sau da yawa wani wanda yake nisantar dukiyar haram komai yawanta, (amma) kuma (da zai samu dama, da) ya dora kansa (ya hau) kan wata mummunar mata mai muni (duk muninta) sai ya aikata haram (na zina) tare da ita.
(Samuwar Hankali) Idan kuwa kuka same shi yana kamewa daga wannan (zina) to (har yanzu dai) ku yi hankali da shi kada ya yaudare ku har sai kun duba hankalinsa, sau da yawa wani ya bar wannan duka amma ba shi da wani hankali mai karfi, sai ya kasance abin da yake batawa da jahilcinsa ya fi abin da yake gyarawa da hankalinsa.
(Son Zuciya) Amma idan kuka sami hankalinsa mai karfi ne, to (har yanzu dai ku yi hattara da shi) ku yi hattara dai kada ya yaudare ku har sai kun ga shin yana tare da son ransa a kan (watsi da) hankalinsa, ko kuma yana tare da hankalinsa ne a kan (watsi da) son ransa.
(Son Shugabanci batacce) Sannan yaya sonsa yake ga shugabanci na barna da nisantarsa gareshi. Hakika a cikin mutane akwai wanda ya rasa duniya da lahira, yana barin duniya don duniya, yana ganin dadin jagorancin barna ya fi dadin dukiyoyi da ni'imar halal da aka halatta, sai ya bar wannan duka don neman jagoranci har sai idan aka gaya masa cewa ka ji tsoron Allah, sai girman kai ya kwashe shi da barna, to wutar jahannama ta wadatar masa, kuma tir da makoma .
Yana mai gangara kawararo gaba gadi, farkon barna tana jansa zuwa ga mafi nisan matukar tabewa, kuma ubangijinsa yana mai barinsa da kansa bayan nemansa ga abin da ba zai iya masa ba a cikin taurin kansa, shi yana mai halatta abin da Allah ya haramta, yana mai haramta abin da Allah ya halatta, ba ruwansa da abin da ya kubuce masa na addininsa idan dai shugabancin da ya tabe saboda shi ya kubuta, wadannan su ne wadanda Allah ya yi fushi da su ya la'ance su kuma ya tanadar musu da azaba mai wulakanci .
(Mutumin kwarai) Sai dai cikakken mutum, madalla da mutumin da yake sanya son ransa kan biyayya ga umarnin Allah madaukaki, kuma karfinsa ya kasance ya bayar da shi cikin yardar Allah, yana ganin kaskanci tare da gaskiya shi ya fi kusanci zuwa ga daukakar har abada a kan daukaka cikin barna.
Kuma ya san cewa mafi karancin abin da zai iya jurewa na cutuwarta (duniya) zai kai shi ga dawwamar ni'ima ne a gidan da ba ya rasuwa ba ya karewa(lahira), kuma mafi yawan abin da yake samun sa na farin cikinta (duniya) idan ya bi son ransa zai kai shi ga azabar da babu yankewa gareshi babu gushewa (a lahira), to wannan mutumin madalla da shi (ya cika) mutum, da shi ne zaku yi riko, kuma ku yi koyi da sunnarsa (aikinsa), kuma ku yi tawassali da shi zuwa ga ubangijinku, domin shi ba a mayar masa da addu'a, kuma ba a hana shi abin da ya nema.
Littafin da yake gabanka mai karatu shi ne Littafin "Sakon Hakkoki" na Imam Aliyyu Zainul-abidin wanda aka san shi da asSajjad, ko "Sayyidus Sajidin". Shi bayani ne mai kima matuka da ya ishi mutun rayuwar duniya gaba daya, wanda da al'umma ta kiyaye shi, da ba a samu sabani tsakanin mutane biyu ba, da duniya ta koma kamar aljanna saboda zaman lafiya, da yalwa da arziki, da kauna da so sun maye gurbin kiyayya da gaba, da sulhu da zaman lafiya sun maye gurbin yaki da kashe-kashe!.
Imam Ali asSajjad shi ne Imami na Hudu cikin jerin wasiyyan annabi (s.a.w) wadanda su ne ruwayoyi suka ambace su da Ahlul-baiti da suka hada sayyida Zahara (s.a) da kuma goma sha biyu tsarkaka da manzon Allah (s.a.w) ya yi umarni da riko da su bayan wafatinsa kamar yadda ya zo a manyan littattafan ruwayoyi na hadisai. Sai dai kauce wa wannan wasiyya ta manzon Allah (s.a.w) ya sanya al'umma fadawa cikin rudani da bambance-bambance har zuwa wannan zamanin.
Allah (s.w.t) yana fada cewa: "Kawai Allah yana son ya tafiyar da daud'a daga gareku ne Ahlul-baiti kuma ya tsarkake ku tsarkakewa" .
Wasiyyar manzon Allah (s.a.w) ga al'ummarsa: "Lallai ni mai bar muku nauyayan (alkawura) biyu ne; Littafin Allah da Ahlin gidana, ba zaku taba bata ba bayana har abada matukar kun yi riko da su" .
Hadisai sun yi nuni da su a littattafai daban-daban, kamar yadda Shehu Usman dan Fodio Allah ya kara masa yarda ya kawo sunansu a cikin Nasihatu Ahluzzaman a yayin da yake kawo salsalar Imam Mahadi (a.s) wanda zai zo a karshen duniya. Da al'umma ta fuskanci koyarwarsu da ba ta samu kanta cikin wannan faganniya da rudani ba, sai dai abin da ya faru ya riga ya wakana.
Domin tubarraki zamu so kawo sunyensu kamar haka: Imam sayyidi Ali (a.s), sai Imam Hasan (a.s), sai Imam Husain (a.s), sai Imam Aliyyu Zainul-abidin (a.s) wanda shiryarwarsa take kunshe cikin wannan littafin, sai Imam Muhammad al'Bakir (a.s), sai Imam Ja'afar asSadik (a.s), sai Imam Musa alKazim (a.s), sai Imam Ali arRidha (a.s), sai Imam Muhammad al'Jawad (a.s), sai Imam Ali al'Hadi (a.s), sai Imam Hasan al'Askari (a.s), sai Imam Muhammad al'Mahadi (a.s).
Da yake ruwayoyi biyu ne, don haka mun kawo su da maimaicin da suka zo da shi a ruwayoyi mabambanta saboda sabanin da yake tsakaninsu, sai dai mun sanya ruwayar da tafi fa'idoji masu yawa, ita kuwa ruwayar da ta fi sanadi mai karfi mun sanya ta a kasa.
Muna rokon Allah ya sanya Imam Khoamain (k.s) cikin ladan wannan rubutun sakamakon yau ta yi daidai da ranar juyayin wafatinsa.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Saturday, June 04, 2011

Imam Aliyyu Zainul-abidin (a.s)

Ali Dan Husain Assajjad (a.s), sunansa da Nasabarsa: Aliyyu dan Husaini dan Ali dan Abi Dalib (a.s). Babarsa; ita ce Shahzinan 'yar Yazdajir dan Shahribar dan Kisra, an ce sunanta Shahri Banu. Alkunyarsa: Abu Muhammad, Abul Hasan, Abul-Husaini, Abul Kasim. Lakabobinsa: Zainul Abidin, Sayyidul-abidin, Assajjad, Zussafanat, Imamul Muminin, Almujtahid, Azzahid, Al'amin, Azzakiyyi. Haihuwarsa: 5 Sha'aban 38 H, a wata ruwaya 15 Jimada Akhir. Matansa: An rawaito cewa ya auri mata bakwai, Ta farko ita ce: Ummu Abdullahi, amma sauran duk Kuyangi ne. 'Ya'yansa: 1-Imam Bakir (a.s) 2-Abdullahi 3-Al-Hasan 4-Al-Husaini 5-Zaid 6-Umar 7-Al-Husainil Asgar 8-Abdurrahman 9-Sulaiman 10-Ali 11-Muhammad Asgar 12-Khadija 13-Fadima 14-Aliyya 15-Ummu Kulsum. Tambarin zobensa: Wama taufiki illa bil-Lahi. Littattafansa: Sahifatus sajjadiyya da Risalatul hukuk. Tsawon rayuwarsa: shekara 57. Tsawon Imamancinsa: Shekara 35. Sarakunan zamaninsa: Mu'awiya da Yazidu dan Mu'awiya, da Mu'awiya dan Yazidu dan Abi Sufyan, da Marwan dan Hakam, da Abdulmalik dan Marwan, da Walid dan Abdulmalik. Tarihin shahadarsa: An yi sabani a kan hakan amma an ce 12 Muharram ko 18 ko 25 ga Muharram, haka nan shekara an ce 94 ko 95 H. Inda ya yi shahada: Madina. Dalilin shahadarsa: Guba da aka ba shi a lokacin halifancin Walid dan Abdulmalik. Kabarinsa: Makabartar Bakiyya Madina.
A cikin tsawon lokacin imamancinsa ya ga rashin imani da kekashewar zuciya mai tsanani daga matsantawar da gwamnatin Umayyawa ta yi masa. Sun saka masa tsaro mai takurawa, kuma sun ajiye masa 'yan leken asiri domin kada ya ci gaba da harkar da'awar Musulunci wacce mahaifinsa Imam Husain (a.s) ya ciyar da ita gaba ta hanyar sadaukar da ransa da ya yi a ranar Karbala. Sai dai cewa gaba dayan abubuwan da suka aiwatar, da riga kafin Umayyawa a game da Imam Ali dan Husain (a.s) bai iya hana shi ci gaba da harkar da'awar musuluncin ba. Ya riga ya dauki wasiyyoyi da kira a matsayin wata hanya ta yada Musulunci da yakar Umayyawa. An tattara da yawa daga cikin addu'o'insa a cikin littafi guda daya aka kira shi da suna "Assahifa Assajjadiyya".
Assahifa Assajjadiyya: Shi littafi ne da ya kunshi addu'o'i guda 54 daga addu'o'in Imam Ali dan Husain (a.s), an tattara shi aka wallafa shi a zamanin Imam Ali dan Husain (a.s), kuma an rubuta shi guda biyu. Imam Muhammad al-Bakir ne ya ajiye guda daya wanda sauran imamai suka gaje shi, daya kuwa shi ne wanda Zaidu dan Aliyyu Zainul-abidin ya ajiye wurinsa, 'ya'yansa suka gaje shi.
Assahifa yana da babban muhimmanci a wurin musulmai, sun kula da shi babbar kulawa, kuma ba zai gushe ba abin kulawa da muhimmanci. Muhimmancinsa yana bayyana a cikin abubuwa masu zuwa:
1. Saboda shi yana kunshe da addu'a ne, addu'a kuwa tana daga cikin mustahabbai mafi muhimmanci na Musulunci.
2. Daukar Littafin a matsayin abin dogaro (da ake komawa gare shi) a cikin ilimomin harshen larabci da adabobinsa.
3. Daukar sa a matsayin abin dogaro (da ake komawa gare shi) a cikin ilimomin Akidar Musulunci.
4. Daukar sa a matsayin madogara (da ake komawa gare shi) a cikin ilimin kyawawan halaye.
5. Daukar sa a matsayin madogara (da ake komawa gare shi) a cikin wasu Ilimomi
Risalatul Hukuk: Shi ne wannan littafin da yake gaban mai karatu, shi dai wani tari ne na bayanai daga koyarwar Imam Ali dan Husain (a.s) da yake kunshe da hakkokin dan Adam daban-daban. Yana kunshe ne da hakkoki guda hamsin na koyarwar Musulunci da Imam Ali Sajjad dan Husain (a.s) ya yi bayani a kai. Ya hada da hakkin Allah (s.w.t), da na mutum a kansa, da iyali, da jama'a, da na daula.

Sanadin Ruwaya
Aliyyu bn Ahmad dan Musa ya karbo daga Muhammad al'Asadi, daga Ja'afar dan Malik alFazari, daga Khairan dan Dahir, daga Ahmad dan Ali dan Sulaiman alJabali, daga babansa, daga Muhammad dan Ali, daga muhamamd dan Fudhail, daga Abi Hamza asSumali ya ce:
Wannan ita ce Risalar Ali dan Husain (a.s) zuwa ga wasu daga sahabbansa:
Ka sani Allah madaukaki yana da hakkoki da suka kewaye ka a cikin duk wani motsi da kake yi, ko wani nutsuwa da kake yi, ko wani hali da kake da shi, ko wani masauki da kake sauka, ko wata gaba da ka juya ta, ko wani abu da ka sarrafa.
Kuma mafi girman hakkin Allah a kanka shi ne wanda ya wajabta maka ga kansa daga hakkinsa wanda shi ne asalin hakkoki, sannan sai kuma abin da ya wajabta maka ga kanka tun daga samanka kanka har zuwa tafin kafarka, a bisa sassabawar gabobinka.
Sai ya sanya wa harshenka wani hakki a kanka, kuma jinka yana da wani hakki a kanka, ganinka yana da wani hakki a kanka, hannunka yana da wani hakki a kanka, kafarka tana da wani hakki a kanka, cikinka yana da wani hakki a kanka, farjinka yana da wani hakki a kanka, to wadannan su ne gabobi bakwai wadanda da su ne ake yin ayyuka.
Sannan sai madaukaki ya sanya wa ayyukan hakkoi a kanka, sai ya sanya wa sallarka tana da hakki a kanka, haka azuminka yana da hakki a kanka, sadakarka tana da hakki a kanka, kyautarka tana da hakki a kanka, kuma ayyukanka suna da hakkoki a kanka.
Sannan sai ya fitar da hakkoki a kanka zuwa ga waninka daga ma'abota hakkoki a kanka, sai ya wajabta su a kanka; hakkoki jagororinka, sannan sai hakkokin al'ummarka, sannan sai hakkokin danginka; wadannan su ne hakkokin da sauran hakkoki suke rassantuwa daga garesu.
To hakkokin jagororinka guda uku ne da ya wajabta su a kanka: hakkin mai jagorantarka da mulki, da hakkin mai jagorantakarka da ilimi, da hakkin mai jagorantakarka da mallaka.
Kuma hakkokin al'ummarka da ya wajbta a kanka guda uku ne: Hakkin al'ummarka da mulki, sai hakkin al'ummarka da ilimi domin jahili nauyin al'umma ne kan malami, sannan sai hakkin al'umma da mallaka kamar hakkin mata da abin da ka mallaka na kuyangi.
Kuma hakkokin dangi da aka wajabta a kanka suna da yawa daidai gwargwadon kusancin dangantaka: Hakkin babarka, sannan sai hakkin babanka, sai hakkin danka, sai hakkin dan'uwanka, sai hakkin nakusa sannan sai mai biye masa a kusanci, sai hakkin wanda ya fi cancanta sai kuma mai biye masa.
Sannan sai hakkin ubangijinka mai ni'imta maka, sai hakkin ubangidanka wanda yake ni'imta maka, sannan sai hakkin masu kyautata maka, sai hakkin mai yi maka kiran salla, sai hakkin limaminka a sallarka, sai hakkin abokin zaman wuri daya, sai hakkin makocinka, sai hakkin abokinka, sai hakkin wanda kuka hada hannu, sai hakkin dukiyarka, sai hakkin wanda kake bin sa bashi, sai hakkin wanda yake bin ka bashi, sai hakkin wanda kuke cudanya da shi, sai hakkin wanda kuke gaba da rigima da ya kai ka kara kotu, sai hakkin wanda kuke gaba da rigima da ka kai shi kara kotu. Sannan sai hakkin wanda ka nemi shawararsa, sai hakkin wanda yake ba ka shawara, sai hakkin wanda ya nemi ka yi masa nasiha, sai hakkin mai yi maka nasiha, sai hakkin wanda ya grime ka, sai hakkin wanda ka girma, sai hakkin mai tambayarka (rokonka), sai hakkin wanda ka tambaya (ka roka), sai hakkin wanda ya munana maka da wata magana ko wani aiki da gangan ne ya yi maka ko ba da gangan ba, sai kuma hakkin jama'arka a kanka, sai hakkin ma'abota zaman amana, sai kuma hakkokin da suke kanka daidai gwargwadon dalilan halaye, da sabuban da suka wakana.
To farin ciki yana ga wanda Allah ya taimaka masa a kan yin abin da ya wajabta masa na hakkokinsa, kuma ya datar da shi ga wannan ya ba shi katari.
Matanin Bayanin Hakkoki
Hakkokin Allah da Sassan Jiki
Hakkin Allah: "Amma hakkin Allah mafi girma, shi ne ka bauta masa, ba ka tarayya da shi da wani abu, idan ka yi haka da tsarkin niyya, to Allah ya daukar maka alkawari a kansa cewa zai isar maka lamarin duniya da lahira".
Hakkin Rai: "Amma hakkin ranka a kanka shi ne ka sanya ta cikin biyayya ga Allah, sai ka ba wa harshenka hakkinsa, ka ba wa jinka hakkinsa, ka ba wa ganinka hakkinsa, ka ba wa hannunka hakkinsa, ka ba wa kafarka hakkinta, ka ba wa cikinka hakkinsa, sai ka ba farjinka hakkinsa, kuma sannan sai ka nemi taimakon Allah (s.w.t) a kan hakan.
Hakkin Harshe: "Kuma hakkin harshe; shi ne ka kare shi daga mummunar magana ta alfahasha, da saba masa alheri, da barin shiga maganar da ba ta da wani amfani, da kyautata wa mutane, da kyautata zance game da su".
Hakkin Ji: "Amma hakkin ji shi ne a tsarkake shi daga giba -yi da wani-, da jin abin da bai halatta a ji ba, da tsarkake shi daga sanya shi hanyar zuwa ga zuciya, sai dai idan wata magana ce mai kima da zata farar da wani alheri a cikin zuciyarka, ko kuma zaka samu wata dabi'a mai daraja da girma da ita, domin shi ji shi ne kofar magana zuwa ga zuciya wanda yake kaiwa ga fahimtar abubuwa daban-daban na alheri da na sharri. Babu kuma karfi sai da Allah".
Hakkin Gani:"Amma kuma hakkin gani shi ne ka rufe shi daga ganin abin da bai halatta ba, ka yi lura da gani da shi ".
Hakkin Kafa: "Amma kuma hakkin kafafuwanka, shi ne kada ka yi tafiya da su inda ba ya halatta gareka, a kansu ne zaka tsaya kan siradi, ka duba domin kada su zamar da kai sai ka halaka cikin wuta".
Hakkin Hannu: "Amma hakkin hannunka shi ne kada ka shimfida ta kan abin da bai halatta gareka ba, sai ka samu azabar Allah a gobe -kiyama- da wannan shimfidawar da ka yi, ka kuma samu zargi daga mutane a gidan yau -duniya-. Sannan kada ka rike ta daga abin da Allah ya wajabta mata, sai dai ka kiyaye ta da rike ta daga mafi yawan abin da bai halatta gareta ba, da shimfida ta zuwa ga mafi yawan abin da bai zama wajibi a kanta ba, sai ta kasance ta yi hankali, ta daukaka a wannan gida -duniya-, sannan lada kyakkyawa ya wajaba gareta daga Allah a gidan gobe -lahira-".
Hakkin Ciki: "Kuma amma hakkin cikinka shi ne kada ka sanya shi salka -jaka- ga haram kadan ne ko mai yawa, (kuma kada ka kara a kan koshi) kuma ka nufi halal da shi, kada ka fitar da shi daga haddin karfafa zuwa haddin wulakanci da zubar da mutunci, domin koshi mai kai ma'abocinsa zuwa ga maye wanda wulakanta kai ne, da jahilci, da kuma zubar da mutunci".
Hakkin Farji: "Amma hakkin farjinka shi ne ka kare shi daga zina, kuma ka kiyaye kada a gan shi".