HAKKOKI A MUSULUNCI
 

Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com

Kur'ani Mai Daraja:
Kuma sama ya daukaka ta, kuma ya sanya sikeli. Kuma ku daidaita awo da adalci, kada ku rage sikelin. Kuma kasa ya sanya ta domin talikai ne.[1].

Gabatarwar Mawallafi
Muna godiya ga Allah da ya ba ni damar rubuta wannnan Littafi game da hakkokin zamantakewar al'umma. Wannan littafin an wallafa shi ne da nufin isar da sakon gyara da sanin ya kamata tsakanin juna a zamantakewa a matsayin al'umma daya, da kuma sanin hakkin Allah (S.W.T) da na mutum a kan dan'uwansa mutum da kokarin ganin kiyaye hakan.
Sanin hakkokin Allah da halittarsa da suke kanmu wani abu ne wanda yake mafi muhimmanci a rayuwarmu, domin da shi ne zamu iya tasra rayuwarmu ta duniya da lahira. Tun asali ma ba komai ne kasancewar al'umma mai kamala da sanin ya kamata ba sai kasancewarta ma'abociyar kiyaye dokoki da hakkokin da yake kanta na mahaliccinta da na sauran halittu da suka hada da mutane da dabbobi da sauran samammu, wannan kuwa a matsayinta na daidaiku ne ko a matsayinta na jama'a.
Mun yi amfani da misalai masu yawa a littafin domin ya zama kusa da cimma abin da muke so na fahimtarsa, don cimma buri na kawo gyara ga al'umma da yanayin da kowa zai iya karantawa ya kuma fahimci sakon da ake son isarwa.
Ina rokon Allah ya bayar da ladan rubuta wannan littafi ga Ahlul Bait (A.S) kuma ya karbi wannan dan kokari namu ya taimake mu a kan hidimar addininsa.
Hafiz Muhammad Sa'id
Rabi'ul Awwl 1424. H.K
Khurdad 1382 H.SH
Mayu 2003. M

Hakkokin Allah Madaukaki A Kanmu[2]
Hakkin Allah (S.W.T) shi ne kadaita shi ba tare da yin shirka da shi ba, kuma da bin umarninsa da nisantar haninsa, da bauta masa ba tare da shirka ba, da yin Salla, da Zakka[3], da Azumi, da hajji, da son abin da yake so, da kin abin da yake ki, da tsayawa kan iyakar da ya gindaya mana. Amma akwai magana kan cewa tun da kadaita Allah ba ya yiwuwa sai da saninsa shin zai yiwu a yi koyi[4] a akida? wato imani da Allah da kadaita shi ya kasance a bisa dogaro da biyayya ga fatawar malami ko kuwa hakan ba ya inganta?
Sanannen abu shi ne bai halatta ba a dogara da fatawa a kan imani da samuwar Allah ko kadaita shi[5], wajibi ne a akida a yi imani da hakan a zuciya tare da gasgatawa da hakan bisa dalili na hankali, wannan kuwa ba ya dogara bisa fatawar malami. Misali a kan haka; da wani malami zai ce da kai: Ka yi sallar Jumma'a da Azahar tare wajibi ne, wato Juma'a ba ta isarwa sai ka hada da Azahar, wannan Malami kuma da shi kake koyi sai ya mutu ko kuma ka gano wani wanda ya fi shi ilimi ya ce: Ai Azahar kawai ta isa ko Jumma'a kawai ta isa yaya zaka yi? Amsa ita ce, sai ka koma wa fatawar Malami na biyu domin nan furu'a ce kuma tana kama da aikin likita ne a Asibiti da kake komawa wanda ya fi kwarewa domin magani ko tiyata.
Amma a Akida da wani malami zai ce da kai: Ai ya gano Allah biyu ne ko sama da hakan yaya zaka yi? Sai ka bi shi? A'a. A nan sai ka ce: Malam nan dai rike Akidarka ko ka kawo wani dalili karbabbe na hankali domin ba a yi wa kowa koyi a kan Akida, haka ma da zai ce: Ya gano shi ya yi ka ba Allah ne ya halicce ka ba.
Hakkokin Allah (S.W.T) a kan 'yan Adam suna da yawa kuma aiki jajir yana kanmu, sai a mike domin a san su a kuma aikata su. Rashin sanin hakkokin Allah ya sanya jahiltarsa, jahiltarsa kuwa daidai take da jahiltar kawuka kamar yadda ya zo a wasu ruwayoyi, don haka ne jahiltarsa ta sanya rashin sanin kawukanmu[6], rashin sanin kawukanmu kuwa ya kai mu ga rashin girmama junanmu. Wannan ne ya sanya ba mai girmama ra'ayin dan'uwansa har a siyasar duniya, duba ka ga yadda aka dauki al'amarin addini kansa cikin jahilci ana jifan juna da kafirci, ana kafirta juna alhalin babu wani dalili na shari'a da zai hana ma'abota mazhabobi mabambanta su yi komai are.
Kuma yana da kyau malamai su kafa wata majalisa da zata hada kowane bangare domin kusanto da ra'ayin juna domin tattaunawa da fahimtar juna don amfanar al'umma gaba daya har ma a koyi yadda ake haura katangun mazhabar juna domin wanda ya ga wata mazhaba a wurinsa ita ta fi sai ya haura ya ketara zuwa gareta. Haka nan ya kamata katangun su zama gajeru daidai yadda za su yi dadin haurawa ga mai son haurawa, kuma wannan shi ne yake iya sanya a san abin da kowa yake a kai da fahimtarsa.
Rashin sanin Allah ya sanya ana iya yi wa mutane fashin tunani wanda ya fi fashin kaya da rayuka muni da hadari, har al'umma ta koma jayayya kan abin da bai kamata ya kai ga sabani ba. Duba ka ga rikici kan NEPU da NPC da na PRP da NPN da sauransu, har ma cikin Addini kamar sabani da rikicin 'yan kabalu da 'yan sadalu wanda har ya kai ga sakin aure, da kuma rikicin shin Annabi ya san gaibi ko bai sani ba? Kuma da zaka tambayi masu rikicin menene ma'anar gaibi da ka samu cewa babu wanda ya sani, amma ana iya kashe juna a kan irin wadannan. Nisantar tunani ingantacce mai kyau ya kai ga yin fada a kan Bushanci da Sadamanci har da kashe juna a lokacin Yakin Gabas Ta Tsakiya Na Biyu.
Haka nan a wannan lokaci a kan canja wa wasu rikice-rikicen riga sukan fito da sababbun riguna kamar ba su ba ne, sai dai babu mai iya gane su sai mai idon basira da Ilimi da tunani, misalinsa a yau shi ne batun 'yan Shi'a da Ahlussunna.
Bambancin fahimta ba matasla ba ne matukar Allah daya, manzo daya, Littafi daya, in dai ba neman fitina ba, kasancewar wannan mabiyin Ahlul Bait (A.S) ne, wancan kuma mabiyin hanafiyya ne ko shafi'iyya ko malikiyya, ko kuma wancan Sufi ne ko Arifi bai kamata ba ya cutar ko ya jawo rigima da fitina. Ba ma tsakanin musulmi ba, har ma tsakaninsu da wasunsu bai kamata ba a samu sabani da rigima!.

Tsarin Allah Madaukaki
Allah ya saukar da tsarinsa mai cike da hikima wanda ya saba da tsari irin na Kwaminisanci da Demokradiyya, Tsari ne wanda aka jahilce shi a duniya wanda da an san hakikaninsa da hatta wanda ba musulmi ba, ba zai nemi wani tsari ba sai shi. Akwai wasu tsarurruka a Duniya amma ko kadan ba a iya kwatanta su da tsarin Musulunci, Kwaminis ya kafu ne bisa Fomular Hegel da Marks ya dauka ya yi amfani da ita, Hegel ya yi amfani da nazarinsa ne a kafa dalili da ilimin tunanin dan Adam, amma su Marks sun yi amfani da ita a nazari na tarihi ne da kuma juyi na al'umma don neman hada fada tsakanin masu jari da ma'aikata da kuma yakar dabi'ar halittar mutu ta ikon mallaka. Tsari ne mai yakar 'yan jari-hujja da abokan hamayya, amma ta hanyar zalunci da yakar dabi'ar halittar dan Adam da kisan kare dangi, tsari ne da bai san akwai Allah ba.
Amma Demokradiyya Ita tana dauke da jari-hujja ne da ya sanya mutum a matasyin Ubangiji da yake da iko sakakke, yana da ikon ya bautar, ya tatse, ya shanye jinin talaka, sannan ya wurgar da kashin, tsari ne mai tsotse talaka har kashinsa ya mayar da shi kamar kwarangwal.
Amma duba Musulunci ka ga ni, koma ka san Allah ka ga tsari da mulki wanda ya shimfida da yadda aka sanya dokoki aka ba wa kowane mutum hakkinsa da ya hada mace, namiji, mai kudi, talaka, mai mulki, da wanda ake mulka, da yaro, da babba. Ba zalunci, ba zalunta, ba take hakkin juna, babu yakar dabi'ar halittar dan Adam, ba bambanci ko fifiko sai da takawa.
Musulunci tsari ne cikakke bai zo da tsari irin na Demokradiyya ba, ya zo ne da AsalatusShura[7], Musulunci tsari ne mazhabi[8], amma Demokradiyya tsari ne Ilmi[9].

Daraja Da Sakamako Gwargwadon Sani Ne
Mu sani kamalar hankali yana cikin sanin Allah ne, kuma Allah yana saka wa mutane da ladan aiki gwargwadon saninsu ne. Duba ka gani mana Annabi Nuhu (A.S) duk da ya dade yana shan wahala an ce tun yana shekara arba'in yake kira ga Allah (S.W.T) kuma ya rayu kusan shekara 2500 amma bai kai darajar Annabi Muhammad ba, ba domin komai ba sai domin cewa annabi Muhammad (S.A.W) ya fi shi sanin Allah (S.W.T), shi kuma Allah yana sakawa daidai gwargwadon saninsa ne ga masu aiki na gari na daga bayinsa.
Wata rana wani Mala'ika ya yi mamakin karancin ladan wani mutum mai yawan bauta ga Allah, sai yake cewa da Ubangiji: Ya Ubangiji yaya wannan bawa yana bauta mai yawa amma ladansa kadan ne? Sai Allah ya ce da shi: Ina sakawa gwargawdon sanina ne amma tafi wajansa ka gani, sai Mala'ika ya tafi wajansa, da safiya ta yi suna maganar ciyawa da take fitowa lokacin damuna ta mutu lokacin rani sai mai bauta ya ce da Mala'ika: Ai da Ubangijinka yana da jaki da ciyawan nan ba ta lalace a banza ba da yana da jaki da mun kiwata shi. Haka nan Mala'ika ya ga karancin hankalin wanann bawan shi ya jawo masa karancin lada: Haka nan abin yake wanda yafi sanin Allah ibadarsa ta rana daya tafi ta jahili na shekaru da yawa.
Ga kissar kamar yadda take a ruwaya: Wata rana wani Mala'ika yana yawo sai ya wuce wani tsibiri da wani mai bauta yake rayuwa a ciki sai ya tambayi Allah ya nuna masa ladan wannan mai bauta, sai Allah ya nuna masa, sai Mala'ika ya karanta ladansa, sai Allah ya ce da shi: Ka zama tare da shi, sai Mala'ika ya zo masa a surar mutum, sai ya tambayi Mala'ika: Wanene kai? Sai Mala'ika ya ce: Ni wani mai bautar Allah ne na ji labarinka ne da ibadarka sai na zo don in kasance tare da kai, sai ya zauna da mai bauta wuni daya, da safiya sai Mala'ika ya ce: Wannan wuri yana da shuke-shuke bai dace da komai ba sai ibada. Sai mai bauta ya ce: Ai wurin yana da aibi. Mala'ika ya ce: Menene aibin? Sai ya ce: Ubangijinmu ba shi da dabbobi, da Ubangijinmu yana da jaki da mun kiwata shi a nan, ga ciyawa nan tana lalacewa a banza. Sai Mala'ika ya ce: Shin Ubangijinka ba shi da jaki ne? Sai ya ce: Ai da yana da jaki da wannan ciyawa ba ta lalace ba! Sai Allah ya yi wa Mala'ika wahayi da cewa ni ina saka masa daidai gwargwadon hankalinsa ne[10].
Ko mutane haka suke yi a ayyukansu domin a bisa dabi'ar dan Adam ilimi shi ne yake bayar da kima da daukaka, kuma sabawa dabi'ar haka tana nufin rushewar dan Adam. Wannan al'amari na saba wa dabi'ar dan Adam shi ne ya sanya rushewar tsarin gurguzu, shi tsari ne da ya shahara da yakar dabi'ar dan Adam musamman a abin da ya shafi mallaka.
Misali; A tattalin arziki, lokacin da su Lenin suka so kafa Gurguzu (Kwaminisanci) da suka ga ba zai yiwu ba sai suka kafa Gurguzu mai sauki (Soshiyalizm): A nazarinsu aiki shi ne yake bayar da kima ko mallaka. Saboda haka a misali mai kaya idan ya kai zinarensa wajan makeri don ya yi masa dan kunne da shi, idan ya kera ba zai ba shi dankunne ba sai ya ba shi kudin zinarinsa, domin aikin kira da ya yi shi ne yake bayar da kima da mallaka. Wannan kuwa al'amari ne da ya saba wa dabi'ar dan Adam, a sakamakon haka ne ba su je ko'ina ba suka rushe. Yanzu ta kai ga cewa hatta Akidun da suka dasa na rashin samuwar mahallicci sun rushe, har a ranar 1 ga Disamba 2002 Gidan Rediyo/Telebijin na IRNA ya shelanta cewa: A yanzu kashi sittin cikin dari na mutanen Rasha sun yarda akwai Allah, al'amarin da su Lenen suke ganin haka a matsayin rashin hankali ne sakamakon maye na banju da Duniyar dan Adam ta sha ta fada cikin dimuwa.
Kwatanta aikin Lebura da Purincipal, haka nan kwatanta aikin Manajan banki da na Masinja, da na Saje da Janar, Me ya sa albashin aikin na sama na rana daya ya fi albashin aikin dayan da tazara mai yawa, wannan ba domin komai ba ne sai bambancin sani da tunani da na sama yake amfani da shi fiye da na kasa. Haka nan ne yake wajan Allah tunani da sani su suke bayar da kima ba kawai aiki ba. Amma kada mu manta cewa sanin da ba a aiki da shi mummunan abu ne maras amfani.

Masu Hana Sanin Allah Da Hakkokinsa
Sannan kuma ba a bari Annabawa (A.S) sun kafa Daular Allah ba, kai hatta da lokacin Manzo (S.A.W) ya sha matsala da munafukai, amma duk da haka annabawa (A.S) sun kafa ci gaban da ba kamarsa a Duniya.
Kasar Farisa ta fi kowace kasa aikata Addinin Musulunci a hukumance da a siyasance, amma su ma ba su kai kashi hamsin cikin dari ba sakamakon yanayi. Ya zo a ruwayoyi cewa; Imam Mahadi (A.S) ne kawai Allah zai ba shi ikon kafa hukuma ta Allah mai aiki da cikakkiyar shari'a[11], shi kuwa zai samu wannan ne saboda Allah zai ba shi damar hukunci da hakikanin yadda abu yake ne ba da zahiri kawai ba[12]. Imam Sadik (A.S) yana cewa: Idan imam Mahadi (A.S) ya shugabanci mutane zai yi hukunci tsakanin mutane da hukuncin Dawud (A.S), ba ya bukatar sheda ko rantsuwa, a kowane hukunci Allah yana yi masa ilhamar hakikanin abin da ya wakana, kuma da dogaro da wannan ilimin nasa ne zai yi hukunci[13].
Sai ga wasu wadanda suke kiran kansu musulmi ba sa son a bi Allah a kasashenmu na musulmi, suna kokarin ganin hana sanin Allah ta kowane hali, da kokarin toshe duk wani kokarin fahimtar addininsa da hakkokinsa a kanmu. Sai ga Addini ana wasa da shi kowa ya fiye bangaranci da mazhabanci sai ga rarraba, sai ga jifan juna da kafirci, sai ga
Da mutane sun san Allah hakikanin sani kuma suka bi umarninsa, da sun ci arzikinsa ta sama da ta kasa. Rashin saninsa[14] ya sabbaba rashin sanin yadda za a bauta masa ko a gode masa. Domin su malam tsutsa sun shiga cikin goro sun hana shi sakat, don haka aka kasa aiwatar da abin da Allah ya zo da shi ta hannun Annabawansa. Don haka ne ya bar wasiyyan Annabi su ci gaba da shiryar da mutane bayansa (A.S), amma duka an kashe su ne daya bayan daya[15].
Ba kawai sanin Allah (S.W.T) mahalicci ba har ma furu'a kamar siyasa, da hukunce-hukunce, da zamantakewar dan Adam, da dokoki, da tsarin musulunci duk an jahilci da yawansu a yankunanmu da sauran kasashen musulmi.
Amma nau'in matsalar yammacin Duniya ta bambanta da ta sauran kasashen musulmi ta wani banbare ne, domin su wannan hasken da yake hannunmu da ba a aiki da shi, su ba su da shi, babban misali muna iya duba al'amura kamar a Ilimin zamantakewar dan Adam, su sun sanya mutum ne a matsayin Ubangijin kansa, shi ne mai sanya doka da shar'antawa a bayan kasa amma a Musulunci ba haka ba ne, wannan yana daga abin da ya nesanta su daga sanin Allah.

Hatta Musulmi Sun Jahilci Addini
Kamar yadda yake game da kuskuren da Turai suka yi na mummunar fahimta da kuma jahiltarsu game da musulunci, haka su kansu musulmi suka yi masa mummunar fahimta kuma suka jahilce shi. Babban misali a kasashenmu shi ne: Da zaka ambaci kalmar shari'a sai mutane su yi tunanin irin fille kai, da jefewa, da gutsure hannaye da kafafu.
Misali da zaka tambayi wanda ba musulmi ba a sabanin da makiyan kasarmu na ciki ko na waje suka haifar kan batun shari'a a Arewa me yake nufi da ba shari'a? Zai ce: Ba gutsure hannu da makamantan wannan, haka nan amsar da musulmi zai iya ba ka kenan idan yana maganar shari'a. wato wannan shi kenan shi ne musulunci.
Saboda haka dole ne a tashi don kawar da jahilci da miyagun hannayensa masu guba da suke tafiyar da tunanin mutane game da musulunci har aka kai ga fadawa cikin irin wannan dimuwa. Musulunci yana da fadi ba babi daya ba ne, ya kamata a nemi saninsa daga masanansa na ainihi, ba kowa ne ya san shi ba don ba gado ba ne kuma ba al'ada ba ce.

Ba A Karanta Akidu Da Tarihi
Babbar matsala a cikin al'ummarmu ita ce kauracewa Ilimin sanin Allah da shagaltuwa da furu'a kawai, wannan kuwa ya tauye tunanin mutane game da saninsa (S.W.T). Ash'arawa sukan takaita a kan Littafin Kawa'idi ne da mafi yawa ba sa ma fahimtarsa, wanda ya yi zurfi shi ne wanda ya kai ga Sharhi Ummul Barahin, da kyar zaka sami wanda ya wuce hakan sai daidaiku. Ba a ma san Al'makalat da Al'ibana na Al'ash'ari shi kansa mai Mazhabar Ash'ariyya ba, yawanci ba a san wanda ake bi a Mazhaba ko Akida ba.
Haka sanin Allah ya yi nesa da mutane suka yi nisa da shi, haka ma al'amarin tarihin musulunci da ba a karanta shi wai akwai rigima a ciki da ba a so a sani, wai idan aka yi fada da uwa da uba Shin ka so ka sani?
Sai na ce da mai wannan tunani: Da bambanci, domin na su baba bai shafi makomarka ta Lahira ba, kuma ba ka son sanin waye Manzo (S.A.W) ya bari tsakaninsu wanda bin sa ya zama hujja a kanka. Amma na tarihin musulunci ya shafe ka, domin zai gaya maka makomarka ne, da abin da Manzo (S.A.W) ya bar maka a matsayin tsiranka a duniya da lahira.
Na biyu, ana bukatar ma'aunin waye maganarsa ta fi zama hujja don ka yi aiki da ita, wannan duk ya shafi makomarka ne.
Haka aka haramta wa al'ummarmu sanin Akidu da ilimomi har ka san menene gasakiya ka bi, menene a ganinka ba daidai ba ne ka bari. Duba ka ga ni mana Shehu Dan Fodia (R.A) yana ganin daga cikin bala'in da ya game kasashenmu na Hausa shi ne koyi a Usuluddin amma har zuwa yanzu abin da Shehu ya so a kawar na koyi a Usuluddin ya ci gaba. Koda yake wasu malamai sun tafi a kan cewa; wanda ya fadaka, ya yarda har a zuciyarsa, ya yi imani da samuwar Allah da kadaita shi a bisa sahihiyar Akidar musulunci, duk da tun yana yaro ya yi koyi da malamai ne ko iyaye, amma irin wannan imanin yana isarwa gare shi.

Hakkin Da Yake Kan Annabawan Allah
Annabawa (A.S) sun zo ne domin motsa hankali[16] ya yi tunani ya yi imani a Akidar samuwar Allah da kadaita shi a ibada da zatinsa da siffofinsa da ayyukansa, da kuma yarda da annabawan da ya aiko da riko da sakonnin da suka zo da su. Annabawa ba su ce a bi su ido rufe ba dalili ba, wannan al'amari ne ya sanya Allah yake ba su mu'ujiza da take dalili ce na hankali a kan cewa sakon da suke dauke da shi daga gareshi ne, wannan kuwa zai samar da nutsuwa a zukata har su karbi sakonsa.
Amma hukuncin furu'a (hukunce-hukunce) su an sanya su bisa biyayya da maslaha ne wacce ba kasafai aka santa ba sai dai a bi umarnin Allah a ciki, don haka ne Allah yake sanya wa kowane Annabi (A.S) wasiyyi da zai yi wa mutane bayanin abin da sakon ya kunsa bayan wafatinsa, kamar yadda annabin rahama (S.A.W) ya yi wasiyya ga wannan al'umma da imam Ali (A.S) da goma sha daya daga 'ya'yansa a bayansa.
Matsalolin da wasiyyan Annabi suka fuskanta na kawar da su daga fagen jagorancin al'umma a hukumanci da kisa sun sanya Allah (S.W.T) ya boye na karshensu imam Mahadi (A.S) domin kada a kashe shi domin ya zo a karshen duniya ya cika ta da adalci bayan an cika ta da zalunci. Shi kuma imam Mahadi (A.S) kafin ya boyu ya yi wasiyya da riko da malamai na gari. Saboda haka duk wanda ya kai matakin Ijtihadi wato ya daukaka kan sauran mutanen duniya gaba daya a ilimi, da takawa, da adalci, da kamala, da tsentseni kuma ya kasance dan halal ne, to ya zama dole ne a bi shi[17].