BOYAYYAR TASKA
 

Hafiz Muhammad Sa’id
hfazah@yahoo.com

Ahlul Baiti a Kur’ani:
"Kuma muka yayyanka su sibdi (jikoki) goma sha biyu, al’ummu…".[1].

Gabatarwar Mawallafi
A wannan littafi muna so mu yi nuni da wasu matakai da marhaloli da wahalhalu da Wasiyyan Annabawa (A.S) suka shiga tun daga wancan lokaci har zuwa irin wannan zamani namu, da matakan da mutane sukan dauka a kan abin da yakan faru a kowane lokaci na rarraba da daukar bangare daban-daban, al’amarin da yakan raba al’ummu gida biyu a Tarihin al’ummu da suka gabata.
Da yake mutane a kowane zamani hali daya ne da su al’ummar karshe ta Manzon Allah (S.A.W) ba ta fita daga irin wannan ba, shi ya sa aka samu sabani da ya kai su ga rarraba zuwa mazhabobi da sabanin akidu. Amma wani abin da za a gode wa Allah shi ne; al’ummar nan ta bambanta da sauran al’ummu, domin su wadancan al’ummu bayan sun yi nesa da Wasiyyan Annabawan sukan kuma yi rashin sa’ar canza Addinin nasu gaba daya kuma a kautar da Akidunsu daga sahihancinta[2], amma wannan al’umma Allah (S.W.T) da ludufinsa ya yi alkawarin kare littafinta, da ba ya karbar canji har kiyama ta tashi, wanda Ahlussunna da Shi'a duk sun hadu a kan hakan.
Ambaton wannan littafi da “Boyayyar Taska” ya zo ne domin wasu dalilai kamar haka;
1- Bincike domin gano wace taska ce Annabi Muhammad (S.A.W) ya bari wacce mutum ya nutsu har ga Allah da cewa idan ya mutu a kanta ya kubuta. Amma a gane, duk wanda yake kan wata hanya ko wata Mazhaba ba shi da ikon cewa lallai shi kadai ne a kan gaskiya sauran duka sun tabe wuta zasu, domin bai sani ba tayiwu nasu ya fi nasa gamdakatar. Domin haka ne dole a kiyaye hadin kai tsakanin juna da zamantakewa tare da girmama mazhaba da Ra’ayin juna. Muna fatan kafa wani kwamiti na musamman da zai kunshi majalisa ta malamai da ta kunshi malaman kowane mazhaba domin tabbatar da hadin kan al’umma.
2- Karin haske game da wasu dalilai da mabiya Ahlul Baiti (A.S) suke riko da su daga Kur’ani da Sunna domin samar da karin fahimtar dalilansu game da riko da tafarkinsu, duk da ya kasance a takaice ne kwarai da gaske amma an ce: “Da babu gwara kadan”.
Kammala wannan littafin ya zo daidai da ranar haihuwar Sibdul Akbar Imam Hasan Dan Ali Dan Abi Dalib (A.S) 15 Ramadan watan azumi 1424 Hijira kamariyya, daidai 19 Aban 1382 Hijira Shamsiyya. Wanda ya yi daidai da 10 Nuwamba 2003 Miladiyya, Ranar litinin a kidayar nan kasar Farisa. Don haka ne nake fatan Allah (S.W.T) ya karbi wannan aikin, ya sanya yardarsa a ciki, ya sanya mu cikin wadanda ake gafartawa zunubai a wannan wata mai albarka, kuma ya mika ladan ga Imam Hasan (A.S).
Hafiz Muhammad Kano Nigeria
hfazah@yahoo.com


Wasiyyan Annabawa
Dabi’ar Mutum: Wani abin mamaki, al’ummu[3] da dama sun gabata, amma a kullum abin da yake faruwa a cikin al’ummar da ta gabata idan ta baya ta zo sai ta maimaita irinsa. Wannan wani abu ne da ayoyin Kur’ani mai girma da Hadisai madaukaka suka yi nuni da shi a fadinsa Ubangiji madaukaki yana cewa:
“Shin sun yi (wa juna) wasici da shi ne? Wato shin wadanda suka gabata suna Wasiyya ga masu zuwa ne idan kun zo ku ma ku yi irin abin da muka yi? Wannan al’umma tamu ba ta kubuta daga irin wannan tarko ba domin ta fuskanci irin abin da al’ummar Annabi Musa (A.S) da Isa (A.S) da Annabawan da suka gabace su (A.S) suka fuskanta kuma ta bi sawunsu taku da taku, don haka sai muka ga bari mu kawo Tarihi takaitacce na Ma’asumai kuma Wasiyyan Annabawa da suka gabata kamar yadda ya zo a littattafan Tarihi. Amma bari mu fara da uwa uba Annabi Adam (A.S) wanda yake babanmu kuma daya daga cikin bayi da Allah bai yi kamarsu ba a cikin halittunsa.

Wasiyyan Annabi Adam (A.S)
Tarihi ya tabbatar mana da cewa, Annabi Adam (A.S) yana da wasiyyai guda biyu; daya an kashe shi a lokacin rayuwar Annabi Adam (A.S) wato shi ne Habila (A.S) da kabila la’ananne ya kashe shi, wannan al’amari ya faru ne yayin da Kabila da Habila suka yi kurbani sai Allah ya karbi na Habila wannan karbar ita take nuna takawarsa da fifikonsa a wajan Allah a kan dan’uwansa Kabila, saboda haka ne Kabila ya yi masa hassada. Duk da gaskiya ta bayyana Allah (S.W.T) ya kunyata Kabila ya tabar da aniyarsa kuma ta bayyana a fili cewa ma’abocin daraja shi ne Habila (A.S) amma mugun ciwon nan na hassada da aka saba yi wa bayin Allah ita bai hana shi ya fasa mummunar aniyarsa ta kashe dan’uwansa ba. Saboda haka sai ya kashe shi ya gudu daga babansa ya ci gaba da yada barna da gaba da babansa. Haka nan bayan haihuwar HibatulLahi wasiyyin Annabi Adam (A.S) wato Annabi Shis (A.S) sai batacce Kabila ya dauki aniya sai ya ga bayansa kamar yadda Abu Lahab ya rika yi wa Manzon Allah (S.A.W), ya tara runduna da shi da zuriyarsa suka yaki Hibatullah (A.S) suka kore shi zuwa wani tsuburi daga tsuburan kogunan Duniya da shi da zuriyarsa.
Haka nan sarakuna daga zuriyar Kabila suka ci gaba da mulki har suka kai ga juyar da mutane daga Tauhidi da karkatar da su daga hanyar shiriya, suka kirkiro giya da gumaka har ta kai ana bauta wa irin su Ya’uka, da Yagus, da Nasra, da Suwa’a, da Wudda, da sauran gumaka, al’amarin da ya sanya Ubangiji (S.W.T) ya aika Annabi Nuhu (A.S) zuwa ga sarakunan lokacinsa ya zauna a cikinsu shekara dubu ba hamsin, an yi sarakuna da dama da sukan zo su wuce amma al’umma ba ta yi imani da shi ba har Allah ya halakar da ita da Dufana.
Bayan halakar da mutanen da Dufana da kuma wafatin Annabi Nuhu (A.S) sai Ashararai daga zuriyarsa Hamu da Yafusu da sahabbansa suka yi galaba a kan Wasiyyinsa Samu (A.S) da Shi’arsa suka kafirce wa Allah da Manzonsa Nuhu (A.S), suka kuma dawo da bautar gumaka da sunansu na da Ya’uka, da Yagus, da Nasra, da Suwa’a, da Wudda. Sarauta ta ci gaba a hannun zuriyar Kabila da I’waja har zuwa kan Kan’ana baban Namarzu kafirin sarkin nan a lokacin Annabi Ibrahim (A.S) wanda ya kasance daga zuriyar Hamu Dan Nuhu ne. Amma Samu Dan Nuhu (A.S) ya ci gaba da rike sakon Allah, kuma sakon bai gushe ba daga wasiyyi zuwa wasiyyi mai bi masa har zuwa kan Nakhur kakan Annabi Ibrahim (A.S) zuwa Tarikha babansa, har zuwa kansa (A.S).

Bayan Annabi Ibrahim Da Musa (A.S)
Amma idan ka ji abin da ya faru bayan wafatin Annabi Ibrahim (A.S) sai ka zubar da hawaye, domin annabawa da salihai daga zuriyar Ibrahim (A.S) ba su samu damar yin hukunci ba sai na dan lokaci kankani, ashararan ‘ya’yan Ishaka (A.S) suka samu galaba a kan annabawa da salihai suka karkashe su, suka kuma kora wasunsu zuwa dazuka da tsaunuka haka nan a bin ya ci gaba har zuwan Annabi Musa (A.S). Duba Tarihin Isu Dan Annabi Ishak da galabar da ya samu kan Annabi Ya’akub (A.S) wasiyyin Ishak (A.S), Isu ya ci galaba kan Annabi Ya’akub (A.S) ya kuma kwace tafiyar al’amarin Baitul Mukaddas daga hannun Annabi Ya’akub (A.S), an ce Isu ne farkon wanda ya kirkiro kebance hurumi ga mai mulki kuma farkon wanda ya kirkiro haraji. Amma annabi Ya’akub (A.S) ya ci gaba da hakuri babu iko a hannunsa ya kuma yi wasiyya ga Annabi Yusuf (A.S), mai karatu ba na tsammanin zaka iya mantawa da kissar Annabi Yusuf (A.S) da wahalar da ya sha a hannun munafukan ‘yan’uwansa. Haka nan al’amari ya ci gaba har zuwa kan Annabi Musa (A.S).
Labarin wahalhalun da Annabi Musa (A.S) ya sha a hannun Bani Isra’ila ba boyayye ba ne ga wannan al’umma da aka saukar wa Kur’ani mai girma, shi ma ya kasance yana da Wasiyyai biyu da dayansu shi ne Annabi Haruna (A.S) wanda ya rasu a lokacin rayuwar Annabi Musa (A.S) wanda ya tafi ya bar shi da al’umma cikin kwana arba’in kawai, amma a cikin wadannan kwanaki sai aka yi wa wasiyyin tawaye aka ma dauki Musa Samiri wanda yake munafiki ne a al’ummar Annabi Musa (A.S) kuma Annabi Musa (A.S) ya kore shi daga rundunarsa, amma ya dawo ya yi sihiri ya kuma iya jawo hankulan ‘Ya’yan Isra’ila suka bar Annabi Haruna (A.S) suka bi Musa Samiri, a nan muna iya tambayarka mai karatu? yaya kake gani idan da ya zamanto Musa ya rasu ne fa? kuma yaya al’amarin zai kasance da ba zai dawo ba.
To haka nan kuwa abin ya faru, sai ga shi kafin rasuwarsa ya shelanta wa al’ummarsa wasiyyinsa Yusha’u Dan Nun (A.S) amma bayansa sai al’ummar ta ki bin Wasiyyin ta hada kai da munafukai aka wahalar da shi aka kuma yi masa tawaye. Yahudawa ba su bi Yusha’u Dan Nun (A.S) ba sai ‘yan kadan shi ma a lokacin suna cikin dimuwa ta shekara arba’in ne da Allah ya saukar musu saboda kin biyayya ga Annabin Allah Musa (A.S). A wannan shekarun dimuwar ne Allah ya dauki ran Annabawansa; Annabi Musa (A.S) da wasiyyinsa na farko Annabi Haruna (A.S) zuwa gare shi, amma bayan shekara arba’in dimuwa ta kau sai Annabi Yusha’u (A.S) ya gaya musu sakon Allah na su ta shi su yaki mutane Jabberai. Amma suka yi masa tawaye aka nemi kashe shi, sannan aka hada runduna ta munafukai domin yakar sa, wani abin mamaki shi ne rundanar da ta yake shi ta kasance karkashin jagorancin matar Annabi Musa (A.S) Safura ‘yar Shu’aibu (Amma wasu ma’abota tarihi sun nuna ba ‘yar Annabi Shu’aibun da ya aura a garin Madyana ba ce domin ita sunanta Safra).
Da haka ne fajirai da munafukai suka yi galaba a kan muminai, rigingimu suka ci gaba har ta kai ga kashe Annabi Yusha’u (A.S) da kashe sauran wasiyyan Annabi Musa daya bayan daya. Aka assasa Daular Alkalai (kamar yadda ake kiranta) kabilun Bani Isra’ila suna shugabanci irin na kama ka ba ni bisa zagaye na dangi-dangi, zamani ya ja har zuwa lokacin Annabi Dawud (A.S).

Wasiyyan Dawuda Da Sulaiman (A.S)
Amma bayan wafatin Annabi Sulaiman (A.S) Tarihi ya fadi yadda Sahabbansa da ashararan danginsa suka yi wa wasiyyinsa Asifu Dan Barhaya (A.S) da jama’arsa, suka kawar da shi daga rike shugabancin da Annabi Sulaiman ya bar shi a kai. Da tun farko sun san cewa Annabi Sulaiman ya rasu da ba su bari Asifu (A.S) ya rike mulki ba koda da rana daya, da mulkin bai kai shekara a hannunsa ba. Haka nan aka kawar da shi aka dawo da Rahab’am makiyin Annabi Sulaiman wanda Annabi Sulaiman (A.S) ya kore shi zuwa kasar Misira ya kuma haramta masa dawowa Falasdin, aka dora shi kan mulkin Annabi Sulaiman (A.S) sannan daga baya suka yi ta sabani, aka lalata falsafa[4] da koyarwa ta Annabi Sulaiman aka kirkiro hadisai na karya har ma da na shirka aka jingina ga Annabi Sulaiman (A.S) har Allah ya tsarkake shi a cikin Kur’ani mai girma. Haka nan Daular ta daddare ta rarraba tsakaninsu saboda yawan sabani da son juciya da jahilci, mafi yawancinta ya fada hannun makiyansu, yankin Kudus ya rage a hannunsu, aka dauko daya daga zuriyar Annabi Sulaiman wanda yake ba wasiyyi ba ne nasa aka ba shi gwamnan garin Al-khalil, amma makiyan Annabi Sulaiman da ya kore su a rayuwarsa mulki ya rage a hannunsu ne.

Bayan Masihu Mai Albarka Isa Dan Maryam
Amma bayan Isa (A.S) ya daukaka zuwa ubangijinsa sai ga ukuba mafi tsanani daga al’ummarsa da Rumawa a kan wasiyyansa. Rumawa ba su gushe ba suna korar wasiyyansa musamman Sham’unus Safa da sauran Hawariyawa da muminai da suke tare da su, har lokacin da Bulus ya zo bayan shekara talatin da daukaka Annabi Isa (A.S) ya yi da’awar cewa ya ga Isa (A.S) ya kuma bayyana gare shi a hanyarsa zuwa “Sham” daga sama a garin “Hauran”. Bulus ya kasance mutum ne da yake kashe duk wanda yake bin da’awar Annabi Isa (A.S) kuma bai san komai game da addinin Isa (A.S) ba, ya kasance yana bin su gari gari yana kashewa, amma sai rana daya ya zo ya yi da’awar Isa (A.S) ya bayyana a gare shi yana mai cewa da shi: “Don me ya sa zaka rika gaba da ni haka”.
Sai ya yi nadama kamar yadda Tarihi ya kawo, daga nan kuma sai ya zama shi ne mai fada a ji a Addinin, ya kori Hawariyawa da Wasiyyai (A.S) aka kashe na kashewa aka kore na kore wa zuwa dazuka da tsaunuka, sannan kuma yawancin Akidu na asasin Kiristanci daga koyarwarsa ne, Mabiyansa suka yawaita, ya ci gaba da bin ragowar Hawariyawa da muminai da suka yi lokaci daya da Annabi Isa (A.S) har sai da suka kare. Wani abin mamaki shi ne, ina sauran al’umma suke da zasu yarda da makiyin da ya zo ya gane gaskiya har zai zama ra’ayoyinsa su ne daidai game da Addini da za a bar na Wasiyyan Isa (A.S).

Bayan Fiyayyen Halittu Manzo (S.A.W)
Haka nan Tarihi ya rubata mana rikici da sabani da suka wakana bayan wafatin Manzon Allah (S.A.W) har ya zamanto ba wanda ya halarci jana’izar fiyayyen halittu sai Sayyidi Ali (A.S) da wasu daga sahabbansa, amma sauran al’umma suna can suna jayayya a kan waye zai zama halifa!, alhali ga shi ba a ma binne shi ba!. Sai al’umma ta shiga sabani wasu suna cewa: Halifanci na Ali ne domin shi aka yi wasiyya da shi, kamar hadisin wasiyya ko hadisud-dar, da hadisin manzila, da hadisin Gadir khum, har ma an yi wa Imam Ali (A.S) bai’a a ranar Gadir wacce ba ta wuce wata biyu ba kafin rasuwar manzon Allah (S.A.W)[5], saboda haka ba wanda zasu yi wa bai’a sai Ali (A.S).
Wasu jama’a suna ganin a bar al’amarin ya zama tsakanin kuraishawa suna musaya da fasin da halifanci kamar yadda ake yi da kwallo. Rigima a Sakifa ta kai ga zare takobi amma Allah ya sa ba a zubar da jini ba, har abin ya kai ga Umar dan Khaddabi da wasu daga Ansar da ba sa shiri da Sa’ad Dan Ubbad suka yi bai’a ga Abubakar Dan Abi Kuhafa a matsayin halifan Manzo (S.A.W), daga nan ne suka bar Sakifa zuwa wajan da ake zaman juyayi da makoki na Manzo Allah (S.A.W), aka kuma tayar da wani rikici a wajan tsakanin musulmi, al’amarin abin sanya kuka ne a tayar da hayaniya a wajan makokin Manzo (S.A.W), har da zare takobi wani daga jama’a yana nuna takubi ga wuyan masu zaman makoki yana ku tashi ku yi bai’a!
Amma Ahlul Bait (A.S) daidai da rana daya ba su taba yarda da bai’ar halifa na farko ba, ruwayoyi suna cewa: Sayyidi Ali (A.S) bai yi bai’a ba sai bayan wafatin Zahra (A.S) shi ma bisa tilas, ya daga hannunsa ya buga kan na halifan musulmi[6]. Ahlul Baiti (A.S) sun ki yarda da halifancin wani wanda ba Imam Ali ba suna masu dogaro da da hujjar cewa; Manzon Allah (S.A.W) ya yi wasiyya ga Ali (A.S) tun yana raye. Imam Ali (A.S) da mabiyansa jama’ar muminai mabiya wasiyyar Manzo da aka fi sani da Shi’ar Ali ko Shi’ar Ahlul Baiti (A.S) ba su yi bai’a ba har bayan wafatin Fadima (A.S) bayan sun ga cewa idan ba su yi ba to za a kashe su ko a kona gidajensu.
Wanda ya fi kowa tsanantawa kan halifan farko daga Ahlul Baiti (A.S) ita ce Fadima (A.S) har ma ta yi fushi da halifa na farko da na biyu, ta kuma yi fushi da su ba ta kara yi musu magana ba, kuma ta yi alkawarin yi musu addu’a a kowace salla, da kuma kai su kara wajan Annabi (S.A.W), haka nan har ta mutu ba ta kara kallon su ko yi musu magana ba kamar yadda ya zo a Littafin Sahihul Bukhari, da Imama wassiyasa, kuma ta yi wasiyya ga Imam Ali (A.S) da idan ta mutu kada wani ya halarci kabarinta daga al’ummar Manzo (S.A.W) sai Shi da ‘Ya’yanta da wasu mutune da ba su wuce biyu ba.
Wannan al’amarin ya jawo har yanzu ba wanda ya san kabarinta a nan Madina, wani abin mamaki shi ne ba ma mai tambayar kabarinta daga al’ummar musulmi ko dalilin da ya sa ba a san inda yake ba. Wannan ya sanya har yanzu kowa yana da kabari da za a yi nuni zuwa gareshi amma banda Fadima ‘yar Annabin wannan al’umma (A.S) har yanzu babu wanda ya san kabarinta, Tarihi yana cewa: Idan Imam Mahadi (A.S) ya bayyana shi ne zai nuna kabarin nata.

Su Waye Wasiyyan Annabi (A.S)
Ahlul Baiti (A.S) da mabiyansu sun imani da cewar Manzo rahama ya yi wasiyya ga mutum goma sha biyu a bayansa wadanda su ne halifofinsa, haka ma Ahlussunna sun tafi a kan Manzo ya yi nuni da cewa: “Halifofinsa har kiyama ta tashi guda goma sha biyu ne dukkansu daga kuraishi” a wata ruwaya Bani Hashim. Littattafai masu yawa na Ahlussunna da Mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S) sun kawo har sunayensu wanda ya fara daga Ali (A.S) zuwa Mahadi (A.S) kamar adadin Nakibai na Bani Isra’ila da kuma Hawariyawan Annabi Isa (A.S) kamar haka: Ali Dan Abi Dalib (A.S) Hassan Dan Ali (A.S) Husaini Dan Ali (A.S) Ali Dan Husaini (A.S) Muhammada Dan Ali (A.S) Ja’afar Dan Muhammad (A.S) Musa Dan Ja’afar (A.S) Ali Dan Musa (A.S) Muhammad Dan Ali (A.S) Ali Dan Muhammad (A.S) Hasan Dan Ali (A.S) sai na karshensu Imam Muhammad Mahadi Dan Hasan (A.S) wanda zai cika Duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci.
A kowace al’umma wasiyyan annabawa da mabiyansu ‘yan kadan masu tawaye ga halifofi da sarakuna sukan shiga halin wariya da kawar da su gefe guda a tsawon rayuwar duniya, sai ‘yan kadan daga cikinsu da sukan rike jagoranci na wani dan lokaci. A kodayaushe al’amarin shugabanci da iko yakan ci gaba a hannun wadanda suka yi galaba a kan wasiyyan annabawa ne.
Farkon sabani da ya faru a al’ummar Manzo (S.A.W) shi ne na ranar da ya yi wafati yayin da jama’r annabi ta saba wa wasiyyar da ya bari na jagorancin imam Ali (A.S) a kan al’umma, wasu kuwa ‘yan kadan da aka fi sani da Shi’ar Ali (A.S) ko kuma Shi’ar Ahlul Baiti (A.S) suka dake a kan hakan[7].
Daya bangaren da ya yi galabar samun halifancin Manzo (S.A.W) wanda daga baya aka kira su da Ahlussunna a lokacin halifancin Mu’awiya dan Abu Sufyan. Koda yake yana da kyau a gane cewa da farko kalmar Sunna da ake nufi an kafa a wannan shekaru ba ana nufin abin da Manzo ya bari ba ne, abin da ake nufi shi ne la’antar Imam Ali ne da Daular Umawiyya ta assasa lokacin Halifancin Mu’awiya Dan Abi Sufyan, shi ya sanya Hajjaj Assaffah Assakafi yakan ce: “Shekarar kafa Sunna da jama’a, Shekarar Arba’in”[8].
Saboda haka Ahlussunna a wancan lokaci suna da ma’ana daban da ma’anar da ake nufi a yau, kamar yadda Wahabiyawa da suke bin Mazhabar Ahlil Hadisi ta Ahmad Dan Hanbali ana kiran su da Ahlussunna, wato ba su yarda da hankali ba koda a wajan tabbatar da al’amuran Akida kamar Samuwar Allah da Siffofinsa sai ta hanyar hadisai, ko da yake su ma da farko ana kiransu Ahlil Hadis ne. Akwai kuma ma’anar da yawanci take zuwa kwakwalen mutane game da Ahlussunna a yau wato wanda ba ya kan tafarkin Ahlul Bait (A.S).
Ahlussunna sun ci gaba da mulki a Duniyar musulmi shekaru masu yawa wanda da farko an kafa sharadin halifanci ga Kuraish a lokacin wafatin Manzo (S.A.W) har halifanci ya koma hannun Turkawa ta hanyar dogara da fatawar Abu Hanifa da ya jefar da sharadin kuraishanci ga halifan musulmi, al’amarin da ya sanya a siyasance Daular ta sanya hannun karfe wajan kare Mazhabar hanafiyya da kuma daukaka shi fiye da sauran ma’abota mazhabobi, Daular ta fara daga kakan su halifofin Daular Usmaniyya wato Usman har zuwa lokacin da Daular ta rushe a lokacin Kamal Atatuk a hannun Turawan yamma ‘yan mulkin mallaka, suka rusa daular suka kuma salladu a kan kasashen musulmi da arzikinsu gaba daya.

Abin Da Ya Faru A Tsawon Tarihin Musulmi
A duk tsawon wadannan shekaru dubu daya da dari hudu tun ranar da Manzo (S.A.W) ya yi wafati har zuwa yau mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S) wata al’umma ce da take karkashin zalunci na kuraishi na Umayyawa, sannan a hannun Abbasawa da Usmaniyyawan Turkawa. A Tarihin dan Adam mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S) su ne Jama’ar da ta fi kowace al’umma dadewa tana asakala da masu mulki kuma suna karkashin zalunci mai tsanani na masu hukunci, karanta Tarihin al’ummu da jama’u da suka yi dauki ba dadi da asakala da sarakunansu shi yake nuna gaskiyar wannan magana.
Duba Tarihin “Sufurin Makabin” jama’ar da suka yi asakala da sarakunan Yahudawa da Gwamnatin Rum bayan Musa (A.S), nan da nan a ka kore su suka koma duwatsu da dazuka da koguna da sahara, suka kuma rubuta masifun da suka same su da tarihinsu har suka kare. Haka ma muminan da aka bari bayan Isa (A.S) suka fuskanci irin wannan su ma nan da nan suka kare.
Amma Mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S) sun fuskanci kashe Imamansu tun daga na farko har na goma sha daya da kuma haramta musu rubuta ra’ayoyinsu, kusan farkon abin da dauloli sukan fitar na sharudda a kan mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S) shi ne haramta musu rubuta ra’ayoyinsu koda ma Hadisan Annabi ne da Tafsirin Kur’ani, kuma da haramta wa mutane su karanta ra’ayoyinsu, da littattafansu, ko su saurara daga garesu, ko su yi tunani game da su don su san ra’ayoyinsu, har ma a wasu dauloli da aka yi duk wanda yake karanta littattafansu ko yake rubuta su daga cikinsu ana jifansa da tuhumomi ne kamar makiyin Sahabbai ne! da sauran kage-kage da makiyan Sunna da Shi’a din ne suka kage su, kai ana iya jifan sa da fita daga musulunci, kuma a halatta dukiyarsa, da mutuncinsa, da jininsa.
Halifancin kuraishawa ya kare daga kan Almu’utasim Abbasi, a wannan lokaci ne Rundunar Turkawa suka mamaye duk wani abu da ya shafi tafiyar da daula, hatta da halifa a wajan su ya zama kamar dan aiki ne da yake daukar albashi! Sa’annan halifancin kuraishawa ya kare koda a suna a hannun Turkawan Usmaniyawa, shi kuwa halifancin Turkawa ya kare a hannun ‘Yan mulkin mallakar yamma, dukkan alkawuransu, da dokokinsu, da siyasarsu, suka zama Tarihi.
Amma abin mamaki shi ne siyasar Turkawa ta gaba da mazhabar Ahlul Baiti (A.S) da yada karairayi a kan mabiyansu ta wanzu cikin kwakwalen mutane, kuma da dama daga Ahlussunna suna dauke da dakon wannan farfaganda da karairayi da aka yada kan Mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S).

Fifita Wasu Mutane A Kan Manzo (S.A.W)
Sannan mafi yawansu a aikace suka ci gaba da ganin sarakunan Kuraishawa da na Usmaniyawa a matsayin rukunai ne daga rukunan Addinin musulunci da Allah (S.W.T) ya saukar wa manzonsa (S.A.W) da su tare da sauran rukunonin Addini, kuma duk wani abu da yake kishiyantar halifofi yake sukansu to a tunanin mafi yawansu shi wannan ya kafirce wa Allah da Manzonsa. Ta haka ne halifofin Kuraish da na Usmaniyya suka zama wani yanki daga yankin musulunci a wajansu, kai shi ne ma yanki mafi girma a zukatansu, har ba ka isa ka samu wanda yake kishin Allah da Manzonsa ba kamar yadda yake kishin wadannan halifofin Umayyawa da Abbasawa.
Har ma akwai wani malami mai fassara a kasashenmu da aka taba cin zarafin Manzon Allah, da mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S) suka tashi a kan haka sai ire-irensa suka ce: “Ai kotu ake kaiwa”. Amma wani abin mamaki shi ne sai ga irinsu suna yin karya a kan mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S) wai suna zagin Sahabbai! Har ya ce: Suna zagin Sayyidina Umar! Ya kuma fashe da kuka yana mai cewa: Mutane suna gani ba su yi komai ba! Abin mamaki da tambaya a nan shi ne, bai taba jin zagin wani sahabi daga garesu ba, kuma bai taba ganin wanda ya ji zagin ba, amma sai ga shi yana kuka a Gidan Radio /Talabijin yana kuma neman a dauki mataki a kai.
Amma sai ga shi yana da tabbacin an ci mutuncin Annabi, kuma ba wanda ya tashi ya nuna fushinsa a wancan lokaci sai mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S) amma yake sukan abin da suka yi wai me ya sa ba su je kotu ba, kuma ba a ga ya nuna koda bakin ciki ba da cin mutuncin da aka yi wa Annabi (S.A.W), balle ma ya yi kukan cin mutuncin, wannan duk yana daga mummunar tarbiyyar da guggubin mulkin Sarakunan Daulolin Umayyawa da Abbasawa da Turkawa suka bari ta hanyar nuna darajarsu da rashin ko in kula da daukaka darajar Fiyayyen halittu, Ma’aiki (S.A.W).
Tambaya a nan shi ne a lokacin da aka ci zarafin Manzon Allah da kalmomin da idan aka gaya wa duk wani wanda mutum yake so irinsu sai ya dauki mataki me ya sa ba mu ga irinsa ya yi kukan ba?, abin mamaki ba ma ya yi kuka ba, shi yana ma ganin laifin wadanda suka ce ba su yarda ba ne, yana ma ganin laifinsu ne alhali a kan kare Manzon (S.A.W) kuma da kona jaridar da ta ci mutuncinsa wasunsu ma sun rasa rayukansu, wasu kuma sun yi gidan kaso ko sun rasa wasu gabobi nasu.
Haka nan irin wadannan mutane suke kulla gaba da mabiya Ahlul Bait (A.S) a kwakwalensu ba tare da sun kafa wani dalili kwakkwara ba a kan haka, ina ganin wannan suka da kagen karya da aka fara shi a kan mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S) tun lokacin sarakunan Umayyawa da Abbasawa ya kuma yi tsanani a lokcin Usmaniyawan Turkawa yana da kyau mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S) su dauki mataki a kansa koda kuwa ta hanyar kotuna da rubuce-rubuce da kuma gidajen watsa labarai ne, domin su kunyata irin wadannan mutane da suka zamanto ragowa ne su na kage da farfagandar kakanninsu na lokacin da ya shude a kan mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S).