FASALI NA BIYAR
 
43- Tashin Kabari Da Tashin Kiyama
Mun yi imani da cewa Ubangiji zai tayar da mutane bayan mutuwarsu a wata sabuwar halitta a ranar da aka yi wa bayi alkawarinta, sai ya saka wa masu biyayya ya azabtar da masu sabo, wannan al’amari ne da baki dayansa da abin da ya tattara na daga sauki, abu ne wanda dukkan shari’o’in da aka saukar daga sama da masana Falsafa suka yi ittifaki a kai, kuma babu wata madogara ga musulmi sai dai ya yi imani da Akidar Alkur’ani mai girma wacce Annabinmu mai girma ya zo da ita (S.A.W), domin duk wanda ya yi imani da Allah imani yankakke ya kuma yi imani da Muhammad manzo ne daga gare shi wanda ya aiko shi da Shiriya da Addinin gaskiya to babu makawa ya yi imani da abin da Alkur’ani ya ba da labarinsa game da tashin kiyama, da sakamako da azaba, da aljanna da ni’ima, da wuta da kuna, kuma Alkur’ani ya bayyana haka a sarari kuma ya yi nuni da shi a cikin abin da ya kai kusan ayoyi dubu.
Idan har shakku ya samu wani game da wannan ba don komai ba ne sai domin yana shakku game da ma’abocin sakon, ko kuma game da samuwar mahaliccin halittu da kudurarsa, ba komai ba ne sai shakkun da yake bujuro masa game da asalin addinai dukkaninsu, da kuma ingancin shari’o’i gaba dayansu.

44- Tayar Da Matattu
Tayar da jikkuna wani al’amari ne da yake larura daga laruran Addinin Musulunci, Alkur’ani mai girma ya yi ishara game da shi: “Shin mutum yana tsammanin ba za mu tattara kasusuwansa ba ne. A’aha, Lalle mu masu iko akan mu daidaita yatsunsa ne”. Surau Alkiyama: 3. Da fadinsa: “Idan kayi al’ajabi to abin al’ajabi ce maganarsu cewa ashe idan muka mutu muka zama turbaya za a dawo da mu halitta sabuwa”. Ra’ad: 5. Da fadinsa: “Shin mun gajiya ne da halittar farko, a’a su dai suna cikin rudewa ne game da sabuwar halitta”. Surar Kaf: 14.
Tayar da jikkuna ba wani abu ba ne sai dawo da mutum ranar tashin kiyama da jikinsa bayan rididdigewa da sake dawo da shi zuwa ga kamarsa ta farko bayan ya zama rididdigagge. Ba wajibi ba ne a yi imani da dalla-dallan tayar da jikkuna fiye da abin da Alkur’ani ya ambata ko sama da abin da ya fada na daga; Hisabi da Siradi da Auna ayyuka da Aljana da Wuta da Sakamako da Ukuba daidai gwarbwadon abin da bayaninsa ya zo a cikin Kur’ani mai girma.
“Bai wajaba ba sanin hakikar da babu mai iya kaiwa gare ta sai ma’abocin zurfin ilimi, kamar ilimin cewa shin jikkuna zasu dawo ne da kan kansu ko wasu makamantansu ne? Kuma shin rayuka zasu rasu ne kamar jikkuna ko kuwa zasu ci gaba da kasancewa har sai sun sadu da jikkuna yayin tashin kiyama? Kuma cewa shin Tashin kiyama ya kebanci mutum ne ko ya hada har da dukan dabbobi ne? Kuma shin tashin a lokaci daya ne ko a sannu-sannu ne? Kuma idan yin imani da Aljanna da Wuta wajibi ne amma bai zama dole a san cewa samammu ne a halin yanzu ba, ko kuma sanin cewa a sama suke ko a kasa ko kuma sun saba. Haka nan idan sanin ma’auni ya zama wajibi amma bai wajiba ba a san cewa ma’aunin na ma’ana ne ko kuwa yana gurin gwada nauyi ne biyu. Kuma ba dole ba ne a san cewa siradi jiki ne siriri ko kuwa daidaituwa a kan tafarki madaidaici ne. Hadafi wannan bayani shi ne a Musulunci ba a shardanta bincike domin sanin cewa wadannan abubuwa suna da jiki ne ko kuwa…”[57].
Wannan akidar ta tashin kiyamar da saukin nan nata ita ce wacce Musulunci ya zo da ita, idan mutum ya so ya wuce haka domin saninta dalla-dalla sama da abin da Kura’ani ya zo da ita domin ya gamsar da kansa don kore shakkun da masu bincike da masu kokwanto ke tayarwa ta hanyar dalilan hankali ko bahasin dalili na zahiri to yana wahalar da kansa ne kuma zai fada a cikin mushkiloli da jayayya maras iyaka.
A Addini babu adinda yake tilasta wannan zurfafawar dalla-dalla da littattafan masana Akida da malaman falsafa suke cike da shi, kuma babu wata larurar Addini ko ta zamantakewa ko siyasa da take tilasta irin wadannan rubuce-rubucen da makalolin da aka makale littattafai da ita babu wata fa’ida, wadanda suka karar da karfi da kokari da lokuta da tunanin masu jayaya ba tare da fa’ida ba. Gamsuwarmu game da gazawar mutum game da riskar wadannan al’amuran da suke boyayyu a gare mu, kuma wadanda suke sama da fahintarmu da samuwarmu, wadanda suka dara matsayinmu, sun wadatar wajen raddin wadannan shubuhohi da shakkun da ake tayarwa game da wadancan bayanai. Tare da sanin cewa Allah (S.W.T) mai iko ne a kan ya ba mu labarin hakikanin aukuwar Tashin kiyama da tashi daga kabari.
Ilimin dan Adam da gwaje-gwajensa da bincike-bincikensa mustahili ne su iya samo wani abu da bai san shi ba, ba ya kuma karkashin gwajinsa da bincikensa da ba zai iya saninsa ba sai bayan mutuwarsa da ciratarsa daga wannan duniya zuwa wata duniyar daban, idan haka ne yaya za a saurari ya yi huknci da tabbatarwa ko kore wannan abu balle ya shiga bayanansa dalla-dalla da abubuwan da suka kebanta da shi, sai dai idan ya dogara a kan bokanci da zato da mamaki kamar yadda yake a dabi’ar dan Adam ya yi mamakin dukkan abin da bai saba da shi ba, kuma iliminsa da riskarsa ba su san shi ba, kamar mai fada da jahilcinsa yana mai mamakin tashi daga kabari da tashin kiyama: “Wanene zai rayar da kasusuwa alhali suna rididdigaggu”.
Ba komai ne ya sa shi mamakin ba sai rashin sabawa da ganin matacce rididdigaggen an mayar masa da sabuwar rayuwa, sai dai mai wannan mamakin ya manta da yanda aka halicce shi tun farko alhalin da can ya kasance rasasshe, gabobinsa da yankunan jikinsa riddidigaggu an hada su ne daga kasa da abubuwan da ta kunsa, da kuma sarari da abin ya tattaro har ya zama mutum madaidaici mai hankali: “Shin mutum ba ya gani ne mu mun halitta shi daga digon maniyyi sai ga shi yana mai husuma bayyananne. Kuma ya buga mana misali ya mance halittarsa”.
Ana gaya wa mai irin wannan maganar da ya mance kansa: “Wannan da ya fare ta tun karo na farko shi ne zai raya ta kuma shi masani ne game da dukan halitta”. Kuma a ce masa: Gashi bayan ka san mahaliccin halittu da kudurarsa kuma ka san Manzo da abin da ya ba da labari game da shi, da gajiyawar iliminka hatta a gano sirrin halittarka da sirrin samuwarka, da yadda ka girma da kuma yadda ka fita daga marhalar digon mani da ba ya jin komai ba ya hankalta zuwa marhalolin da ke biye da aka harhada daga kwayoyin halitta manesanta, domin ka zamanto mutum madaidaici mai hankali mai tunani mai riska da mariskai. Kuma a ce da shi: Yaya kake mamakin dawo maka da rayuwa sabuwa bayan ka zama rididdigagge, kana kokarin tsinkayar sanin abin da kwarewarka ka da iliminka ba zasu iya gano shi ba? A kuma ce masa: Ba ka da wata mafita sai mika wuya kana mai ikrari da wannan hakika wadda mai juya al’amuran halittu, masani, mai kudura, wanda ya samar da kai daga rashi. Kuma dukkan wani kokari na binciko abin da ba zai yiwu a gano shi ba, kuma iliminka ba zai kai gare shi ba, to kokari ne maras amfani, da rudani cikn dimuwa, da bude ido a cikin duhu mai dudum.
Dan Adam duk da irin inda ya kai gare shi na ilimi a wannan zamani, ya kago lantarki, da rada[58], da amfani da makamin kare dangi, da sauran kage-kagen da, da an yi magana game da su a shekarun baya da an kirga su a cikin mustahilan abubuwa ababan yi wa isgili, amma duk da haka mutum ya kasa gano hakikanin wutar lantarki, da sirrin kwayar zarra, ya kasa gano hatta hakikanin daya daga cikin siffofinta, to yaya zai ji kwadayin gano sirrin halitta da samuwa, sannan ya kara gaba yana son ya san sirrin Tashin kiyama da Tashi daga kabari.
Haka ne, ya kamata ga mutum bayan ya yi imani da Musulunci ya nisanci bin son zuciya kuma ya shagaltu da abin da zai gyara masa lahirarsa da duniyarsa, da kuma abin da zai daukaka masa matsayinsa a gurin Allah, kuma ya yi tunani a kan abin da zai taimake shi a kansa da kuma abin da zai fuskanta bayan mutuwa na daga tsananin kabari da hisabi bayan halarta a gaban mai Mulki mai yawan sani. “Kuma ku ji tsoron ranar da wata rai ba ta wadatar wa wata rai komai kuma ba a karbar ceto daga gareta kuma ba a karbar fansa daga gareta kuma ba a taimakon su”. Bakara: 48.
GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN TALIKAI


[4] - Wato abubuwan da suke wajibi kowa-da-kowa ya san su.
[5] - Shi ne nazarin dalilan shari'a domin samun masaniya game da rassan hukunce-hukuncen shari'ar da shugaban Manzanni (S.A.W.) Ya zo da ita kuma ba ta canzawa ko sakewa da sakewa zamani da kuma halaye.
[6] - Ihtiyadi shi ne bin fatawar malamai da aiki da mafi nutsuwar zance daga cikin fatawowinsu.
[7] - Wato idan wasu suka yi sun dauke wa sauran mutane.
[8] - Abin da yake bai damfara ko dogara da wuri ba.
[9] - Abin da yake ya damfara ko ya dogara da wuri.
[10] - Karfici a nan ba irin wanda yake fitar da mutum daga Musulunci ba ne kamar yadda yake sananne cewa kafirci matakai matakai ne.
[11] - Siffofin Idafa su ne siffofin da suke nuna alaka tsakanin bangare biyu, wato bangaren Allah da kuma na bayinsa, kamar arzutawa da halittawa.
[12] - Shi ne wanda samuwarsa daga waninsa take wato shi abin halitta ne.
[13] - Wannan ra’ayi ne na daya daga malaman mu’utazila da mabiyansa, abin da yake nufi shi ne, siffofin tabbatar da kamala ga Allah suna komawa ga kore tawaya ne, kamar idan aka ce mai iko ne to awajansu abin da ake nufi shi ne ba gajiyye ba ne, amma wai ba a iya cewa ma’anar ta mai iko ne, domin gudun kada a kamanta shi da bayinsa. A lokacin da wannan ra’ayi ya kai su ga tauye Allah (S.W.T) domin idan aka ce mai ilimi yana nufin ba jahili ba amma kuma ba ya nufin ma’anar mai ilimi, wannan a gun mu mazhabar imamiyya isna ashariyya tauye Allah ne da kore masa kamala, Allah ya tsare mu daga kaucewar tunani.
[14]- Wannan ra’ayi ne na Ash’ariyya da suke ganin siffofin ma’ani ba kawai ma’ana ba ne da Allah shi ne hakikanisnsu na zahiri, kamar yadda sauran siffofinsa suke, a’a haka nan wadannan siffofi suna da tabbatattun hakikaninsu a zahiri na hakika da suke hawa akansu (siffantuwa da su) wato suna da masadik, kamar Malam Ali da yake da sunaye ne da siffofi, da za a ce masa malam Ali dan Muhammad baban Isa dogo ne kuma kakkaura da sauransu, sai a ce siffofinsa dan Muhammad baban Isa da dogo da kakkaura duk a zahiri suna da daidaikun da suke siffantuwa da su, sai ya zama Malam Ali shi yana nuni izuwa gareshi ne kawai banda sauran siffofi, sauran siffofi kuma suna da nasu masadik na hakika da suke hawa kansu a zahiri. Da maganar Ash’ariyya gaskiya ne da anan Allah ya zama guda takwas, kamar yadda a misalinmu malam Ali zai zama su biyar, wato malam Ali da dan Muhammad da baban Isa da dogo da kuma kakkaura.
[15] - Wato siffofn kari guda bakwai da masu wannan nazari suka ce su ba Allah ba ne amma sun dadu ga zatin Allah kuma zatin yana bukatarsu a ra’ayin Ash’ariyya kamar yadda ya gabata a bayaninmu na lamba ta uku, da kuma Siffofin khabariyya; kamar hannun Allah da idonsa da fuskarsa da suke da tawili da ma’anar da laraba suka sani alokacin saukra da littafin Al-kur’ani mai girma, Sifffofin khabariyya siffofi ne wadanda ake tawilinsu kamar tawilin hannu da karfi ko iko ko alkawarin Allah kamar yadda ya zo da kinayoyi da kalmomin aro a Alkur'ani mai girma.
[16] - Alhalin Allah yana ko'ina bai kebanta da wani wuri ba.
[17] - A sani masu wannan ra’ayi suna magana ne a matakin yiwuwa a hankalce saboda musunsu ga rawar da hankali zai iya takawa a wannan fage, amma a aikce ba su siffanta shi da wannan miyagun siffofi ba sai da lazimin maganarsu, wato sakamakon abin da suke fada suka kuma tafi a kai zai kai ga siffanta Allah da miyagun siffofin tawaya irin wadannan a hankalce.
[18] - Su ne mutanen da suka tafi a kan cewa ayyukan bayi a bisa hakika ayyukan Allah ne ba tare da wani tawili ba a kan haka, don haka Allah (S.W.T) shi ne yake aikata ayyukan bayi kai tsaye.
[19] - Mujabbira, da Ash’ariyya suna da wannan ra’ayi da aka san shi da jabar na musun wasida da tsakanin da Allah ya halitta ya kuma sanya shi tsakaninsa da bayinsa da falalarsa, kamar ‘ya’yan mangwaro da suke zuwa daga itace, wato sai suka ce kai tsaye Allah ne ya halitta su ba tare da wata rawa da shuka a matsayinta na wasida ta taka ba. Wannan shi ne kwatankwacin ayyukan bayinsa a wajansu, don haka kai tsaye ayyukansu ayyukansa ne.
[20] - Sabanin Mujabbira da Ash’ariyya, Mu’utazilawa sun tafi akan Tafwidi da ma’anarsa take nufin cewa babu hannun Allah a cikin ayyukan bayi ko kadan, wannan ra’ayi da shi da na farkon duka a gun mazhabar imamiyya kuskure ne.
[21] - “Da rai da abin da Ya daidaita ta kuma ya cusa mata fajircinta da kuma takawarta”. Surar Shamsi: 7-8.
[22] - Adifa al’amura ne kamar ki, so, fushi, yarda, da sauran halayen rai da zuciya.
[23] - “Manzanni masu bushara kuma masu gargadi domin kada mutane su zama suna da wata hujja a kan Allah bayan Manzanni kuma Allah mabuwayi ne Mai hikima”. Surar Nisa’i: 165.
[24] - “Kuma sai muka yi wahayi ga Musa kan cewa jefa sandarka sai ga shi tana hadiddiye abubuwan da suke kirkira. Kuma gaskiya ta tabbata abin da suke aikatawa kuma ya baci, Sai aka rinjaye su a nan sa’annan suka juya suna kaskantattu, Kuma aka kifar da masu sihirin suna masu sujada”. Surar A’araf; 117-120.
[25] - “Kuma Manzo zuwa ga Bani Isra’ila cewa lalle ni na zo muku da aya daga Ubangijinku ni ina halitta muku daga laka abin da yake kamar surar tsuntsu kuma in hura a cikinsa sai ya zamanto tsuntsu da izinin Allah kuma ina warkar da makaho da mai albaras kuma ina raya matattu da izinin Allah kuma ina ba ku labarin abin da kuke ci da wanda kuke taskacewa a gidajenku lalle a cikin wannan akwai aya gare ku idan kun kasance muminai”. Surar AI- Imran: 49.
[26] - Duba fadin Allah madaukakin sarik:
“Kuma idan da mutane da aljannu zasu taru a kan su zo da kwatankwacin wannan Alkur’anin to da ba zasu zo da makamancinsa ba koda kuwa sashensu na taimakon sashe”. Surar Isra’i: 88. “Ko suna cewa shi ne ya kage shi ne ka ce to ku zo da surori goma makamantansa kagaggu kuma ku kira duk wanda za ku iya wanda ba Allah ba in kun kasance masu gaskiya”. Surar Hud: 13 kalubalantar su kan su kawo sura guda kamarsa: “Kuma idan har kun kasance a cikin kokwanto daga abin da muka saukar to ku zo da sura daya kamarsa kuma ku kira shaidunku da ba Allah ba in kun kasance masu gaskiya”. Surar Bakara: 23 Allah Ta’ala Yana cewa: “Ko suna cewa ya kage shi ne ka ce ku zo da sura guda kamarsa kuma ku kira duk wanda za ku iya koma bayan Allah in kun kasance masu gaskiya”. Surar Yunus: 38.
[27] - Isma shi ne rashin aikata sabo a kowane hali da zamani a rayuwar mai ita, shin a lokacin yarinta ne ko girma ko tsufa, kafin aike da daukar nauyi ko a lakacin hakan.
[28] - Fadinsa madakaki: “Kuma lalle mun rubuta a littafi bayan ambato cewa duniya bayina salihai ne zasu gaje ta, lalle a cikin wannan akwai isarwa ga mutane masu ibada”. Surar Anbiya’i: 105-106. Hadisai kuma sun zo da silsila daban daban har zuwa kan Manzo (S.A.W.) da kuma Imamai (A.S) cewa: Mahadi (A.S) daga ‘ya’yan Fatima (A.S) zai bayyana a karshen zamani domin ya cika duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci.
[29] - Amirul muminin Aliyyu Dan Abi Talib (A.S) ya siffanta shi a daya daga cikin hudubobinsa yana cewa: “Ya zabe shi bishiyar Annabawa da fitila mai haske da kuma mai tsororuwar daukaka da mafi darajar gurare, da fitilun haskaka duffai kuma shi ne mabubbugar hikima”. Daga cikin wannan hudubar har ila yau Amirul Muminin (A.S) yana cewa: “Likita mai zazzagawa da maganinsa ya shirya kayan aikinsa yana amfani da su duk lokacin da bukata ta kama wajen warkar da makantattun zukata, da kuraman kunnuwa, da bebayen bakuna, yana bibiyar guraren gafala da maganinsa da kuma guraren rudewa, ba su yi amfani da hasken hikima ba, ba su kunna kyastu makoyar ilimi ba, su sun zamanto kamar dabbobi masu kiwo a duwatsu masu tsauri.” (Nahajul Balagha Huduba: 108).
[30] - Ubangiji madaukai yana cewa: “Mu Mu ne Muka saukar da ambato kuma lallai Mu masu karewa ne gare shi”. Surar Hijri: 9.
[31] - Duba fadinsa madaukaki: “Kuma yayin da Isa dan Maryam ya ce: Ya Bani Isra’la lalle ni Manzon Allah ne gare ku, mai gaskata abin da yake gaba gare ni na Attaura kuma mai bayar da bushara game da wani Manzo da zai zo bayana sunansa Ahmad. Sai dai a yayin da ya zo musu da hujjoji bayyanannu sai suka ce wannan sihiri ne bayyananne”. Surar Saff: 6.
[32] - Fadinsa madaukaki: “Idan ma ba ku taimake shi ba to ai Allah ya riga ya taimake yayin da wadanda suka kafirta suka fitar da shi yana na biyun su biyu yayin da suke cikin kogo yayin da yake cewa ma’abucinsa kada ka damu hakika Allah yana tare da mu, sai Allah ya saukar da nutsuwarsa gareshi ya kuma taimake shi da rundunoni da ba ku gan su ba, kuma ya sanya kalmar wadanda suka kafirta makaskanciya kalmar Allah kuma ita ce madaukakiya kuma lalle Allah Mabuwayi ne mai hikima”. Surar Tauba: 40.
[33] - Kamar yadda yake a fadar Ubangiji “Ka ce Ya Ubangiji Ka kara mini ilimi”. Surar Taha: 114.
[34] - Masu ruwaya a tafarkin Sunna da Shi’a sun hadu a kansa.
[35] - Masu fadin cewa imamai ubangizai ne ko kuma su ba ma mutane ba ne.
[36] - Masu imani da shigar Ruhin Ubangiji madaukaki jikin imamai.
[37] - Koma wa Littafin Sakifa na mawallafin wannan littafin domin Karin bayani da sharhi ga wasu ayoyin kur’ani da makamantansa.
[38] - Tanasuhi shi ne ciratar wata rai daga wani jiki zuwa wani jikin daban da ba na farko ba.
[39] - Babul Ikbal aladdu’a daga kitabuddu’a na littafin Usulul Kafi daga Imam Sadik (A.S).
[40] - Daga maganar Imam Rida (A.S), duba littafin Kamiluz ziyarata da Ibn Kulawaih Sh: 122.
[41] - Tuhaful Ukul: sh, 24.
[42] - Kamiluz ziyarati: shafi: 131.
[43] - Usulul Kafi, Kitabul iman, Babu ziyaratul ikhwan.
[44] - Usulul Kafi, Kitabul iman, Babul wara’i.
[45] - Usulul Kafi, Kitabul iman, Babut ta’a wat takawa.
[46] - Usulul Kafi, Kitabul iman, Babu Hakkil mu’umini ala akhih.
[47] - Usulul Kafi, Kitabul iman, Babul wara’i.
[48] - Tuhaful Ukul: sh, 66.
[49] - Al- Wasa’il Kitabul Bai’i Babi na 78.
[50] - Sun kasance suna cewa Allah ya yi rahama ga wanda ya raya al’amarinmu.
[51] - Alwasa’il, Kitabul amri bil ma’arufi wan nahayi anil munkari: Babi 17.
[52] - Alwasa’il, Kitabul hajji, Abwabu ahkamul ushura, Babi 122, hadisi 7.
[53] - Usulul Kafi, Kitabul ushura, Babi na farko.
[54] - Wato yana nufin Imam Assadik (A.S).
[55] - Alwasa’il kitabul hajji, Abwabul ushura: babi 122, hadisi 16.
[56] - In ji fawallafin littafin.
[57] - Kitabu Kashiful gita’i, shafi 5.
[58] - Na’urar hangen abubuwa daga nesa.
[59] - Allah Ta’ala Ya Tsarkaka Ga Barin Irin Wadannan Siffofi Daukaka Mai Girma.