KUR'ANI MADAUAKAKI:
"MU NE MUKA SAUKAR DA AMBATO KUMA MU MASU KARIYA NE GARESHI".

DAGA SURAR LAIL ZUWA SURAR NASI
Surar Dare

Tana karantar da dangantaka tsakanin d'abi'a da halitta da aK'ibar mutum bisa aikinsa, da kuma kasuwar abubuwa tsakanin alheri da sharri.Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai1. Ina rantsuwa da dare a lokacin da yake rufewa.2. Da lokacin rana yayin da bayyana.3. Da abin da ya halitta namiji da mace.4. HaK'iK'a ayyukanku, mabambanta ne.5. To, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taK'awa.6. Kuma ya gaskata kalma mai kyawo.7. To, za Mu sauK'aK'e masa har ya kai ga sauki.8. Kuma amma wanda ya yi rowa, kuma ya wadatu da kansa.9. Kuma ya K'aryatar da kalma mai kyawo.10. To, za Mu sauK'aK'e masa har ya kai ga tsanani.11. Kuma dukiyarsa ba ta wadatar masa da komai idan ya gangara (wuta).12. Lalle aikinMu ne, Mu bayyana shiriya.13. Kuma lalle ne Lahira da duniya Namu ne.14. Saboda haka, Na yi maku gargad'i da wuta mai babbaka.15. Babu mai shigarta sai mafi shaK'awa.16. Wanda ya K'aryata, kuma ya juya baya.17. Kuma mafi taK'awa zai nisance ta.18. Wanda yake bayar da dukiyarsa ,alhali yana tsarkaka.19. Alhali babu wani mai wata ni'ima wurinsa wadda ake neman sakamakonta.20. Face dai neman yardar Ubangijinsa Mafi d'aukaka.21. Kuma tabbas da sannu zai yarda.

Surar Hantsi

Tana karantar da ni'imomin da Allah Ya yi wa Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da neman ya yi godiya a kansu ta hanyar biyayya ga umarnin Allah.Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai1. Ina rantsuwa da hantsi2. Da dare a lokacin da ya rufe (da duhunsa)3. Ubangijinka bai K'yale ka ba, kuma bai K'i kaba4. Kuma lalle K'arshe ce mafi alheri a gare ka daga farko5. Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta ba ka kyauta sai ka yarda.6. Ashe, bai same ka maraya ba, sa'an nan Ya yi maka mafaka?7. Kuma Ya same ka ba ka da shari'a, sai Ya shiryar da kai?8. Kuma Ya same ka matalauci, sai Ya wadata ka?9. Saboda haka, amma maraya, to, kada ka rinjaye shi.10. Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa kyara.11. Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka fad'a.Surar Yalwatawa

Tana nuna ni'imomin da Allah Ya yi wa Annabi, (s.a.w) domin ya K'ara godiya ga Allah (s.w.t)Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai1. Shin ba Mu yalwata maka zuciyarka ba.2. Kuma Muka saryar maka da nauyinka.3. Wanda ya nauyaya bayanka.4. Kuma Muka d'aukaka maka ambatonka.5. To, lalle ne tare da tsanani akwai wani sauK'i.6. Lalle ne tare da tsanani akwai wani sauK'in.7. Saboda haka idan ka K'are sai ka kafu.8. Kuma ka yi kwad'ayi zuwa ga Ubangijinka.Surar B'aure

Tana karantar da cewa dukkan abin da ya shafi imani da aiki na gari ba ya tab'ewa, amma sauran abubuwa suna halakaDa sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'aiIna rantsuwa da B'aure da Zaitun.Da Dutsen Sina.Da wannan gari amintacce.Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon daidaito.Sannan Muka mayar da shi mafi K'asK'antar K'asK'antattu.Sai dai wad'anda suka yi imani, kuma suka yi ayyuka na K'warai, To wad'annan suna da sakamako wanda ba ya yankewa.To, bayan haka me ya sanya ka K'aryata sakamako.Ashe Allah ba Shi ne Mafi iya hukuncin masu hukunci ba?Surar Gudan Jini

Tana karantar da cewa karatu shi ne gaba da komai, amma a gama shi da sunan Allah, kuma duk wanda ya kauce wa hanyar Allah zai samu uK'uba
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai1. Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta.2. Ya hahitta mutum daga gudan jini.3. Ka yi karatu, kuma Ubangijinka shi ne Mafi karimci.4. Shi ne wannan da ya koyar da alK'alami.5. Ya sanar da mutum abin da bai sani ba.6. A'aha! Lalle, ne mutum yana girman kai.7. Domin ya ga kansa, ya wadatu.8. HaK'iK'a zuwa ga Ubangijinka makoma take.9. Shin, ka ga wanda ke hana.10. Bawa idan ya yi salla?11. Ashe, ka gani, idan ya kasance a kan shiriya?12. Ko ya yi umurni da taK'awa?


13. Ashe, ka gani, idan ya K'aryata, kuma ya juya baya?14. Ashe, bai sani ba cewa Allah Yana gani?15. A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, tabbas zamu ja gashin maK'warK'wad'a.16. MaK'warK'wad'a, maK'aryaciya, mai laifi.

.

17. To sai ya kira K'ungiyarsa.18. Zamu kira zabaniyawa.19. A'aha kada ka bi shi, kuma ka yi sujada, ka nemi kusanci.


Surar Daraja

Tana karantar da son Allah ga wannan al'umma ta Musulmi da Ya ba su Dare mai Daraja "Lailatul K'adr" domin Ya yawaita ladar ayyukansu ko da yake rayukansu ba su da tsawo kamar na al'ummomin farko, kamar yadda take nuna cewa; alaK'ar Allah (s.w.t) da bayinsa ba ta yankewa da yankewar Annabci.Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai.1. Lalle ne Mu, Mun saukar da shi a cikin Dare mai daraja.2. To, me ya sanar da kai abin da ake cewa Lailatul K'adari?3. Lailatul K'adari mafi alheri ne daga watanni dubu.4. Mala'iku da Ruhi suna sauka a cikinsa da izinin Ubangijinsu daga kowane umurni.5? Aminci ne shi har b'ollowar alfijiri.Surar Hujja

Tana karantar da halayen kifirai da mutanen Littafi, wato Yahudu da Nasara game da Annabi (s.a.w), da Mushirikai tun gabanin da kuma bayan bayyanarsa.Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai1. Wad'anda suka kafirta daga mutanen Littafi, da mushirikai, ba su kasance masu gushewa daga gaskiya ba har sai da hujja ta zo musu.2. Wani Manzo daga Allah yana karanta wasu takardu masu tsarki.3. A cikinsu akwai wasu littattafai masu d'aukaka.4. Kuma wad'anda aka bai wa Littafi ba su rarrabu ba sai bayan hujja ta zo musu.5. Kuma ba a umarce su da komai ba sai su bauta wa Allah suna masu tsarkake addini gare Shi, masu daidaito, kuma su tsayar da salla, kuma su bayar da zakka, kuma wannan shi ne addinin nagarta.6. HaK'iK'a ne wad'anda suka kafirta daga mutanen Littafi da mushirikai suna cikin wutar Jahannama suna madawwama a cikinta, wad'annan su ne mafi sharrin talikai.7. HaK'iK'a wad'annan nan da suka yi imani kuma suka yi ayyuka na gari, wad'annan su ne mafifitan talikai.8. Sakamakonsu, a wurin Ubangijinsu, shi ne gidajen Aljannar Adnu, K'oramu suna gudana daga K'arK'ashinsu suna madawwama a cikinta har abada, Allah Ya yarda da su, kuma su ma sun yarda da Shi, wannan (sakamako ne) ga wanda ya ji tsoron Ubangijinsa.Surar GirgizaDa Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin K'ai

(1)

1. Idan aka girgiza k'asa girgizawarta.

(2)

2. Kuma k'asa ta fitar da kayan nauyin da suke cikinta.

(3)

3. Kuma mutum ya ce: Mene ne ya same ta?.

(4)

4. A ranar nan zata fad'i labaranta.

(5)

5. Cewa Ubangijinka ne ya yi mata umarni.

(6)

6. A ranar nan mutane zasu zo jama'a-jama'a domin a nuna musu ayyukansu.

(7)
7. To wanda ya aikta wani aiki gwargwadon nauyin zarra na alheri, zai gan shi.

(8)

8. Kuma wanda ya aikata wani aiki gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi.
Surar DawakaiAllah Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin K'ai

(1)


1. Ina rantsuwa da dawakai masu gudu, suna masu k'ugin ciki.

(2)

2. Da masu k'yasta wuta k'yastawa.

(3)

3. Sannan da masu kai hari lokacin Asuba.

(4)

4. Sai su tayar da k'ura da shi (harin).

(5)
5. Sai su kutsa cikin jama'ar mayak'a da ita (k'urar).

(6)

6. Hak'ik'a mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa.

(7)

7. Kuma lalle shi mai sheda ne a kan hakan.

(8)

8. Kuma lalle shi mai tsananin so ne ga alheri.


(9)

9. Shin ba ya sanin idan aka tone abin da yake cikin kaburbura.

(10)

10. Kuma aka bayyana abin da yake cikin zukata.

(11)

11. Lalle Ubangijinsu masani ne game da su a wannan ranar.


Surar Mai K'wank'wasaDa Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin K'ai

(1)

1. Mai K'wank'wasa.

(2)

2. Mece ce mai k'wank'wasa.

(3)

3. Kuma me ya sanar da kai mece ce mai k'wank'wasa.

(4)

4. Ranar da mutane zasu kasance kamar fari masu watsuwa.

(5)

5. Kuma duwatus su kasance kamar gashin suf da aka sab'e.

(6)

6. To amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi.

(7)

7. To shi yana cikin wata rayuwa yardajjiya.

(8)
8. To amma kuma wanda ma'aunansa suka yi sako-sako.

(9)

9. To uwarsa Hawiya ce.

(10)

10. Me ya sanar da kai mece ce ita?.

(11)

11. Wata wuta ce mai zafi.Surar Yawan Tara Arziki
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin K'ai

(1)

1. Rigen Yawan tara arziki ne ya shagaltar da ku.

(2)

2. Har kuka ziyarci kaburbura.

(3)

3. A'aha! Zaku sani.

(4)

4. Sannan tabbas zaku sani.

(5)

5. Hak'ik'a da ku san sani na yak'ini.

(6)

6. Da kun ga wutar Jahim.

(7)

7. Kuma tabbas zaku gan ta idanu k'uru-k'uru.

(8)


8. Sannan tabbas za a tambaye ku a wannan ranar game da ni'imar.

Surar ZamaniAllah Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin K'ai

(1)

1. Ina rantsuwa da zamani

(2)

2. Hak'ik'a mutum yana cikin hasara.

(3)

3. Sai dai wad'anda suka yi imani, kuma suka yi ayyukan k'warai, kuma suka yi wa juna wasici da bin gaskiya, kuma suka yi wa juna wasici da yin hak'uri.
Surar Mai Zumd'eDa Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin K'ai

(1)

1. Azaba ta tabbata ga dukkan wani, mai zumd'e, mai gatsine.

(2)

2. Wanda ya tara dukiya ya yi tattalinta.

(3)

3. Yana tsammanin dukiyarsa zata dawwamar da shi.

(4)

4. A'aha! Lalle sai an jefa shi a cikin hud'ama.

(5)

5. Kuma me ya sanar da kai ko mece ce hud'ama.

(6)

6. Wutar Allah ce abar hurawa.

(7)

7. Wacce take lek'awa a kan zuciya.

(8)

8. Hak'ik'a ita abar kullewa ce a kansu.

(9)

9. A cikin wasu ginshik'ai mik'ak'k'u.Surar GiwaDa Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin K'ai

(1)

1. Ashe ba ka ga yadda ubangijinka ya aikata ga mutanen giwa ba?

(2)

2. Ashe bai sanya kaidinsu a cikin tab'ewa ba.

(3)

3. Kuma ya aika musu da wasu tsuntsaye gungu-gungu.

(4)

4. Suna jifar su da wasu duwatsu na yumb'un wuta.

(5)

5. Sai ya sanya su kamar karmami abin cinyewa.Surar K'uraishawaDa Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin K'ai

(1)

1. Saboda sabon k'uraishawa.

(2)

2. Sabonsu na tafiyar hunturu da ta bazara.

(3)

3. Don haka sai su bauta wa ubangijin wannan d'akin.

(4)

4. Wanda ya ciyar da su daga yunwa, kuma ya amintar da su daga wani tsoro.

Surar taimakoDa Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin K'ai

(1)

1. Shin ka ga wanda yake k'aryatawa game da sakamako?

(2)

2. To wannan shi ne yake tunkud'e maraya.

(3)

3. Kuma ba ya kwad'aitarwa bisa ciyarwar miskini.

(4)
4. To azaba ta tabbata ga masallata.

(5)

5. Wad'annan da suke masu shagala daga sallarsu.

(6)

6. Wad'annan da suke yin riya.

(7)

7. Kuma suke hana taimako.Surar Alheri Mai YawaDa Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin K'ai

(1)

1. Lalle ne mu, mun yi maka alheri mai yawa.

(2)

2. Saboda haka ka yi salla domin ubangijinka, kuma ka yi suka (soke taguwa/rak'umi).

(3)

3. Hak'ik'a mai aibata ka shi ne mai yankakken baya (maras albarka).
Surar KafiraiDa Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin K'ai

(1)

1. Ka ce; Ya ku kafirai.

(2)

2. Ba zan bauta wa abin da kuke bauta wa ba.

(3)

3. Kuma ba zaku zama masu bauta ga abin da nake bauta wa ba.

(4)

4. Kuma ni ba zan zama mai bauta wa abin da kuke bauta wa ba.

(5)

5. Kuma ku ba zaku zama masu bauta wa abin da nake bauta wa ba.

(6)

6. Addininku na gareku, kuma addinina yana gareni.Surar Cin NasaraDa Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin K'ai

(1)

1. Idan taimakon Allah da cin nasara suka zo.

(2)

2. Kuma ka ga mutane suna shiga addinin Allah jama'a-jama'a.

(3)

3. To, ka yi tasbihi da gode wa ubangijinka, kuma ka neme shi gafararsa, Lalle shi ya kasance mai yawan karb'ar tuba ne.Surar Harshen wutaDa Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin k'ai

(1)

1. Hannaye biyu na AbuLahab sun halaka, kuma ya halaka.

(2)

2. Dukiyarsa da abin da ya tara, ba su tsare masa komai ba.

(3)

3. Zai shiga wuta mai huruwa.

(4)

4. Tare da matarsa mai d'aukar itace.

(5)
5. A cikin wuyanta akwai igiyar kaba.Surar TsarkakewaDa Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin k'ai

(1)

1. Ka ce: Shi ne Allah makad'aici.

(2)

2. Allah Sid'if yake.

(3)

3. Bai haifa ba, kuma ba a haife shi ba.

(4)

4. Kuma babu wani da ya kasance tamka a gareshi.Surar AsubaDa Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin k'ai

(1)

1. Ka ce ina neman tsari ga ubangijin safiya.

(2)

2. Daga sharrin abin da ya halitta.

(3)

3. Daga sharirn dare idan ya yi duhu.

(4)
4. Daga sharrin mata masu tofi a cikin k'ulle-k'ulle.

(5)

5. Daga sharrin mahassadi yayin da ya yi hassada.
Surar MutaneDa Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin k'ai

(1)

1. Ka ce ina neman tsari ga ubangijin mutane.

(2)

2. Mamallakin mutane.

(3)

3. Abin bautar mutane.

(4)

4. Daga sharrin mai waswasi mai b'oyewa.

(5)

5. Wanda yake sanya waswasi a cikin zukatan mutane.

(6)

6. Daga aljanu da mutane.