TARJAMAR KUR'ANI MAI DARAJA
 

Hafiz Muhammad Said
hfazah@yahoo.com

KUR'ANI MADAUAKAKI:
"MU NE MUKA SAUKAR DA AMBATO KUMA MU MASU KARIYA NE GARESHI".

DAGA SURAR NABA'I ZUWA SURAR INFID'AR
Surar Fatiha

Ayoyinta 7 ne, Ana kiranta Uwar Littafi domin ta tara ilmin da yake a cikin Kur'ani a dunk'ule. Basmala a cikinta take ga k'ira'ar Asim, ruwayar Hafs, amma banda a k'ira'ar Warsh.1. Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin k'ai.2. Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai.3. Mai rahama mai jin k'ai.4. Mai mallakar ranar sakamako.5. Kai kad'ai muke bautawa kuma kai kad'ai ne muke neman taimako.


6. Ka shiryar da mu tafarki madaidaici.7. Tafarkin wad'anda ka yi wa ni'ima, ba wad'anda aka yi fushi da su ba, kuma ba b'atattu ba.

Ubangijin halittu ya tara ilmin Tafiyar da lamurran bayi da halitta su, kamar rayarwa, da matarwa, da ciyarwa, da shayarwa, da tufatarwa, Mai rahama Ya tara dukan rahamar duniya da dukkan ni'imomin samarwa gaba d'aya. Mai jin k'ai ya tara ni'imar duniya mai dogewa zuwa Lahira kamar ni'imar imani. Mai mallakar ranar sakamako, ya had'a dukan abin da ya shafi makoma. Kai muke bauta wa kuma Kai muke neman taimako, ya tara tauhidin bauta da ibada. Hanya madaidaiciya, ta had'a Littafin Allah da Ahlul Baiti (a.s) a matsayin wasiyyar Ma'aikin Allah. Wad'anda aka yi wa ni'ima, su ne Alayen Ibrahim da Alayen Muhammad (a.s). Wad'anda aka yi fushi da su, da kuma b'atattu, sun tara dukkan mutanen da suka kauce wa tafarki madaidaici.


Surar LabariDa sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai1. A kan me suke tambayar juna?2. A kan muhimmin labari mai girma?3. Wanda suke sab'a wa juna a cikinsa?4. A'aha! Za su sani.5. Kuma, a'aha! Za su sani.6. Ashe, ba Mu sanya k'asa shimfida ba?7. Da duwatsu turaku (ga rik'e k'asa)?8. Kuma, Mun halitta ku maza da mata?9. Kuma, Muka sanya barcinku hutawa?10. Kuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura?11. Kuma, Muka sanya lokacin rana na neman abin rayuwa?12. Kuma, Muka gina sammai bakwai masu k'arfi, , a samanku?13. Kuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rana(.14. Kuma, Muka saukar ruwa mai yawan zuba daga cikakkun giragizai?15. Domin, Mu fitar da k'waya da tsiri da shi?16. Da itacen lambuna masu lillibniya?17. Lalle ne, ranar rarrabewa ta kasance abin k'ayyade wa lokaci.18. Ranar da za a yi busa a cikin k'aho, sai ku zo, jama'a-jama'a.19. Kuma, aka bud'e sama, sai ta kasance k'ofofi.20. Kuma, aka tafiyar da duwatsu, sai suka kasance k'ura.21. Lalle ne, Jahannama ta kasance madakata.22. Makoma ce ga masu k'etare iyakoki.23. Suna, masu zama a cikinta, zamunna.24. Ba su d'and'anar wani sanyi a cikinta, kuma ba su d'and'anar wani abin sha.25. Sai dai tafasasshen ruwa da rub'ab'b'en jini.26. Sakamako mai dacewa.27. Lalle ne, su, sun kasance ba su fatar wani sauk'in hisabi.28. Kuma, suka k'aryata da ayoyinMu, k'aryatawa!29. Kuma kowane abu Mun k'ididdige shi, a rubuce.30. Saboda haka ku d'and'ana, domin haka ba za Mu k'ara muku komai ba sai azaba.31. Lalle ne, masu tak'awa na da wani wurin samun babban rabo.32. Lambuna da inabobi.33. Da cikakkun 'yan mata, tsaran juna.34. Da hinjalan giya cikakku.35. Ba sa jin yasassar magana a cikinta, kuma ba sa jin k'aryatawa.36. Sakamako daga Ubangijinka, kyauta mai yawa.37. Ubangijin sammai da k'asa da abin da yake a tsakaninsu, Mai rahama, ba su da ikon yin wata magana daga gare Shi.38. Ranar da Ruhi da mala'iku zasu tsaya a cikin sahu, ba sa magana, sai wanda Allah Ya yi masa izini, kuma ya fad'i abin da yake daidai.39. Wancan shi ne yini na gaskiya, to wanda ya so, ya rik'i makoma zuwa ga Ubangijinsa.40. Lalle ne, Mu, Mun yi muku gargad'in azaba makusanciya, ranar da mutum ke dubi zuwa ga abin da hannayensa suka aikata, kuma kafiri ya ce; Kaicona, da dai na zama turb'aya!
Surar Masu FizgaDa sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai1. Ina rantsuwa da mala'iku masu fisgar rayuka da k'arfi.2. Da masu d'aukar rayuka da sauk'i a cikin nishad'i.3. Da masu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo.4. Sa'an nan, su zama masu gaugawa (da umurnin Allah) kamar suna tsere.5. Sa,an nan, su kasance masu shirya gudanar da umurni.6. Ranar da mai girgiza abubuwa (busar farko) za ta kad'a.7. Mai biyar ta (busa ta biyu) na biye.8. Wasu zukata, a ranar nan, masu jin tsoro ne.9. Alhali idanunsu na k'ask'antattu.10. Suna cewa; Ashe lalle za a iya mayar da mu a kan sawunmu?11. Ashe, idan muka zama k'asusuwa rududdugaggu?12. Suka ce; Waccan kam komawa ce, tab'ab'b'iya!13. To, ita kam, tsawa guda kawai ce.14. Sai kawai ga su a bayan k'asa.15. Shin, labarin Musa ya zo maka?16. A lokacin da Ubangijinsa Ya kiraye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato D'uwa?17. Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi ya k'etare haddi.18. Sai ka ce masa, Ko za ka so ka tsarkaka.19. Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoronSa?20. Sai ya nuna masa ayar nan mafi girma.21. Sai ya k'aryata, kuma ya sab'a.22. Sa'an nan ya juya baya, yana tafiya da sauri.23. Sai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira.24. Sai ya ce; Ni ne Ubangijinku mafi d'aukaka.25. Saboda haka Allah Ya kama shi, domin azabar maganar k'arshe da ta farko.26. Lalle ne, a cikin wannan hak'ik'a akwai abin kula ga wanda yake tsoron Allah.27. Shin, ku ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta.28. Ya d'aukaka rufinta, sa'an nan Ya daidaita ta.29. Kuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta.30. Kuma, k'asa a bayan haka Ya mulmula ta.31. Ya fitar da ruwanta daga gare ta da makiyayarta.32. Da duwatsu, Ya kafe su.33. Domin jiyarwar dad'i a gare ku, kuma ga dabbobinku.34. To, idan uwar masifu mafi girma, ta zo.35. Ranar da mutum zai yi tunanin abin da ya aikata.36. Kuma, a bayyana Jahim ga mai gani.37. To, amma wanda ya yi girman kai.38. Kuma, ya zab'i rayuwar duniya.39. To, hak'ik'a Jahim ita ce makoma.40. Kuma, amma wanda ya ji tsoron tsayi a gaban Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai.41. To, lalle ne Aljanna ita ce makoma.42. Suna tambayar ka game da alk'iyama, wai yaushe ne matabbatarta?43. Me ya had'a ka da ambatonta?44. Zuwa ga Ubangijinka k'arshen al'amarinta yake.45. Kai mai gargad'i kawai ne ga mai tsoronta.46. Kamar su a ranar da za su gan ta, ba su zauna ba face a lokacin marece ko hantsinta.Surar Had'a Fuska

Tana karantar da rashin bambanci tsakanin musulmi, rik'on addini da gaskiya shi ne d'aukaka, An ce wannan sura ta sauka ne lokaci da Abdullahi bn Maktum ya zo wajen Usman sai ya d'aure fuskarsa saboda yana makaho kuma mabuk'aci

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai.


1. Ya had'a fuska kuma ya juya baya.2. Saboda makaho ya zo masa.3. To, me ya sanar da kai cewa watak'ila shi ne zai tsarkaka.4. Ko ya tuna, sai tunawar ta amfane shi?5. Amma wanda ya wadatu da dukiya.6. Sa'an nan kai kuma ka bijira zuwa gare shi!7. To, me zai cuce ka idan bai tsarkaka ba?8. Kuma, amma wanda ya zomaka yana gaugawa.9. Alhali shi yana jin tsoron Allah.10. Kai kuma ka shagala ga barinsa!11. A'aha! Lalle ne, wannan tunatarwa ce.12. Saboda wanda ya so ya tuna Shi.13. A cikin littattafai ababan girmamawa.14. Ababan d'aukakawa, ababan tsarkakewa.15. A hannayen mala'iku marubuta.16. Masu daraja, masu d'a'a ga Allah.17. An la'ani mutum (kafiri), mamakin yawan kafircinsa!18. Daga wane abu, (Allah) Ya halitta shi?19. Daga d'igon maniyyi, Ya halitta shi sa'an nan Ya k'addara shi.20. Sa'an nan Ya saukake masa hanyarsa.21. Sa'an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari.22. Sa'an nan, idan Ya so lalle ne zai tayar da shi.23. Hak'ik'a bai wada aikata abin da (Allah) Ya umurce shi ba.24. To, mutum ya duba zuwa ga abincinsa.25. Lalle ne Mu, Mun zubo ruwa, zubowa.26. Sa'an nan, Muka tsattsage kasa tsattsagewa.27. Sa'an nan, Muka tsirar da k'waya ,a cikinta.28. Da inabi da ciyawa.29. Da zaituni da itacen dabino.30. Da lambuna, masu yawan itace.31. Da 'ya'yan itacen marmari, da makiyaya ta dabbobi.32. Domin jin dad'i a gareku, ku da dabbobinku.33. To, idan mai tsawa (busa ta biyu) ta zo.34. Ranar da mutum yake gudu daga dan'uwansa.35. Da uwarsa da ubansa.36. Da matarsa da d'iyansa.37. Ga kowane mutum daga cikinsu, a ranar nan akwai wani sha'ani da ya ishe shi.38. Wasu fuskoki, a ranar nan, masu haske ne.39. Masu dariya ne, masu bushara.40. Wasu fuskoki, a ranar nan, akwai k'ura a kansu.41. Bak'i zai rufe su.42. Wad'annan su ne kafirai fajirai.Surar Kisfewa

Tana karantar da Tashin kiyama gaskiya ne, kuma Kur'ani gaskiya ne, daga Allah yake, babu ragi babu kari, ya taho ta hannun aminci daga Allah zuwa ga Annabi.Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai1. Idan aka kisfe rana.2. Kuma idan taurari suka gurb'ace.3. Kuma idan duwatsu aka tafiyar da su.4. Kuma idan rak'uma masu cikkuna aka sake su wawai.5. Kuma idan dabbobin daji aka tattara su.6. Kuma idan tekuna aka mayar da su wuta.7. Kuma idan rayuka aka aurar da su (ga matattu).8. Kuma idan wadda aka turbud'e ta da rai aka tambaye ta.9. Saboda wane laifi ne aka kashe ta?10. Kuma idan takardun ayyuka aka watsa su.11. Kuma idan sama aka fed'e ta.12. Kuma idan Jahim aka hura ta.13. Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita.14. Rai ya san abin da ya halartar.15. To, ba sai Na yi rantsuwa da taurari matafa ba.16. Masu gudu suna b'uya.17. Da dare idan ya bayar da baya.18. Da safiya idan ta yi lumfashi.19. Lalle ne shi (Kur'ani), maganar wani manzo ne mai girma.20. Mai k'arfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi.21. Wanda ake yi wa d'a'a ne, amintacce a can.22. Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne.23. Kuma lalle ne, ya gan shi a cikin sararin sama mabayyani.24. Kuma shi, ga gaibi ba mai rowa ba ne.25. Kuma shi ba maganar shed'ni abin la'ana, ba ce.26. Shin, to ina za ku tafi?27. Lalle ne shi ba komai ba ne sai ambato ga talikai.28. Ga wanda ya so daga cikinku, ya shiryu.29. Kuma ba zaku so ba sai idan Allah Ubangijin talikai ya yarda.Surar Tsagewa

Tana karantar da gaskiyar Tashin Kiyama, kuma ayyukan mutum na duniya ana tsare da su domin hisabi da sakamako.
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai1. Idan sama ta tsage.2. Kuma idan taurari suka watse.3. Kuma idan tekuna aka facce su.4. Kuma idan kaburbura aka tone su.5. Rai ya san abin da ya gabatar, da abin da ya jinkirtar.6. Ya kai mutum! Me ya rue ka game da Ubangijinka, Mai karimci.7. Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaita ka, Ya kuma tsakaita ka.8. Ya gina ka a kan kowace irin sura Ya so.9. A'aha, ba haka ba, kuna k'aryatawa game da sakamako!10. Lalle ne akwai matsara a kanku.11. Masu daraja, marubuta.12. Suna sanin abin da kuke aikatawa.13. Lalle ne, masu d'a'a ga Allah suna cikin ni'ima.14. Kuma lalle ne, fajirai, suna cikin Jahim.15. Za su shige ta a ranar sakamako.16. Ba za su faku daga gare ta ba.17. Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa ranar sakamako?18. Sa'an nan, me ya sanar da kai abin da ake ce wa ranar sakamako?19. Rana ce da wani rai ba ya iya mallakar komai domin wani rai, al'amari a ranar nan ga Allah yake.