Yazid dan Mu'awiyya, shi ma ya dauki mataki irin na ubansa akan Imam Husain (a.s.), ya kashe shi tare da mutanen gidansa, ya ribaci zuriyar Manzon Allah (s.a.w.a.) yayin da Imam Husaini (a.s.) ya jagoranci yunkurin bijirewa hukumar Banu Umayya ta zalunci da aka tilasta ta a kan al'umman musulmi.
Bayan Imam Husaini (a.s.) ya yi shahada, musulmi sun karkata hankalinsu ga Imam Ali bn Husain, Zainul Abidin (a.s.), suna ganinsa a matsayin wata alama kana kuma makoma gare su, don haka ne masu yunkuri
gwagwarmaya suke neman izininsa. Don haka ne ma a zamaninsa an sami masu jihadi domin kare Ahlulbaiti (a.s) da yawa, kamar yunkurin Madina da Makka da na Mukhtar Al-Thakafi da na Tawwabun, dukkansu suna yaki domin daukar fansa kan wadanda suka kashe Imam Husaini (a.s.). A wancan lokacin mutane suna ganin Imam Zainul Abidin a matsayin kololuwar bijirewa azzalumai duk da cewa bai motsa ba. Matsayin da ya dauka kan Yazid bn Mu'awiyya da Marwan bn Hakam da Abdul Malik bn Marwan da sauran azzaluman mahukunta, matsayi ne na mai bijirewa a asirce da taimakon masu yunkuri ba tare da shelar hakan ba. har ma Imam (a.s.) ya roki rahamar Allah ga Mukhtar, wanda ya dauki fansa kan wadanda suka kashe Imam Husaini (a.s.) ya kuma yaba da jihadin Mukhtar. Sannan kuma Imam (a.s.) ya yi amfani da makamin addu'a([239])(*) mai bayyana irin ra'ayinsa na siyasa da akida, mai sabawa da ra'ayin su Yazid.
Imam Bakir (a.s.) dan Imam Zainul Abidin (a.s.) shi ma ya nuna matsayin da yake kai na bijirewar siyasa daga Banu Umayya. Imam ya sha wahala kwarai a hannunsu, musamman ma Hisham bn Abdul Malik mai bayyana kiyayya da gaba ga Alawiyyawa. A zamaninsa ne Zaid bn Ali dan uwan Imam Bakir (a.s.) ya fito jihadi.
Shi dai wannan halifa na Banu Umayya ya tabbatar cewa tushen wannan yunkuri na Zaid daga Imam Bakir da dansa Ja'afar Sadik (a.s.) yake. Don haka sai ya kira su daga Madina zuwa ga helkwatarsa da ke Sham, yayin da Imam Bakir (a.s.) ya shiga fadar Hisham sai ya yi sallama yana nuni zuwa ga mahalarta majalisar, amma bai yi gaisuwar sarauta ga halifan ba. Sai Imam ya zauna ba tare da da wani izinin sarki ba, hakan ya kara wa Hisham kiyayyarsa ga Imam har ma ya kama sukansa da cewa:
"Ya Muhammad bn Ali, ko yaushe sai an sami wani mutum daga cikinku yana raba kan musulmi, da kiran jama'a don su bi shi, domin wauta da karancin ilmi".
Sai Hisham ya ci gaba da suka, jama'ar da ke fada su ma suka fara sukar Imam din bayan Hisham ya yi shiru. Da ganin wannan ka san cewa an umurce su da hakan ne kafin ma Imam din ya shigo tare da dansa, Imam Sadik (a.s.). Ganin haka ke da wuya, sai Imam Bakir (a.s.) ya mike tsakiyar majalisar yana mai raddi ga sarki da cewa:
"Ya ku mutane! Ina kuke zuwa ne? Ina aka nufa da ku ne? Da mu Allah Ya shiryar da farkonku, da mu kuma Zai cika (shiryar) da na karshenku. Idan kuna da mulki abin gaggautarwa, to mu muna da mulki da aka jikirta, kuma babu wani mulki bayan namu, domin mu ne masu mulkin karshe".
Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: "Kuma kyakkyawan karshe tana tabbata ga masu tsoron Allah". (Surar A'araf, 7: 128). Jin haka, ya sa Hisham ya tsare shi ([240]).
To a cikin kurkukun ma Imam Bakir (a.s.) bai yi shiru ba, ya wayar da kan fursunoni kan batutuwan siyasa da jihadi har fursunonin suka sami tasirin wa'azinsa, inda suka tayar da hargowa a cikin kurkukun. Ganin haka, sai shugaban kurkukun ya isar da lamarin zuwa ga Hisham, inda shi kuma ya yi umarni da a fitar da Imam (a.s.) daga kurkukun a mai da shi birnin Madina, a hannun wani dan aiken sarki ([241]).
Muhammad bn Jarir Tabari ya rubuta cewa dalilin da ya sa aka mai da Imam Bakir (a.s.) zuwa Madina shi ne bazuwar tasirinsa kan tunanin mutanen Sham sakamakon wata muhawara da ta gudana tsakaninsa da wani shugaban kiristoci([242]).
A wata muhawara da ta gudana tsakanin Hisham bn Abdul Malik da Zaid, a lokacin da labarin yunkurin Zaid din ya isa kunnen Hisham, Hisham ya ce da Zaid: "Na sami labarin kana ambaton halifanci kuma kana burinsa, alhali kai ba ka cikin mazowansa, kuma kai dan baiwa ne".
Sai Zaid ya mayar masa da martani da cewa, Annabi Isma'il dan baiwa ne kuma Allah Ta'ala Ya ba shi annabta. Sannan Hisham ya dora ambaton Imam (a.s.) da zagi, yana mai tambayan Zaid da cewa:
"Dan'uwanka Bakara kuwa...", sai Zaid ya amsa masa da cewa: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ambace shi da Al-Bakir([243])(*) kai kuma ka kira shi da Bakara (wato saniya), lalle sabaninka da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi yawa kuma za ka saba da shi a ranar lahira kamar yadda ka saba da shi a nan duniya, domin Annabi (s.a.w.a) zai shiga aljanna kai kuwa za ka shiga wuta". To wannan shi ne matakin da Imam Bakir (a.s.) ya dauka da kuma yunkurinsa na siyasa, har lokacin da ya yi shahada.
To daga nan sai zamanin dansa Imam Ja'afar Sadik (a.s.), a wannan lokaci na Imam Sadik (a.s.) kuwa bala'i ya yawaita kan al'ummar Annabi (s.a.w.a), ya kuma fi tsanani kan Alayensa (s.a.w.a). Imam Sadik (a.s.) ya kasance shi ne jagoran bijirewa azzalumai ta hanyar siyasa duk da yake bai yi magana bayyananniya kan masu iko ba. Masu yunkuri suna neman shawararsa da goyon bayansa, kai har da neman ya karbi jagorancin harkar, kamar yadda Abu Muslim Khorasani ya bukata yayin da ya mika mubaya'arsa ga Imam. Imam Sadik (a.s.) ya ki karbar wannan mubaya'a saboda rashin cikar sharudda da kasantuwar yanayi bai dace ba, kamar dai yadda ya yi lokacin yunkurin Zaid a zamanin Hisham bn Abdul Malik Ba'umayye.
Abul Abbas Saffah ya yi kokarin kashe Imam domin saninsa da mukaminsa na jagoranci da goyon bayansa ga bijirewa mahukunta. To amma Allah Ya kare shi daga sharrinsa, duk kuwa da cewa ya taba kiran Imam din daga Madina zuwa garin Hira da ke kasar Iraki, inda ya tsananta masa da kuma sanya shi karkashin 'yan leken asiri.
Yayin da Abu Ja'afar Mansur ya gaji Al-Saffah, shi ma ya ji tsoron matsayin Imam Sadik (a.s.) kamar yadda magabatansa suka ji, sau da yawa ya kan kira Imam (a.s.) daga Madina zuwa Iraki.
Ga yadda yake siffanta karfin Imam a fagen siyasa da tasirinsa kan masu gwagwarmaya, inda ya ke cewa: "Wannan bakin cikin (yana nufin Imam Sadik) da rike makoshin halifofi, korarsa ba ta halalta, kisan sa ba ya halalta. Ba don mun hadu da shi a bishiya mai kyakkyawan tushe, mai rassan da suka gabata, mai dadadan 'ya'ya, an kuma albarkaci zuriyarta aka tsarkake ta cikin Littattafai ba, da an sanya shi cikin mummunan karshe, saboda labarin da muka samu na tsananin aibantamu da mummunan magana da yake fada game da mu ([244])". Wannan shi ne matsayin Imam Sadik (a.s.) da aikin da ya yi na bijirewa azzaluman mahukunta, da goyon bayan masu yunkurin kawo gyara.
Daga nan sai zamanin Imam Musa bn Ja'afar Kazim (a.s), dan Imam Sadik (a.s.), a lokacinsa cutar da musulmi da karkata addini da kwadaitar da mutane da dukiya sun tsananta a hannun Abbasiyawa. Don haka ne Imam (a.s.) ya kasance jogora wajen gyaran al'amarin Musulunci.
An sanya Imam (a.s.) karkashin leken asiri a zamanin Mansur wanda shi ya kai matuka wajen zaluntar Alawiyyawa da kwace dukiyoyinsu, da gina turakun gadoji da kadarkai da soraye a kansu da ransu, da azabtar da su cikin kurkuku.
To amma bayan da Muhammad Al-Mahdi ya gaji sarautar Abbasiyyawa sai tsoransa ga Imam Kazim ya yi tsanani, don haka sai ya kirayi Imam (a.s.) daga Madina zuwa Bagadaza domin ya hukunta shi. Al-Mahdi ya sa aka rufe Imam Kazim (a.s.) a kurkuku har zuwa wata rana da halifan ya ga Imam Ali bn Abi Talib (a.s.) a mafarko yana ce da shi: "To, shin, kuna fatan idan kun juya za ku yi barna a cikin kasa, kuma ku yanyanke zumuntarku?" (Surar Muhammadu, 47: 22). Wannan sai ya tsoratar da Mahdi ya fitar da Imam Kazim (a.s.) daga kurkuku.
A mulkin Al-Hadi, sarkin Abbasiyawa, ne bala'i ya tsananta kan Imam (a.s.) da kuma Alu Ali (a.s.). Ya ci gaba da korarsu da kashe su da neman batar da su gaba daya musamman ma bayan yunkurin Husain bn Ali wanda aka fi sani da waki'ar Fakh. Imam Kazim (a.s.) ya gamu da tsanantarwa da matsarwa har sai da ta kai Al-Hadi din ya hukumta Imam (a.s.) da hukumcin kisa ya kuma tasanma aiwatar da hakan. Malaman tarihi sun ruwaito cewa alkali Abu Yusuf almajirin Imam Abu Hanifa shi ne ya shiga tsakanin Al-Hadi da wannan kuduri da ya dauka na kashe Imam Kazim (a.s.), don Al-Hadin ya zaku kan kashe Imam (a.s.) har cewa ya yi: "Allah ya kashe ni idan na yi wa Musa ibn Ja'afar afuwa".
Daga nan sai Al-Hadi ya sanya Imam Kazim (a.s.) a kurkuku da hana shi damar gudanar da aikinsa na ilmantarwa da jagoranci a bayyane. Amma mutuwa ba ta bar shi ya aikata mummunan nufinsa, don kuwa ta kawo karshen wannan azzalumi jabberi.
Daga nan sai lokacin Haruna Rashid wanda aka sami jayayya mai tsananin gaske tsakaninsa da Imam Kazim (a.s.). Haruna Rashid ya yi kiran Imam da ya taho daga birnin Madina zuwa Iraki, inda ya ci gaba da tozarta shi da sanya shi a kurkuku da azabtarwa nau'i daban-daban, wadanda suka hada da daure shi da karfe yana daukansa daga wannan kurkukun zuwa wancan. Imam (a.s.) ya zauna a kurkuku tsawon shekaru, daga karshe Haruna Rashid ya ci da shi guba ta hannun shugaban dogarawan-sa mai suna Al-Sandi bn Shahik. Imam (a.s.) ya yi shaha-da ne a ranar 25 ga watan Rajab a shekara ta 183 bayan hijira.
Daga nan sai zamanin Imam Ridha, Aliyu bn Musa bn Ja'afar (a.s.), wanda shugabancinsa na siyasa ya wajabtawa Abbasiyawa la'akari da shi a sakamakon karfin alkadarin Imam (a.s.) da kaunar al'umma gare shi ga kuma tsanantar bijirewa ga Abbasiyawa. Wannan yanayi ya tilastawa halifan Abbasiyawa Ma'amun sanya Imam (a.s.) a matsayin magajinsa. Imam Ridha (a.s.) ya karbi wannan matsayi ba don sonsa ba, kana kuma da sharadin cewa shi ba zai shiga harkokin shugabanci ba, sannan idan Ma'amun ya mutu, halifanci zai koma hannunsa. To amma Imam Ridha (a.s.) ya yi shahada yayin da Ma'amun ya ba shi guba a shekara ta dari biyu da uku bayan hijira.
To bayan shahadar Imam Ridha (a.s.), wanda ya karbi jagoranci al'umma da lamarin Imamanci shi ne dansa Imam Muhammad Jawad (a.s.) wanda ya yi zamani da Ma'amun na dan lokaci. Ma'amun ya yi mu'amala da shi da girmamawa a munafunce, ya aurar masa da 'yarsa Ummul Fadhl domin ya sami soyayyar al'umma, yayi hakan ne kuwa domin ya juya hankulan mutane ya karkata ra'ayin masu gaba da shi, wadanda suke ganin Imam (a.s.) a matsayin jagora. Sai dai fa Ma'amun bai tsinana komai ba domin Imam Jawad (a.s.) ya bar Bagadaza ya koma birnin Kakansa Manzon Allah (s.a.w.a.) saboda ci gaba da aikinsa na ilmantarwa da jagorancin al'umma a can.
To bayan da Ma'amun ya mutu sai dansa Al-Mutasim ya hau karagar mulkin Abbasiyawa, sai dai kuma shi Al-Mutasim bai jima a kan mulkin ba, to amma dai shi ma ya kasance yana jin tsoron Imam Jawad (a.s.) da kuma hadarin zamansa a Madina. To shi ma Al-Mutasim bai yi wata-wata ba sai ya kama tafarkin iyayensa yayin da ya dauko Imam daga Madina ya kawo shi helkwatarsa domin ya sanya ido a kansa. Marubuta tarihi sun ce Imam Jawad (a.s.) ya yi shahada ne a hannun Mutasim ta hanyar guban da ya sa masa cikin abinci a shekarar da ya kawo shi Bagadaza a lokacin kuwa hijira tana da shekara dari biyu da ashirin da biyar.
To bayan shahadar Imam Jawad (a.s.) dansa Imam Ali Hadi shi ne ya gaji jagorancin al'umma da Imamanci daga mahaifin nasa. A zamanin Mutawakkil Abbasi ne Imam Hadi (a.s.) ya fuskanci keta da cutarwar Abbasiya-wa. Mutawakkil da ma sananne ne da son wasa da kuma gaba da Alayen Manzon Allah (s.a.w.a.) da kashe su da korar su da yanke abincinsu da hana mutane taimakonsu. Imam Hadi (a.s.) ya kasance yana tsorata halifa Mutawakkil saboda haka sai ya dauko shi daga Madina ya kai shi garin Samarra ya sa ido sosai a kansa, ya kuma tilasta masa zama a can. To lokacin da al'amurra suka yi zafi wa Mutawakkil, sai ya fara barazanar kisa ga Imam Hadi (a.s.) baya ga daure shi da ya sha yi. A wasu lokuta ya kan sa a binciki gidan Imam Hadi (a.s.) da kai hari wa gidan, bugu da kari kan tsananta sanya ido a kansa saboda tsoron irin tasirin da Imam (a.s.) yake da shi a idon al'umma.
Marubuta tarihi sun ambaci dalilan da suka sa Mutawakkil ya ta da Imam Hadi (a.s.) daga Madina. Sibt Al-Jawziyya ya ce: "Malaman tarihi sun ce: Ya fito da shi daga Madinar Manzon Allah (s.a.w.a.) zuwa Bagadaza ne don yana tsananin kin Aliyu da zuriyarsa sai kuma ya sami labarin irin matsayin Aliyu Hadi a Madina da karkatar mutane zuwa gare shi. Wannan ya sa shi tsoronsa([245])".
Bayan shahadar Imam Hadi (a.s.) garin Samarra a shekara ta 254 bayan hijira, sai dansa Imam Abu Muhammad Hasan Askari (a.s.) ya kasance Imami mai kula da harkar al'umma da kuma shiryar da su. To shi ma dai matsayinsa kan Abbasiyawa tamkar na iyayensa ne, wajen fito-na-fito a fagen siyasa. To shi ma dai mahu-kumtan ba su bar shi don kuwa sun cutar da shi kamar yadda suka cutar da mahaifansa. Al-Muhtadi bn Al-Wasik sarkin Abbasiyawa ya sanya shi a kurkuku a garin Samarra, inda ya mika shi ga hannun gandurobobin kurkukun wadanda suka shahara da mugun hali da zalunci don azabtar da shi, amma Imam (a.s.) ya yi tasiri kansu har suka shiryu suka zamo mutanen kwarai.
Malaman tarihi sun kiyaye abubuwan da suka sami Imam Hasan Askari (a.s.) na matsanancin bala'i, kamar abin da Ahmad bn Muhammad ya ruwaito, inda ya ce:
"Yayin da Al-Muhtadi da fara kashe magoya bayan Ahlulbaiti (a.s) sai na rubuta wa Abu Muhammad Hasan Askari (a.s.) na ce masa: Ya shugabana, godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya shagaltar da shi (Muhtadi) daga barinka. Hakika na sami labari cewa yana maka barazana da cewa: "Wallahi sai na kore su daga duk sababbin kasashe", sai Abu Muhammad (a.s.) ya rubuta da hannunsa cewa: "Wannan shi zai takaita rayuwarsa([246])".
An ruwaito cewa, Imam Askari (a.s.) ya kasance cikin kurkuku a zamanin Al-Mutamad har lokacin da ya kira shi don warware wata matsala da ta faru tsakanin musulmi da wani malamin Nasara, a kan shayarwa (ruwan sama). Sai Imam (a.s.) ya warware ta, to a saboda haka Al-Mutamad ya fito da shi daga kurkukun kuma ya nemi a saki mabiyansa da ke tare da shi a kurkuku, hakan kuwa aka yi, wato a ka sake su.
Wannan shi ne kadan daga tarihin Ahlulbaiti (a.s) a fagen siyasa da fito-na-fiton da suka yi da hukumomin zalunci na lokacinsu wadanda suka doru a kan al'umma. Idan an duba da kyau za a ga cewa, silsilar Imamai goma sha daya mai albarka ta Ahlulbaiti (a.s) ta kasance wani fage ne na jagorantar al'umma da kuma shiryar da su. Don kuwa kowane Imami za a ga shi ne jagorar al'um-mar da ya kasance a cikinta, wanda kuma ya fi kowa ilmi da sanin ya kamata. Irin wannan tsari ba zai yiyu a same shi ba sai da shiri gabatacce daga Allah Ta'ala. Kuma babu makawa wannan bibiya ta jagorancin Ahlulbaiti (a.s) yana sanar da mu mukaminsu da fagensu na shugabancin akida da siyasa a rayuwar wannan al'umma.

Dubi Cikin Mazhabobin Fikihu
A zamanin Manzon Allah (s.a.w.a.) musulmi suna samun hukumce-hukumce da dokoki masu tsara al'amurransu na zamantakewa da ibada, kamar su salla, rabon gado, zaman iyali, kasuwanci, jihadi, aikin hajji da abin da ya shafi kasa da filaye da shari'u da sauransu ne kai tsaye daga Annabi (s.a.w.a), domin shi ne mai isar da sako, mai kira zuwa ga shiriya ta hanyar wahayi.
Bayan da ya koma ga Ubangijinsa Mahalicci, al'ummar musulmi sun koma ga Littafin Allah da Sunnar Ma'aiki (s.a.w.a.), suna daukar dokoki da sanin ra'ayin shari'a kan dukkan abubuwan da suka shafe su ta hanyar sahabbai da Ahlulbaiti (a.s), wadanda suka kiyaye Sunna da kuma Littafin Allah. Daga nan al'ummar musulmi ta sami ci gaba cikin salon rayuwa, saboda faruwar sabbin abubuwa cikin rayuwar mutane. Babu shakka wadannan sabbin abubuwa suna bukatar hukumcin Musulunci da sanin dokokin shari'a domin daidaitasu. Wannan fadada-wa cikin shari'a ya fara samuwa kusan a karshen karnin farko a zamanin Imam Muhammad Bakir (a.s.), wanda shi ne malamin Madina, kuma mokamar dukkan malaman zamaninsa. Malaman tarihi da na fikihu sun ruwaito cewa saboda hakan ne ma ake kiransa da Al-Bakir, domin fadadawarsa wajen ilmomi da yada su. A zamanin dansa Imam Ja'afar Sadik (a.s.) ne fannonin ilmi da fikihu da shari'a suka yi fure, yayin da shugabannin mazhabobi suka yi karatu a wajen Imam Sadik (a.s.) din. Da shi babansa Imam Bakir (a.s.) sun kasance masu ruwaito Sunna ne da kuma bayanin abin da Littafin Allah da sunnar suka kunsa, ba wai masu ijtihadi ba ne su.
A zamanin Imam Sadik ne aka fara samun mazhabobin fikihu kamar masu bin ra'ayi da kiyasi, wato mazhabar Imam Abu Hanifa, wanda ya yi karatu na wani lokacin a wajen Imam Sadik (a.s.) da sauran mazhabobi, wadanda daga baya suka takaitu cikin mazhabobi guda hudu, wato: Mazhabobin Malikiyya, Hannifiyya, Shafi'iyya da kuma Hambaliyya. Wadanda su ma wadannan mazhabobi sun rarrabu a tsakaninsu a wajen tafarkin Ijtihadi da yarda da wata ruwaya, a gefe guda kuma ga mazhabar nassi wacce Imam Sadik (a.s.) yake jagoranta, wacce ta dogara da Littafin Allah da Sunnar Annabi (s.a.w.a) wajen fitar da hukumce-hukumcen Musulunci, sannan kuma take watsi da ra'ayi da kiyasi. A daidai lokacin da kuma sauran mazhabobin suka sanya wasu hanyoyi da gano shari'a bayan Littafin Allah da Sunna, kamar su:
1. Kiyasi.
2. Istihsan (ganin dacewar ko kyaun abu)
3. Masalihul Mursala (maslahar al'amari)
4. Fathul Zara'i'i wa sadduha (bude kofar hanzari da rufe ta)
Mazhabobin Ahlussunnan nan guda hudu, Hanafiyya, Malikiyya, Hambaliyya da Shafi'iyya sun sassaba kan karbar wadannan hujjoji, ba su hadu gaba daya akansu ba. Za ka ga wasunsu suna tabbatar da wannan su yi watsi da wancan daga cikin hujjojin (hanyoyin samun hukumci).
A dalilin sassabawa wajen dauka ko watsi da wasu hujjoji mazhabobin fikihu guda hudun nan suka sami sabani tsakaninsu kuma suka saba da mazhabar nassi wacce A'imman Ahlulbaiti (a.s) suke jagoranta. Kuma a dalilin hakan ne mazhabobin nan biyar suka sassaba ka bayanan hukumce-hukumcen filla-filla. Wannan sabanin yana komawa ne ga abubuwa na tushe guda biyu, su ne:
1. Rikon wasu hujjojin (na fitar da hukumcin shari'a) daban tare da Alkur'ani da Sunna da sashen mazhabobin suka yi da kuma rashin riko da su a wajen wani sashen.
2. Sassabawa wajen karbar sashen ruwayoyi (hadisai) ko watsi da su domin dogaro da sharuddan karbar hadisi da gaskata sashen maruwaita ko a'a.
A sarari yake cewa sabanin da ke tsakanin mazha-bobin Musulunci, sabani ne na ilmi wanda bai kamata ya raba musulmi ba, ko ya nisanta tsakaninsu. Domin abin lura shi ne ana iya magance irin wannan sassabawa ta hanyar muhawara da bincike mai tsabta wanda babu son zuciya ciki. Wajibi ne irin wannan bincike a yi shi karkashin ginshikin ilimi yardaddu ga dukkan musulmi, tare da bude kofar ijtihadi wacce take rufe a wurin wasu mazhabobi. Yana da muhimmanci a gane cewa wannan sabani ba tsakanin Sunna da Shi'a yake ba, sai dai ya wanzu ne tsakanin mazhabobin fikihu kamar guda shida: Hanafiyya, Malikiyya, Shafi'iyya, Hambaliyya, Ja'afariyya da Zaidiyya, a kara kuma da ra'ayoyi da ijtihadin sashin malaman fikihu ko cikin wadannan mazhabobi ambatattu ko waje da su.
Yayin da aka bude kofar ijtihadi wa dukkan sassan musulmi, malaman fikihu kuma suka karbi aikinsu da aka sansu da shi, to za a iya iyakance ginshikan istinbadi (tsamo hukumci daga Alkur'ani da hadisi ko dai wani tushe na shari'a) da ayyana ko mene ne mabubbugan shari'a da kuma hanyar ciro hukumce-hukumce daga mabubbugar nan na tushe (wato Alkur'ani da Sunna). Domin ta hanyar komawa garesu su biyun da kokkofin ruwayoyi da hadisai da zubar da wadanda ba su inganta ba daga cikinsu, ba tare da son kai ko karkata ga wani ra'ayi ba, to musulmi za su iya yin watsi da mafi yawan sabanin da yake tsakaninsu, kuma za su iya gane abin da yake shi ne dai-dai, kuma su iya hade kansu waje guda. Duk da haka, irin ra'ayoyi da mahanga na ilmi da malaman fikihu suke da su za su wanzu, kamar yadda yake tsakanin malaman fikihu na ko wacce mazhaba ta Musulunci, kuma wannan wata dabi'a ce ta ilimi a duk wani fagen ilmi da ka sani a rayuwar dan'Adam. Saboda ba makawa a sami ra'ayoyin malamai a fagen ijtihadi da istinbadi domin malaman fikihu ba za su iya gano ainihin hukumce-hukumcen Ubangiji dukkansu gaba daya ba. Dole a samu mujtahidi (mai yin ijtihadi) yana dacewa yana kuskure kuma shi abin yi wa uzuri ne da kuma sakantawa da lada matukar ya yi bincikensa bisa tushen ilmi da ingantacciyar hanya ta shari'a.
Ga wasu misalan yadda ra'ayoyin malaman fikihu suke dacewa ko sassabawa, ba kuma tare da la'akari da ko daga Shi'a ko Sunna suke ba:
Imamiyya da Hambaliyya sun ce: Tahiyar farko wajiba ce a salla, amma Hanafiyya da shafi'iyya da Malikiyya sun ce mustahabi take ba wajiba ba. Amma tahiya ta karshe kuwa wajiba ce a ganin Shafi'iyya da Imamiyya da Hambaliyya, amma Malikiyya da Hanafiyya sun ce mustahabi ce .
Batun sallama kuwa, Shafi'awa da Malikawa da Hanbalawa sun ce wajiba ce, Hanafawa kuma suka ce ba wajiba ba ce. To amma Imamiyya kuma sun saba, wasu suna cewa wajiba ce, saura kuwa suka ce mustahabi ce. Daga cikin masu cewa mustahabi ce kawai har da Shaikh Mufid, Shaikh Tusi da Allama Hilli([247]).
Dangane da sallar jam'i kuwa, Hanbalawa sun ce wajiba ce, wajibcin kuwa kan kowane mukallafi ne idan har zai iya, amma idan ya bar jam'i ya yi salla shi kadai, to ya yi zunubi, amma sallar tasa ta inganta. Imamiyya da Hanafiyya da Malikiyya da mafiya yawa cikin Shafi'awa sun ce ba ta wajaba wajibci na aini (wanda dole kowa ya yi) ko ma na kifaya (wanda wani yake dauke wa wani) ba, sai dai mustahabi ce mai karfi.
Kan cancantar zakka kuwa, shafi'awa da Hanbalawa sun tafi a kana cewa wanda ya mallaki rabin abin da zai ishe shi, ba a sa shi cikin fakirai, ba ya halalta a ba shi zakka. Imamiyya da Malikiyya suka ce fakiri a shar'ance shi ne wanda bai mallaki abin da zai biya bukatunsa da na iyalansa a shekara ba. Saboda haka duk wanda ke da wata gona ko kaddara ko dabbobi amma ba za su biya bukatun iyalansa tsawon shekara ba, to ya halalta a ba shi Zakka.
Imamiyya da Shafi'iyya da Hambaliyya sun ce wanda yake da ikon nema ba ya halalta ya karbi zakka. Hanafawa da Malikawa kuma suka ce ya halalta kuma ana iya ba shi.
Kan kwana a Muzdalifa a yayin aikin hajji kuwa, Hanafiyya da Shafi'iyya da Hanbaliyya sun ce wajibi ne a kwana a can, wanda ya bar shi sai ya yi yanka (haka Al-Mugni ya kawo). Imamiyya da Malikiyya kuwa suka ce bai wajaba ba, amma shi ya fi.
Wajen jifa a Jamratul Akba kuwa, Malikiyya da Hanafiyya da Hambaliyya da Imamiyya suka ce bai halalta a yi jifa gabannin alfijir ba, idan kuwa aka yi hakan ba da wani uzuri ba, sai an sake. Sai dai sun halalta gabatarwar domin uzurai kamar gajiyawa ko rashin lafiya ko tsoro. Shafi'awa kuwa suka ce babu laifi a yi jifa gabannin alfijir domin lokacin da aka ambata na mustahabbanci ne ba wajibci ba (Al-Tazkira da Bidaya na Ibn Rushdi).
Kan daurin aure Imamiyya da Hambalawa da Shafi-'awa cewa suka yi ba ya halalta a daura aure da rubutu, watau dole ne a yi da baki. Hanafawa suka ce yana inganta idan mai neman aure da wacce ake nema ba sa guri guda.
Shafi'awa da Malikawa suka ce: waliyi na iya aurar da baliga shiryayya idan budurwa ce ko ba da yardarta ba. Idan kuwa bazawara ce, to sai da yardar ta, ba zai gudanar da daura mata aure shi kadai ba, ita ma haka. Ko da yake wajibi ne shi zai yi siga, ita ba za ta iya siga ba.
Hannafawa kuwa suka ce baliga mai hankali tana iya zabin miji da siga da kanta, budurwa take ko bazawara, ba wanda yake da walicci a kanta ko hakkin sabawa zabinta da sharadin ta zabi mutumin da ya yi daidai da ita, kuma kada ta yi aure da mafi karanci daga sadakin tamkarta.
Mafi yawan malaman Imamiyya sun ce baliga shiryayya tana da mallakar dukkan lamurran da suka shafi kulla wata yarjejeniya har da na aure, budurwa take ko bazawara, hakan kuwa saboda balaga da kuma shiryuwarta ne. Tana iya daura aure wa kanta ko waninta, ko ta yi da kanta ko da wakili, ko ta bayar ko karba. Ita kamar namiji take ba tare da wani bambanci ba .
Batun sakin aure kuwa, Abu Zuhra ya fada cikin littafinsa Ahwalul Shaksiyya shafi na 283 cewa: "A mazhabar Hanafiyya saki yana aukuwa ne daga kowani mutum idan ba yaro ko mahaukaci ko mai raunin hankali ba, saboda haka saki yana aukuwa daga mai wasa ko mai maye daga abin da yake haram, ko wanda aka tilasta". A shafi na 286 ya ce: "Tabbatacce yake a mazhabar Hanafiyya cewa sakin wanda ya yi kuskure ko mantuwa yana aukuwa"([248]).
A shafi na 284 kuma ya ce: "Malik da Shafi'i sun dace da Abu Hanifa da mutanensa kan batun sakin mai wasa, Ahmad ya saba da shi, yana ganin rashin aukuwar sakin". Imamiyya sun ruwaito daga Ahlulbaiti (a.s) cewa: "Babu saki sai ga wanda ya nufi sakin".
Dangane da iddar macen da ta yi zina kuwa: Hanafawa da Shafi'awa da mafiya yawa daga Imamiyya sun ce: Idda ba ta wajaba domin zina, domin ruwan (maniyyin) mazinaci ba shi da wata alhurma (girmama-wa). Saboda haka ya halalta a daura aure wa macen da ta yi zina, da kuma ingancin takar ta ko da tana da ciki. Amma Hanafawa sun haramta takar mai ciki sai ta haihu duk da yake ana iya daura mata aure.
Malikawa kuwa sun ce: Wanda ya yi zina da mace tamkar takan ta ne cikin rashin sani, dole ne ta yi istibra'i gwargwadon idda sai fa idan ana nufin tsayar da haddi kanta ne, a nan kam sai ta yi istibra'i da haila guda. Hanbalawa kuwa suka ce: Idda wajiba ce kan mazinaciya kamar yadda take kan sakakka (AlMugni, juzu'i na 6 da kuma Majma'ul Anhar)
Kan batun wasiyya ga ciki (wato dan da ke cikin ciki) kuwa, malaman fikihu sun saba kan cewa shin dole ne a samu cikin yayin wasiyyar ko kuma a'a.
Imamiyya da Hanafiyya da Hambaliyya da Shafi'iyya bisa mafi ingancin zantuttukansu sun ce ana shardanta hakan, kuma cikin ba ya gado sai idan an san cewa samamme ne yayin wasiyyar. Ana tabbatar da hakan ne, idan matar ta haihu kafin wata shida bayan an yi wasiyyar idan tana da miji mai iya saduwa da ita. Idan kuwa ta haihu bayan wata shida ko fiye, to ba a bai wa ciki kome daga cikin wasiyyar saboda yiyuwar samuwar sabon ciki. Tushe shi ne rashin samuwar ciki yayin da aka yi wasiyyar. Wannan kauli kuwa ya ginu ne kan rashin halalcin wasiyya wa wanda ba samamme ba.
Malikawa kuwa sun ce: Wasiyya tana inganta wa cikin da yake samamme ne da wanda zai samu nan gaba, domin suna ganin halalcin wasiyya wa wanda ba samamme ba. (Dubi Tazkiratul Hilli da Fikihu ala Mazahib Al-Arba' da litattafan fikihu na Hanbaliyya da dama a babin wasiyya).
Wadannan misalai ne 'yan kadan daga fikihu idan an kwatanta mazhabobin Musulunci da junansu. Muna iya ganin yadda wasu mazhabobi suka dace ko suka saba da juna a mas'alolin hukumce-hukumce. Za a ga Malikiyya da Shafi'iyya sun dace da Imamiyya, su saba da Hanafiyya da Hambaliyya, ko Hanafiyya ko Hambaliyya su dace da Imamiyya, su saba da sauran mazhabobi Ahlussunna, da dai sauran irin wannan. Saboda haka sassabawa ba ta dogara da kasancewa cikin Sunna ko Shi'a, sassabawar ta ilimi da tunani, ba sabawar Sunna da Shi'a ba ce, ko kusa, sai dai sabawa ce ta tsarin ilmin ciro hukumce-hukumce na mazhabobin nan biyar. Saboda haka ya zama wajibi a kan mu mu tantance dalilai na shari'a ta hanyar tattaunawa ta ilmi domin isa ga dacewa, sabili da hukumcin Allah dai daya ne akan kowace mas'ala.
Masu kokarin nuna cewa sabanin da ke akwai tsakanin Sunna da Shi'a tamkar ya mai da su kishiyoyi masu jayayya tsakanin juna, ba abin da suke yi sai karkata gaskiya da nisantar tsarin kubutaccen tattaunawa ta ilmi. Babu abin da suke yi sai aiki wa abokan gaban musulmi ta hanyar wargaza hadin kan musulmi.

Musulmi Al'umma Ce Guda
"Kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kuma kada ku rarraba. Kuma ku tuna ni'imar Allah a kanku, a lokacin da kuka kasance makiya, sai Ya sanya soyayya a tsakanin zukatanku, saboda haka kuka wayi gari, da ni'imarSa, 'yan'uwa. Kuma kun kasance a kan gabar rami na wuta, sai Ya tsamar da ku daga gare ta. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ayoyinsa, tsammaninku, za ku shiryu # Kuma wata jama'a daga cikinku, su kasance suna kira zuwa ga alheri, kuma suna umurni da alheri, kuma su na hani daga abin da ake ki. Kuma wadannan su ne masu cin nasara # Kuma kada ku kasance kamar wadanda suka rarrabu, kuma suka saba wa juna, bayan hujjoji bayyanannu sun je musu, kuma wadannan suna da azaba mai girma". (Surar Aali Imrana, 3: 103-105)
"Saboda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini, kana mai karkata zuwa ga gaskiya, halittar Allah da Ya halitta mutane a kanta. Babu musanyawa ga halittar Allah, wannan shi ne addini madaidaici, kuma amma mafi yawan mutane ba su sani ba # Kuma masu mai da al'amari gare Shi kuma ku bi Shi da takawa, kuma ku tsayar da salla, kuma kada ku kasance daga mushirikai # Watau wadanda suka rarrabe addininsu, kuma suka kasance kungiya-kungiya, kowace kungiya tana mai farin ciki da abin da ke a gare ta kawai. (Surar Rum, 30: 30-32)
"Kuma abin da kuka saba wa juna a cikinsa, ko mene ne, to hukumcinsa (a mayar da shi) zuwa ga Allah. Wancan Shi ne Allah Ubangijina, a gare Shi na dogara, kuma zuwa gare Shi nake mayar da al'amarina. (Surar Shura, 42: 10)
"Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi da'a ga Allah, kuma ku yi da'a ga ManzonSa da ma'abota al'amari daga cikinku. Idan kun yi jayayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa idan kun kasance kuna imani da Allah da Ranar Lahira. Wannan ne mafi alheri, kuma mafi kyau ga fassara". (Surar Nisa'i, 4: 59) "Kuma lalle ne wannan al'ummarku ce, al'umma guda, kuma Ni, Ubangijinku ce, sai ku bi Ni da takawa". (Surar Mu'uminun, 23: 52)
"Kuma ku yi da'a ga Allah da MazonSa, kuma kada ku yi jayayya har ku raunana kuma karfinku ya kau, kuma ku yi hakuri, lalle ne Allah Yana tare da masu hakuri". (Surar Anfal, 8: 46)
Tun al'ummar musulmi tana jaririya a hannun Manzon Shiriya, Muhammadu (s.a.w.a), abokan gaban musulmi daga masu bautar gumaka da yahudawa da nasara da munafukai da masu neman fadanci domin arzurta kansu, suke kokarin kekketa al'ummar da hura wutar sabani da rarraba. Hakika da'awar Musulunci a karkashin jagorancin Manzon Allah (s.a.w.a.) ta fuskanci wannan kaidin ta kuma yi nasara kan yahudawa da mushrikai da munafukai, albarkacin jagoranci Annabi (s.a.w.a) da kuma lizimtar sahabbansa, zababbu.
Tarihin yadda Musulunci ya sha kokawa da wadan-nan magabta a zamanin Annabi (s.a.w.a) yana cike da abubuwa masu bayyana mana yadda masu jayayya da Musulunci, magabtan al'umma suka yi aiki da makamin rarrabawa da shuka sabani. Duk wanda ya bibiyi Alkur'ani Mai Girma da Sunnar Annabi (s.a.w.a) da dalilan saukar ayoyin Alkur'anin, sannan kuma ya dubi tarihin farkon sakon Musulunci zai lura da cewa sakon ya yaki wannan ciwon mai neman rusa addini, yakin da ba kakkautawa. Ya kuma gargadi musulmi kan kada su fada cikin sabani da rarraba kamar yadda al'ummar da suka shude suka fada. Alkur'ani ya hori musulmi da hadin kai da riko da juna, ya kuma yi gargadi kan rarraba da sassabawa da jayayya, yana mai suranta irin makomar masu yin hakan da cewa: "...Kuma kada ku yi jayayya har ku raunana, karfinku kuma ya tafi...".
Hakika Alkur'ani ya yi gargadi kan jayayya da sabani wanda shi yake kai mutane da makoma mai muni da rauni da ragwanci da kasawa da gushewar karfi da daula. Haka nan kuma ya gargade mu kan zamowa kungiyoyi masu gaba da neman halaka juna, sashi na dukan sashi, sashi na la'antar wani sashin tamkar yadda mushirikai da batattun al'ummai masu keta kalmar Allah da wasa da shari'o'inSa suka kasance. Alkur'ani mai girma yana fuskantar da wannan al'umma da ta hada kai bisa kalmar tauhidi:
"...Saboda haka ka tsayar da fuskarka ga addini... wannan shi ne addini madaidaici".
Da kuma kira zuwa ga riko da igiyar Allah: "Kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kuma kada ku rarraba...".
Da kuma cewa wannan al'umma guda ce: "Kuma lalle ne wannan al'ummar ku ce, al'umma guda daya, kuma Ni Ubangijinku ne, sai ku biNi da takawa". "Kuma lalle ne wannan al'ummarku ce, al'umma guda daya, kuma Ni Ubangijinku ne, sai ku bauta Mini".
Kamar haka ne Alkur'ani ya sanya matakan hada kan al'umma kamar haka:
1. Wanda ake wa bauta Shi kadai ne, kuma abin nema shi ne kadaita Shi da bauta masa.
2. Manufar addini ita ce tsayin daka da kuma muwafaka da halittar da Allah Ya yi mutane a bisa kanta.
3. Cewa wajibi ne kan al'umma ta tara karfinta wurin kira zuwa ga Musulunci da tabbatar da al'umma mai kira zuwa ga alheri da umurni da kyakkyawa da hana mummunan aiki, da daukar sakon Allah (S.W.T.) zuwa ga 'yan'Adam baki daya:
"Kuma wata jama'a daga cikinku, su kasance suna kira zuwa ga alheri, kuma suna umurni da alheri da kuma hani daga abin da ake ki".
An umurci musulmi da wannan aikin a madadin rarraba da sabani da jayayya domin kada su halakar da karfinsu kan kokawan cikin gida har ma su raunana su zamo abin hadiyewa ga abokan gaba. Alkur'ani mai girma yana kiran hankulanmu domin mu gane dalilan sabani da kuma tabbatar da tushen hanyoyin warware shi:
(a). Sabani kan shari'a da tunani irin na Musulunci wajibi ne a mai da shi ga Alkur'ani da Sunna.
"Idan kun yi jayayya cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa...".
"Kuma abin da kuka saba wa juna a cikinsa, ko mene ne, to hukumcinsa (a mayar da shi) zuwa ga Allah".
Alkur'ani yana hana mu mayar da jayayya ta ilimi da shar'antawa zuwa wata matsala ta rarraba da sabani da gaba da keta al'ummar musulmi, ya ce: "Kuma kada ku yi jayayya har ku raunan, karfinku ya kau....".