Sai ya ce: "Abin da ake nufi da 'Khatam' shi ne 'al-Dab'u' watau rufi a kan zukatan kafirai domin yi musu ukuba kan kafircinsu, kamar yadda Allah (S.W.T.) ya ce:
"A'a Allah ne Ya rufe a kansu (zukatansu) saboda kafircinsu, saboda haka ba za su yi imani ba face kadan([186])". (Surar Nisa', 4: 155)
To haka ne tafarkin Ahlulbaiti (a.s) yake fayyace manufar shiriya da bata da kuma cewa Allah (S.W.T.) bai halicci mutane suna batattu ko shiryayyu ba. Sai dai Ya bar musu zabi, Ya ba su nufi, Ya kuma bayyana musu hanyar alheri tare da gargadi kan hanyar sharri da halaka, Allah Ta'ala Yana cewa: "Lalle ne Mu, Mun shiryar da shi (mutum) ga hanyar kwarai, ko ya zama mai godiya, ko kuma ya zama mai kafirci". (Surar Insan, 76: 3)
Kuma Yana cewa: "Kuma Muka shiryar da shi ga hanyoyi biyu". (Surar Balad, 90: 10) Watau Mun sanar da shi hanyar alheri da ta sharri, zabi kuma na gare shi.
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya fassara ayar da cewa: "Su dai hanyoyi ne guda biyu, hanyar alheri da hanyar sharri. Kada hanyar sharri ta fi soyuwa gare ku bisa hanyar alheri([187])".
Tafarkin Ahlulbaiti (a.s) ya zabi ra'ayi tsarkakakke na bayani kan halayyar dan'Adam na alheri ko sharri, da wata ka'ida: "Babu Jabru ba tafwidhu, sai dai al'amari ne tsakanin al'amurra biyu, watau mataki tsakanin matakai biyu". Yayin da aka tambayi daya daga cikin Imaman Ahlulbaiti (a.s), shin akwai wani mataki tsakanin tilasta-wa (jabru) da sajarwa (tafwidh)? Sai ya amsa da cewa: "Abin da yake tsakaninsu ya kai fadin tsakanin sama da kasa".
Wannan shi ne takaitaccen bayanin tafarkin Ahlul-baiti (a.s) kan batun Jabru da Tafwidh, haka ne kuma akidar musulmin da suka yi koyi da tafarkinsu take.

Ra'ayin Ahlulbaiti (a.s) Dangane da Batattun Kungiyoyi
Babu shakka makiya Musulunci sun san cewa Ahlul-baiti (a.s) su ne mabubbuga ta asali da tsarkakar addini mai kwaranye wa musulmi dukkan wahalhalu da bala'u. Su masu daraja ne a zukatan musulmi bai daya.
Kowa yana ganin girman alkadarinsu, yana tsarkake duk abin da ya fito daga gare su ko ya karkare zuwa gare su. Don haka ne masu neman rushe addini da shuka masa dasisa suke fuskantar wannan tushe na Musulunci domin su sami damar shuka barna alhali suna karkashin inuwar Ahlulbaiti (a.s). Suna daukar tutar Ahlulbaiti (a.s) da sunan goyon bayansu domin su sami damar kaidi da rushe akidar tauhidi, alhali Ahlulbaiti (a.s) sun barranta daga gare su da kuma tsine musu albarka. Wadannan irin jama'a sun kirkiri akidun bata da karkatacciyar falsafa mai cewa Allah Yana hululi (wato Ya shiga jikin wata halitta daga cikin halittunSa) cikin Imamai - Allah Ya daukaka ga barin hakan- da cewa Allah Ya sakar wa Imamai (a.s.) al'amurran arzurtawa da tasiri cikin halittar aljanna da wuta.
Ba su tsaya nan ba sai da sashinsu ya dangantawa Imamai (a.s.) allantaka. Duk hakan kuwa sun yi shi ne domin kaidi wa Musulunci da musulmi da rusa akidar tauhidi. Hakika masu wannan aiki sun sami asali ne daga kungiyoyi irin na Majusawa, Manawiyya da Mazdakawa wadanda suka shiga Musulunci a munafurce, ba tare da sun yi imani ba. Haka nan, akwai tunanin kiristoci da yahudawa a cikin wannan yunkurin rusawa([188]) (*).
Wadannan mabarnata sun bi wancan hanyar suka rudar da hankula da shuka rikici da kirkirar ruwayoyi da ra'ayoyi fandararru, suka danganta su ga Ahlulbaiti (a.s) bisa karya. Saboda haka manyan malami suka rubuta littattafai kan masu ruwaya wato Ilmul Rijal domin tona asirin makaryata da masu kirkira da masu munanan akida tun zamanin Manzon Allah (s.a.w.a.) har ya zuwa karshen jerin Imamai (a.s.), amintattun maruwaita daga Manzon Allah (s.a.w.a.). Ta hanyar ne suka jefar da duk wata ruwaya ta karya da kuma duk wani maruwaici mai kirkira ake gane shi, kamar yadda Najashi ya yi cikin sanannen littafinsa nan na Rijalul Najashi da Shaikh Dusi cikin littattafansa na Al-Fihrist da kuma Rijalul Dusi da dai sauransu.
Tarihi yana sanar mana samuwar wasu kungiyoyi fandararru wadanda suka danganta kansu da Ahlulbaiti (a.s) kamar 'yan Gullatu da 'yan Mufawwidha, alhali kuwa Ahlulbaiti (a.s) sun barranta da su, sun la'ane su da kuma koransu. Baya ga haka ma, malaman mazhabar Imamiyya (Shi'a) suna hukumta su da cewa su najasa ne.
Al-Nawbakhti([189])(*) cikin littafinsa mai suna Firakush Shi'a ya ambato kungiyoyi daban-daban na 'yan Gullatu da 'yan Mufawwidha, da kuma ambaton matsayar Imaman Ahlulbaiti (a.s) dangane da su, ga kadan daga cikin abin da yake cewa:
"Amma batun sahabban Abul Khaddab Muhammad bn Abi Zainab al-Ajda al-Asadi da duk wanda yake da ra'ayi irin nasa, to lallai sun watse lokacin da suka ji cewa Imam Sadik (a.s.) ya la'anci Abul Khaddab, ya kuma barranta daga gare shi da sahabbansa". Har zuwa inda yake cewa: "Wata kungiya daga cikinsu ta ce Abu Abdullah Ja'afar bn Muhammad Sadik shi ne Allah - Allah Ya daukaka ga barin haka daukaka mai girma - sannan Abul Khaddab kuma Annabi ne mursali.
Wata kungiyar kuwa cewa ta yi: "Ja'afar bn Muhammad shi ne Allah - Wal iyazu billah- kuma Shi Allah (S.W.T.) wani haske ne mai shiga jikkunan wasiyyai ya kuma zauna a cikinsu. Wannan haske sai ya kasance shi ne Ja'afar bn Muhammad Sadik, sannan ya fita daga jikinsa ya shiga jikin Abul Khaddab([190])". Bayan al-Nawbakhti ya bijiro da wadannan batattun akidu sai ya ce:
"Wadannan kungiyoyin 'yan Gullatu masu da'awar Shi'a, sun sami asali ne daga addinan Kharmadaniyya(**) da Mazdakiyya([191])(*)da Zindikiyya([192])(**) da Dahriyya([193])(***) duk madaurinsu guda ne, Allah Ya la'ancesu. Dukkansu sun tafi a kan kore rububiyyar Allah Mahalicci (Allah Ya daukaka ga barin hakan), sun kuma tabbatar da ita wa jikkuna ababen halitta da nufin wai jikkunan su ne bigiren da Allah Yake zama, sannan kuma shi Allah Ta'ala wani haske ne da ruhi mai ciratuwa daga wannan jikin zuwa wani. Face dai su sun sassaba ne kurum wajen shugabannin da suke bi, sashinsu yana barranta daga sashi yana kuma la'antarsa([194]).
Al-Nawbakhti ya kara da nakalto fandararrun kungiyoyin da suka riga suka mace, masu fakewa da jingina kansu ga Ahlulbaiti (a.s) kamar haka:
"Wata kungiya ta ce wai Muhammad bn Hanafiyya dan Imam Ali (a.s.) 'shi ne Mahdi, Imam Ali ya kira shi da Mahdi, bai mutu ba kuma ba zai mutu ba, wannan ba ya halatta, sai dai kawai shi ya faku ne, ba a kuma san inda yake ba. Zai dawo ya mallaki kasa, babu wani Imami bayan fakuwarsa har zuwa dawowarsa wajen sahabbansa, su ne kuma sahabban Ibn Karb([195])". Sannan ya ce:
"Hamza bn Ammara al-Barbari cikinsu yake kuma shi mutumin Madina ne, sai ya rabu da su ya yi ikirarin cewa shi Annabi ne, shi kuma Muhammad bn Hanafiyya shi ne Allah - wal iyazu billahi -. Ya kuma ce shi ne Imam sannan kuma wasu abubuwa guda bakwai za su sauko masa daga sama, da su ne zai cinye dukkan kasa ya mallake ta. Ya kuma sami mutane daga Madina da Kufa da suka bi shi kan hakan. Imam Bakir (a.s.) ya tsine masa ya barranta daga gare shi, ya karyata shi, a sanadiyyar hakan ne kuma ya sa 'yan Shi'a suka barranta daga gare shi([196])".
Haka nan ma Imam Sadik (a.s.) ya la'anci Sa'id al-Nahdi wanda wadannan fandararrun kungiyoyin nan suke bi. Imam din ya kira shi shaidan, wanda ya yi wa Imam karya([197])".
Ga wasu ruwayoyin malaman Shi'a kan matsayin da Imam Sadik (a.s.) ya dauka dangane da wadannan 'yan Gullatu da kuma fandararrun ra'ayoyinsu. Misalin hakan shi ne abin da Imam din ya ce kan Abul Jarud da mabiyansa kamar yadda Ibnu Nadim ya nakalto cikin Alfihrist. "Imam Sadik (a.s.) ya la'ance shi ya ce: 'shi makahon zuciya ne da idanu([198])'.
Kamar yadda kuma Imam din ya la'anci Abu Mansur al-Ajli, daya daga cikin 'yan Gullatu, an ruwaito cewa: 'Al-Kishshi ya kawo cikin Rijal dinsa shafi na 300 cewa Imam Sadik ya la'ance shi sau uku. Sannan kuma Yusuf bn Umar al-Thakafi, gwamnan Iraki, ya tsire shi a zamanin Hisham bn Abdul Malik([199])'.
Hakika Imam Sadik (a.s.) ya bayyana matsaya kan wadannan 'yan gullatu, daga nan ya ambaci wasu daga cikinsu, su ne: Mughira bn Sa'id, Bazi, Sirri, Abul Khaddab Muhammad bn Abi Zainab al-Ajda', Mu'ammar, Bashshar Sha'iri, Hamza Barbari da Sa'id Nahadi, sai ya ce: "Allah Ya la'ance su, mu dai ba mu rabuwa da makaryata msu yi mana karya ko kuma wani mai gurgun tunani. Allah Ya isar mana ga dukkan makaryaci, Ya kuma dandana musu zafin karfe([200])".
A wani hadisin kuma Imam Sadik (a.s.) ya barranta daga 'yan Gullatu, inda yake cewa: "Ya ku jama'ar Shi'a - shi'ar Alu Muhammadu- ku kasance matsakaita, wadanda suka wuce gona da iri (masu guluwi) su dawo gare ku, wadanda kuwa suka yi nawa su risko ku". Sai wani mai suna Sa'id ya ce: 'Allah Ya sanya ni fansarka! Wane ne mai guluwi? Sai Imam ya ce masa:"Wasu mutane ne masu fadi game da mu, abin da mu ba mu fada ba, wadannan ba su daga gare mu, mu ma ba mu daga gare su". Sai mutumin ya ce: 'To wane ne mai nawa? Sai ya amsa masa da cewa: "Shi ne mai bidar (gaskiya) yana nufin alheri, alherin zai same shi kuma za a sakanta masa da shi([201])".
Daya daga cikin sahabban Imam Sadik (a.s.) ya ruwaito cewa yayin da Imam din ya sami labarin cewa Abul Khaddab na wuce gona da iri sai idanunsa suka cika da hawaye yana cewa:
"Ya Ubangiji, na barranta ya zuwa gareKa, daga abin da Al-Ajda yake ikirari a kaina, gashina da fatar jikina sun ji tsoronKa. Ni bawa ne a gare Ka dan bawanKa, makaskanci mai tawali'u".Daga nan sai ya sunku'i da kai na dan lokaci kamar yana ganawa da wani abu, sai ya daga kansa yana cewa:"Haka yake, haka yake! Bawa mai tsoro, makaskanci gaba ga Ubangijinsa, kankani, mai tsananin tsoro. Wallahi ina da Ubangijin da nake bautarSa, bana yi masa tarayya da kome. Me ya same shi (Abul Khaddab)? Allah ya kunyata shi, Ya zuba masa tsoro. Kada kuma Ya ba shi aminta daga firgici a ranar kiyama…..ba haka amsawar Annabawa take ba, ko ta mursalai, ba kuma amsawa ta ba. Amsawa ta kam ita ce fadar cewa: Ya Allah na amsa maKa, na amsa maKa Ya Allah ba Ka da abokin tarayya([202])".
Sadir ya ce: 'Na ce da Abu Abdullah (a.s.) cewa wasu mutane suna ikirarin cewa ku alloli ne, suna kuma kafa hujja da fadar Allah (S.W.T.) cewa:"Kuma Shi ne Wanda ke abin bautawa a sama, kuma bautawa a kasa"", (Surar Zukhruf aya ta 84),sai ya ce:"Ya kai Sadir! (Ka sani) jina da ganina da fatata da namana da gashina duk sun barranta daga wadannan mutane, Allah ma Ya barranta da ga gare su. Ba kan addinina wadannan suke ba, ba kuma kan na iyayena ba. Na rantse da Allah ba zai tara ni da su ba ranar lahira, kuma ba su zo a wannan rana ba face Allah Na fushi da su([203])".
Kamar yadda suka yi wa Imam Bakir da Sadik (a.s.) karairayi kuma suka barranta daga gare su, haka nan ma suka yi wa Imam Musa Kazim (a.s.) bayan shahadarsa. Suka ce bai mutu ba, sai dai kawai an daukake shi ne kamar yadda aka daukaki Annabi Isa (a.s.) kuma nan gaba zai dawo. Imam Ridha (a.s.) dan Imam Kazim (a.s.) sai ya barranta daga gare su, ya kuma la'ance su.
Kamar yadda Imam Sadik (a.s.) ya ce ba za a rabu da masu yi wa Ahlulbaiti (a.s) karya ba, domin su rikita tafarkinsu, domin kaidi ga Musulunci, haka nan Ahlulbaiti (a.s) suka bayyana matsayinsu dangane da wadannan masu niyyar ruguza Musulunci.
Yana daga ni'imomin Allah ga Musulunci da musulmi cewa wadannan kungiyoyi sun gushe, babu abin da ya rage sai ambatonsu cikin littattafan tarihi. Sai dai abin ban mamaki da takaici shi ne wasu masu mugun nufi suna danganta tafarkin Ahlulbaiti (a.s) da tatsuniyo-yi da barnace-barnace domin bakanta tafarkin Ahlulbaiti (a.s). Duk wani mai nufin alheri ba zai yarda da wannan ba bayan kuwa su Ahlulbaiti (a.s) da kansu sun barranta daga duk abin da ya saba wa tafarki madaidaici, kamar yadda muka ambata a baya. Babu shakka babu abin da masu sukar mabiya tafarkin Ahlulbaiti (a.s) suke yi face barazana ga hadin kan musulmi.
A daya gefen kuma, duk masu bincike suna iya ganin abubuwan da ake danganta su da sauran mazhabobin musulmi na akida, kamar su jabru da cewa Allah jiki ne kuma Yana zama a bisa kujera da cewa fadin kujerarSa taki bakwai ne, da cewa Allah zai shigar da kafarSa cikin wuta a ranar lahira sai Ya bice zafinta, da cewa Shi Yana saukowa nan duniya bisa wani farin jaki da dai sauransu.
Hakika a sarari yake cewa duk wadannan zantuttuka, kamar tatsuniyoyin Gulatu, suna warware akidar tauhidi, addinin Musulunci kuwa yana barranta daga gare su.

Tafarkin Ahlulbaiti (a.s) Wajen Tarbiyyar Mabiyansu
Imam Ja'afar Sadik (a.s.) ya ce: "Ni ina kin a ce mutum ya mutu alhali akwai wata ta'adar Manzon Allah (s.a.w.a.) da ta rage bai aikata ba([204])".
Babu shakka Ahlulbaiti (a.s) sun ba da muhimmanci kwarai wajen ilmantarwa da tarbiyyar mabiya da sahab-bansu da kuma shiryar da su zuwa hanya sahihiya ta tabbatar da rayuwa irin ta mai akida da halayen kwarai da biyayya ga hukumce-hukumcen Musulunci. Sun karfafa kan gina tarbiyyar musulmi bisa dacewa da Littafin Allah da Sunnar Manzon Allah (s.a.w.a.) domin samar da gwarzaye masu daukar hasken Musulunci da kira zuwa gare shi ta yadda hasken zai watsu kan sauran jama'a su amfana da ilmi da kuma aiki. Ahlulbaiti (a.s) sun yi hakan ne saboda tabbatar da haraka ta Musulunci cikin al'ummar duniya bayan da muggan manufofin masu neman ruguza addini suka bayyana ko ina. Muna iya ganin wannan kokarin nasu a fili cikin halayensu da wasiyyoyinsu da tarbiyyarsu ga mabiyansu. Daga cikin maganganun Imam Bakir (a.s.) akwai raddi kan masu cewa duk wanda ya kaunaci Ahlulbaiti (a.s) ba ya bukatar lizimtar farilloli Musulunci. Imam ya bayyana musu tafarkin Musulunci na gaskiya wanda Ahlulbaiti (a.s) suke kai, kuma suke kaunar dukkan musulmi ya yi riko da shi. Idan ba ka san shi ba, to shi ne tafarkin ilmi da akida ta gaskiya da aiki da duk abin da Alkur'ani ya zo da shi, Annabi (s.a.w.a) kuma ya iyar da shi ya kuma rayu a kansa. Imam din ya ce:
"Wallahi ba mu da wata kubuta daga Allah, babu wata dangantaka tsakaninmu da Allah, ba mu da wata hujja a kan Allah, kuma ba a kusantar Allah sai da biyayya. Wanda ya zama mai biyayya daga cikinku to jibintarmu za ta amfane shi, wanda kuwa yake mai sabo daga cikinku, jibintarmu ba za ta amfane shi ba([205])".
Amru bn Sa'id bn Hilal ya ce da Abu Ja'afar (a.s.): 'Allah Ya sanya ni fansar ka! Ni da kyar nake saduwa da kai, sai dai bayan shekaru, to ka yi mini wasicci da wani abin da zan rika', sai ya ce masa:"Ina maka wasicci da tsoron Allah da tsantsaini da kokari, ka sani cewa tsantseni ba ya amfani sai tare da kokari([206])".
Daga cikin abin da Imam Sadik (a.s.) ya yi wasicci da shi ga wani mabiyinsa, Abu Usama ya kuma umurce shi da ya isar da shi ga sauran mabiyansa, shi ne cewa:
"Ku ji tsoron Allah ku kasance ado a gare mu, kada ku zamo abin kyama. Ku janyo mana dukkan soyayya, ku ije mana duk wani mugun abu, domin mu ba kamar yadda aka fada dangane da mu muke ba. Muna da hakki cikin Littafin Allah da dangantaka da Manzon Allah (s.a.w.a.) da tsarkakewa daga Allah, da haifayya tsarkakakkiya, ba mai ikirarin hakan, koma bayanmu, face makaryaci*. Ku yawaita ambaton Allah da tuna mutuwa da karatun Alkur'ani da salatin Annabi (s.a.w.a) domin akwai (ladan) kyawawan aiki goma ga ko wane salati a gare shi([207])".
Imam Sadik (a.s.) ya yi wasicci wa Isma'il bn Ammar, daya daga cikin sahabbansa, da cewa: "Ina ma wasicci da tsoron Allah da tsantseni da gaskiya cikin magana da mai da amana da kyautatawa makwabta da yawan sujada, don da wannan ne Annabi (s.a.w.a) ya umurcemu([208])".
Hisham bn Salim ya ce: 'Na ji Abu Abdullah (a.s.) yana fada wa Hamran cewa: "Ka dubi wanda ya kasa ka, kada ka dubi wanda ya fi ka, domin haka ya fi (tabbatar da) wadar zuci ga abin da aka yanka maka, kuma za ka fi cancantar kari daga Allah. Ka sani cewa kadan na dawwamammen aiki wanda aka yi yakini, a wajen Allah, ya fi mai yawa dawwamamme amma babu yakini a cikinsa. Ka sani cewa babu tsantsenin da ya fi nisantar ababen da Allah Ya haramta, da kuma kamewa ga barin cutar da musulmai da yi da su. Babu kuma abin da ya fi kyan hali faranta rai. Kuma babu dukiyar da tafi amfani daga wadatuwa da kadan mai biyan bukata. Babu jahilcin da ya fi jiji da kai daci([209])".
Imam Sadik (a.s.) ya ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w.a.) kan siffofin muminai cewa: "Wanda ya yi bakin cikin mummunan aikinsa, ya yi farin ciki da kyakkyawan aikinsa, to mumini ne([210])".
Wadannan bayanai suna nuna siffar mumini mai riko da addini irin wanda Ahlulbaiti (a.s) suka yi kokarin samarwa kuma wannan shi ne tafarkinsu na tarbiyyar al'ummar musulmi. Shi ne kuma kiran da suka yi wa al'ummar Annabi (s.a.w.a) na lizimtar Littafin Allah da Sunnar Ma'aiki (s.a.w.a.) da gina rayuwa bisa wannan shiriya da tafarki mai karfi. Babu abin da ya fi dacewa ga musulmi sai bin shiryarwarsu da wasiccinsu da kuma wa'azinsu.

Gudummawar Ahlulbaiti (a.s) A Fagen Siyasa
Babu shakka al'ummar musulmi ta san matsayin Ahlulbaiti (a.s) da hakkinsu a kan wannan al'umma na shugabantarta. Domin haka ne za a iya ganin cewa Ahlulbaiti (a.s) suna matakin kololuwa a fagen siyasa da shugabancin Musulunci, domin su shiryar da al'umma, su tabbatar da gyara da aiwatar da hukumce-hukumcen addini da tsayar da adalci.
Duk wanda ya karanci tarihin Musulunci zai gani a sarari cewa shugabantar al'umma bayan zamanin Khulafa'u al-Rashiduna ta koma mulukiyya mai dora kanta bisa bayin Allah da jan hankulansu da dukiya da mukamai da kuma dankwafe hukumce-hukumcen shari'a da wasa da su. Wannan wasa da shari'a da makomar al'umma ya janyo sassabawa da juyin-juya-hali da jayayya mai tsanani da zubar da jinin kungiyoyi masu sabanin ra'ayoyi da tunace-tunace masu warware juna sun zama sakamakon wannan. Wasunsu suna goya wa sarakuna baya kan zaluncinsu da kuma horar da mutane su mika wuya da hana su bijirewa da warware mubaya'arsu ga azzalumai. Wasu kuma sun yi amfani da wannan damar (ta jayayya tsakanin musulmi) wajen tabbatar da mugun nufinsu na ruguza addini yayin da suka dora kira da halalta dukkan haram da dukiyoyi da mata da rusa wajibai, kungiyoyi irinsu 'yan Karamida, Mazdakiyya da Kharmiyya da dai sauransu. Wasu kuma suka dora kira zuwa ga rudani da rusa dukiyar hukuma da zubar da jini da kafirta kowa da kowa kamar su Khawarijawa.
Da wannan fantsamar ra'ayoyin siyasa masu sassabawa da fitinu da yake-yake na cikin gida, al'umma ta fuskanci hadari mai munin gaske. Ahlulbaiti (a.s), a matsayinsu na jagororin al'umma, sun kasance mafus-kanta da tushen sakon Musulunci wanda duk wata mishkila ta akida da tunani wacce ta kalubalanci musulmi ana iya warware ta a hannunsu. Domin wannan matsayi nasu na matabbacin tafarkin gaskiya, musulmi suna bin ra'ayinsu da riko da matsayin da suka dauka kan al'amurra. Face wadanda suka damfaru da masu iko, masu kare ayyukansu domin biyan bukatar kansa. A nan za mu yi dubi cikin tafarkin Ahlulbaiti (a.s) akan abubuwan da suka shafi ayyukan siyasa.

Tafarkin Ahlulbaiti (a.s) Kan Ayyukan Siyasa
Duk wanda ya bibiyo salon siyasar Ahlulbaiti (a.s) da gwagwarmayarsu ta bayyane da ta boye a tsawon karno-ni biyu da rabi zai iya gano cewa aikin da suka yi na siyasa yana bisa ginshikai kamar haka:
(1). Tarbiyyantar da al'umma kan kin zalunci da tabbatar da manufar adalci da bayyana fikirar imamanci da siyasa da fayyace rukunan hukumci da shugabanci cikin addinin Musulunci. Sun yi haka ne domin karfafa fahimtar siyasa ga al'umma da karfafa kulawarta da kiyayyarta ga azzalumai, da farkar da ita daga barci. Wanda ya yi bitar abin da Ahlulbaiti (a.s) suka ruwaito suka watsa daga Manzon Allah (s.a.w.a.) dangane da wannan al'amari, zai gane muhimmancin wannan mataki wajen farfado da ruhin siyasa da kiyayewa ta Musulunci. A nan za mu ambaci wasu daga cikin ruwayoyin da suke magana dangane da shugabanci da kuma nauyin da suka hau kan shugaba musulmi, da kuma kyamar da Musulun-ci yake wa zalunci da kuma kira zuwa ga adalci, don mu fahimci fikira da tunanin Ahlulbaiti (a.s) wajen fada da zalunci da kuma kwadaitar da al'umma zuwa ga canji da kuma motsi na siyasa.
An ruwaito daga Imam Muhammad Bakir (a.s.) cewa wani dattijo daga kabilar Nakh'a ya ce: "Na ce wa Abu Ja'afar (a.s.) cewa: Ni na kasance gwamna ne tun zamanin Hajjaj har yau din nan, shin za a karbi tuba ta? Sai na yi shiru, sannan na sake maimaita wannan tambayar, sai yace min: "A a; har sai ka mai da wa duk wani mai hakki, hakkinsa([211])".
Abu Hamza al-Thumali ya ruwaito daga Imam Abu Ja'afar al-Bakir (a.s.) cewa: "Yayin da Aliyu bn Husaini (a.s.) ya zo cikawa sai ya rungume ni ya zuwa kirginsa sannan ya ce: "Ya dana, ina maka wasicci da abin da babana (a.s.) ya mini wasicci yayin da cikawa ta zo masa, kuma da abin da ya ambata cewa babansa ya yi masa wasicci. Ya ce: Ya dana, na hane ka zaluntar wanda ba shi da mai taimako kanka sai Allah([212])".
Imam Sadik (a.s.) ya ce: "Babu zaluncin da yafi zaluncin da wanda aka zaluntan ba shi da mai taimakonsa a kan shi sai Allah Mai Girma da Daukaka([213])".
Imam Sadik (a.s.) ya ruwaito daga kakansa Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: "Ku tsoraci zalunci domin shi duhu ne a ranar lahira([214])".
Imam Sadik (a.s.) ya ce: "Allah Mai Girma da Daukaka Ya yi wasicci ga wani Annabi da cikin Annabawansa wanda yake cikin masarautar wani jabbarin sarki cewa: 'Ka je wajen wannan azzalumin ka ce da shi; Ni ban shugabantar da kai domin zubar da jini da tara dukiya ba, sai dai kawai na shugabantar da kai ne domin ka raba Ni da sautin (karar) wadanda aka zalunta. Domin Ni ba zan bar zaluncin da aka yi masu ba ko da kafirai ne([215])".
Imam Sadik (a.s.) ya ce: "Da wanda ya aikata zalunci da mai taimakonsa da kuma wanda ya yarda da shi, to dukkansu ukun masu tarayya ne (cikin zaluncin) ([216])".
Imam Sadik (a.s.) din dai ya ce: "Duk wanda ya yi uzuri wa zaluncin azzalumi, Allah zai dora masa wani azzalumi da zai zalunce shi, kuma idan ya yi addu'a ba za a amsa masa ba, kuma Allah ba zai ba shi ladar zaluncin da aka masa ba ([217])".
Abu Basir ya ruwaito cewa: "Mutane biyu sun zo wajen Imam Sadik (a.s.) a kan wani lamari na mu'amala tsakaninsu. Yayin da Imam (a.s.) ya ji zancen kowannensu, sai ya ce: "Hakika wanda ya cimma bukatarsa da zalunci bai cimma kome ba. Lallai za a biya wanda aka zalunta da addinin azzalumin fiye da abin da shi ya dauka daga dukiyar wanda aka zalunta", daga nan sai ya ce: "Duk wanda yake aikata wa mutane sharri kada ya yi kyama idan aka yi masa. Hakika babu abin da dan Adam zai girba face abin da ya shuka. Babu wanda zai girbi abu mai dadi baicin ya shuka mai daci, babu kuma wanda zai girbi mai daci baicin ya shuka mai dadi". Sai mutane biyun nan suka yi sulhu kafin ma su tashi daga gare shi ([218])".
A'imman Ahlulbaiti (a.s) sun ruwaito cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Duk wanda ya tafi tare da azzalumi domin ya taimake shi, alhalin ya san cewa shi azzalumi ne, to, hakika ya fice daga Musulunci ([219])".
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Adalci na sa'a guda ya fi ibadar shekaru saba'in na sallar dararensu da azumtar yininsu. Zalunci a hukumci na sa'a guda kuma ya fi tsanani da girma wajen Allah a kan sabon shekara sittin ([220])".
Jabir bn Abdullah al-Ansari (r.a.) ya ce: 'Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Wanda ya nemi yardar wani sarki da abin da yake fusata Allah, to ya fita daga addinin Allah ([221])".
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Wanda ya shugabanci mutum goma sannan bai yi adalci a tsakaninsu ba, zai zo ranar lahira hannayensa da kafafunsa da kansa na cikin ramin gatari ([222])".
Imam Ali (a.s) ya ce: "Duk mutumin da ya shugabanci wani al'amari na musulmi, sannan ya rufe kofa (ya ki sauraronsu) to yana cikin azabar Allah Mai Girma da Daukaka da la'anarSa har sai ya bude kofarsa ga mai wata bukata da mai (karar) wani zalunci, sun shigo ([223])".
Kamar haka A'imma (a.s.) suke tarbiyyar mabiyansu da karkato da ra'ayin jama'a zuwa ga canji da gyara da shiga fagen siyasa ta hanyarta ta asali.
(2). Yankewa daga Azzalumai: Bayan shiryarwa da tarbiyya kan munin zalunci, Ahlulbaiti (a.s) sun kara da umurni da yanke hulda da azzalumai, kamar yadda ya zo cikin hadisi cewa:
"Duk wanda ya yi tafiya tare da azzalumai, alhali yana sane da cewa azzaluman ne, to hakika ya fice daga Musulunci" da kuma cewa: "Mai aikata zalunci da mai taimaka masa da mai yarda da shi dukkansu masu tarayya da juna ne".
Haka nan suke kira da yanke hulda da azzalumai da rashin taimaka masu. An ruwaito cikin hadisi cewa: "Idan ranar alkiyama ta zo mai kira zai yi kira: Ina azzalumai da mataimakansu; wanda ya shirya masu kurtun tawada ko ya daure musu wata jaka ko ya fere musu kan alkalami, ku tara su tare da azzalumai ([224])".
Kyakkyawan misalin yankewa azzalumai shi ne abin da A'imma (a.s.) suka yi da matakan da suka dauka dangane da zalunci da azzaluman mahukuntan Umayyawa da Abbasiyawa a zamanin Imam Sajad, Imam Bakir, Imam Sadik, Imam Kazim, Imam Ridha ([225])(*), Imam Jawad ([226])(**), Imam Hadi da kuma Imam Hasan Askari (a.s.).
A wannan lokacin A'imma (a.s.) sun gamu da wahalhalu daban-daban daga mahukunta, kamar cutarwa da kora da sa ido da shiga kurkuku da matsi da tsoratarwa, za mu kawo kadan daga cikin irin wadannan abubuwa a cikin wannan littafi.
A matsayin misali na irin wannan yankewa, shi ne matsayin da Imam Sadik (a.s.) ya dauka dangane da halifan Abbasiyawa Abu Ja'afar Mansur wanda ya shahara da mugun hali da zubar da jini da zalunci ga zuriyar Imam Ali (a.s.). Malaman tarihi sun rubuta cewa, wata rana Mansur ya rubuta wasika zuwa ga Imam Sadik (a.s.) yana neman zama da shi don kokarin sanya shi cikin malaman hukuma. Sai Imam yaki duk kuwa da halin tsoratarwa da kaushin halin da mahukuntan suke nunawa.
Ga abin da Mansur ya rubuta: "Me zai hana ka ziyarce mu kamar yadda mutane suke ziyartarmu"?, sai Imam (a.s.) ya rubuta masa cewa: "Babu abin da muke tsoronka dominsa, babu wani abu daga sha'anin lahira a gare ka wanda zai sa mu kaunaci (saduwa da) kai dominsa. Ba ka kuma cikin wata ni'ima ballantana mu yi maka murna, ba ma kuma ganinsa a matsayin azaba ballantana mu yi maka jaje". Sai Mansur ya rubuto amsa ya ce: "Ka zauna da mu saboda ka yi mana nasiha". Sai Imam (a.s.) ya amsa masa da cewa:"Mai nufin samun duniya ba ya maka nasiha, wanda kuwa yake nufin lahira ba ya zama da kai ([227])". Haka nan dai matsayar A'imma (a.s.) da raddinsu ya kasance ga mahukuntan da ba sa tsai da shari'a, ba su lizimtar ginshikanta.
To haka nan ma malaman fikihun mazhabar Ahlulbaiti (a.s) suka bi tafarkin Imamansu wajen yanke hulda da azzaluman mahukunta ta hanyar fatawoyinsu masu haramta taimakawa azzalumai ko karbar aikin hukumominsu. Suna kawo wannan ne galibi a babin makasib wato hanyoyin neman abin masarufi. Bari mu kawo maganar Shahid Muhammad bn Jamal(*) Makki al-Amuli wanda aka fi sani da Shahidul Awwal (Allah Ya rahamshe shi) yayin da yake kawo sana'oi haramtattu cewa: "Da taimakon azzalumai cikin zalunci" (yana daga cikin haramtattun sana'oi), shi kuma mai sharhin littafin ya ce: "Kamar yi musu rubutu da kawo musu wanda suke zaluntarsa da dai makamantansu ([228])".
Malaman sun hana karbar duk wani aiki a hukumar azzalumai sai dai da nufin yi wa Musulunci hidima da tunkude zalunci ga barin bayin Allah, ta yadda dai za a samu wani gyara ko wani amfani ga al'umma.
(3). Gwargwarmaya da abin da ya shafi amfani da karfi: Wajibcin umurni da aiki mai kyau da hana mummuna wani ginshiki ne wanda ya tabbatar da gwagwarmaya domin kawar da zalunci, kuma an lizimta da shi ga musulmi.
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Shugaban shahidai shi ne Hamza da kuma mutumin da ya mike ya umarci sarki azzalumi (da kyakkyawan aiki) ya hana shi (mummuna) sannan sarki ya kashe shi".
Duk wanda ya bibiyi tsarin rayuwar Ahlulbaiti (a.s) a fagen siyasa da sabawa zaluncin da suka yi, zai ga cewa hanya ce guda wajen sabawa zalunci da kira zuwa ga gyara da gwagwarmaya. Gwagwarmaya ta faro ne a zamanin mulkin Mu'awiyyah dan Abu Sufyan, yayin da ya dora dansa Yazid a kan wuyar al'ummar musulmi duk da cewa bai cancanci shugabanci ba kuma ya rasa dukkan sharuddansa. Wannan ta'asa ta janyo fasadi da kaucewar al'umma, abin da ya sanya Imam Husaini (a.s.) yin shelar jihadi. Imam (a.s.) ya zauna a Makka na tsawon wata hudu bayan barowarsa birnin Madina, daga bisani sai ya fuskanci kasar Iraki. Can a Karbala ne aka yi gumurzu tsakanin rundunar Yazid da jama'ar Imam Husaini (a.s.) 'yan kalilan, a can tsarkakken jini ya zuba, Imam (a.s.) ya yi shahada. Zubar da jinin Imam Husaini (a.s.) tare da Ahlulbaitinsa da kuma mabiyansa ya girgiza al'umma ya tashe ta daga barcin da take ciki. Wannan kuwa shi ne farkon tawaye wa azzaluman mahukunta masu fakewa da Musulunci don cimma burinsu da warware mubaya'ar jabu da shelar kawar da hukumcin bata-gari mai sabawa rukunan Musulunci. Wannan tawaye wa azzalumai shi ya yaye zanin malaman da suke kiran mutane zuwa kaskanci da mika kai bori ya hau, da gurbata ra'ayin ilahirin jama'a da karfafa cewa sai an lizimci mubaya'ar azzalumi an cika masa alkawari komin lalacewarsa. Wadannan muggan malamai dangin Bal'ama dan Ba'ura sun yi kunnen uwar shegu da fadar Manzon Allah (s.a.w.a.) ce wa: "Ba a karbar rantsuwar mai sabo", Da kuma fadinsa (s.a.w.a) cewa: "Babu biyayya ga halitta cikin sabon Mahalicci".
Suna yin biris da fadin Allah Ta'ala cewa: "Kuma kada ku karkata zuwa ga wadanda suka yi zalunci, sai wuta ta shafe ku". (Surar Hud, 11:113).
Shi Shugaban shahidai, Imam Husaini bn Ali (a.s.) ya kaddamar da gwagwarmayarsa ne a shekara ta sittin da daya bayan hijira, kuma a wannan shekarar ne ya yi shahada a can yankin Karbala na kasar Iraki. Da wannan ne kuma ya rushe dukkan kiraye-kirayen muggan malamai na rauni gaban hukumomin zalunci da yarda da su. Hakika sautin shahada da jini ya rinjayi na kwadayi da kaskanci.
Imam Husaini (a.s.) ya bayyana wa mutane dalilan fitowarsa da tsarin da yake tafe bisansa da cewa:
"Ni ban fito domin girman kai ko alfahari ba, ba kuma domin barna a bayan kasa ko zalunci ba. Abin da kawai ya fito da ni shi ne neman gyara a cikin al'ummar kakana, Manzon Allah (s.a.w.a.). Ina nufin yin umurni da kyakkyawan aiki da hana mummuna, in kuma bi irin rayuwar kakana da babana ([229])".
Sannan ya ayyana wa mutane siffofin shugaba wanda shi ne ja-gora mai jan ragamar musulmi, da wajibcin tsayuwa don gwagwarmayar sauya mai hukumci a yayin da ya karkace ya bar wadannan ginshikin. Ga abin da Imam Husaini (a.s.) ya rubuta wa mutanen Kufa:
"Ina rantsuwa da cewa ba wani ne shugaba ba face mai hukumcin da ya tsayar da adalci, mai riko da addinin gaskiya, mai tsare kansa bisa (umurnin) Zatin Allah ([230])".
Daga cikin abin da ya rubuta wa manyan mutanen garin Basra kuwa, cewa ya yi: "Ni ina kiranku zuwa ga Littafin Allah da Sunnar AnnabiSa (s.a.w.a), domin an riga an kashe sunna an raya bidi'a. To idan kun saurari fadina kuka bi umurnina zan shiryar da ku tafarkin shiriya. Aminci ya tabbata a gare ku da rahamar Allah ([231])".
Hakan nan Imam Husaini (a.s.) ya tabbatar wa al'umma yadda shari'a ta yi umarni da sabawa azzalumin shugaba, ya kuma yi shelar rukunan jihadi mai tsarki, domin sauya hukumcin azzalumai.
Bayan jihadin Imam Husaini (a.s.) mai albarka, Ahlulbaiti (a.s) sun taimaka wa yunkuri daban-daban da Alawiyyawa suka yi tsawon sama da karni biyu, a fadin kasashen musulmi.
Zaid bn Ali bn Husaini, wato dan Imam Zainul Abidin kuma jikan Imam Husaini (a.s.) ya yi yunkuri a shekara ta 121 bayan hijira. Wannan kuwa ya faru ne a zamanin Imam Sadik (a.s.) wanda kuwa ya goyi bayansa ya kuma yi juyayin shahadar Zaid(*).
Fudhail Rassan ya ce: "Na shigo wajen Abu Abdullah (a.s.) bayan an kashe Zaid bn Ali, sai aka shigar da ni cikin uwar daki, sai ya ce da ni: "Ya kai Fudhail, an kashe baffana? Sai na ce 'fansar ka nake (e an yi haka), sai ya ce:"Allah Ya jikansa, lallai shi ya kasance mumini mai sani, mai ilmi, mai yawan gaskiya. Lallai da ya yi nasara da ya cika alkawari. Lallai da ya sami mulki da ya san inda zai sanya shi ([232])". Haka aka yi ta samun taimakawar Ahlulbaiti (a.s) wa masu yunkurin kawo gyara cikin Alawiyyawa.
Daya daga cikin bayyanannen misalin irin wannan mataki na siyasa kuwa, shi ne matakin da Imam Kazim (a.s.) ya nuna dangane da yunkurin da Husaini bn Ali ya yi a shekara ta 169 a birnin Madina, yunkurin da aka fi sani da Yunkurin Fakh ([233])(*) wanda aka yi shi a watan Zulkida na wannan shekarar.
Duk da cewa Imam Kazim (a.s.) ya ga alamun rashin nasarar yunkurin a wancan lokacin, babu shakka magan-ganun da ya yi sun nuna cewa yana goyon bayan ra'ayin jihadi. Ga abin da ya fadi wa shi Husainin yayin da ya ga yayi niyyar fita wannan arangama:
"Za a kashe ka, saboda haka ka tsananta yaki domin mutanen fasikai ne, suna bayyana imani suna boye munafunci da shirka. Lalle ne mu daga Allah muke kuma wajenSa za mu koma! Ga Allah nake neman ladan rashinku ([234])".
Yayin da Husain ya yi shahada aka kawo kawukan wadanda suka yi shahada tare da shi wajen mahukuntan Abbasiyawa, sai aka tambayi Imam Kazim cewa wannan kan Husaini ne? sai ya ce:
"E, lalle ne mu ga Allah muke, kuma lalle ne mu zuwa gare Shi za mu koma. Na rantse da Allah, ya mutu musulmi ne salihi, mai yawan azumi, mai umurni da kyakkyawa, mai kuma hana mummuna, babu tamkarsa cikin mutanen gidansa ([235])".
Shi dai Husain ya kasance ne yana kiran mutane da cewa: "Ina kiranku ne zuwa ga abin da Alu Muhammadu suka yarda da shi, da aiki da Littafin Allah da sunnar Annabi (s.a.w.a) a tsakaninku, da kuma tsayar da adalci a tsakanin jama'a([236])". Kiran da Husain ya yi, kira ne zuwa ga biyayya ga mutumin da ya cancanci shugabanci, wanda yake daga Alu Muhammadu, kuma shi ne Imam Kazim (a.s.), kamar yadda Zaid ya yi nufin mai da shugabanci ga Imam Sadik (a.s.) da ya yi nasara. Hakika halifan Abbasiyawa ya fahimci goyon bayan da Imam Kazim (a.s.) yake yi wa yunkurin Husain a yakin Fakh.
Allamah Majilisi ya ruwaito cewa: "Sai ya (halifan Abbasiyawa) ci gaba da zagin Dalibiyawa (jikokin Ali bn Abi Talib) har ya ambaci Musa bn Ja'afar (a.s.), sai ya zage shi yana cewa: 'Wallahi Husaini bai yunkura ba sai da umarninsa (Musa bn Ja'afar), ba abin da ya bi face abin da yake so domin shi (Imam Kazim) ne ma'abucin wasiyya a cikin mutanen wannan gidan. Idan na bar shi, Allah Ya kashe ni ([237])".
Imam Jawad, jikan Imam Kazim (a.s.) shi ma ya bayyana tasa matsayar dangane da masu gwagwarmar, inda ya ce: "Bayan Dif (Karbala), ba a cutar da mu kamar cutarwar Fakh ba ([238])".
Akwai misalai masu yawa na yunkuri da goyon bayan Ahlulbaiti (a.s) gare su, har wannan (yunkurin) ya zama tafarki da salo na aikin siyasa wanda yake da goyon bayan shari'a.
(4). Gwagwarmaya ta Siyasa: Wannan yana da muhimmancin gaske a rayuwar siyasar al'umma a duk lokacin da azzalumin shugaba ya bayyana ba ya gudanar da hukumce-hukumcen Allah Ta'ala, ba ya kuma tsaifa adalci a tsakanin mutane. Kowane Imami na Ahlulbaiti (a.s) ya shugabanci al'umma a fagen siyasa a zamaninsa, kuma ya kasance shi ne alamar bijirewa azzalumai a zukatan jama'ar musulmi. Wannan kuwa shi ne ya bai wa yunkure-yunkuren da aka yi siffar dacewa da shari'a. Halifofin Banu Umayya da Banu Abbas wadanda tarihi ya yi wa shaidar rashin lizimtar addini da barin adalci sun san irin kimar Ahlulbaiti (a.s) a zukatan musulmi, saboda haka suka bi hanyoyi daban-daban domin su nisantar da kaunar Ahlulbaiti (a.s) daga mutane, hanyoyi kamar su tsoratarwa da kai su kurkuku da kisa da rashawa da mukamai da sauransu. A matsayin misali, Mu'awiyya ya yi tawaye ga Imam Ali (a.s.) ya yake shi duk da cewa shi ne halaltaccen halifa.
Baya ga haka kuma, bai tsaya ba sai da ya yaki Imam Hasan (a.s.) ya yi tawaye wa halifancinsa, ya kashe shi da guba a shekara ta hamsin, bayan hijira.