"Hakika manyan malamai da shuwagabanni sun karbi hadisi daga Ja'afar al-Sadik, cikinsu har da: Malik bn Anas, Shu'ba bn Hajjaj, Sufyan al-Thawri, Ibn Jarih, Abdullah bn Amru, Ruh bn Kasim, Sufyan bn Uyaina, Sulaiman bn Bilal, Isma'il bn Ja'afar, Hatim bn Isma'il, AbdulAziz bn Mukhtar, Wahb bn Khalid, Ibrahim bn Dahhan da dai sauransu. Ya ce: Muslim ya fitar da hadisi cikin Sahihinsa yana mai kafa hujja da hadisinsa (Imam Sadik). Wasu kuma suka ce: Wadanda suka ruwaito daga gare shi sun hada da Malik, Shafi'i, Hasan bn Salih, Abu Ayyub al-Sajistani, Umar bn Dinar da Ahmad bn Hambal. Malik bn Anas ya ce: Ido bai ga ba, kunne bai jiba, kuma bai fado wa zuciyar wani mutum wanda ya fi Ja'afar Sadik a falala da ilmi da ibada da tsantsaini([143])".
Uztaz Shaikh Mahmud Abu Zuhra, shaihin malami a Jami'ar Azhar ta kasar Masar ya yi magana kan Imam Sadik (a.s.) a cikin gabatarwar littafinsa mai suna Imam Sadik, ya ce:
"Bayan haka; hakika mun yi niyyar mu yi rubutu kan Imam Ja'afar Sadik, da taimakon Allah da gamo da katar daga gare Shi. Hakika mun yi rubutu kan bakwai daga shuwagabanni masu daraja, ba mu jinkirta rubutu kansa domin ya kasa wani daga garesu ba, a'a, shi yana da fifikon gabatuwa bisa mafiya yawansu. Yana kuma da fifiko makebanci bisa manya-manya daga cikinsu domin Abu Hanifa ya kasance yana ruwaitowa daga gare shi yana kuma daukarsa a matsayin mafi sanin abin da mutane suka sassaba a kansa, kuma mafi kewayewa da ilmi cikin dukkan fukaha'u. Imam Malik ya kasance mai halartarsa domin karatu da ruwaya. Imam Ja'afar Sadik yana da falalar malanta kan Abu Hanifa da Malik, wannan kuwa ya isa daraja. Saboda wannan, jinkirtawa ba ta yiyuwa domin nakasinsa kuma ba a gabatar da waninsa domin fifiko. Kuma bayan haka ma shi jikan Aliyu Zainul Abidin ne, wanda ya kasance shugaban mutanen Madina a zamaninsa wajen falala da daraja da addini da ilmi, kuma mutane kamarsu Ibn Shihab al-Zuhri da kuma da dama daga cikin tabi'ai sun yi dalibta a hannunsa. Shi ne dan Muhammad Bakir wanda ya tsaga ilmi ya kai ga ainihinsa. Shi yana daga wadanda Allah Ya tattara musu daraja a zatinsu da daraja ta girman asalinsu na dangin Hashimi da kusanci da Annabi (s.a.w.a) ([144])".
Amru bn Mukdam ya kasance yana cewa: "Idan na dubi Ja'afar bn Muhammad na kan gane cewa shi daga tsatson Annabawa ya fito".
Shahararren malamin tarihin nan Ya'akubi ya siffanta Imam Sadik (a.s.) da cewa: "Ya kasance mafificin mutane, mafi ilmin addinin Allah. Mazowa ilmi wadanda suka ji daga gare shi sun kasance idan za su ruwaici wani abu daga gare shi su kance; 'Malam ya ba mu labari([145])'.
Wannan dan haske ne kadan daga sanarwar malamai da maruwaita da masu hadisi da kuma shaidarsu mai bayyana matsayin Ahlulbaiti (a.s) da bigirensun nan na ilmi da imani madaukaki.
7- Imam Musa bn Ja'afar al-Kazim (a.s.):
Batun kuma Imam Musa bn Ja'afar (a.s.) kuwa, shi ne dan Imam Ja'afar Sadik (a.s.). Ya sami tarbiyya cikin kulawan babansa wanda daga gare shi ne Imam Musa Kazim ya dibi ilmi da tsantsaini da kyawawan dabi'u. Saboda haka ne ma babansa ya masa shaida da cewa mai girman alkadari da madaukakin matsayi, da kuma cewa dansa Musa shi ne shugaban Ahlulbaiti (a.s), shi ne Imami wanda za a koma gare shi domin karbar ilmomi da masaniya.
Hadisi ya zo daga gare Imam Sadik din yana fadawa wani sahabinsa cewa: "Lallai wannan da nawa da ka gani, da za ka tambaye shi abin da yake tsakanin bangwayen Littafi guda biyu (Alkur'ani) da ya ba ka amsa da ilmi cikakke([146]).
Malaman Ilmul Rijal da na tarihi sun siffanta shi da cewa shi malami ne mai gaskiya kuma mai ibada ne wanda ya shahara da tsantsaini da takawa da girman al'amari da madaukakin halin kwarai. Za mu ambaci abin da Hafiz al-Razi ya fadi cikin littafinsa na Ilmul Rijal kan irin wannan shaidar, inda yake cewa:
"Musa dan Ja'afar dan Muhammad dan Ali dan Husain dan Ali dan Abu Dalib ya yi ruwaya ne daga babansa, shi kuma dansa Ali bn Musa da dan'uwansa Ali bn Ja'afar sun ruwaito daga gare shi, ya ce; Na ji babana yana fadawa Abdurrahman cewa: An tambayi babana game da shi sai ya ce: Mai gaskiya ne, mai yawan gaskiya, shugaba daga shuwagabannin musulmi([147])".
Muhammad bn Ahmad al-Zahabi ya fadi game da shi cewa: "Musa ya kasance daga masu (gwanayen) hikima kuma daga bayin Allah masu tsoron Allah([148])".
Kamaluddin Muhammad bn Dalha al-Shafi'i ya ce: "Shi ne shugaba mai girman alkadari, mai madauka-kin al'amari, babban mujtahidi mai kyautata ijtihadi, wanda ya shahara da ibada, mai dogewa bisa biyayyar Allah, wanda ya shahara da karamomi. Yana kwana yana sujjada da tsayuwa, cikin yini kuwa yana mai sadaka da azumi. Saboda tsananin afuwarsa da kauda kai ga barin masu zaluntarsa aka yi masa lakabi da Kazimu (mai hadiye fushi) ([149])".
Mu'umin Shabalanji ya ce: "Musa al-Kazim (r.a.) ya kasance mafi yawan ibada a zamaninsa kuma mafi ilmi([150])".
8- Imam Aliyu bn Musa al-Ridha (a.s.):
Amma batun dansa wato Aliyu bn Musa al-Ridha (a.s.) kuwa, to hakika ya kasance tamkar mahaifinsa wajen ilmi da tsantsaini da cikar kyawawan halaye. Ya karbi ragamar shugabancin addini da nauyin Imamanci a bayan babansa. Ya kai matsayi mai daukaka da daraja wanda ya tilastawa halifan Abbasiyawa Ma'amun ya nada shi magajinsa a bayansa, duk da gaba da fito-na-fito da ke tsakanin Alawiyyawa da Abbasiyawa.
Hakika malamai sun ba da shaida a majalisun ilmi da muhawara, kan matsayin Imam Ali Ridha wajen ilmi da karimci da siffantuwarsa da tsantsaini da takawa.
Ga wasu daga cikin wadannan maganganu:
Al-Wakidi ya ce: "Ya kasance mai gaskiya, yana ba da fatawa a masallacin Manzon Allah (s.a.w.a.) alhali yana dan shekara ashirin da 'yan kai. Yana daga dabaka ta takwas ta tabi'ai na mutanen Madina([151])".
Amma babansa Musa bn Ja'afar (a.s.) wanda muka riga da muka san matsayinsa na ilmi da tsantsaini da tsoron Allah, shi ma ya ba da shaidar ilmin Aliyu bn Musa al-Ridha da kuma shiryarwa zuwa ga karbar addini da shiriya daga gare shi, inda yake cewa:
"Wannan dan'uwannaku Ali bn Musa, shi ne mafi sani a duk mutanen gidan Muhammadu, don haka ku tambaye shi batun addininku, kuma ku kiyaye abin da yake fada muku([152])".
9- Imam Muhammad bn Aliyu al-Jawad (a.s.):
Amma Imam Jawad (a.s.), shi ma tamkar mahaifa da magabatansa tsarkaka yake wajen ilmi da zuhudu da kuma tsoron Allah.
Sibd bn Al-Jawzi yana cewa: "Muhammad al-Jawad shi ne Muhammad bn Ali bn Musa bn Ja'afar bn Muhammad bn Ali bn Husain bn Ali bn Abi Dalib. Sunan kunyarsa shi ne Abu Abdullah, wasu kuma su kan ce masa Abu Ja'afar. An haife shi ne a shekara ta 165 bayan hijira, ya yi shahada kuma a shekara ta 220, ya kasance bisa tafarkin babansa wajen ilmi da takawa da zuhudu da kyauta([153])".
Muhammad bn Ammar ya ruwaito cewa: "Na kasance wajen Ali bn Ja'afar(*) bn Muhammad a Madina, na kasance a wajensa har na tsawon shekara biyu ina rubuta abin da na ji daga wajen dan'uwansa (Imam Musa bn Ja'afar Kazim) sai Abu Ja'afar Muhammad bn Ali Ridha ya shiga masallacin Manzon Allah (s.a.w.a.), sai Ali bn Ja'afar ya yunkura ya mike ba takalmi ba abaya, sai ya sumbanci hannunsa ya girmama shi.
Sai Abu Ja'afar ya ce da shi: "Ya baffana, zauna mana, Allah Ya yi maka rahama".
Sai ya ce: "Ya shugabana, ya ya zan zauna alhalin kana tsaye?! Yayin da Ali bn Ja'afar ya dawo gurin zamansa sai abokansa suka dora sukarsa, suna cewa: 'Kai baffan babansa ne kuma ka ke yi masa haka!!
Sai ya ce: "Ku saurara - sai ya kama gemunsa - idan Allah Mai girma da Daukaka bai nufi wannan furfurar da cancantar shugabanci ba amma Ya nufi wannan saurayin, Ya kuma ajiye shi inda Ya ajiye shi, shin zan yi inkarin falalarsa ne? Muna neman tsarin Allah daga abin da kuke fadi, kai bari dai ni bawansa ne ma([154])!".
Mahmud bn Wuhaib al-Bagdadi al-Hanafi ya ce: "Muhammad al-Jawad bn Ali al-Ridha, sunan kunyarsa shi ne Abu Ja'afar", daga nan sai ya ce: "shi ne magajin babansa wajen ilmi da fifiko, ya fi duk 'yan'uwansa daraja da kamala([155])".
10- Imam Aliyu bn Muhammad al-Hadi (a.s.):
Amma Imam Ali al-Hadi (a.s.) dan Imam Muhammad al-Jawad (a.s.) lallai yana da falala mai girma da daukakar al'amari wajen ilmi da tsantsaini, tamkar abin da Mahaifansa masu kyauta suke da shi. Ana masa alkunya da Abul Hasan.
Mu'min al-Shabalanji ya ce: "Ya kasance mai yawan munajati (addu'a), an fadi cikin al-Sawa'ik cewa: Abul Hasan ya kasance magajin babansa wajen ilmi da kyautattaki([156])".
Abdulhayy bn al-Ammad al-Hambali ya ce: "Abul Hasan, Ali bn Muhammad bn Ali al-Ridha bn al-Kazim, Musa bn Ja'afar al-Sadik, ba'alawiyye, bahusainiyye, wanda aka fi sani al-Hadi, ya kasance fakihi ne kuma shugaba mai yawan ibada([157])".
Alhafiz Imaduddin Abul Fida, Isma'il bn Umar bn Kathir yana cewa: "Shi Abul Hasan, Ali al-Hadi, shi ne dan Muhammadal-Jawad dan Ali al-Ridha dan Musa al-Kazim dan Ja'afar al-Sadik dan Muhammad al-Bakir dan Ali Zainul Abidin dan Husain al-Shahid dan Ali dan Abi Dalib, daya daga Imamai goma sha biyu. Shi ne baban Hasan bn Ali al-Askari. Ya kasance mai yawan ibada mai zuhudu. Mutawakkil al-Abbasi ya mai da shi garin Samarra, inda ya zauna a can sama da shekaru ashirin da watanni, ya kuma yi shahada ne a can a shekara ta 254 bayan hijira([158])".
An ruwaito daga Yahya bn Harthama wanda Mutawakkil, sarkin Abbasiyawa, ya aika domin taho da Imam Hadi (a.s.) daga Madina zuwa Samarra, ya ce:
"Sai na tafi Madina, da na shiga garin sai mutanenta suka yi kuwwa mai tsanani wanda ba a taba jin irin ta ba, su na masu tsoron wani abu zai faru da Ali. Suna nuna wannan damuwa ce saboda ya kasance mai kyautata musu, mai lizimtar masallaci, ba ya wata karkata zuwa ga duniya. Sai na fara kwantar musu da hankali, ina rantse musu cewa ba a umurce ni da munana masa ba kuma na zo cutar da shi ba ne. Daga nan sai na binciki gidansa, ban sami kome bai sai Kur'ani da addu'oi da littattafan ilmi, a saboda haka sai na ga girmansa ya daukaka a idanuwana([159])".
11- Imam Hasan bn Aliyu al-Askari (a.s.):
Imam Hasan al-Askari kuwa shi ne dan Imam Ali al-Hadi (a.s.), shi ma tamkar mahaifansa masu kyautatawa yake wajen ilmi, masaniya, tsantsaini da jihadi. Malamai da ma'abuta tarihi sun ba da shaidar hakan. Za mu ambaci kadan daga cikin wadannan maganganu na masana, kamar haka:
Shamsuddin Abu Muzaffar, Yusuf bn Faragili, jikan bn Al-Jawziyya, yace: "Ya kasance malami mai gaskiya, ya ruwaito hadisi daga babansa da kakansa([160])".
1. Ali bn Sabbag al-Maliki ya ce:
"Darajojin shugabanmu Abu Muhammad Hasan al-Askari suna nuni da cewa shi mai daraja ne dan mai daraja, babu wanda ke shakka ko kokwanton imaman-cinsa. Kuma na san cewa da ana sayar da karimci da waninsa ne mai saye shi kuwa mai sayarwa. Shi tilo ne a zamaninsa ba shi da na biyu, ba a kwatanta shi da kowa, ba shi da kishiya. Shi ne shugaban mutanen lokacinsa, shi ne kuma Imaminsu. Zantuttukansa daidaitattu ne, ayyukansa kuwa abin yabo([161])".
12- Imam Muhammad bn Hasan al-Mahdi (a.s.):
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Ranaku da darare ba za su kare ba har sai Allah Ya tasar da wani mutum cikin Ahlulbaitina sunansa kamar sunana, zai cika kasa da adalci kamar yadda aka cika ta da zalunci da danniya([162])".
An karbo daga Ali bn Abi Dalib (a.s.) daga Annabi (s.a.w.a) cewa ya ce: "Da a ce babu abin da ya saura na lokaci face yini guda, to da Allah Ya tasar da wani mutum daga cikin Ahlulbaitina ya cika kasa da adalci bayan an cika ta da zalunci".
Haka Abu Dawud ya kawo hadisin cikin Musnad dinsa. Kuma Abu Dawud din da Tirmidhi sun ruwaito shi cikin Sunan dinsu, kowannensu daga Abu Sa'id Khudri (r.a.) ya ce: "Na ji Ma'aiki (s.a.w.a.) yana cewa: "Mahdi daga gare ni yake, goshinsa mai fadi, mai dogon hanci, zai cika kasa da adalci kamar yadda aka cika ta da zalunci".
Abu Dawud ya kara da cewa: "Zai yi mulkin shekaru bakwai, ya kara da cewa hadisi ne tabbatacce mai inganci([163]).
Hadisan da suka zo ta hanyoyin malaman hadisi da ruwaya daga mazhabobin musulmi daban-daban, suna da yawa ainun, dukkansu sun tafi a kan cewa sunan Mahdi shi ne Muhammadu, kuma shi cikin Ahlulbaitin Annabi (s.a.w.a) yake. Sai dai sun saba kan ko waye shi. Abin da ya tabbata wajen mabiya Ahlulbaiti (a.s) da ma wasu ban da su shi ne; shi Mahdi shi ne Imam Muhammad bn Hasan al-Askari bn Ali Hadi bn Muhammad al-Jawad bn Ali Ridha bn Musa al-Kazim bn Ja'afar Sadik bn Muhammad Bakir bn Ali Zainul Abidin bn Husain bn Ali bn Abi Dalib (a.s.). Kuma an haife shi a tsakiyar watan Sha'aban shekara ta 255 bayan hijira, a garin Samarra. Kuma da ikon Allah, bai gushe ba yana nan a fake, zai bayyana a wani lokaci da kasa za ta cika da zalunci da danniya domin ya cika ta da adalci, kamar yadda hadisai suka nuna. Da kuma cewa Annabi Isa (a.s.) zai yi salla a bayansa. Wannan shi ne takaitaccen bayani kan Imaman Ahlulbaiti (a.s) da mukaminsu da kuma matsayinsu.
Daga gare su ne aka karbi ilmi fikihu da hadisi da tafsiri da ilmummukan akida da shari'a da dai sauransu.

Tauhidi A Tafarkin Ahlulbaiti (a.s)
"Farkon addini sanin Allah, cikar saninSa kuwa kadaita Shi, cikar kadaita Shi kuwa tsarkake niyya gare Shi([164])".
"Allah ba Ya karbar aiki ba tare da an sanShi ba, babu kuma yadda za a sanShi sai da aiki. To wanda ya sani sanin zai shiryar da shi zuwa aiki, wanda kuwa bai yi aiki ba, to ba sani a gare shi. Ku saurara! Lallai shi imani sashinsa daga sashe yake([165])".
Tauhidi ka'ida ce ta Musulunci, shi ne kuma ginshikin fahimta da tunani, kuma shi ne matattarar ilmi da aiki. Shi ne matakin farko da kuma ka'idar sauya shari'a da ka'idoji da halaye kwarai da kuma tafarkin tunani.
Manufar Tauhidi tana matsayin ginshiki wajen gina wayewa ta Musulunci wacce ta kebanta da rininta na tauhidi; Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: "Rinin Allah! Kuma wane ne mafi kyau ga rini daga Allah? Kuma mu, a gare Shi, masu bautawa ne". (Surar Bakara, 2: 138)
Rinin nan na tauhidi wanda ya banbanta wayewa irin ta Musulunci daga wata wacce ba ita ba, kuma wanda shi ya ba ta siffofi iyakantattu na aike (daga Allah) shi ya sanya wa rayuwar musulmi da tunaninsa wani zubi kebantacce.
Lallai Alkur'ani mai girma da Sunna mai tsarki su ne tushen tunani na matsalolin akida. Hakika sun ba mu bayani cikakke kan akidar tauhidi, sun bayyana mana samuwar Allah Mahalicci, Mai Girma da Daukaka, sun kebance mana bayanin siffofinSa na kamala tare da tabbatar masa da cikakkiyar tsarkaka daga dukkanin nakasa. Ginshikan wannan akidar ta tauhidi sun cika, musulmin farko kuwa sun yi imani da su, kamar yadda suka ji su daga Manzon Allah (s.a.w.a.) suka kuma karanta su cikin Littafin Allah Mai Daukaka.
Addinin Musulunci ya watsu yayin da aka ci kasashe da yaki, al'ummai masu wayewa da falsafar jahiliyya kamar su Farisa da Hindu da Sin, sun shigo Musulunci. Haka nan mutane mabiya karkatattun addinan Kiristanci da Yahudanci wadanda kuma sun sami tasirin falsafa da akidojin Kiristanci da Yahudanci su ma sun shigo Musulunci. A hada da abin da aka debo daga tunani da falsafar Yunaniyawa da masu kama da su. Duk wannan ya tsirar da jayayya da shakku, sannan karairayi da bakin manufofi suka shigo akidar tauhidi, yayin da wannan wayewar mai rusawa ta kutsa kai, sai aka samu cewa akidar tauhidi ta kada ta yi rauni a wajen wadanda suka shagalta da bahasi kan akida da ilmin falsafa. Matsaloli da suka shafi rawar da dan'Adam yake takawa a ayyukansa kamar su Jabr (watau tilastawa) da tafwidh (ba da ikon zabi) da kuma Guluwi (masu wuce gona da iri) da tajsim (kudurta cewa Allah jiki ne) da bayani kan Isra'i da Mi'iraji, duk irin wadannan suka taso, da rudani cikin tunanin mutane. Sakamakon haka sai aka sami mazhabobi da kungiyoyi daban-daban suka tsiro tare da akidoji karkatattu, manisanta daga akidar asali ta tauhidi. Wannan ya sa Imaman Ahlulbaiti (a.s) da malamai masu tunani irin na Musulunci sun shiga fagen fama da masu wadannan karkatattun akidu. Jayayyar da har a wannan zamanin gurbinta bai gushe ba, duk da cewa sashin karkatattun kungiyoyin ya bace. Wannan fama da jayay-ya tsakanin wasu kungiyoyi daban-daban ya wanzar da gurabansa masu kyau da kuma munana, ana iya ganinsu cikin tunanin musulmi na akida da mafuskantar bayanin matsalolin akida.
Saboda abin da Allah (S.W.T.) Ya yi baiwa da shi ga Ahlulbaiti (a.s) na tsarkakar fahimta da kewayewa ga dukkan ilmomin shari'a da sanin Allah da kiyayewarsu da ilmin Littafin Allah da na Sunnar Annabi (s.a.w.a), lallai su da mazhabarsu sun taka rawar gani wajen warware rikice-rikice da rusa karkatattun ra'ayuyyuka da kuma kare manufar tauhidi da tsare tsarkinta. Muna da muhawarorin Imaman Ahlulbaiti (a.s) da hadisansu da tafsiran ayoyin tauhidi da bayanansu masu gusar da rudani domin fahimtar Musulunci ta gudana bisa tafarkinta na asali ba tare da karkata ba ko mummunan fahimta wa ayoyin da yi musu tafsiri na son zuciya ko bin wata batacciyar falsafa, karkatacciya. Wannan bayani na Imamai kan fahimtar Littafin Allah da saninsu da Allah (S.W.T.) ya haifar da wani tunani hadadde mai riko da akidar tauhidi.
Idan mutum ya yi nazarin al'amarin akidar tauhidi da rassanta da matsalolinta bisa tafarkin Ahlulbaiti (a.s) zai riski tsarkaka da zurfin sha'anin tauhidi, kuma zai gane cewa ginshikin akida da duk wata wayewa shi ne kadaita Allah (S.W.T.). Daga nan za a gane cewa akidar tauhidi ta ginu ne bisa tushen; "Tabbatar da cikakken kamala ga Allah (S.W.T.) da tsarkake Shi daga dukkan tawaya da kuma kore duk wani abokin tarayya ko makamanci ko tamka ko kuma kishiya".
Imam Ali (a.s.) ya kafa tushen wannan mahanga ta tauhidi da cewa: "Tauhidi shi ne kada ka takaita Allah cikin rayawarka takaitacciya, adalci kuwa shi ne kada ka dora wa Allah tuhuma([166])". A cikin hadisai da muhawarori masu yawa, Imaman Ahlulbaiti (a.s) sun tabbatar da akidar tauhidi tare da raddi kan rudanin da mabarnata da zindikai kamar su Aldaisani da Ibn Abi Al-Awja'a da ibn Almukaffa da mulhidai da 'yan gullatu da 'yan jabru da tafwid da makamantarsu, suka shigar.
A nan za mu kawo wani sashe na wadannan asasai na tauhidi wadanda suke nuna akidar Alkur'ani da kuma ayyana tushen ilmi, tunani na tauhidi, tsabtansa da kuma asalinsa.
Imam Sadik (a.s.) ya ruwaito Amirul Muminina (a.s) yana cewa: "Ku nemi sanin Allah ta hanyar Allah, Manzon Allah kuma ta hanyar sakon (Musulunci), wadanda aka ba su shugabanci (Ulul Amri) kuwa ta wajen umurninsu da kyakkyawa da haninsu ga mummunan aiki da adalci da kyautatawa([167])".
Alfath bn Yazid ya ruwaito daga Imam Ali bn Musa Ridha (a.s.) cewa: "Na tambaye shi kan mafi kankantar sanin Allah, sai ya amsa min da cewa:"shi ne yarda da kuma furuci da cewa babu abin bauta koma bayan Allah, babu makamancinSa, babu tamkarSa kuma Shi Dawwamam-me ne ba mai gushewa ba, da kuma cewa babu wani abu tamkarSa([168])".
Nafi'u bn Al-Azrak ya tambayi Imam Abu Ja'afar, Muhammad Bakir (a.s.) cewa: "Ka ba ni labari yaushe ne Allah Ya kasance?, sai ya ce: "Yaushe ne bai kasance ba har zan ba ka labarin lokacin da Ya kasance? Tsarki ya tabbata wa Wanda bai gushe kuma ba zai gushe ba, Makadaici, Wanda ake nufinSa da bukata, bai riki abokiyar zama ba ko kuma da([169])".
Imam Sadik (a.s.) ya ruwaito cewa wani malamin yahudawa ya taho ma Imam Ali (a.s.) yana tambayarsa cewa: "Ya Amirul Muminina! Yaushe Ubangijinka Ya kasance? Sai ya ce masa:"Tir da kai, ana 'yaushe ya kasance' ga Wanda ba samamme ba ne? Amma wanda samamme ne ba da wani ba, ba a ce wa 'yaushe ya samu'. Shi Allah samamme ne gaban gabani ba tare da wani 'gabani' ba kuma samamme ne bayan 'baya' ba tare da wani 'baya' ba, kuma babu wai iyakar karshe da za a ce karshenSa ya kai iyaka". Sai malamin ya ce da Imam: "Kai Annabi ne?", Sai Imam (a.s.) ya amsa da cewa: "Kaitonka, ni ba kowa ba ne face bawa cikin bayin Manzon Allah (s.a.w.a.) ([170])".
Imam Bakir (a.s.) ya ce: "Na hane ku yin tunani kan Allah, sai dai duk yayin da kuke nufin duban buwayar Allah to ku dubi girman halittun Allah([171])".
Imam Sadik (a.s.) ya yi wasiyya ga wani sahabbinsa (Muhammad bn Muslim) da cewa: "Ya Muhammad! Su mutane, magana ba za ta gushe gare su ba har sai sun yi magana kan (zatin) Allah. To idan kun ji ana hakan ku ce: 'Babu abin bauta face Allah Makadaici, Wanda babu wani abu tamkarsa([172])'".
Imam Bakir (a.s.) yana cewa: "Ku yi magana kan kome, kada ku yi magana kan batun zatin Allah([173])".
Yayin da wani ya tambayi Imam Ali (a.s.) cewa: 'Ina Allah Yake gabannin Ya halicci halitta', sai Imam ya yi masa bayani cewa Allah ba Shi da bukatar bigire, Ya karfafa tsarkakar Mahalicci Madaukaki ga barin wannan, haka nan tsarkakke Ya ke ga barin bukatuwa ya zuwa ga zamani. Wani mai tambayan kuma ya tambaye shi cewa: 'Ina Ubangijinmu Yake kafin Ya halicci sama da kasa?, Sai Imam (a.s.) ya amsa da cewa: "Ina tambaya ce kan bijire, Allah kuwa Samamme ne yayin da ba a samar da bigire ba([174])".
Yayin da kuma aka tambaye shi kan ganin Allah (S.W.T.) sai ya tsarkake Allah ga barin ganuwa. Ga tambayar: "Ya Amirul Muminina! Shin ka ga Ubangijinka lokacin da kake bauta masa? Sai ya ce: "Kaitonka! Bana bautar Ubangijin da ban ganshi ba", sai ya ce masa to yaya ka gan shi?, sai Imam (a.s.) ya amsa masa da cewa: "Tir da kai, idanu ba sa riskar Allah da gani irin na ido, sai dai zukata sun gan Shi da matabbatan imani([175])".
Muhammad bn Hakim ya ce: "Abul Hasan Musa bn Ja'afar (a.s.) ya yi rubutu ya aike wa babana cewa: "Allah (S.W.T.) Ya daukaka, girmanSa ya buwaya ga barin riskar ainihin siffarsa. Ku siffanta Shi da abin da Ya siffanta kanSa da shi, ku kuma kame ga barin koma-ba-yanSa([176])".
Al-Mufaddal ya ce: 'Na tambayi Abul Hasan wani abu kan sifa, sai ya ce: "Kada ku ketare abin da ya ke cikin Alkur'ani([177])".
Abdur Rahman bn Atik Alkasir ya ce: 'Na rubuta tambaya zuwa Abu Abdullah al-Sadik (a.s.) ta hannun Abdul Malik bn A'yun cewa: "Wasu mutane a Iraki suna siffanta Allah da wani yanayi da kuma kama, to idan ka yarda, Allah Ya sanya ni fansarka, ina so ka rubuto min da bayani kan ingantac-cen matsayi kan tauhidi. Sai ya rubuto mini da cewa: "Ka yi tambaya - Allah Ya jikanka - kan tauhidi da kuma abin da wadannan mutane suke fadi. Daukaka ta tabbata ga Allah Wanda babu wani abu tamkarSa, Shi ne Mai ji, Mai gani. Allah Ya daukaka ga barin siffantawar masu siffantawa, wadanda suke kamata Allah da halittarSa, masu kage wa Allah. To ka sani -Allah Ya rahamshe ka- cewa ingantacce tafarki wajen tauhidi shi ne abin da Alkur'ani ya saukar da shi na siffofin Allah Mai Girma da Daukaka. To ka kore ga barin Allah (S.W.T.) dukkan korewa da kamantawa, domin babu korewa ba kuma kamantawa. Shi ne Allah Tabbatacce Ya daukaka ga barin siffantarwar masu siffantawa. Kada ku ketare Alkur'ani ku bata bayan (cikakken) bayani([178])".
Batun dayantuwar zatin da tsarkake shi ga barin kama da halitta kuwa, Hamza bn Muhammad ya ce: 'Na rubuta tambaya ga Abul Hasan Al-Kazim (a.s.) kan jiki da kama (da ake danganawa ga Allah), sai ya rubuto min cewa: "Tsarki ya tabbata ga Wanda babu wani abu tamkarSa, ba jiki babu kama([179])".
Haka nan muke karanta tauhidi tsarkakakke, kubutacce na Allah (S.W.T.) a mazhabar Ahlulbaiti (a.s) da karantarwarsu da ke nuna ainihin ruhin Alkur'ani da abubuwan da yake tattare da su, da abin da ayoyinsa suka kunsa. Da wannan ne suka tabbatar da akidar tauhidi, suka kore barnace-barnace da shubuhohi da bata wadanda aka jarrabi tunanin Musulunci a wancan lokacin. Haka kuma wannan bayani yake raddi kan batattu da karkatattun 'yan gulatu(*) (masu wuce gona da iri wajen soyayya), 'yan Mufawwida (masu cewa an bar dan'Adam haka kawai a sake komai yayi daga gare shi ne), 'yan Mujassima (masu siffanta Allah da jiki), 'yan Hululi (masu akidar cewa Allah Yana shiga wasu halittu) da kuma masu akidar haduwa, wato Allah Ya hadu da halittanSa suka zama abu guda.
Haka kuma bayanan Ahlulbaiti (a.s) sun fayyace al'amurra wa wadanda suka shiga rudani suka cudanya tafarkin Ahlulbaiti (a.s), tsarkakakke na gaskiya, wanda bai yarda da karairakin 'yan gulatu da 'yan mufawwida da 'yan hululi ba wadanda suka yi da'awar suna bin Ahlulbaiti (a.s), da wadancan kungiyoyi na bata.
Sau da yawa masu neman raba kan musulmi suna cudanya gaskiya da karairayi, suna karkatar da gaskiya, suna kage da kuma gafalantar da jahilai domin shuka gaba da raba kan al'umma da taimaka wa abokan gaba.

Adalcin Allah Da Sharhi Kan Halayyar Dan'adam
"Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai Hikima". (Surar Aali Imrana, 3: 18)
Adalci siffa ce, cikin siffofin Allah (S.W.T.). Muna iya ganin gurabun adalcinSa a dukkan bangarorin samammu, kamar fagen halitta da samarwa da fagen dabi'a da halittar mutum da dabba da tsiro, haka kuma muna ganin wannan adalcin cikin shari'a da dokokin Ubangiji. "Lalle Allah Na yin umurni da adalci da kyautatawa". (Surar Nahli, 16: 90)
Haka ma adalcin Ubangiji ya bayyana cikin abin da Yake hukumtawa da kaddarawa kan halittunSa na hukumci da kaddara, da cikin abin da Ya shar'anta na shari'u da sakonni. Kamar yadda yake bayyana a fagen lahira, ranar hisabi da sakamako. Zai sakantawa mai kyautatawa da kyautatawar, mai mummunan aiki kuwa da irin aikinsa. "Kuma Ubangijinka ba Ya zaluntar kowa". (Surar Kahf, 18: 49) "Sa'an nan kuma a cika wa kowane rai abin da ya sana'anta". (Surar Bakara, 2: 281)
"Allah ba Ya kallafawa rai face ikon yinsa, yana da ladan abin da ya aikata, kuma a kansa akwai zunubin abin da ya yi ta aikatawa...". (Surar Bakara, 2: 286)
Bisa wannan tsarin ne musulmin farko suka tafi wajen fahimtar alakarsu da Allah (S.W.T.) da fahimtar halayyar 'yan Adam da ayyukansu. Daga bisani sai falsafa ta shigo ga kuma ra'ayoyin ilmin tauhidi dukkansu masu sassabawa juna. Hakika wadannan sun tsirar da ra'ayoyi uku kan fassarar ayyukan mutane da alakarsu da iradar (nufi) Allah Madaukakin Sarki. Wadannan ra'ayoyi kuwa su ne:
1. Jabru (Tilastawa).
2. Tafwidhu (Sakarwa).
3. Babu Jabru ballantana Tafwidhu.
Hakika wadansu kungiyoyi da mazhabobi sun yi mummunan fahimta wa zahirin wadansu ayoyin Alkur'ani, kamar fadinSa (S.W.T.) cewa: "Zahirinsu ya sanya irin wannan kungiya suka yarda da Jabru. Abin da wannan ra'ayi yake nufi shi ne dan'Adam ba ya mallakar nufi kuma ba shi da zabi, shi ba kome ba ne face bigire da gurin saukar kaddararrun abubuwa daga Allah (S.W.T.). A bisa wannan ra'ayi, mutum abin tilastawa ne, ba shi da wani zabi cikin al'amurransa. Masu irin wannan ra'ayi ana kiransu da sunan Mujabbira.
Ra'ayi na biyu kuwa shi ne mai cewa an sakar wa dan'Adam ikon zabi wajen ayyukansa, da kuma nufinsa babu nufin Allah a cikin ayyukansa. Kai suna ganin ma cewa Allah ba Ya iya hana mutum yin abin da ya yi nufin yi ko sabo ne kamar kisan kai, zalunci, shan giya, ko kuwa ayyukan biyayya ne kamar su adalci, kyautatawa, salla da dai sauransu. To da wannan, dan'Adam yana da 'yanci ga barin Allah (S.W.T.), wannan kuwa shi ne ra'ayin Mu'utalizawa.
To Imaman Ahlulbaiti (a.s) sun yi raddi wa wadannan ra'ayoyi guda biyu, sun nuna bacinsu gaba daya. Kowanne daga ra'ayoyin nan biyu sun saba da abin da Alkur'ani ya zo da shi, akidar tauhidi kuwa ta kafu kan tushensa ne. su Imamai (a.s.) sun fayyace mana cewa akwai bayyananniyar alaka tsakanin irin yadda ake fahimtar halayyar mutum da imani da adalcin Allah. Suka ce lallai abin da ra'ayin cewa mutum ba ya mallakar wani nufi ko zabi sai dai shi abin tilastawa ne kurum, yana janyo tuhumtar Mahalicci Mai girma da Daukaka da zalunci da kore adalci daga gare Shi, lallai kuwa Ya girmama daga hakan. Saboda ma'anar wannan shi ne Allah Ya tilastawa mutum aikata sharri sannan kuma Ya yi masa ukuba dominsa, haka nan Ya tilasta masa aikata alheri sannan kuma Ya hana shi ladansa. Domin haka ne Imamai (a.s.) suka kakkabe wannan mumunan fassara wanda da yawan musulmi suka fada ciki a dalilin gurguwar fahimtar da suka yi wa zahirin wadansu ayoyi kamar cewa: "Yana batar da wanda Ya so, Yana kuma shiryar da wanda Ya so".
Imaman Ahlulbaiti (a.s) sun yi wa matsalolin shiryarwa da batarwa tafsiri bayyananne mai dacewa da adalcin Allah (S.W.T.). Bayanin wannan yana tafe.
Haka nan kuma Imamai (a.s.) sun yi watsi da ra'ayin masu cewa an sakarwa mutum akala sai yadda ya ga dama zai yi, ba tare da Allah Yana iya hana shi ba. Sun bayyana cewa wannan ra'ayi karkatacce da cewa tuhumar Allah ne da rashin cikakken iko kan bayinSa da gajiyawarSa kan hakan. Alhali kuwa Allah (S.W.T.) Mai cikakken iko ne, kuma Mamallakin dukkan halittunSa.
Imamai (a.s.) suna da matsaya matsakaiciya dangane da al'amarin da ya shafi adalcin Ubangiji. Wannan matsaya tana kore Tilastawa da Sakarwa, tana cewa: (Nufin mutum baya iya rabuwa da nufin Allah). Sun bayyana wannan alakar da take tsakanin nufin mutum da nufin Ubangiji bayani cikakke a akidance. Nan gaba za mu kawo ruwayoyinsu masu nuna wannan ra'ayi.
Kafin mu kawo wadannan ruwayoyi, bari mu yi dan sharhi kan batutuwan da mazhabar Ahlulbaiti (a.s) suka bambanta da masu ra'ayoyi kan mas'alar adalcin Allah, bisa abubuwa guda uku na asasi:
Dan'Adam yana da nufi da ikon zabin duk aikin da zai yi, ko na alheri ko na sharri, haka kuma kin aikata shi. Mutum yana iya kisan kai ko sata ko zalunci ko karya, da wannan nufin da ikon da yake da shi. Haka kuma yana da daman tsai da adalci da aikata aikin kwarai da yin salla da barin haramtattun abubuwa, da wannan nufi nasa da iko.
Hakika Allah (S.W.T.) Yana da ikon hana mutum kowane aiki, kamar yadda yake da ikon sa mutum aikata kowane aiki ba tare da zabin mutum ya sami tasiri ba. Sai dai Allah ba Ya tilastawa kowa aikata alheri ko sharri.
Amma Shi Allah, domin tausayinSa da jin kanSa, Yana shiga tsakanin bawan da ya cancanci taimakonSa wajen aikata mummunan aiki, domin jin kai. Haka ma Yana taimaka masa wajen aikata alheri idan ya cancanci taimakon.
1. Wani abin da yake da dangantaka da adalcin Ubangiji kuma shi ne: Allah Yana sakantawa kowane mutum ranar kiyama da abin da ya aikata, alheri ko sharri. Sai dai kuma wata kungiyar ta musulmi tana ganin cewa mai yiyuwa ne Allah Ya shigar da mai kyautata aiki cikin wuta, mai mummunan aiki kuma aljanna, suna kuma dogara ne, bisa kuskure da mummunan fahimta, kan wannan aya mai girma: "Ba a tambayarSa ga abin da Yake aikatawa, alhali kuwa su ana tambayarsu". (Surar Anbiya, 21: 23)
Wasu jama'a daga cikin musulmi sun dogara da wannan ayar ne bisa tafsiri na kuskure, suka ce ba ya wajaba kan Allah (S.W.T.) Ya cika alkawarin sakayya da Ya yi a ranar kiyama. Imaman Ahlulbaiti (a.s) sun mai da martani kan wannan zance da cewa, wannan ya sabawa gaskiyar Allah Ta'ala da adalcinSa.
Wancan ra'ayin yana daidaita mai kyautatawa da mai mummunan aiki, hakan kuwa yana rusa kimar kallafawa bayi da kuma sanya shari'a. Ingantaccen zance dai shi ne babu wani aikin da ba shi da sakamako, ko kuma mai daukar laifin yinsa, kamar yadda aya ta ce:
"To wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai ganshi. Kuma Wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi". (Surar Zalzala, 99: 7-8)
2. Ra'ayoyin sashin musulmi sun tafi a kan cewar ya dace ga Allah (S.W.T.) Ya kallafawa bayi abin da yafi karfinsu, wannan kuwa sun fade shi ne domin dogara kan fahimta ta kuskure da suka yi wa wannan aya mai girma: "Ya Ubangijinmu Kada Ka sanya mu daukar abin da babu iko gare mu da shi". (Surar Bakara, 2: 286)
Imaman Ahlulbaiti (a.s) sun kore wannan fahimta suna masu bayanin cewa ta saba da adalcin Allah da kuma bayyanannen fadi na Alkur'ani mai girma, cewa: "Allah ba Ya kallafa wa rai face abin da zai iya dauka". (Surar Bakara, 2: 286)
To yanzu za mu kawo sashen ruwayoyi da tattauna-war Ahlulbaiti (a.s), masu mana sharhin wadannan ginshikai na asali da fassara halayyar mutum da alakar da ke akwai tsakanin nufin mutum da ta Allah (S.W.T.). Wadannan ruwayoyi suna kulla tafsiri da sharhin halay-yar mutum da tushen adalcin Allah domin su karfafa mana dayantaka (ta Ubangiji) fahimta da tunani da kuma i'itikadi cikin sakon Musulunci. A lokaci guda sun bata ra'ayin Jabru da Tafwidhu da ma dukkan sauran tunace-tunace da kirdado wadanda suka fice daga tafarkin Alkur'ani.
Imam Sadik (a.s.) ya ce: "Allah Ya halicci halittu Ya kuma san makomarsu. Ya umarce su (da ayyukan biyayya) Ya hane su (ayyukan sabo). Kuma bai umarce su da abu ba face Ya sanya musu hanyar barin abin. Ba su zamowa masu riko (da umarnin) ko masu bari face da izinin Allah([180])".
Yayin da Imam Ali bn Abi Dalib (a.s.) ya tafi kasar Sham (Syria), domin yakar Mu'awiyya a Siffin, wani daga sahabbansa ya tambaye shi cewa:
"Ya Amirul Muminina! Ka ba mu labarin wannan tafiya tamu, shin da hukumcin Allah ne ko da kaddararSa?" sai ya amsa masa da cewa: "Saurara dattijo, na rantse da Allah ba kwa hawan wani tudu ko ku gangara cikin wani kwari face bisa hukumcin Allah da kaddararSa".Sai Dattijon ya ce: 'Ga Allah nake neman ladar wahalata, Ya Amirul Muminina'. Sai Imam Ali (a.s.) ya ce da shi:"Kaiconka! Ta yiyu kana zaton hukumci lizimtacce da kaddara yankakkiya! Da haka al'amarin yake da sakamako da horo sun baci, kuma da alkawari da narko sun warware. Allah (S.W.T.) Ya umarci bayinSa bisa zabinsu, Ya hana su domin gargadi, Ya kallafa musu sassauka bai kallafa musu mai tsanani ba, Yana biyan kadan da mai yawa. Ba a saba masa domin rinjaya, ba a tilastawa don a yi maSa biyayya. Bai aiko Annabawa don wasa ba, kuma bai sauko da Littafi wa bayi haka a banza ba. Bai kuwa halicci sammai da kasa da abin da yake tsakaninsu a banza ba; "Wannan shi ne zaton wadanda suka kafirta. To, bone ya tabbata ga wadanda suka kafirta daga wuta([181])".
An ruwaito daga Imam Ali bn Musa al-Ridha (a.s.) cewa an ambaci Jabru da Tafwidhu a gabansa, sai ya ce: "Shin ba zan sanar da ku wata ka'idar da ba za ku sassaba a cikinta, kuma duk wanda ya yi jayayya da ku sai kun rinjaye shi ba?Sai muka ce: 'E, a sanar da mu', sai ya ce:"Allah Mai Girma da Daukaka ba a biyayya gare Shi domin tilastawa, ba a saba masa don rinjaya, ba ya sake da bayinSa cikin mulkinSa. Shi ne Mamallakin abin da Ya mallakar masu, Mai iko kan abin da Ya ba su ikonSa. Idan bayinSa sun yi biyayya gare Shi, ba zai tare ko Ya hana su ba. Idan kuwa suka zabi su saba masa, in Ya ga damar tare su sai Ya yi, idan kuwa bai tare su ba suka aikata sabon, to ba kuwa Shi Ya jefa su ciki ba". Daga nan sai ya ce: "Wanda duk ya kiyaye wannan maganar, to lallai zai rinjayi mai sabawa da shi([182])".
A cikin littafin Sharh al-Aka'id na Shaikh Mufid an ce: "An ruwaito daga Abul Hasan na Uku (a.s.) yayin da aka tambaye shi batun ayyukan bayi; shin halittattu ne daga Allah Ta'ala? Sai ya amsa da cewa: "Da Shi Ya halitta su da bai barranta da su ba, alhali Yana cewa: 'Lalle ne Allah Barrantacce ne daga masu shirka'. Barrantan nan ba ta shafar zatinsu, Ya dai barranta ne daga shirkarsu da munanan ayyukansu([183])".
A cikin littafin Kitabul Tauhid na Muhammad bn Ajlan, ya ce: "Na tambayi Abu Abdullah (a.s.) cewa: 'Shin Allah Ya sakar wa bayi al'amarinsu ne?', sai ya ce: "Karimcin Allah ya wuce gaban Ya saki al'amurransu gare su", sai nace: 'To kenan Allah Ya tilasta wa bayi aikata ayyukansu kenan?, sai ya ce: "Adalcin Allah Ya wuce gaban tilastawa bawa yin wani aiki sannan kuma Ya azabta shi a kan wannan aiki([184])".
A ruwaito cikin Uyunul Akhbar al-Ridha (a.s.) wajen fadar Allah Ta'ala cewa: "Kuma Ya (Allah) bar su a cikin duffai, ba su gani". (Surar Bakara, 2: 17)
Abu Abdullah (a.s.) ya ce: "Ba a siffanta Allah da bari kamar yadda ake siffanta halittunSa, sai dai yayin da Ya san cewa ba su dawowa ga barin kafirci da bata ba, sai Ya hana su taimako da ludufi (tausayi), Ya bar su da zabinsu([185])".
Har ila yau ya zo cikin wannan littafin wajen tafsirin Imam Ridha (a.s.) kan fadin Allah (S.W.T.) cewa: "Allah Ya sa rufi a kan zukatansu".