"Wannan dalili ne kan mazhabar Shafi'i domin umurnin na wajibci ne([20]) saboda haka salati ga Annabi yana wajabta. Kuma salatin ba ya wajaba in ba a tahiya ba, saboda haka yana wajaba ne a cikin tahiya([21])".
Fakhrurrazi ya karkare da cewa: "Idan Allah da Mala'ikunSa sun yi wa Manzon Allah (s.a.w.a.) salati, to wata bukata kuma yake da shi ga salatinmu?
To muna iya cewa yi masa salati ba wai don yana bukatuwa ga salatin ba ne, don kuwa idan ba haka ba ne, to ai babu bukatar salatin Mala'iku bayan salatin Allah a gare shi. Amma ba kome ba ne yasa muke masa salati face bayyana girmamawarmu gare shi, da tausayawarSa gare mu domin Ya saka mana domin salatin. Don haka ne Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Wanda ya yi mini salati sau guda, Allah Zai masa goma").
A ciki Durrul Mansur na Imam Suyudi, Abdurrazak da Ibn Abi Shaiba da Ahmad da Abd bn Humaid da Bukhari da Muslim da Abu Dauda da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ibn Mardawihi, daga Ka'ab bn Ujrah, ya ce wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, mun san yadda ake maka sallama, to ya ya ake maka salati? Sai ya ce: "Ka ce: Ya Allah Ka yi tsira a kan Muhammadu da Alayen Muhammadu kamar yadda Ka yi tsira kan Ibrahim da Alayen Ibrahim, lallai Kai ne Abin godiya, Mai girma".
Malamin ya kawo hadisai goma sha takwas ban da wannan hadisin dukkan su suna nuni ga tarayyar Alayen Manzon Allah (s.a.w.a.) da shi cikin salati. Ma'abuta littattafan hadisi sun ruwaito su daga sahabbai daban-daban. Ga wasu daga cikinsu: Ibn Abbas da Dalha da Abu Sa'id al-Khudri da Abu Huraira da Abu Mas'ud al-Ansari da Buraida da Ibn Mas'ud da Ka'ab bn Umrah da Ali (a.s.).
Sannan kuma a cikinsa Imam Ahmad da Tirmizi sun fitar da hadisi daga Hasan bn Ali (a.s.) cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Marowaci shi ne wanda aka ambace ni a gurinsa bai mini salati ba([22])".
Kamar haka ne malaman fikihu suka ruwaito wajibcin salati ga Annabi Muhammadu da Alayensa (a.s.) cikin tahiyar salla([23]) da wajibcin kawo ambaton Alayen Muhammadu cikin salla.
Duk wanda ya sa ido a kan wannan aya zai fahimci cewa manufar shar'anta salatin da lizimtar da shi shi ne girmama Alayen Manzon Allah (s.a.w.a.), wadanda Allah Ya tafiyar da dauda daga gare su kuma Ya tsarkake su matukar tsarkakewa, domin al'umma ta yi koyi da su, ta bi tafarkinsu, kuma ta fake a gare su lokacin fitinu da sassabawa.
To wadannan da salla ba ta inganta sai gami da an masu salati, su ne Shuwagabannin al'umma, su ne a ka yi nuni da su kuma aka lamunce a yi koyi da su. Ba don tabbata da lamuncewar tsayuwarsu da kubutar abin da ya fito daga gare su ba, da Allah bai umurci musulmi a dukkan zamunna da su rataya da su da yi musu salati cikin kowace salla ba.
Hakika cikin wannan maimaitawa - maimaita salati ga Annabi da Alayensa, da kuma farlanta hakan a kowace salla - akwai jaddadawa da jan hankulan musulmi cikin kowace salla saboda muhimmanci Ahlulbaiti (a.s) da matsayinsu, da kuma koyi da su da rayuwa bisa tafarki da hanyarsu.

Ta Biyar: Surar Insan
"Hakika mutane na gari suna sha daga wani kofin (giya) da mahadinta ya kasance mai kamshin kafur ne.
(Shi kafur din) wani marmaro ne da bayin Allah suke sha daga gare shi suna bubbugo shi bubbugowa ta hakika. (Don ko) suna cika alkawari na bakance suna kuma tsoron ranar da sharrinta ya kasance mai tartsatsi ne. Suna kuma ciyar da abinci tare da kuma suna son sa; ga miskini da maraya da kuma ribatacce a yaki. (Suna cewa): "Mu kawai muna ciyar da ku ne saboda Allah, ba ma nufin sakamako ko godiya daga wurinku. Hakika mu muna jin tsoron rana mai sa daure fuska matsananciya daga Ubangijinmu". Sai Allah Ya kare su (daga) sharrin wannan ranar Ya kuma hada su da haske da kuma farin ciki. Ya kuma saka musu da Aljanna da alhariri saboda hakurin da suka yi. Suna masu kishingida a cikinta a kan gadaje ba sa samun zafin rana ko sanyi a cikinta. Inuwowinta suna kusa da su, an kuma yiwo kasa-kasa da 'ya'yan itacenta kasa sosai. Ana kuma kai-ka-wo da korai na azurfa da kofuna wadanda suka kasance na karau. Karau din na azurfa ne, sun auna su, aunawa daidai da bukata. Ana kuma shayar da su wata giya a cikinta wadda mahadinta ya kasnce mai kanshin zanjabilu ne (watau citta mai yatsu). (Shi zanjabilu) wani marmaro ne a cikinta da ake kiran sa Salsabilu. Samarin hadimai dawwamammu da ba sa tsufa kuma suna kai-ka-wo tsakaninsu, idan ka gan su sai ka yi tsammanin su wani lu'u-lu'u ne wanda aka baza. Idan kuma ka yi kallo a canza ka ga ni'ima da kuma mulki kasaitacce. A samansu akwai tufafi sakar alhariri koraye da kuma abawarsa, aka kuma yi musu ado da warawarai na azurfa, Ubangijinsu kuma Ya shayar da su abin sha mai tsafta. Hakika wannan ya kasance sakamako ne a gare ku, kuma aikinku ya kasance abin godewa.
A cikin wadannan ayoyi masu albarka, Alkur'ani ya yi zancen Ahlulbaiti (a.s) ya kuma sanya su su ne koluluwar masu gabatar da wani bisa kansu wajen ciyarwa da kuma takawa. Alku'ani ya sanya su misali da ja-gora ga dan'Adam, domin sauran mutane su yi koyi da su da kuma rayuwa bisa tafarkinsu.
Abin da ya faru har ya sa aka saukar da wadannan ayoyi dominsa yana nuni ne da matsayin Ahlulbaiti (a.s) da kaiwarsu matuka wajen aikatawa da lizimtar shari'a da kuma fuskantar Allah cikakkiya. Kuma su ne mutanen kirkin da aka yi musu albishir da aljanna, to duk wanda ya yi koyi da su, ya yi tafiya a kan tafarkinsu, to za a tashe shi tare da su. Zamakhshari ya kawo bayani kan wannan aya cikin tafsirinsa. Ga abin da ya ce:
(Daga Ibn Abbas (r.a.): Wata rana Hasan da Husaini (a.s.) sun yi rashin lafiya, sai Manzon Allah (s.a.w.a.) tare da wasu mutane suka ziyarce su don gai da su, sai ya ce wa Imam Ali (a.s.): Ya Abal Hasan, da dai ka yi bakance kan rashin lafiyar 'ya'yanka. Sai Aliyu da Fadima da baiwarsu Fiddha suka ce idan suka sami sauki daga wannan ciwo nasu, za su yi azumin kwanaki uku. Sai kuwa suka warke, alhalin kuwa a wannan gida mai albarka babu wani abu na daga abinci. Sai Aliyu (a.s.) ya yi bashin sa'i uku na Sha'ir daga wani Bayahude mai suna Sham'un Alkhaibari, daga nan sai Fadima ta nika sa'i guda ta yi gurasa biyar, adadin mutanen gidan. Sai ta sanya gurasar a gabansu domin su yi buda baki, bayan lokacin shan ruwa ya yi. Sun shirya za su ci kenan sai ga wani almajiri ya tsaya a kofa ya ce: Assalamu Alaikum, mutanen gidan Muhammadu (s.a.w.a), ni miskini ne daga miskinan musulmi, ku ciyar da ni, Allah Ya ciyar da ku daga abincin aljanna. Sai suka fifita shi (wajen cin abincin) wato suka dauka suka ba shi, su kuwa suka kwana ba su dandani kome ba, sai ruwa, sannan kuma
suka wayi gari da azumi a bakinsu. Da suka kai maraice, suka sake shirya abincin buda baki, sai ga wani maraya ya tsaya a kofa ya yi bara, nan take suka dauki abincin suka ba shi, suka kwana haka. A rana ta uku ma suka ci gaba da azumi, shi ma da lokacin buda baki ya yi suka shirya dan abin da ya sawwaka, a nan ma sai ga wani kamamme ya zo shi ma yana neman abin da zai ci. Sai suka dauki abin da suka tanada suka ba shi.
Da suka wayi gari sai Aliyu (r.a.) ya kama hannun Hasan da Husaini suka nufi gurin Manzon Allah (s.a.w.a.). Yayin da Annabi (s.a.w.a) ya gansu suna karkarwa kamar 'ya'yan tsaki saboda tsananin yunwa, sai ya ce: "Babu abin da zai bakanta mini rai fiye da halin da na ganku a ciki". Sai ya tashi ya tafi tare da su sai ya ga Fadima (a.s.) tana wurin sallarta alhali bayanta ya mannu da cikinta, idanunta sun fada. Ganinta cikin irin wannan hali ya bakanta wa Manzon Allah (s.a.w.a.) rai, sai ga Jibrilu (a.s.) ya sauko ya ce: "Karbi ya Muhammadu, Allah Na tayaka murna batun Ahlulbaitinka", sai ya karanta masa wannan surar([24]).

Ta Shida: Ayoyi
Hakika ayoyin Alkur'ani masu yawa sun sauka da batun Imam Aliyu bn Abi Talib (a.s.) wanda aka yi tarbiyyarsa cikin gidan Manzon Allah (s.a.w.a.) tun yana karami([25]).
Ya tashi karkashin kiyayewarsa (s.a.w.a) don haka ya kwaikwayi halayensa. Ya yi imani da shi, gaskanta shi da kuma binsa tun yana dan shekara goma. Sannan kuma Imam Ali (a.s.) ya kasance mai daukar tutar Manzon Allah (s.a.w.a.) kuma shi ne jarumin sojansa wanda ya kere kowa a dukkan yake-yakensa, da suka hada da Badar, Uhud, Hunain, Ahzab, Khaibar, Zatu Silasil da dai sauransu. A saboda irin jaruntar da ya nuna a irin wadannan yakuna, ya sa Manzon Allah (s.a.w.a.) da kansa ya jinjina masa da bayyanar da wasu kalmomi dawwamammu da suka kasance ado ga littatta-fan tarihi sannan kuma abin koyi na koli cikin sadaukar-wa da kuma jihadi.
Idan muka yi bincike kan asbabun Nuzul (dalilan saukar ayoyi), za mu samu cewa abin da ya sauka dangane da Amirul Muminina, Aliyu bn Abi Talib (a.s.) - ban da abin da muka ambata na Ahlulbaiti (a.s) - suna bayani ne:
1. Kan jaruntar Aliyu (a.s.) gwarzontaka da kuma sadaukarwarsa a kan tafarkin Allah.
2. Kan hakurinsa bisa cutarwa da izgili.
3. Kan gudun duniya, takawa ilimi da kuma kaunarsa ga muminai.
Bari mu ambato wasu misalai kamar haka:

Ayar Wilaya
"Abin sani kawai, majibincinku Allah ne da ManzonSa da wadanda suka yi imani, wadanda suke tsayar da salla, kuma suna bayar da zakka alhali suna masu ruku'i. Kuma wanda ya jibinci Allah da ManzonSa da wadanda suka yi imani, to, kungiyar Allah su ne masu rinjaye". (Surar Ma'ida, 5: 55-56)
Zamakhshari cikin tafsirinsa ya bayyana cewa: "Wannan aya ta sauka ne dangane da Aliyu (Allah Ya karrama fuskarsa) lokacin da wani ya roke shi alhaliyana cikin ruku'in salla, sai ya sake masa zobensa wanda yake loko-loko a dan kuriyarsa, wanda cire shi baya bukatar aiki mai yawa da ka iya bata salla. Idan ka ce ta ya ya za a ce da Ali ake alhali lafazin na jam'i ne? sai in ce maka: An zo da shi akan lafazin jam'i ne ko da yake dalilin saukar ayar a kan mutum guda ne domin a kwadaitar da mutane wajen yin tamkar aikinsa, sai su sami tamkar ladansa. Domin kuma tambihi cewa halayen muminai wajibi ne su kasance da wannan koluwa wajen kwadayin aikin alheri da bibiyar lamarin mabukata ta yadda idan wani abin da ba ya son jinkiri ya lizimce su suna cikin salla, ba sa jinkirta shi sai an idar da sallar([26])
Al-Wahidi ya ambata cewa al-Kalbi ya fadi cikin dalilin saukar wannan aya, cewa: "Lalle karshen wannan aya a kan Aliyu dan Abi Talib (r.a.) take domin ya ba da zobensa ga wani mai bara alhali yana cikin ruku'un salla([27])".
Littattafan tafsiri da hadisi masu yawa sun ambato cewa wannan aya mai albarka ta sauka ne dangane da Imam Ali (a.s.). Akwai cikakken bayani kan hakan cikin wadannan littattafa ga mai karin bayani([28]).

Ayar Tablig (Isar daSako)
Ya kai Manzo! Ka iyar da abin da aka saukar maka daga Ubagijinka. Kuma idan baka aikata ba, to, ba ka iyar da sakonSa ba kenan, kuma Allah Zai tsare ka daga mutane([29]) (Surar Ma'ida: 5:67.
An saukar da wannan aya ne a wani kwari da ake ce ma Ghadir Khum. Ga bayanin akan abin da ya faru:
An ruwaito cewa, yayin da Manzon Allah (s.a.w.a.) yake dawowa daga Hajjin Ban Kwana([30]) sai wannan aya (da muke magana a kanta) ta sauka a gare shi a rana ta goma sha takwas ga watan Zul Hajji([31]).
To sai ya yada zango a Ghadir Khum daga Juhfa([32]), inda a nan ne kuma hanyoyi suka rarrabu zuwa birnin Madina, Masar da kuma Sham. Sai ya tsaya a nan har wadanda suke bayansa suka iso, wadanda suke gaba kuwa suka komo inda yake([33]). Akwai wasu itatuwan kaya a rarrabe, sai aka hana Sahabbai sauka a karkashinsu. Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya sa aka sare wadannan itatuwa na kaya([34]), sai ya sa aka yi kiran salla([35]), ya sallaci azahar tare da jama'a cikin garjin rana([36])
Daga nan sai ya mike ya gudanar da huduba bayan ya yi godiya ga Allah da kuma tsarkake Shi da kuma yin wa'azi ga al'umma, sai ya ce: "Hakika an kusa a kira ni kuma in amsa, ni kuma abin tambaya ne ku ma abin tambaya ne, to me za ku ce?
Sai suka amsa: "Za mu ba da shaidar cewa kai ka isar da sako, ka yi nasiha, to Allah Ya saka maka da alheri".
Sai Annabi (s.a.w.a) ya ce: "Shin ba kwa shaidar cewa babu abin bauta da gaskiya face Allah ba, kuma Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa, da cewa aljanna gaskiya ce, wuta ma gaskiya ce"?
Sai suka ce: "Haka ne, mun shaida hakan".
Sai ya ce: "Ya Allah Ka shaida", sai ya ci gaba da cewa: "Shin ba kwa ji".
Sai suka ce: "Na'am" (watau suna ji).
Sai ya ce: "Ya ku mutane! Ni mai gabata ne ku kuma masu iske ni ne a bakin tabki, fadinsa tamkar tafiyar tsakanin garin Basra da San'a'([37]) ne, akwai kofuna na azurfa, yawansu kamr adadin taurari, ni kuma mai tamabayarku ne batun abubuwa biyu masu nauyi (Sakalaini), to ku kula da yadda za ku kasance game da su a bayana".
Sai wani ya yi kira ya ce: "Mene ne wadannan nauyaya biyu, Ya Manzon Allah?
Sai ya ce masa: "Littafin Allah, gefe yana hannun Allah, gefe kuma yana hannunku, to ku yi riko da shi, ba za ku bata ba, ba za ku canjba ba, da kuma iyalina, mutanen gidana. Hakika Mai Tausayawa, Masani, Ya sanar da ni cewa su biyun ba za su rabu da juna ba har sai sun iske ni a bakin tafki. Na roka musu wannan wajen Ubagijina, saboda haka kada ku gabace su sai ku halaka, kada ku takaita (ga barinsu), sai ku halaka, kada ku sanar da su domin sun fi ku sani([38]).
Sannan sai ya ce: "ashe ba ni ne nafi cancanta ga kowane mumini a kan kansa ba"?
Sai suka ce: "Haka ne, Ya Manzon Allah([39])".
Daga nan sai ya kama hannun Aliyu bn Abi Talib (a.s.) ya daga sama har mutane suka ga farin hammatarsa([40]), ya ce:
Ya ku mutane! Allah Shi ne Majibincina, ni kuma ni ne majibincinku([41]). To duk wanda na ke majibincinsa, wannan Aliyun majibincinsa ne. Ya Allah! Ka jibinci wanda ya jibince shi, Ka yi gaba da wanda ya yi gaba da shi([42]), Ka taimaki wanda ya taimake shi, Ka wulakanta wanda ya wulakanta shi([43]), Ka so mai son sa, Ka ki wanda ya ki shi([44])". Sannan sai ya ce: "Ya Allah Ka shaida([45])".
Ba su (Manzon Allah da Aliyu) rabu ba har sai da Allah Ya saukar da wannan aya: "A yau Na kammala muku addininku, kuma na cika muku ni'imaTa a kanku, kuma Na yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku". (Surar Ma'ida, 5:3)
Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Allahu Akbar! Bisa kammalar addini da cikar ni'ima da yardar Ubangiji da Manzancina da walittakan Aliyu([46])".
Akwai ayoyi masu yawa, wadanda wannan karamin littafi ba zai iya tattaro su ba, da suke magana a kan matsayin Ahlulbaiti (a.s) da karamar su da girman mutanen ciki, wadanda wasu daga cikinsu sun kebanta ne ga Uban wannan itace mai tsarki, wato Imam Ali (a.s.). Mai karatu zai iya samun wadannan ayoyi cikin littattafan tafsiri, hadisi, tarihi da kuma masu bayani kan falalolin wadannan taurari da kuma wadanda suka yi magana kan Asbabun Nuzul na wadannan ayoyi. To amma bari mu kawo kadan daga cikin irin wadannan ayoyi, su ne kuwa:
(1). Fadin Allah Madaukakin Sarki: "Abin sani kawai kai mai gargadi ne kuma a cikin kowadanne mutane akwai mai shiryarwa". (Surar Ra'ad, 13:7)
Hadisi ya zo cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya sanya hannunsa bisa kirjinsa, ya ce: "Ni mai gargadi ne, ko wadanne mutane kuma suna da mai shiryarwa", sai ya yi nuni da hannunsa zuwa Ali (a.s.), sai ya ce kai ne mai shiriyarwan, Ya Aliyu, da kai masu shiryuwa za su shiryu a bayana([47])".
(2). Fadar Allah Madaukakin Sarki: "Shin wanda ya zama mumini yana kamar wanda ya zama fasiki? Ba za su yi daidai ba". (Surar Sajada, 36: 18)
Wannan mumini kuwa shi ne Aliyu (a.s.), fasikin kuma shi ne Walid bn Ukba([48]).
(3). Fadar Allah Madaukakin Sarki:
"Shin wanda ya kasance a kan hujja bayyananna daga Ubangijinsa, kuma shaida na binsa daga gare shi..." (Surar Hudu, 11:17)
Manzon Allah (s.a.w.a.) shi ne yake bisa hujja bayyananna a al'amarinsa, shaidan kuwa shi ne Imam Ali (a.s.) ([49]).
(4). Fadar Allah Madaukakin Sarki:
"...to lalle Allah Shi ne Mataimakinsa da Jibrilu da Salihin muminai..." (Surar Tahrim, 66: 4) Salihin muminai a nan shi ne Aliyu bn Abi Dalib (a.s.) ([50]).
(5). Fadar Allah Madaukakin Sarki:
"...kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye". (Surar Alhakkatu, 69: 12)
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya karanta wannan aya, sai ya juya ga Ali (a.s.), ya ce: "Na roki Allah da ya sanya shi shi ne kunnenka". Sai Ali (a.s.) ya ce: "Babu wani abu da na ji daga Manzon Allah (s.a.w.a.) na manta shi([51])".
Al-Wahidi ya nakalto cikin Asbabun Nuzul daga maruwaita daga Buraida, cewa: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce wa Aliyu (a.s.) cewa: "Allah Ya umurce ni da in kusato da kai, kada kuma in nisantar da kai, cewa kuma in ilmantar da kai, don ka kiyaye, kuma Allah Ya yi alkawarin Zai sa ka kiyaye din. Sai aya ta sauka: "Kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye".
(6). FadinSa Madaukakin Sarki cewa: "Hakika wadanda suka ba da gaskiya suka kuma yi aiki na nagari, to (Allah) Mai rahama Zai sanya soyayya a tsakaninsu". (Surar Maryam, 19: 96)
Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce wa Aliyu (a.s.) cewa: "Ya Aliyu ka ce: "Ya Allah Ka sanya mini wani alkawari, kuma Ka sanya mini soyayya cikin zukatan muminai". Sai Allah Ya saukar da wannan ayar dangane da Aliyu (a.s.) ([52]).
(7). Fadar Allah Ta'ala cewa: "Lalle ne wadanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan kwarai, wadannan su ne mafifita alherin halitta" (Surar Bayyina, 98:7)
Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: "Ya Aliyu, mafifita alherin halitta (a cikin wannan aya) su ne, kai da 'yan shi'arka([53])".
(8). Fadar Allah Madaukakin Sarki cewa: "Yanzu kwa mayar da shayar da alhazai da raya Masallaci mai alfarma kamar wanda ya ba da gaskiya da Allah da ranar lahira kuma ya yi jihadi domin Allah?..." (Surar Tauba, 9: 19) Lalle wadannan su ne Abbas da Dalha, wanda ya yi imani kuwa shi ne Aliyu (a.s.). Akwai wasu ayoyi da dama a kan wannan lamari da muke magana a kansa, amma za mu takaita saboda takaitawa.

Ahlulbaiti (a.s.) Cikin Sunnar Annabi
Dukkan wanda ya bibiyi sunnar Manzon Allah (s) da tarihinsa na aikace da kuma alakarsa da mutanen gidansa wadanda nassin Alkur'ani ya kawo, sannan shi (Manzo) kuma ayyanasu (Aliyu da Fadima da 'ya'yansu biyu), zai san cewa mutanen wannan gida suna da wata rawar da za su taka a bangaren nauyin rike sako da kuma wayewar wannan al'umma. Hakika Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance mai tsare-tsare domin al'ummar tasa da kuma shirya da ita domin ta karbi wannan ni'ima ta Ahlulbaiti (a.s), da umarnin Allah (S.W.T.).
Hakika wannan yanki mai haske na tsare-tsaren Annabi (s.a.w.a), wadanda ya yi da umurnin Allah, ya soma ne da aurar da Fadima (a.s.) ga Imam Ali (a.s.), da dasa wannan itaciya mai albarka, domin rassanta su mamaye sansanin wannan al'umma, tsawon rayuwarta.
An ruwaito Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce wa Aliyu (a.s.) yayin da ya aurar masa da Fadima (a.s.) cewa: "Lalle Allah Madaukakin Sarki Ya umurce ni da in aurar maka da Fadima bisa sadaki gwargwadon nauyin miskalin azurfa dari hudu, shin ka yarda da hakan". Sai Aliyu (a.s.) ya ce: "Lalle na yarda da hakan, Ya Manzon Allah". Anas bin Malik ya ce: Sai Annabi (s.a.w.a) ya ce: "Allah Ya hada kanku, Ya arzurta kokarinku, Ya albakace ku, Ya kuma fitar da zuriya mai albarka". Sai Anas ya ce: "Wallahi, hakika kuwa Allah Ya fitar da zuriya mai albarka daga gare su"([54]).
An ruwaito cewa yayin da Annabi (s.a.w.a) ya aurar da Fadima ga Aliyu (a.s.), sai ya shiga wajenta ya kira ta sai Ummu Aiman ta kawo kasko da ruwa a ciki, sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi tofi a ciki sannan ya yayyafa a kanta da tsakanin nononta, sannan ya ce: "Ya Allah! Ni ina nema mata tsarinKa da zuriyarta daga shaidan jefaffe". Sai kuma ya ce wa Ali (a.s.): "Miko min ruwa", sai Aliyu (a.s.) ya kawo masa, sai ya zuba a kansa da kuma tsakanin kafadunsa (a.s.), sai ya ce: "Ya Allah! Ina nema masa tsarinKa da zuriyarsa daga shaidan jefaffe".
A wata ruwayar kuma cewa aka yi, sai ya bukaci a kawo masa ruwa, bayan ya yi alwala da shi sai ya zuba a kan Aliyu da Fadima (a.s.), sai ya ce: "Ya Allah! Ka albarkace su cikin zuriyarsu([55])".
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana neman uzuri ga duk wani daga cikin sahabbai da ya zo neman a ba shi Fadima (a.s.), yana mai cewa: "Hukumci bai sauko ba tukunna([56])".
Hakika wannan kula ta Ubangiji da AnnabinSa ta aurar da Fadima (a.s.) ga Aliyu (a.s.) ta sanya aurar da ita bai faru ba face da umurni daga Allah (S.W.T.) domin wannan ya yi nuni ga matsayin Ahlulbaiti (a.s) da kuma alherin al'umma da Manzon Allah (s.a.w.a.) yake nufi da alakarsa da su. Wannan matsayi na su kuwa shi ne Alkur'ani mai girma ya fassara, haka nan ma sunnar Annabi (s.a.w.a) mai daraja.
Watakila hasken da muke tsinkaya daga ruwayoyi da hadisai Manzon Allah (s.a.w.a.) da Ahlulbaiti (a.s) (wadanda kuwa masu yawa ne) suna riskar da mu ne irin zurfaffar kula ta Allah da ManzonSa (s.a.w.a) wajen gina wannan gida, da yawaita soyayya da albarka da kula gare shi. Domin mutanen wannan gida su zama ja-gororin al'umma cikin rayuwarsu da kuma hanyoyin tsirarsu daga bala'u da kuma kasancewa tsari da makoma ta hadin kanta yayin da ta rarraba, kamar yadda ruwayoyi da hadisai suka yi nuni da hakan.
Manzon Allah (s.a.w.a.) yana danganta zuriyar Aliyu da Fadima (a.s.) da kansa, yana cewa: "Lalle su zuriyata ne 'ya'ya ne, kamar yadda Alkur'ani ya bayyana hakan da cewa: "To, wanda ya yi musu da kai a cikinsa, a bayan abin da ya zo maka daga ilmi, to ka ce: "Ku zo mu kirayi 'ya'yanmu da 'ya'yanku da matanmu da matanku da kanmu da kanku". (Surar Ali Imrana, 3: 61)
Abin nufi da 'ya'yansa a wannan aya su ne Hasan da Husaini (a.s.), kamar yadda maganganun malaman tafsiri da ma'abuta tarihi suka sanar da mu.
Hakika Manzon Allah (s.a.w.a.) ya karfafa wannan ma'anar wa al'ummarsa sau da yawa, bari mu ambaci kadan daga cikinsu. Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Allah Ya sanya zuriyar kowane Annabi daga tsatsonsa, (ni kuma) Ya sanya zuriyata cikin tsatson wannan", yana nufin Aliyu (a.s.) ([57]).
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana rungumar Hasan da Husaini (a.s.), yana cewa: "Dukkan 'ya'yan wani uba dangantakarsu ta ubansu ce, ban da 'ya'yan Fadima, ni ne ubansu, da ni ake dangantasu". Imam Ahmad ya fito da wannan hadisin cikin al-Manakib([58]).
Hakika Manzon Allah (s.a.w.a.) yana karfafa matsa-yin Ahlulbaiti (a.s) a kowani muhimmin lokaci, domin al'umma ta koma gare su, ta lizimci tafarkinsu, ta kuma yi riko da soyayyarsu. A ruwayoyi da dama, muna samun cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya nuna mana su a matsayin tudun tsira ga wannan al'umma, yana gwama su da Alkur'ani, yana kuma sanya rawar da za su taka a fagen akida da rike sakon Musulunci, mai lizimtar Littafin Allah ne, ba sa rabuwa da shi. Hakan kuwa don al'umma ta fuskanto su wajen fahimtar Alkur'ani mai girma, da ciro ma'anoninsa da hukumce-hukumcensa.
Littattafan hadisi da tarihi sun taru bisa kawo hadisin Annabi (s.a.w.a) da ake kira da Hadisin Nauyaya Biyu (Hadith al-Thakalain). Musulmi sun ruwaito wannan hadisi duk da bambance-bambancen mazhabobinsu na siyasa da fikihu. Za mu ambace shi a nan tare da sashin isnadinsa (maruwaitan da suka ruwaito shi), kamar yadda masu ruwaya da malaman hadisi suka nakalto.

1- Hadisus Sakalain (Nauyaya Biyu)
Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: "Na kusata da a kira ni in kuma amsa, amma ni mai bari muku abubuwa masu nauyi guda biyu ne, su ne kuwa: Littafin Allah Mai girma da Daukaka, da kuma zuriyata. Littafin Allah wata igiya ce da aka sako ta daga sama zuwa kasa, zuriyata kuwa su ne mutanen gidana (Ahlulbaiti). Allah Mai tausasawa Ya ba ni labari cewa su biyun ba za su taba rabuwa ba har abada har sai sun iske ni a bakin tafki. To ku lura da yadda za ku rike su a bayana([59])".
Al-Shibrawi al-Shafi'i ya nakalto cikin littafinsa mai suna al-Ithafu bi hubbil Ashraf, cewa: "Muslim da Tirmizi sun kyautata shi (hadisin), haka ma Hakim shi ma ya ruwaito shi, lafazin Muslim kuwa daga Zaid bn Arkam cewa ya yi: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya mike a cikinmu domin ya yi mana huduba sai ya yi godiya ga Allah ya yi yabo gare Shi, sannan ya ce:
"Bayan haka, Ya ku mutane, ni dai mai mutuwa ne, kuma zan amsa kiran manzon Ubangijina. To amma na bar muku wasu nauyayan abubuwa guda biyu tare da ku; na farkonsu Littafin Allah, shiriya da haske na cikinsa, to ku kama Littafin Allah ku yi riko da shi". Sannan sai ya ce: "Da Ahlulbaitina, ina gama ku da Allah dangane da Ahlulbaitina([60])".
Al-Shibrawi din kuma ya nakalto cewa: "A wata ruwayar kuma Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa ya yi: "Ni mai bari muku al'amurra guda biyu , ba za ku bata ba idan har kun bi su, su ne kuwa; Littafin Allah da Ahlulbaitina". A wata ruwayar kuma (aka cika da cewa) "ba za su rabu ba har sai sun iske ni a bakin tafki, to ku kula da yadda za ku rike su a bayana([61])". Ya kara da cewa: "Ibn Hajar ya fada cikin Sawa'ikul Muhrika cewa: "Annabi (s.a.w.a) ya ambaci Alkur'ani da zuriyarsa da cewa "Nauyaya Biyu" ne saboda nauyin dukkan wani mutum shi ne abu mafi muhimmanci a gare shi, kuma wadannan guda biyu haka suke. Domin kuwa kowane daga cikinsu taska ce ta ilmummukan addini da sirrorin hankali irin na shari'a, domin haka ne ma aka kwadaitar da koyi da su. Wani kaulin kuma ya ce an ambace su da "Nauyaya Biyu" ne domin wajibcin kiyaye hakkokinsu. Sannan kuma wanda kwadaitarwar ta tabbata a gare su, su ne masana Littafin Allah masu riko da sunnar ManzonSa (s.a.w.a), domin su ne wadanda ba su rabuwa da Littafin har zuwa tabki([62])".
Allama Shaikh Muhammad Jawad al-Balagi ya nakalto cikin tafsirinsa Ala'u al-Rahman fi tafsiril Kur'an cewa: "Haka nan ma kamar hadisin Sakalain wanda yake an tabbatar da ingancinsa kamar yadda 'yan'uwanmu Ahlul Sunna suka ambace shi cikin littattafansu suka kawo ruwayarsa daga sahabbai wadanda suka ji shi daga wajen Manzon Allah (s.a.w.a.):
"Ni mai bari muku Nauyaya guda biyu ko kuma halifofi guda biyu, Littafin Allah da zuriyata, Ahlulbaitina, wadanda idan kun yi riko da su ba za ku bata ba har abada, su ba za su rabu da juna ba har sai sun riske ni a bakin tafki".
(1). Imam Ali bn Abi Talib (a.s)
(2). Abdullahi bn Abbas.
(3). Abu Zar Giffari
(4). Jabir al-Ansari.
(5). Abdullahi bn Umar
(6). Hudhaifa bn Usaid.
(7). Zaid bn Arkam.
(8). Abdurrahman bn Awf.
(9). Dhamratul Aslami.
(10). Amir bn Laili.
(11). Abu Ra'fi'.
(12). Abu Huraira.
(13). Abdullah bn Handab
(14). Zaid bn Thabit.
(15). Ummu Salama.
(16). Ummu Hani.
(17). Khazima bn Thabit.
(18). Sahl bn Sa'ad.
(19). Adi bn Hatam.
(20). Ukba bn Amir.
(21). Abu Ayyub Ansari.
(22). Abu Sai'd al-Khudri.
(23). Abu Shuraih Khuza'i.
(24). Abu Kadama Ansari.
(25). Abu Laili.
(26). Abu Haitham bn Al-Tayhan.
Allama al-Balagi ya ci gaba da cewa: Wadannan su ne muka riga muka ambaci sunayensu bayan Ummu Hani. Kowannensu ya ruwaito shi, shi kadai, kamar wadanda suka gabace shi, sun tsaya a dandalin Kufa tare da mutum bakwai Kuraishawa, suka tabbatar da cewa sun ji wannan hadisi daga Manzon Allah (s.a.w.a.), adadinsu kuwa shi ne talatin da uku.
Kuma abu Nu'aim Al-Isfahani ya ruwaito shi cikin littafin Munkabatu al-Mudahharin da isnadi daga Jabir bn Mad'am da kuma wani isnadin daga Anas bn Malik da Al-Barra'u bn Azib, haka nan Muwaffak bn Ahmad ya ruwaito shi daga Amr bn al-As.
Da wuya a sami wani littafin hadisi babba ko karami ko littafin falaloli da Ahlussunna suka rubuta wanda bai kawo wannan hadisin ba, daga farkon wadanda suka kawo hadisin daga hadda da kuma zukatan mahaddata har zuwa takardun malaman hadisi. Kuma bai gushe ba ana ruwaito shi daga sahabbai guda ko masu yawa. Ta yiwu ma a ruwaito shi daga sama da sahabbai ashirin a littafi guda, ko dai a game kamar yadda ya zo cikin littafin Sawa'ikul Muhrika, ko kuma da isnadi rarrabe kamar yadda ya zo cikin littattafan al-Sakhawi da Suyudi da Samhudi da dai sauransu".
Sannan sai ya ce: "Malaman Imamiyya sun ruwaito shi cikin litattafan-su da isnadinsu masu maimaita juna daga Imam Bakir, Ridha da Kazim da Sadik (a.s.) daga iyayensu (a.s.) daga Manzon Allah (s.a.w.a.) da kuma wadansu isnadan na daban daga Amirul Muminina (a.s) da Umar da Ubayyu da Jabir da Abu Sa'id da Zaid bn Arkam da Zaid bn Thabit da Huzaifa bn Usaid da Abu Huraira da sauransu, dukkanninsu sun ji daga Manzon Allah (s.a.w.a.) ([63]).
A cikin Musnad na Ahmad bn Hambal, ya ruwaito ta hanyar Abi Sa'id al-Khudri daga Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Ni na kusanta da a kira ni in amsa, ni kuma mai barin nauyayan abubuwa ne guda biyu tare da ku, Littafin Allah Mai Girma da Daukaka da kuma Ahlulbaitna, shi Littafin Allah igiya ce da aka sako daga sama zuwa kasa. Kuma lalle Mai Tausasawa Masani, Ya ba ni labarin cewa baza su taba rabuwa da juna ba har sai sun iske ni a bakin tafki, don haka ku kula da yadda za ku rike su a bayana([64])".
Haka nan kuma idan muka duba za mu ga kusan dukkan maruwaita sun ruwaito wannan hadisi da ke gwama Ahlulbaiti (a.s) da Littafin Allah Mai Tsarki. Daga wannan ne musulmi za su fahimci cewa Ahlulbaiti (a.s) su ne makoma baicin Littafin Allah kuma su ne aka bar wa amanar Littafin har su isa ga tabki.

2- Hadisus Safina (Hadisin Jirgin Ruwa)
Yayin da Hadisus Sakalain yake gwama Ahlulbaiti (a.s) da Alkur'ani waje guda domin nauyin da aka dora musu na bayyana Alkur'anin da kwaranye boyayyun abubuwansa da asirorinsa da abubuwan da ke kewaye da shi, to wannan hadisi na Safina kuwa yana bayyana wa al'umma ne cewa su Ahlulbaiti (a.s) su ne jirgin tsira, kuma hanyar kubutar wannan al'umma bayan Manzon Allah (s.a.w.a.). Domin haka, lallai rashin riskan wannan jirgin da rashin hawansa, zai ja wadanda suka ki shiga jirgin zuwa ga nutsewa da halaka. Domin kin binsu, kin bin ja-gora zuwa gabar shiriya da tsira ne.
Al-Shibrawi al-Shafi'i ya nakalto daga Rafi Maulan Abu Zarri, ya ce: "(Wata rana) Abu Zar (r.a.) ya hau dokin kofar Ka'aba, ya kama marikin kofar ya dogara da shi, sai ya ce: "Ya ku mutane, wanda ya sanni to ya sanni, wanda kuma bai sanni ba, to ni ne Abu Zar, na ji Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Ahlulbaitina tamkar jirgin Nuhu suke, wanda ya hau shi ya tsira wanda kuwa ya ki hawa ya fada wuta". Na kuma ji Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: "Ku sanya Alayena (agareku) matsayin da kai yake da shi a jiki, kuma matsayin idanu ga kai. Domin shi jiki baya shiryuwa sai da kai, shi kuma kai ba ya shiryuwa sai da idanu([65])".
Abu Nu'aim([66]) ya ruwaito ta hanyar Sa'id bn Jubair daga Ibn Abbas, ya ce: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Misalin Ahlulbaitina a cikinku, tamkar jirgin (Annabi) Nuhu ne, wanda ya hau shi ya tsira, wanda kuwa ya ki hawa ya nutse (ya halaka) ([67])".
An ruwaito ta hanyar Anas bn Malik, cewa, ya ce Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Abin sani kawai shi ne cewa, misalin Ahlulbaitina a cikinku, kamar jirgin Nuhu ne, wanda ya hau shi ya tsira, wanda kuwa ya ki hawansa ya halaka([68])".
Suyudi ma ya ruwaito wannan hadisin cikin littafinsa Durrul Mansur karkashin tafsirin fadin Allah Madauka-kin Sarki cewa: "Kuma lokacin da Muka ce: "Ku shiga wannan alkarya, sa'an nan ku ci daga gare ta, inda kuka so, bisa wadata, kuma ku shiga kofa kuna masu tawali'u, kuma ku ce: "Kayar da zunubai" Mu gafarta muku laifukanku". Inda ya ce: "Ibn Abi Shaiba ya fitar da hadisi daga Aliyu bn Abi Talib (a.s.) ya ce: "Abin sani dai, misalinmu (Ahlulbaiti) cikin wannan al'umma kamar misalin jirgin Nuhu ne, kuma kamar Kofar Yafuwa (Hidda) ce([69])".
Al-Muttaki ya ruwaito shi cikin littafin Kanzul Ummal (juzu'i na 6 shafi na 216) cewa, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Misalin Ahlulbaitina a cikinku, tamkar jirgin Nuhu ne, wanda ya hau shi ya tsira, wanda kuwa ya ki hawansa ya halaka, kuma tamkar kofar Hidda ne ta Bani Isra'ila". Sannan ya ce Dabarani ma ya ruwaito wannan hadisi daga Abu Zarri([70]).