Ali Dan Musa Ar-Rida (A.S)
Sunansa da Nasabarsa: Ali dan Musa dan Ja’afar dan Muhammad.
Mahaifiyarsa: Kuyanga ce mai suna Najma.
Alkunyarsa: Abul Hasan, Abu Ali...
Lakabinsa: Arrida, Assabir, Arradiyyu, Alwafi, Alfadil.
Tarihin haihuwarsa: 11 Zul-ka’ada 148H.
Inda aka haife shi: Madina.
Matansa: kuyanga ce mai suna: Sakina, an ce sunanta Al-hizran, da Ummu Habib ‘yar Al-mamun.
‘Ya’yansa: 1-Muhammd Al-jawad 2-Al-kani’u 3-Ja’afar 4-Ibrahim 5-Al-Hasan ko Al-Husaini 6-A’isha.
Tambarin zobensa: Masha’Allah la Kuwwata illa bil-Lahi. Tsawon rayuwarsa: shekara 55.
Tsawon Imamancinsa: Shekara 20.
Sarakunan zamaninsa: Abu Ja’afar Al-mansur da Muhammad Al-Mahadi da Musa Al-Hadi da Harunar-Rashid da Al-amin da Al-ma’amun dukkaninsu sarakunan Abbasiyawa ne.
Tarihin shahadarsa: karshen Safar 203H.
Inda ya yi shahada: Garin Duss a Khurasan.
Sababin shahadarsa: Shan guba a lokacin halifa Al-ma’amun. Inda aka binne shi: A Al’karyar San’abad a Duss Khurasan. A yau wurin yana cikin birnin Mash’had.

Muhammad Dan Ali Al-Jawad (A.S)
Sunansa da Nasabarsa: Muhammad dan Ali da Musa dan Ja’afar (A.S).
Babarsa: Kuyanga ce sunanta: Sukaina Al-marsiyya, an ce sunanta Al-khaziran.
Alkunyarsa: Abu Ja’afar Assani da Abu Ali.
Lakabobinsa: Al-jawad, Attakiyyi, Azzakiyyi, Al-kani’u, Al-murtada, Al-muntajab.
Tarihin haihuwarsa: 10 Rajab shekara 195H.
Inda aka haife shi: Madina.
Matansa: Kuyanga ce mai suna Sumana da Ummul fadli ‘yar ma’amun.
‘Ya’yansa: 1-Imam Al-Hadi (A.S) da 2-Musa 3-Fadima 4-Amama.
Tambarin zobensa: Ni’imal kadir Allah.
Tsawon rayuwarsa: shekara 25.
Tsawon Imamancinsa: shekara 17.
Sarakunan zamaninsa: karshan hukuncin Al-amin da Al-ma’amun da Al-mu’utasim.
Tarihin shahadarsa: karshen Zul’ki’ida shekara 220H.
Inda ya yi shahada: Bagdad.
Dalilin shahadarsa: Shan guba a lokacin halifa Al-mu’utasim. Inda aka binne shi: An binne shi a makabartar Kuraishawa a Al-Kazimiyya kusa da kakansa Al-kazim (A.S).

Ali Dan Muhammad Al-Hadi (A.S)
Sunansa da Nasabarsa: Ali dan Muhammad dan Ali dan Musa (A.S).
Mahaifiyarsa: kuyanga ce mai suna Sumana.
Alkunyarsa: Abul Hasan ko Abul Hasan Assalis.
Lakabinsa: Al-Hadi, Al-mutawakkil, Annakiyyi, Al-fattah, Al-murtada, Annajib da Al-alim.
Tarihin haihuwarsa: 15 julhajji 212H.
Inda aka haife shi: Alkarkar Sarya (????) nisanta da Madina mil uku ne.
Matansa: Kuyanga ce ana ce mata Susan.
‘Ya’yansa: 1-Imam Hasan 2-Husaini 3-Muhammad 4-Ja’afar 5-A’isha.
Tambarin zobensa: Hifzul uhud min akhlakil ma’abud.
Tsawon rayuwarsa: Shekara 42.
Tsawon Imamancinsa: 33.
Sarakunan zamaninsa: Karshen mulki Ma’amun da Al-mu’uta- sim da Al-wasik da Al-mutawakkil.
Tarihin shahadarsa: 3 Rajab shekara 254H.
Inda ya yi shahada: Samra’u.
Dalilin shahadarsa: An kashe shi da guba a lokcin mutawakkil. Inda aka binne shi: Samra’u (Irak).

Al-Hasan Dan Ali Al-Askari (A.S)
Sunansa da Nasabarsa: Alhasan dan Ali dan Muhammad dan Ali (A.S).
Babarsa; kuyanga ce mai suna Susan.
Al-kunyarsa: Abu Muhammad.
Lakabinsa: Al-askari, Assiraj, Al-khalis, Assamit, Attakiyyi.
Tarihin haihuwarsa: 8 Rabi’ul Awwal 232H.
Inda aka haife shi: Madina.
Matansa: Kuyanga ce ana cewa da ita Narjis.
‘Ya’yansa; Daya ne shi ne Imam Mahadi Al-muntazar.
Tambarin zobensa: Subhana manlahu makalidus-Samawati wal Ardi.
Tsawon rayuwarsa: Shekara 28H.
Tsawon Imamancinsa: Shekara shida.
Sarakunan lokacinsa: Al-mutawakkil da Al-mustansir da Al-musta’in da Al-mu’utaz da Al-muhtadi da Al-mu’utamad. Tarihin shahadarsa: 8 Rabi’ul Awwal 260 H.
Inda ya yi shahada: Samra’u.
Dalilin shahadarsa; An kashe shi da guba a lokacin Al-mu’utamad.
Inda aka binne shi: a gidansa na Samra’u a Irak.

Muhammad Dan Hasan Al-Mahadi (A.S)
Sunansa da Nasabarsa: Muhammad dan Hasan dan Ali dan Muhammad (A.S).
Babarsa: Kuyanga ce Mai suna Narjis.
Kinayara: Abul Kasim.
Lakabinsa: Al-Mahadi, Al-muntazar, Sahibuz Zamani, Al-hujja, Al-ka’im, Waliyyul Asri, Assahib.
Tarihin haihwarsa: 15 Sha’aban 255 a lokacin Al-mu’utamad. Inda aka haife shi: Samra’u.
Tsawon rayuwarsa: Rayayye ne boyayye daga ganin mutane, zai fito karshen zamani da umarnin Allah (S.W.T) domin ya cika Duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci, muna rokon Allah ya gaggauta bayyanarsa.
Tsawon Imamancinsa: Yana da tsawo, har yanzu yana raye. Buyansa: Yana da buya biyu:
1-Karami: Yana da tsawon shekara 74, ya fara daga shekarar 260 H har zuwa shekarar 329 H.
2-Babba: Ya fara daga shekarar 329H bayan mutuwar jakadansa na karshe har zuwa wannan zamanin.
Jakadunsa: Su hudu ne, su ne mutane suke karbar hukunce-hukuncensa daga gare su a lokacin buyansa karami. Wadannan jakadon su ne; 1-Usman dan Sa’id 2-Muhammad dan Usman 3-Husaini dan Ruhu 4-Ali dan Muhammad Assimiri. Alamomin bayyanarsa: Ba zasu kirgu ba sai dai zamu kawo guda hudu a nan: 1-Fitowar Sufyani 2-Kashe Al-Hasani 3-Zuwan Tutoci Bakake daga Khurasan 4-Fitowar Al-yamani.
Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai

Masdarorin Madogarar Wannan Littafin:
Littafin Salim bn Kais
Tarihin Damishka
Fara’idus Simdaini
Hawahidit Tanzil
Alkamil fittarih
Algadir
Addara’if
Assiradul mustakim
Tuhufatul isna ashariyya
Al’khilaf
Biharul anwar
As’shafa
Sahih Muslim
Sunan Tirmizi
Baihaki
Masnad Ahmad
Ma’a rijalul fikr
Tafsirin Ibn Kasir
Al’anbiya afdhalu minal mala’ika, wa nabiyyuna afdhalul anbiya
Littattafan Da MawallafinLittafin Ya Wallafa:
1. Hakkoki a musulunci
2. Raddin sukan auren mace fiye da daya
3. Mace a al’adu da musulunci
4. Tarbiyyar yara a musulunci
5. Zabar mace ko namijin aure
6. Boyayyar taska (wannan littafin)
7. Tsari da kayyade iyali
8. Kurkuku a doka da tsari
9. Tattaunawar addinai (tare da Annabi Muhammad)
10. Sanin dabi’u na gari
11. Adon wahayi da mu’ujiza
12. Sanin akida sahihiya
13. Cikakken mutum mai kamala
14. Tambaya da amsa game da akida
Littattafan Da MawallafinLittafin Ya Fassara:
1. Tafarki zuwa gadir
2. Makaloli game da Nahajul balaga
3. Dan sako da mai sako da sako
4. Akidojin imamiyya
5. Shi’anci da duniyar gobe
6. Imamanci da nassi
7. Raja’a
8. Bada
9. Hada salloli biyu
10. Tawassuli