Aikin Mutum Ba Ya Iya Nuna Mazhabarsa
Yana da kyau mu sani cewa mazhabar Ahlul Baiti (A.S) daban aikin mabiya mazhabar daban, yana yiwuwa ya yi daidai ko ya saba da koyarwar mazhabar don haka ba a duba aikin mutum a ce haka mazhabarsa take, domin musulunci daban aikin musulmi daban, idan muka gane haka warware abubuwa da dama zasu yi sauki.
Wata rana wani daga masu sukan mabiya Ahlul Bait (A.S) ya ce: Daga Akidar mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S) shi ne shan taba. Sai na ce da shi: Da zaka ce: Daga Akidar Malikawa ko Hanifawa akwai shan taba da za a sha mamakin jahilcinka, domin a lokacin Maliku babu taba ballantana Imam Ali (A.S) da yake shi ne Imamin mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S).
Na farko da sai da ya yi shahada da shekara hamsin da wani abu sannan aka haifi Maliku, na biyu kuma wannan furu’a ne ba Akida ba. Abin da yake yi wa mutane da yawa wahalar ganewa sakamakon jahilci da ya yi kanta cikin al’umma, na kara masa da cewa: Don haka ne nake gaya maka ina kare mazhabin Ahlul Baiti (A.S) ne ba ina kare mabiyansu ba domin zai iya yiwuwa aikin nasu ya saba da mazhabin. Na ce da shi: Da wani kirista zai ji ka yi karya sai ya ce da kai: Lallai musulunci ba shi da kyau. Sai ka tambaye shi; saboda me?. Sai ya ce: Saboda ka yi karya kuma wannan yana nuna karya tana daga Akidun musulunci, ya ya zaka ba shi amsa?. Sai ya ce: Amsar da na bayar.

Ahlul Baiti (A.S) Su Ne Makoma
Haka nan mummunan tunani da wadancan dauloli suka bari kuma suka gadar da shi ga wannan al’umma suka cigaba da yawo da zagayawa a kwakwalen ‘ya’yan wannan al’umma tamu, alhalin su wadannan soke-soke a kan tafarkin Ahlul Bait (A.S) da mabiyansu tun asali sarakuna sun assassa su ne domin tabbatar da mulkinsu, amma abin takaici sun wanzu a kwakwalen miliyoyin mutane har zamaninmu wannan.
Kuma sun ci gaba da zama dalilin takurawa mai tsanani a kan mabiya Ahlul Baiti, amma duk da haka mabiyansu sun ci gaba da wanzuwa a bayan kasa da yada haskensu. Al’amarin ya ci gaba har ya zama akwai lokacin da suka zama su ne rabin al’umma a bayan kasa!
Wani abin da zamu yi lura a kansa shi ne; da yawa daga malaman mazhabobin Ahlussunna sun yi karatu ne wajan Ahlul Baiti (A.S). Maliku ya yi karatu wajan Imam Sadik, haka ma Abu Hanifa, har ma Abu Hanifa ya kasance yana cewa: “Ba don Shekara biyu ba da Nu’uman ya halaka” wato; Ba don karatun shekara biyu da ya yi a wajan Imam Ja’afa Sadik (A.S) ba da ya halaka”[9].
Maliku yana cewa: “Ya kasance ya ga Imam Ja’afar (A.S) mai yawan murmushi da fara’a amma idan aka ambaci Manzon Allah (S.A.W) a gabansa sai launinsa ya koma yalo (saboda girmamawa da shauki), ya ce: Ban taba ganin ya bayar da hadisin Manzon Allah ba sai yana da tsarki”[10]. Wannan kuwa lokacin da yake bayar da amsar dalilin da ya sanya shi girmamawa ga hadisan Manzon Allah (S.A.W) da tasirantuwar da ya yi daga imam Sadik (A.S). Wannan al’amarin yana nuna cewa Imam Assadik (A.S) ya yi masa tasiri wajan sanin Manzon Allah (S.A.W) da kuma girmama Hadisansa. Yayin da kuma shi Shafi’i ya kasance Dalibin Muhammad Dan Alhasan ne, wanda shi ne mutum na uku a Hanafiyya da shi ne ya rene shi, kuma Shafi’in ya gaji littattafan Muhammad Dan Alhasan ne, wanda shi kuma salsalar malamansa tana tukewa zuwa ga Imam Ali (A.S) ne.

Ya Musulmi Hattara Da Makiya!
A takaice dai mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S) su ne mutanen da suka fi kowace jama’a dadewa karkashin farfaganda da karairayi na masu gaba da su a Tarihin dan Adam, kuma sun yi imani da Imamin wannan zamani Imam Mahadi (A.S) da musulmi suka hadu a kan cewa; zai bayyana ya kuma cika duniya da adalci kamar yadda aka cika ta da zalunci.
Tambaya a nan shi ne, Shin idan Imam Mahadi (A.S) ya bayyana zai bar koyarwar kakanninsa ne ya riki wata koyarwa daban ko kuwa?. Wannan wani abu ne da dukkan musulmi suka hadu a kan rashin yiwuwarsa, kuma an sani cewa ba yanda za a yi ya bar koyarwar kakarsa Sayyida Zahara (A.S) da kuma Iyayensa (A.S), hasali ma shi Imami ne daga Imaman Wannan Gida, kuma yana da wata daraja ta musamman da ba wanda Allah ya yi wa ita, domin Annabi Isa (A.S) zai zama cikin rundunarsa karkashin umarninsa kuma ya rika yin salla a bayansa, kuma shi ne wanda zai zo ya cika duniya da haske da shiriyar musulunci ya tumbuke duk wani munafunci da duk sabani, ya zama ba abin da zai iko sai Addinin Allah.
Da yawa mutanen da aka haramta musu ni’imar shiriya ta Ahlul Bait (A.S), wasu farfaganda ta haramta musu karanta littattafansu ne ko sauraronsu, har yanzu a wata kasa a Gabas ta tsakiya da aka fi ko’ina danne hakkin dan Adam hatta a cikin Jami’a an hana kowane dalibi karanta littattafan mazhabar Ahlul Baiti (A.S). akwai wasu wasu mutane da su suna son su ji ko su karanta domin suna son musulunci, kuma suna son fahimtarsa da fadi ba da tsukakkiyar kwakwalwa da tsukakken tunani ba, sannan hankalinsu yana tambayar su cewa: Shin zai yiwu Manzo (S.A.W) ya tafi ya bar duniya ba tare da ya sanya magajinsa, halifansa, wasiyyi, da zai bari bayansa ba! alhali wannan shi ne sakon Allah na karshe! ga shi kuwa hatta idan zai tafi yaki sai ya bar wani mai tsaron gari? Wannan wata tambaya ce da take tasowa a tunanin mutane masu hankali da lura. Wasu masu tunanin suna dada tambayar kawukansu a kan wasu al’amura da suke damunsu kamar haka;
1. Shin Fadima (A.S) zai yiwu ta ki yarda da halifan lokacinta ta kuma yi fushi da shi da zafafawa kamar haka ba tare da ta dogara da dalili na gaskiya ba?
2. Kuma shin zai yiwu ta kira mutane zuwa ga mijinta da neman yi masa bai’a a matsayin halifan da babanta ya bari kuma ya yi wasiyya da shi ba tare da wani dalili ba?
3. Sa’annan su waye wadannan halifofi goma sha biyu da Manzo (S.A.W) ya yi wasiyya da su bayansa kamar yadda ya zo a littattafan dukkan musulmi shi’arsu da sunnarsu, kamar Littafin Sahih Muslim?.
4. Kuma shin hankali zai iya bayar da adadain sarakunan Umayyawa ko na Abbasawa masu yawa haka a matsayin su goma sha biyun? Ko kuma halifofi uku na farko?. mai karatu amsa wannan tambayoyi da gano jawabinsu sahihi shi ne zai iya sanyawa ka gano wannan taskar da aka sanya rasid din shiga Aljanna a cikinta.
Akwai ra’ayoyin masu nazari mabanbanta a game da su waye wadannan goma sha biyun amma muhimmin binciken da zan fi bayar da karfi a kai a nan shi ne, su waye wadannan Ahlul Baiti da Manzo (S.A.W) ya bar wa al’umma tare da Kur’ani mai girma da ba zasu taba rabuwa ba har sai sun riske shi a tafki kamar yadda suka zo a ruwayoyi.

Su Waye Ahlul Baiti Halifofin Manzo (S.A.W)
Ya zo cewa Manzo (S.A.W) ya bar Kur’ani da Ahlul Bait (A.S) ga al’ummarsa, abin tambaya shi ne su waye wadannan Ahlul Bait kamar yadda ya zo a littattafan hadisai?, Manzo (S.A.W) da kansa ya bayyana wa al’umma su waye Ahlin Gidansa tsarkaka kuma masu daraja wajan Allah kuma halifofinsa kamar haka;
Yayin da Ayar nan ta Suratul Ahzab: 33 ta sauka, wato; “Hakika kawai Allah yana son ya tafiyar da dauda daga gare ku Ahlul Baiti kuma ya tsarkake ku tsarkakewa”[11]. Sai Manzo (S.A.W) ya kira Ali da Fadima da Hasan da Husaini (A.S) ya lullube su da wani bargo da aka yi wa zane da bakin gashin rakumi. Wannan Hadisi[12] ya zo a littafin Muslim, da Buhari, da Mustadrik Alassahihaini, da Tirmizi da Abu Dawud da Tafsirin Bagawi, da Ibn Kasir, da gomomin Tafsirai da Littattafan hadisai, kamar yadda wannan hadisin ya maimaitu a lokacin mubahala da kiristocin Yaman da sauran wurare da dama.
Akwai wata mahanga da take ganin cewa Ahlul Baiti (A.S) su ne Alayan Ali, da Ja’afar, da Akil, da Abbas, wannan shi ne nazarin Zaid Dan Arkam. Amma kuma duk mahangan sun hadu a kan kore matan Annabi (R.A) daga kasantuwa cikin Ahlul Baiti. Game da mahangar Zaid kuwa muna iya cewa; idan aka ce ga maganar Manzo (S.A.W) ka sani cewa ba wata magana da take da kima bayanta.
Kamar yadda ruwayoyin sun yi nuni da cewa Ummu Salama (R.A) ta so ta shiga cikinsu amma Manzo (S.A.W) da kansa ya nuna mata ba ta cikin Ahlul Bait (A.S). Akwai kuma wasu hadisai da suka yi nuni da cewa; Ahlul Bait (A.S) su biyar ne da kuma tara daga ‘ya’yan Husain (A.S). Wato halifofinsa guda goma sha biyu da kuma Fadima (A.S) wanda na farkon su shi ne Ali (A.S) na karshensu shi ne Mahadi (A.S)[13].
Ya zo a Tafsirin Ibn Kasir a tafsirin Aya ta 55 ta Surar Ma’ida cewa[14]: Daga Maimun Dan Mahran daga Ibn Abbas, a fadin Allah mai grima da buwaya: “Kawai majibancin lamarinku (Jagoranku) Shi ne Allah da Manzonsa da wadanda suka yi imani wadanda suke tsayar da Salla suke bayar da Zakka alhalin suna masu ruku’u”. Yana mai cewa: Ta sauka ne game da Muminai kuma Ali Dan Abu Talib (A.S) Shi ne na farkonsu. Wato tana mai nuni da cewa na farkon wadanda za a mika wa wilaya da Shugabanci bayan Allah da Manzonsa shi ne Ali (A.S) Sa’annan masu biyo wa bayansa na daga wasiyyai, kamar yadda zamu ga ta sauka ne a lokacin da ya yi sadakar zobensa alhalin yana cikin ruku’i. Wasu littattafan suna cewa; ta sauka game da muminai Ali (A.S) ne na farkonsu, Mahadi (A.S) na karshensu[15].
Mahangar Ahlul Baiti (A.S) game da ma'asumai da Allah (S.W.T) ya sanya su hujja kan al’umma bayan Manzon rahama su goma sha biyu ne, idan ka hada da Ma'asumiya Sayyida Zahara (A.S) Ma'asumai sun zama goma sha hudu kenan, wato Manzon Allah (S.A.W) da Fadima (A.S) da halifofinsa goma sha biyu (A.S) da ya yi wasiyya da bin su.

Takaitaccen Tarihin Manzo Da Ahlin Gidansa
Manzo Muhammad Dan Abdullahi Al-Habib: Sunansa da Nasabarsa: Muhammad dan Abdullahi dan Abdul mudallibi dan Hashimi dan Abdu manafi dan Kusayyi dan Kilabi, nasabarsa madaukakiya tana tukewa zuwa ga Annabi Ibrahim (A.S).
Mahaifiyarsa: Ita ce Aminatu ‘yar wahabi dan Abdu Manafi dan Zuhrata dan Kilabi.
Alkunyarsa: Abul Kasim, Abu Ibrahim.
Lakabinsa: Almusdafa yana da sunaye da suka zo a cikin Kur’ani mai girma kamar, Khataman nabiyyin, da Al’ummi da Almuzzammil da Almuddassir da Annazir da Almubin da Alkarim da Annur da Anni’ima da Arrahma da Al’abdu da Arra’uf da Arrahim da Asshahid da Almubasshir da Annazir da Ad’da’i da sauransu.
Tarihin haihuwarsa: 17 Rabi’ul Auwal Shekarar Giwa (571m) bisa mash’hurin zance gun Ahlul Baiti (A.S), an ce, 12 ga watan da aka ambata.
Wurin haihuwarsa: Makka.
Aikoshi: An aiko shi a Makka 27 Rajab yana dan shekara arba’in.
Koyarwarsa: ya zo da daidaito tsakanin dukkan halitta da ‘yan’uwantaka da rangwame na gaba daya ga wanda ya shiga musulunci, sa’annan ya kafa shari’a madaukakiya da dokoki na adalci da ya karbo daga wajan Allah su kuma musulmi suka karba daga gare shi.
Mu’ujizozinsa: Mu’ujizarsa madauwamiya ita ce Kur’ani amma wadanda suka faru a farkon Musulunci suna da yawa ba sa kuma kirguwa.
Kiransa: Ya kira mutane zuwa ga Tauhidi a Makka a boye shekara uku ya kuma kira su a bayyane shekara goma. Hijirarsa: ya yi hijira daga Makka zuwa Madina a farkon watan Rabi’ul Auwal bayan shekara 13 daga aikensa, wannan ya faru ne sakamakon cutarwa daga kafirai gare shi da kuma ga sahabbansa.
Yakokinsa: Allah ya yi wa Manzo izinin yakar mushirikai da kafirai da munafukai, sai ya yi dauki ba dadi da su a wurare da yawa da mafi girmansu sune: Badar- Uhud- Al-khandak (Ahzab)- Khaibar- Hunaini.
Matansa: KHadija ‘yar Khuwailid (A.S) ita ce matarsa ta farko, amma sauran su ne: Saudatu ‘yar Zami’a da A’isha ‘yar Abubakar da Gaziyya ‘yar Dudan (Ummu Sharik) da Hafsa yar Umar da Ramla ‘yar Abu Sufyan (Ummu Habibia) da Ummu Salama ‘yar Abu Umayya da Zainab ‘yar Jahash da Zainab ‘yar Huzaima da Maimuna ‘yar Al-Haris da Juwairiyya ‘yar Al-Haris da Safiyya ‘yar Huyayyi dan Akhdabl.
‘Ya’yansa: 1-Abdullah 2-Al-Kasim 3-Ibrahim 4-Fadima (A.S) a wani kaulin da Zainab da Rukayya da Ummu Kulsum.
Ammominsa: Tara ne, su ‘ya’yan AbdulMudallib ne: Al-haris da Zubair da Abu Dalib da Hamza da Al-Gaidak da Dirar Al-mukawwam da Abu Lahab da Abbas.
Ammominsa mata: Su shida ne daga iyaye mata daban-daban su ne: Amima da Ummu Hakima da Barra da Atika da Safiyya da Arwa.
Wasiyyansa goma sha biyu ne, su ne: Amirulmuminina Ali dan Abi Dalib (A.S) da Hasan dan Ali da Husain dan Ali da Aliyyu dan Husaini da Muhammad dan Ali da Ja’afar dan Muhammad da Musa dan Ja’afar da Ali dan Musa da Muhammad dan Ali da Ali dan Muhammad da Alhasan dan Ali da Muhammad dan Hasan Mahadi (A.S).
Mai tsaron kofarsa: Anas dan Malik.
Mawakinsa: Hassan dan Sabit, da Abdullahi dan Rawahata, da Ka’abu dan Malik.
Mai kiran sallarsa: Bilal Al-Habashi da Abdullahi dan Ummu Maktum da Sa’ad Al-kirdi.
Tambarin zobensa: Muhammadur Rasulullah!
Tsawon rayuwarsa: shekaru 63.
Tsawon lokacin Annabtarsa: shekaru 23.
Tarihin wafatinsa: 28 Safar 11 H.
Wajan da ya yi wafati: Madina.
Inda aka binne shi: Madina a Masallaci Madaukaki Mai alfarma.

Ali Dan Abi Dalib Al-Murtada (A.S)
Sunansa da Nasabarsa: Ali dan Abu Dalib dan Abdulmudall-ibi dan Hashimi dan AbdulManafi.
Mahaifiyarsa: Fadima ‘yar Asad dan Hashim dan Abdul Manaf Al-kunyarsa: AbulHasan, AbulHusaini, Abus-Sibdaini, Abur Raihanataini, Abuturab...
Lakabinsa: Amirulmuminin, Sayyidul muslimin, Imamul muttakin, Ka’idul gurralmuhajjalin, SayyidulAusiya, Sayyidul Arab, Al-Murtada, Ya’asubuddini, Haidar, Al-Anza’al Badin, Asadul-Lahi…
Ranar haihuwarsa: 13 Rajab shekara talatin bayan shekarar giwa wato bayan haihuwar Annabi (S.A.W) da shekara talatin. Inda aka haife shi: Makka cikin Ka’aba.
Yakokinsa: Ya yi tarayya a yakokin Manzo (S.A.W) gaba daya banda yakin Tabuka da Manzo ya umarce shi da ya zauna a Madina domin tafiyar da al’amuranta, amma yakokin da ya jagoranta da kansa a lokacin halifancinsa su ne: Jamal, da Siffaini, da Nahrawan.
Matansa: 1-Fadimatuz Zahra (A.S) ’yar Manzon Allah (A.S) 2-Amama ‘yar Abil Asi 3-Ummul banin Alkilabiyya 4-Laila ‘yar Mas’ud 5-Asma’u ‘yar Amis 6-Assahba’u ‘yar Rabi’a (Ummu Habib) 7-Khaula ‘yar Ja’afar 8-Ummu Sa’ad ‘yar Urwa 9-Makhba’a ‘yar Imru’ul Kaisi.
‘Ya’yansa: Masu Tarihi sun yi sabani kan yawan ‘ya’yansa amma suna tsakanin 25 ne zuwa 33 a ruwayoyi daban-daban, sai dai mu zamu ambaci fitattun cikinsu ne: (1-4) Al-Hasan da Al-Husaini da Zainabul-Kubura da Zainabus-Sugura (A.S) su ne ‘ya’yan Zahra (A.S) 5-muhammad Al-ausad 6-Al-Abbas
7-Ja’afar 8-Abdullahi 9-Usman dan Ali 10-Muhammad dan Hanafiyya 11-Muhammad Al-Asgar (Abubakar) 12-Yahaya 13- Umar dan Ali 14-Ummu Hani 15-Maimuna 16-Jumana (Ummu Ja’afar) 17-Nafisa.
Tambarin zobensa: Al-mulku lil-Lahil wahidil kahhar.
Tsawon rayuwarsa: Shekar 63.
Tsawon Imamancinsa: Shekara 30.
Tarihin shahadarsa: 21 Ramalana 40H.
Wurin da ya yi shahada: Masallacin Kufa.
Dalilin shahadarsa: Saran takobin nan na la’ananne Abdurrahman dan Maljam yana mai sujada a mihrabin masallacin Kufa.
Inda aka binne shi: Yankin Gariyyi a Garin Najaf.

Fadima Azzahra ‘Yar Muhammad (A.S)
Sunanata da Nasabarta: Ita ce Fadima ‘yar Muhammad (A.S).
Babarta: KHadijatul Kubra (A.S).
Al-kunyarta: Uwar babanta, Uwar Raihantaini, Uwar Imamai.
Lakabinta: Zahra, Al-batul, Assidika, Al-mubaraka, Addahira, Azzakiyya, Al-mardiyya, Al-muhaddasa.
Tarihin haihuwarta: 20 Jimada Akhir a shekara ta biyar da aike gun Ahlul Baiti (A.S).
Inda aka haife ta: Makka Mai girma.
Mijinta: Imam Ali (A.S).
‘Ya’yanta: Imam Hasan (A.S) da Imam Husain (A.S), Zainab uwar musibu (Saboda musibar da ta gani a Karbala), Muhsin (wanda aka yi barinsa a jikin bango), Zainb karama (Zainab As-Sugura).
Tambarin zobinta: Aminal mutawakkilun.
Mai hidimarta: Fidda.
Tsawon shekarunta: 18 a mashhuriyar magana.
Tarihin sahahadarta: 3 Jimada Akhir shekara 11 hijira, a wata ruwaya Jimada Auwal, tana mai ciwon sukan nan… da barin jariri da karayar kirji da hudar nan ta kusa.
Inda aka binne ta: Madina. Amma ba wanda ya san inda kabarinta yake har yanzu.

Hasan Dan Ali Al-Mujtaba (A.S)
Sunansa da Nasabarsa: shi ne Al-hasan da Ali dan Abu dalibi dan Abdulmudallibi (A.S).
Babarsa: Fadim Azzahara (A.S) ‘yar Manzon Allah (S.A.W).
Alkunyarsa: Abu Muhammad.
Lakabinsa: Attakiyyi, Azzakiyyi, Assibd, Addayyib, Assayyid, Alwaliyyi.
Tarihin haihuwarsa: 15 Ramadan 3 H. a mash’huri, a wata ruwaya an ce shekara ta 2.
Inda aka haife shi: Madina.
Yakokinsa: Ya yi tarayya a duk yakokin da aka yi wajan bude kasashen Afrika da kasashen Farisa tsakanin shekara ta 25 zuwa ta 30, ya kuma yi tarayya a duk yakokin da babansa ya yi na Jamal da Siffaini da Nahrawan.
Matansa: 1-Ummu Bashir ‘yar Mas’ud Khazrajiyya 2-Khaulatu ‘yar Manzur Alfazariyya 3-Ummu Ishak ‘yar Dalha Attaimi 4-Ja’ada ‘yar Ash’as.
‘Ya’yansa: 1-Zaid 2-Al-Hasan 3-Amru 4-Al-Kasim 5-Abdullah 6-Abdurrahman 7-Al-husaini 8-Dalhat 9-Ummul Hasan 10-Ummul Husaini 11-Fadimatu ‘yar Ummu Ishak 12-Ummu Abdullah 13-Fadima 14-Ummu Salama 15-Rukayya.
Tambarin hatiminsa: Al-Izzatu lil-Lahi Wahdah.
Tsawon rayuwarsa: Shekara 47.
Tsawon shekarun Imamancinsa: Shekara 10.
Sarakunan zamaninsa: Mu’awiya dan Abi Sufyan.
Tarihin shahadarsa: 7 Safar 49H, an ce 28 Safar 50H.
Inda ya yi shahada: Madina.
Dalilin shahadarsa: Guba da Mu’awiya ya ba shi ta hannun matarsa Ja’ada ‘yar Ash’as.
Inda aka binne shi: Makabartar Bakiyya Madina.

Husaini Dan Ali Asshahid (A.S)
Sunansa da Nasabarsa: Al-Husaini dan Ali dan Abi Dalib dan Abdul Mudallib. Babarsa: Fadima ‘yar Manzon Allah (S.A.W)
Alkunyarsa: Abu Abdullahi.
Lakabobinsa: Arrashid, Addayyib, Assayyid, Azzakiyyi, Almubarak, Attabi’i limardatil-Lah, Addalil ala zatil-Lah, Assibd, Sayyidi shababi Ahlil Janna, Sayyidus-Shuhada’u, Abul ayimma.
Tarihin haihuwarsa: 3 Sha’aban 4 H, ko 5 Sha’aban.
Inda aka haife shi: Madina.
Yakokinsa: Ya yi tarayya da babansa a yakin Jamal da Siffaini da Naharawan kuma shi ne jagoran Askarawan Rundunar Alkawari da imani masu tsanani a kan kafirai da mabiya bata a al’amarin kisan kare dangi da aka yi wa Ahlul Baiti (A.S) a Karbala.
Matansa: 1-Shazinan ‘yar kisra 2-Laila ‘yar Murra Assakafiyya 3-Ummu Ja’afar Al-kada’iyya 4-Arribab ‘yar Imri’ul Kais Al-kalbiyya 5-Ummu Ishak ‘yar Dalha Attaimiyya.
‘Ya’yansa: 1-Ali Akbar 2-Ali Asgar 3-Ja’afar 4-Abdullahi Addari’i 5-Sakina 6-Fadima.
Tambarin zobensa: Likulli ajalin kitab.
Tsawon rayuwarsa: shekara 57.
Tsawon Imamancinsa: shekara 11.
Sarakunan zamaninsa: Mu’awiya da Dansa Yazid.
Tarihin shahadarsa: 10 Muharram 61H.
Inda ya yi shahada: Karbala.
Dalilin shahadarsa: An kashe shi yana mai kare addinin kakansa Muhammad (S.A.W) a gumurzun dauki ba dadin nan na Karbala a kan rundunar fasiki Yazid.
Inda aka binne shi: Karbala.

Ali Dan Husaini Assajjad (A.S)
Sunansa da Nasabarsa: Aliyyu dan Husaini dan Ali dan abi Dalib (A.S).
Babarsa; ita ce Shazinan ‘yar Yazdajir dan Shahribar dan Kisra an ce sunta Shahri Banu.
Alkunyarsa; Abu Muhammad, Abul Hasan, Abul Husaini, Abul Kasim.
Lakabobinsa: Zainul Abidin, Sayyidul Abidin, Assajjad, Zussafanat, Imamul Muminin, Almujtahid, Azzahid, Al’amin, Azzakiyyi.
Tarihin haihuwarsa: 5 Sha’aban 38 H. a wata ruwaya 15 Jimada Akhir.
Inda aka haife shi: Madina.
Matansa: An rawaito cewa ya auri mata bakwai, Ta farko ita ce: Ummu Abdullahi ‘yar Al-Husaini (A.S) amma sauran duk Kuyangi ne.
‘Ya’yansa: 1-Imam Bakir (A.S) 2-Abdullahi 3-Al-Hasan 4-Al-Husaini 5-Zaid 6-Umar 7-Al-Husainil Asgar 8-Abdurrahman 9-Sulaiman 10-Ali 11-Muhammad Asgar 12-Khadija 13-Fadima 14-Aliyya 15-Ummu Kulsum.
Tambarin zobensa: Wama taufiki illa bil-Lahi.
Littattafansa; Sahifatus sajjadiyya da Risalatul hukuk.
Tsawon rayuwarsa: shekara 57.
Tsawon Imamancinsa: Shekara 35.
Sarakunan zamaninsa: Mu’awiya da Yazidu dan Mu’awiya, da Mu’awiya dan Yazidu dan Abi Sufyan, da Marwana dan Hakam, da Abdulmalik dan Marwana, da Walida dan Abdulmalik.
Tarihin shahadarsa: An yi sabani a kan hakan amma an ce 12 Muharram ko 18 ko 25 ga Muharram, haka nan shekara an ce 94 ko 95 H.
Inda ya yi shahada: Madina.
Dalilin shahadarsa; Guba da aka ba shi a lokacin halifancin Walid dan Abdulmalik.
Inda aka binne shi: Makabartar Bakiyya Madina.

Muhammad Dan Ali Al-Bakir (A.S)
Sunansa da Nasabarsa: Muhammad dan Ali dan Husaini dan Ali dan Abi Dalib (A.S).
Mahaifiyarsa: Fadima ‘yar Hasan (A.S).
Alkunyarsa: Abu Ja’afar.
Lakabinsa: Al-bakir da Bakirul Ulum da Asshakir da Al-Hadi.
Tarihin haihuwarsa: 1 Rajaba 57 H, ko 3 Safar.
Inda aka haife shi: Madina.
Matansa: 1-Ummu Farwa ‘yar Al-Kasim 2-Ummu Hakim ‘yar Asid Assakafiyya 3-4 kuyangi biyu.
‘Ya’yansa: 1-Ja’afar Assadik (A.S) 2-Abdullahi 3-Ibrahim 4-Ubaidul-Lahi 5-Ali 6-Zainab 7-Ummu Salama.
Tambarin zobensa: Al-izzatu lil-Lahi.
Tsawon rayuwarsa: Shekara 57.
Tsawon Imamancinsa: shekara 19.
Sarakunan zamaninsa: Walid dan Abdulmalik da Sulaiman dan Abdulmalik da Umar dan Abdulaziz da Yazid dan Abdulmalik da Hisham dan Abdulmalik.
Tarihin shahadarsa: 7 Zulhajj 114H.
Inda ya yi shahada: Madina.
Dalilin shaha-darsa: Guba da Ibrahim dan Walid dan Yazid ya ba shi a lokacin halifancin Hisham dan Abdulmalik.
Inda aka binne shi: Bakiyya a Madina.

Ja’afar Dan Muhammad Assadik (A.S)
Sunansa da Nasabarsa: Ja’afar dan Muhammad dan Ali dan Husaini dan Ali dan Abi Dalib (A.S).
Mahaifiyarsa: Ummu Farwa ‘yar Kasim dan Muhammad dan Abubakar.
Alkunyarsa: Abu Abdullah, Abu Isma’il.
Lakabinsa: Assadik, Assabir, Alfadil, Addahir, Alkamil, Almunji.
Tarihin haihuwarsa: 17 Rabi’ul awwal 83H.
Inda aka haife shi: Madina.
Matansa: Fadima ‘yar Husaini dan Ali dan Husaini (A.S), sauran matansa kuyangi ne.
‘Ya’yansa: 1-Isma’il 2-Abdullah 3-Musa 4-Ishak 5-Muhamma-d 5-Abbas 6-Ali 7-Ummu Farwa 8-Asma’u 9-Fadima. Tambarin hatiminsa: Allahu waliyyi wa Ismati min khalkihi.
Tsawon rayuwarsa: Shekara 65.
Tsawon Imamancinsa: shekara 34.
Sarakunan zamaninsa na Umayyawa: Abdulmalik dan Marwan da Walid dan Abdulmalik da Sulaiman dan Abdulmalik da Umar dan Abdulaziz da Walid dan Yazid da Yazid dan Walid da Ibrahim dan Walid da Marwan Al-himar.
Na lokacin Abbasawa: Abul Abbas Assaffah da Abu Ja’afar Al-Mansur Addawaniki.
Tarihin shahadarsa: 25 Shawwal 148H. Inda ya yi shahada: Madina.
Dalilin shahadarsa: Guba da ya sha a lokacin Mansur dawaniki. Inda aka binne shi: Makabartar Bakiyya a Madina.

Musa Dan Ja’afar Al-Kazim (A.S)
Sunansa da Nasabarsa: Musa dan Ja’afar (A.S).
Babarsa: kuyanga ce sunanta (Hamida).
Alkunyarsa: Abul-Hasan, Abu Ibrahim, Abu Ali, Abu Isma’il.
Lakabinsa: Al-Abdussalih, Assabir, Al-amin, Al-Kazim shi ne ya fi shahara.
Tarihin haihuwarsa: 7 Safar shekara 128H.
Inda aka haife shi: Al-abwa’i a Madina.
Matansa: Dukkaninsu kuyangi ne.
‘Ya’yansa: Yana da ‘ya’ya 37 : 1-Ali Rida 2-Ibrahim 3- Abbas 4-Isma’il 5- Ja’afar 6-Harun 7-Husaini 8-Al-Kasim 9-Ahmad 10-Muhammad 11-Hamza 12-Abdullah 13-ishak 14-Ubaidul- Lahi 15-Zaid 16-Hasan 17-Al-fadl 18-Sulaiman 19-Fadimatul-kubra 20- Fadimatus-sugra 21-Rukayya 22- Hakima 23-Ummu Abiha 24-Rukayya 25-Kulsum 26-Ummu Ja’afar 27-Lubabatu 28-Zainab 29-Khadiza 30-Aliya (Ulayya) 31-Amina 32-Hasana 33-Bariha 34- A’isha 35-Ummusalama 36-Maimuna 37-Ummu Kulsum.
Tambarin zobensa: Hasbiyallah.
Tsawon rayuwarsa: shekara 55.
Tsawon Imamancinsa: shekara 35.
Sarakunan zamaninsa Lokacin Umayyawa: Marwanal himar. Lokacin Abbasawa su ne: Abul Abbas Assaffah da Abu Ja’afar Al-mansur da Muhammad Mahadi da Musa Alhadi da Harunar -Rashid.
Tarihin shahadarsa: 25 Rajab 183H.
Inda ya yi shahada: Bagdad.
Dalilin shahadarsa: An kashe shi da guba a lokacin Harunar-Rashid.
Inda aka binne shi: A Makabartar Kuraishawa a Kazimiyya a Arewacin Bagdad.