A kan imami kuma cewa ya yi:- “(Shi) tauraruwa mai shiryarwa ne, ruwan dadi ne, matsera daga halaka ne, girgije mai kawo ruwa ne, mafakar bayi a lokacin bala’i ne, amintaccen Allah kan halitarsa ne, hujjarsa bisa bayinsa ne, halifansa a kasashe ne, mai kira zuwa ga Allah, mai tsare hurumin Allah ne, daidaiton addini ne, daukakar musulmi ne, fushin munafukai ne, kuma halakan kafirai ne”[29]
Duk nauye-nauye da mas’uliyyar da Annabi ya gudanar, Ali (a.s) da imamai daga ‘ya’yansa suna daukarsu.[30]
A wata riwaya daga Imam Sadik (a.s) akwai ta’kidi kan biyayya ga ‘wasiyyai’. Riwayar ta fayyace cewa wasiyyan su ne wadanda Alkur’ani ya kira da lakabin ulul amri .[31]
Daruruwan riwayoyi da ke rarrabe cikin babi daban-daban suna fayyace mana cewa manufar imam da imamanci a tunanin shi’a ba komai ba ce face jagoranci da gudanarwa na al’amuran musulmar al’umma kuma imaman Ahlulabaiti (a.s) basu takaita wajen da’awar imamanci kan abin da ya shafi tunani da ma’nawiyya kadai ba, a’a suna kira da cewa hukuma ita ma tasu ce. Kiransu mai fadi kamar haka mai kuma tattara dukkan sassa hakika kira ce ta wata harakar siyasa da kuma soji wadda take da zimmar karbar shugabanci.
Wannan batu ya ci gaba da zama boyayye ga masu bincike a zamunnan da suka biyo baya amma a fahimtar sahabban imamai da wadanda suka yi zamani da su batun yana daga mafi bayyanannun al’amura. A cikin daya daga kasidunsa na Hashimiyyat, Kumait yana sifanta imaman Ahlulbaiti da cewa su ne shugabanni masu jagorantar mutane ta wata hanya wacce ta saba gaba daya da hanyar da azzaluman mahukunta suka bi, inda suke mu’amala da mutane tamkar dabbobi.[32]
Mu koma ga maudu’in asali cewa kashin baya a kiran Imam Sadik (a.s) da sauran imaman Ahlulbaiti (a.s) shi ne batun imamanci. A tare da mu akwai riwayoyi masu karfafa juna wadanda suke tabbatar da wannan batu na tarihi. Ana nakalto su a bayyane tare kuma da wannan fayyacewa daga Imam Sadik (a.s) inda ya yi da’awar imamanci. Za mu bayyana nan gaba cewa lokacin da Imam yake bayar da sanarwar wannan kiran nasa, yana ganin kansa cikin wani mataki na jihadi mai bukatar ya yi watsi da mahukuntan zamaninsa, ta hanya bayyananna kuma kai tsaye, sannan kuma ya sanar cewa shi ne ma’abocin hakki na hakika, ma’abocin shugabanci (wilaya) da kuma imamanci. Irin wannan fitowa, bisa al’ada, tana nufin an ketare sauran matakan jihadi wadanda suke gabatarta tare da nasara. Dole ne ya kasance farkawa a siyasance da yanayin zaman jama’a ta zama tuni ta sami goyon baya mai fadi, ana jin shirin mutane ya yi karfi a ko wani wuri, shimfida kan manufa ta kankama ga wani adadin mutane mai dama, sannan jama’a masu yawa sun yi imani da wajibcin kafa hukumar gaskiya da adalci, sannan daga karshe, jagoran ya zama ya riga ya dauki kuduri mai karfi akan wannan fito-na-fito mai tsanani. Idan wadannan sharuddan basu cika ba,sanarda imamancin wani mutum ayyananne da jagorancin sa na gaskiya ga al’umma abu ne mai tattare da ujula ba kuma cimma manufa tare da shi.
Wata mas’alar da ba makawa ga karfafawa game da ita a wannan bayanin ita ce, a wadansu lokutan Imam Sadik (a.s) ba ya takaita kan tabbatar da imamancinsa kadai, yana ma ambaton sunayen imaman gaskiya magabatansa tare da ambaton nasa sunan, watau, bisa hakika, yana gabatar da silsilar imaman Ahlulbaiti tare da sadarwa, daya bayan daya, ta yanda yayyankewa ko rarrabewa ba ya yiwu wa.
Wannna matsayin yana nuni da dangantakar da ke akwai tsakanin jihadin imaman Ahlulbaiti (a.s) da dorewarsa tun daga zamunnan da suka gabata har zuwa lokacin Imam Sadik (a.s). Imam Sadik (a.s) yana bada sanarwar imamancinsa a matsayin shi na wani sakamakon da ba makawa zai biyo bayan imamancin magabatansa, kuma da wannan yake bayyana tushen wanna kiran da zurfin kafuwarta a tarihin sakon musulunci, da dangantakarta da ma’abocin kiran, Manzon mai girma, mafificin tsira da aminci ya tabbata gare shi. Bari mu kawo wasu samfurin kiran Imam:-
Riwayar Amru ibn Abi Mikdam ita ce mafi ban-sha’awa a wannan babin, tana kuma sauwara wani yanayi mai ban mamaki.
A ranar tara ga watan Zulhijja, yayin da mahajjata suka taru a Arfa domin tsayuwa gashi sun riga sun hallara a wannan wuri daga ko ina: kamar daga karshen kasar Kurasan har zuwa gabar tekun Atlantika, a wannan wuri mai hadarin gaske, inda kira a cikinsa tana iya aika amon ta zuwa nisan duniyar musulunci. Imam ya hadu da wannan taron jama’u masu yawa saboda ya isar musu da kalmarsa. Mai ruwaya yace:- na ga Imam ya tsaya cikin jama’an nan, ya daga murya da kyau domin ya isa kunnuwar mahalarta sannan daga bisani ya kai ga kunnuwan talikai, yana kira kamar haka:-“Ya ku mutane ! Lallai Manzon Allah ya kasance shi ne shugaba (imam), sannan Ali ibn Abi Talib, sannan Hassan, sannan Hussaini, sannan Ali ibn Hussain, sannan Muhammad Ibn Ali, sannan ……..” Yana wannan kiran sau uku ga wadanda suke gabansa, da gefensa na dama, da gefensa na hagu da kuma bayansa, kira goma-sha biyu ke nan”[33]
A wata riwayar daga Abu Sabah Alkinani cewa Imam Sadik (a.s) ya sifanta kansa da kuma imaman shi’a da cewa ganima (anfal) da zababben dukiya tasu ce.
Daga Abi Sabah ya ce:- Abu Abdillah ( a.s) ya ce da ni: “Ya Aba Sabah, mu mutane ne wadanda Allah ya farlanta biyayya gare mu. Ganima tamu ce, zababben dukiya namu ne, mu ne matabbata cikin sani kuma mu ne wadanda aka yi wa hasada wadannan da Allah ya fade su cikin littafinsa”[34]
Safwul mali, zababbar dukiya, shi ne kayayyakin da suke da kima matuka daga cikin ganimar yaki. Da ba’a raba wa mayaka irin wadannan kayayyakin kamar yanda ake raba musu sauran dukiyar ganima saboda kada a fifita wani da zababben abu, gudun kada wannan ya zamewa wani wata daraja ta karya. Maimakon haka ana barin irin wadannan kayayyaki ne a hannun shugaban musulunci ya yi amfani da su wajen abin da zai tabbabtar da maslahar musulmi gaba daya. Azzaluman mahukunta su kan dauki irin wannan dukiya su kebanta da ita ta hanyar kwace(gasabi). Imam yana fayyacewa kan cewa zababbar dukiya, wajibi ta zama tasu, haka nan ganima. Wannan yana nufin cewa Imam yana bayyana kansa a sarari a matsayin shugaban musulmi a ganin shari’a, wanda nauyin jujjuya wadannan dukiyoyi dai-dai da abin da yake ganin zai tabbatar da maslahar al’umma a kansa yake.
A wani hadisin Imam Sadik (a.s) yana ambaton sunayen imamai magabatansa daya bayan daya, yana ba da shaidar imamancinsu da wajib cin biyayya gare su. Yayin da ya iso kan sunansa sai ya yi shiru, masu saurare kuma sun sani sarai cewa gadon ilmi da hikima bayan Imam Bakir (a.s) a wajen Imam Sadik (a.s) yake. Kuma da wannan Imam (a.s) yake bayyan hakkinsa na jagorantar al’umma, yana bayyana shi da wani salo mai danganta hakkin nasa da kakansa Ali ibn Abi Talib (a.s). Cikin wadansu babi-babi na littafin Alhujja cikin Alkafi da ma cikin juz’i na arba’in da bakwai na Biharul Anwar akwai irin wadannan hadisai da yawa, suna fayyacewa, wani zubin kuwa suna kinaya kan da’awar imamanci da kuma kira gare ta.
Domin tabbatar da wannan batu na tarihi, akwai hujjoji ko shaidu da suke tabbatar da samuwar wani tsararren shirin sadarwa da yake gudanar da kiran Imam (a.s) a ko ina cikin sassan duniyar musulunci. Mayawaitan hujjoji da ke akwai a kan wannan batu sun sa samuwar wannan shirin sadarwa wani al’amari ne yankakke ba wani shakka a kansa. Wadannan shaidun sun yi yawa da karfin da ana iya kafa hujja da su a kan wannan maudu’i namu, hujja tabbatatta, ko da ba’a sami sahihin hadisi ko guda ba kan wannan batu. Mu dubi wadannan tabbatattun al’amuran tarihin:-
1.Akwai wata tsararrar alaka ta tunani da ta abin da ya shafi dukiya tsakanin imamai (a.s) da mabiyansu, kuma an kasance ana daukar dukiyoyi daga sassa dabam dabam na duniya ana kaiwa Madina kazalika da tambayoyin addini mayawaita.
2.Fadadar fagen da ke wilaya ga mutanen gidan Manzo (s.a.w.a) musamman a yankunan duniyar musulunci wadanda suke masu saurin daukar dumi.
3.Tattaruwar jama’a masana hadisi da maruwaita Kurasanawa da Sistanawa da Kufawa da Basarawa da Yamanawa da Misrawa gaban Imam (a.s).
Shin wannan al’amari wanda sashensa yake munasaba da sajewa da sashe ya faru ne kwatsam ba tare da an shirya shi ba?
Wajibi ne mu yi kari da cewa wannan al’amari ya tabbata ne karkashin ikon siyasa wanda ya yi da gaske wajen watsi hatta da sunan Ali (a.s) kai da ma zagin Ali a kan mimbarori da wanzar da nau’o’in dira da razanarwa kan mabiyansa. To a irin wannan halin, yaya aka iya samar da mabiya mayawaita masu wilaya ga Ahlulbaiti daga cikin talakawa suna taka dubban milamilai saboda su kai kasar Hijaz da birnin Madina da zimmar daukar karatu gaban imaman Ahlulbaiti (a.s) da kuma koyon tunanin musulunci a kan rayuwar dai-daiku da ta jama’a da kuma tattaunawa da su kan batutuwa mayawaita da kuma mas’alolin tawaye wa yanayin barna da fasadi, ko kuma kamar yanda riwayoyi suke kiran al’amarin-mas’alolin ‘tsayawa’ da ‘ficewa’ daga da’a ga azzalumai )?!!
Idan da ace masu kiran Ahlulbaiti suna takaita bayanansu ne kan ilmin imamai (a.s) da zuhudunsu, to me ya sa tattaunawar wadannan mabiyan a kullum take kan batun tawaye ta hanyar daukar makami? Shin wannan baya nuni da samuwar wani tsararren shirin sadarwa saboda kira zuwa imamancin Ahlulbaiti (a.s) da cikakkiyar ma’anar imamanci, watau tsrin tunani da na siyasa?
A nan tambaya za ta zo kan cewa dalilin kawaicin tarihi dangane da samuwar irin wannan tsararren shirin sadarwa a kiran Ahlulbaiti (a.s). Shin mene ne ya sa tarihi bai ambaci komai kan wannan batu a fayyace ba? Amsa ita ce abin nan da muka yi nuni da shi a baya. Ta yiwu sahabban imamai sun lizimci ka’idar nan ta hikima wajen haraka wanda aka sani da takiyya, wanda take ba ta bada duk wani bare a tsarin imama damar kutsa kai. Haka kuma mai yiwuwa ne tarihi bai ce komai ba saboda rashin kaiwa harakar jihadi ta shi’a ga tabbatar da manufofinta da karbar ragamar mulki. Da a ce Banu Abbas basu hau karagar mulki ba da kuwa, ba shakka duk bayanen aikace-aikacensu na sirri da muhimman batutuwan kiransu mai dadi da mara dadi da ya takaita ga zukatansu kadai, ba tare da wani ya san su ba kuma da tarihi bai rubuta komai a kansu ba.
Duk da haka riwayoyin da suke fayyacewa gwargwado kan samuwar mayalwacin kira zuwa ga imamancin Ahlulbaiti (a.s) ba kadan suke ba. Za mu hakura da guda daya mai cewa:-
Wani mutum daga mutanen Kufa ya zo Kurasan, sai ya kira mutane zuwa wilayar Jafar ibn Muhammad (a.s). Wata jama’a sai ta bi shi ta amsa kiransa. wata kuma ta musa masa ta yi inkari wata kuma ta dakata ta yi tsantseni. Sannan riyawar ta ce: Sai mutum daya daga kowace jama’a ya tafo wa Imam Abu Abdillahi (a.s). Mai magana daga cikinsu shi ne wannan da ya dakata ya yi tsantsenin. Sai ya ce : Allah ya kiyaye ka, wani mutum ya zo mana daga mutanen Kufa ya kira mutane zuwa biyayya da wilaya gare ka sai wasu mutane suka amsa masa, wasu suka yi inkari wasu kuma suka ya tsantseni suka dakata. Imam (a.s) ya ce:- “Daga cikin ukun wacce kake ciki? “Ya ce:- Daga jama’ar da ta yi tsantseni ta dakata. Ya ce: To ina tsantsenin ka yake daren kaza da kaza? (sai ya tunatar da shi kasawarsa a wani hali na sha’awa) sai mutumin ya yi shakka. [35]
Kamar yanda ka ji, mai kiran daga mutane Kufa yake, kiran nasa kuwa zuwa imamancin Ja’afar ibn Muhammad Al Sadik (a.s) da wilayarsa da kuma biyayya gare shi ne.
Akwai wadansu hujjoji daban masu bayyana abin da kiran imaman Ahlulbaiti (a.s) da shi’arsu kan imamanci ya kunsa. Jayayya tsakaninsu da abokan hamayyarsu na siyasa (Umayyawa da Abbasiyawa) ta bijiro da shi. Wani lokaci ana wannan jayayya ne ta hanyar kafa hujja a fagen addini da ilmul kalam a wasu lokatan kuma tana daukar salon adabi mai zurfi ta hanyar wake. Duk jayayyar ana yin ta ne kan tabbatar da cancantar imamanci a siyasance da shugabanci ga imaman Ahlulbaiti (a.s) da gwagwarmaya da masu kankamewa kan karagar hukumar musulmi bisa zalunci da kwace. Saboda yin zamani daya da harakar Abbasiyawa da samun nasararta, lokacin Imam Sadik (a.s) ya kasance a cike yake da irin wannan jayayya da mujadala.
Mawakan Abbasiyawa suna kokarin tabbatar da cancantar shugabanci ga Abbasiyawa suna dogaro da hujjojinda, bisa al’ada, masu kwadayin mulki da kuma masu kankamo da karagar sarauta suke gabatarwa. Mawakan shi’a kuwa sukan fuskance su suna gugar wadancan hujjojin suna masu kafa hujja kan fandarar da mulkin Abbasiyawa ya yi daga mandikin musulunci ( dalilan da ya dogara a kansu ) wanda yana kafe ne bisa yarfar da zalunci da aikata laifi da ha’intar hakkokin al’ummar musulunci.
Mukabala ta hanyar wake tsakanin Abbasiyawa da Alawiyyawa tana da muhimmanci a nan saboda irin muhimmiyar rawar da wake ke takawa a wancan lokacin wajen bayyana abin da rai ya kunsa da tunane-tunane saboda kuma irin tsarin da yake da shi kan mabiya cikin talakawa. Ma’abocin littafin “Abbasiyawan Farko” yana ambatar rawar da adabi ya taka a karnin farko da na biyu. Ya ce:-
“Adabi ya kasance yana tasiri a zukata yana kokarin samun goyon bayan jama’a da karkatarsu ga wannan kungiya ko waccar, mawaka da masu jawabi matsayinsu irin wanda jaridu suke da shi ne a yau . Ko wannensu yana bayyana wani ra’ayin siyasa ne yana kuma kare wata kungiya ayyananna, yana bijiro da dalilin ingancikin kirar da yake yi daya bayan daya yana rushe ra’ayoyin abokan hamayya da magana maiu tasiri da salo mai fasaha”[36]
Mawakan fadar Abbasiyawa sun kasance suna kokarin tabbatar da cancantar Abbasiyawa ga halifanci da hujjar alakarsu da Annabi ta hanyar ‘ya’yan baffa, sun kafa hujja kan hakan da cewa gado ba ya riskar ‘ya’yan diya tare da samuwar baffanu. Saboda haka halifanci a bayan Annabi hakkin Abbas, baffan Annabi ne, a bayansa kuma, na ‘ya’yansa ne, watau yayan Abbas. Marwan ibn Abi Hafsa ya ce:-
Kaka zai yiwu, ai bai yiwuwa,
Gadon baffanu a hannun dan diya
Abban ibn Abdilhamid Lahiki ya ce:-
Ya’yan Abbas su ke da gado nai,
Baffa ga dan baffa ai hijjabi ne
Mabiya Ahlulabaiti sai suka zabura saboda ji a jika cewa wannan furuci zalunci ne, suka yi raddi kan wadancan hujjoji da irin tunanin (mandiki) da aka yi amfani da shi a wani lokaci, a wani zubin kuma su kan dauki wani mandikin dabam, daboda kafa hujja kan hakkin imaman Ahlulbaiti na imamanci. Daga wannan akwai kafa hujja da hadisin Gadir kummi kamar zancen Sayyid Himyari, inda ya ce:-
Wanda nake a gare shi shugaba,
Wannan tabbas a gare shi shugaba
Amma sun ki yarda sun ki gamsuwa
Muhammad ibn Yahya ibn Abi Murra Taglibi ya yi raddi kan hujjar mawakin Abbasiyawa wanda ya yi magana kan gadon baffanu, ya ce:-
Me zai hana, kai hakika hakku ne,
Rabon baffa a tattara shi wa dan diya
Rabi daga dukiya na diyarsa ne,
Shi baffa ya tai gida ba ko daya
Kai sakakke me ya kai ka batunta ne?
Ba don kisa ba bai ruku’i ko daya
Du’bal yana ganin cewa duk ma masifun da suka auka wa Ahlulbaiti (a.s) ba don komai ba ne sai domin sun gaji Annabi, sai masu hadama suka yi rub da ciki kan wannan gadon kuma suka cutar da wanda shi ke da hakkin imamancin.
Gadon Ma’aiki ya lahanta madaukaka,
Mutuwa, tsoro wawasonsu suke
Kurayen Umayya su kira su azazzala,
Tuttudar kunci, da masifu kansu ne
Banu Abbasin dinu su barnata,
Ha’inci, zalunci, halinsu ne
Wai shi Rashidu saboda shiriya tasa
Mamun, Amin ka ga fa nasu ne
Shiriya! Wanga bai tsare hakki ko daya
Amincin biyun zagon ga Islama ne
Ba abu ne mawuyaci ba ga mai bincike a kan farkon zamanin Abbasiyawa samun daruruwan misalai kan muhawarori da mukabalar siyasa wadanda suka kai yawan wake-waken da aka yi kan wannan batu. Mawakan shi’a da abokan hamayyarsu su kan kafa hujjoji ne kan kiran da kowannensu yake yi. Ba shi da muhimanci mu san ingancin hujjojin da ake kafawa a wannan jayayya, abin da yake da muhimmanci shi ne mu gane ginshikin jayayyar da ake yi da kuma hakkin da sassan biyun ke da’awarsa. Akwai wani hakkin da ko wani sashe yake da’awa wannan kuwa shi ne gadar Manzon Allah (s.w.a) wajen mulki da jagorancin musulmi.
Jayayyar tsakanin sashen Alawiyawa da na Abbasiyawa ba kan gadar tadodi da dabi’u na gari da ma’nawiyya ko tsarin tunani irin na Annabi (s.a.w.a) ba ne. Ba wai ana sassabawa kan wane ne ya cancanci gadon wata tada ba ne, domin wadannan tadodi ba wani hakki ne da bangare biyun za su yi sa-in-sa a kai ba. Jayayyar dai a kan wani hakki ne wanda sassan biyu suke da’awarsa. Kuma mun ji yanda mawaka a zamanin Imam Sadik (a.s) suke kare hakkin imami na jagorancin musulmar al’umman nan ma na mulkar jama’ar musulunci. Suna kuma kutsawa cikin yaki da wadanda basu da cancantar mulkar musulmi. Akwai shaidu masu yawa kan wannan batu a wake-waken karni na biyu bayan hijjira.
Kafin mu rufe wannan fasali ya dace mu yi nuni da wani salon kafa hujjan daban wanda kuwa shi ne salon wasika. Wadannan wasikun kafa hujja, a wani gefen, suna kunshe da bayanan manufofin kungiyoyi a sarari ba da wata rikitarwa ba. Ta wani gefen kuwa suna jan hankalin talakawa bayan yaduwar manufar bayanan. Kazalika ana samun tasiri mai karfi kan mataimaka da kuma abokan hamayya. Za mu ambaci wasikar da Muhammad ibn Abdillah ibn Hassan, Nafsi Zakiyya, ya aikewa Mansur sarkin Abbasiyawa. Wannan Ba’alawe mai neman juyi yana fayyacewa gaba gadi cewa yana fafutukar kwabe halifanci daga hannun abokin hamayyarsa domin ya kasanse a hannun ‘ya’yan Ali (a.s), ya ce:- “Lallai mahaifinmu Ali ya kasance shi ne wasiyyi kuma shi ne imami, to ta yaya kuka gaji shugabancinsa alhali ‘yayansa suna raye?”[37]
Ga alama Ba’alawen ya kawo wannan hujjan ne saboda raddi kan kafa hujja da Abbasiyawa suka yi kan gadar halifanci, domin banu Abbas ba su mallaki wata hujja ba face wannan da’awar gadon. Nafsi zakkiya ya yi haka ne domin ya toshe musu duk wata kafa da irin nasu mandikin (salon hujja).
Ana iya lura a kalmominsa yanda yake karfafawa kan imammanci kana ya karfafa kan yanayin kiran Gidan Ali wanda wannan mai neman juyin yake wakilta a wannan jayayya.
2. Sharhi kan hukunce-hukunce da tafsirin Alkur’ani dai-dai da abin da mazhabin Ahlulbaiti (a.s) ya gada daga Manzon Allah (s.a.w.a).
Wannan aikin shi ma ana iya ganinsa a rayuwar Imam Sadik (a.s) fiye da yanda ake iya ganin sa a rayuwar sauran imaman Ahlulbaiti (a.s) abin da ma ya sanya ake kiran fikihun shi’a da sunan Fikhun Ja’fari kenan. Hatta masu rintsa ido kan ayyukan Imam Sadik na siyasa sun hadu kan cewa Imam ya kasance yana gudanar da daya daga cikin mafi girman makarantun fikihu a zamaninsa, idan ma ba mafi girmansu ba. Abin da bai gushe ba yana lullube ga barin idanun mafi yawan masu bincike kan rayuwar Imam shi ne ma’ana ta siyasa da ta gwagwarmaya wadanda irin wadannan ayyukan Imam suke dauke da shi. Wannan shi za mu kawo a yanzu.
Da farko ya zama wajibi mu ambata cewa mukamin halifanci a musulunci yana da wadansu sifofin da suke sanya shugaba ya banbanta da shugabanni a wadansu tsare-tsaren shugabanci na daban. Shi halifanci ba wai tsarin siyasa ne kadai ba a’a, shi tsari ne na siyasa da addini a gwame. Baiwa shugaban musulunci lakabin halifa yana karkafa wannan batu: shi halifan Manzon Allah (s.a.w.a) ne a duk wani aikin da Manzo yake aiwatarwa ga jama’a wa lau nauyin da ya shafi addini ne ko kuwa na jagorancin siyasa.
Shi halifa a musulunci yanan dauke da mas’u’liyyar siyasa da ta addini gaba daya. Wannan tabbataccen al’amari ya sa halifofin da suka zo bayan na farko, wadanda rabonsu a cikin ilmomi addini ya yi karanci ainun, ko kuwa basu da wani rabo sam, ya sanya su rufe wannan nakasu ta hanyar malaman addini masu aikata musu abin da suke so. Sai suka baiwa fukaha’u da malaman tafsiri da na hadisi aiki a fada saboda tsarinsu na shugabanci ya tara sassan nan biyu: na addini da na siyasa.
Wata fa’idar samuwar masu wa’azin sarki a tsarin shugabanci, ita ce: azzalumin shugaba mai kama karya, a duk lokacin da ya so, yana iya canja wa hukunce-hukuncen addini fuska ko kuma ya musanya su dai-dai da bukatunsa. Wadancan ma’aikata, malaman fada, su suke aiwatar da wannan domin dadada wa masu azurta su. Suna yin haka ne karkashin rigar istinbadi da ijtihadi mai rudin jama’a.
Mawallafa da marubuta tarihi daga magabata sun ambato mana misalan da kare ba zai ci ba kan kirkirar hadisai da tafsiri da ra’ayi inda ake ganin hannun ikon siyasa a sarari. Za mu yi nuni da wani abu akai a nan gaba. Wannan al’amari wanda da farko(har zuwa karshen karnin farko bayan hijira) ya dauki salon kirkirar riwaya ko hadisi, sannu a hankali ya dauki matsayin fatawa. Daboda haka ne a karshen zamanin Banu Umayya da farkon na Banu Abbas muke ganin bayyanar fukaha’u masu yawa suna amfani da hanyoyin ka’idojin istinbadi masu rauni domin su kafa dokoki dai-dai da zabinsu wanda a kashin gaskiya zabin tsarin da yake shugabanci ne. A fagen tafsirin Alkur’an ma, dai-dai wannan aiki aka zartar. Tafsiri da ra’ayi, galibi, ya sa gaba wajen bayar da fahimce-fahimce wa musulunci, wadanda basu dogara da komai ba face zabin mai fassara da son ransa, wanda ba kome na ne illa son ran tsarin da yake shugabanci.
Wannan shi ne musabbabin rabuwar ilmomin musulunci: na fkihy da hadisi da tafsiri, tun zamunan na farko, zuwa ra’ayoyi biyu.
Ra’ayin Farko:- Ra’ayin da ke da alaka da tsarin azzulumar hukuma mai kwace. Yana bambata da dayan wajen sadaukar da gaskiya domin tabbatar da ‘maslaha’ wacee bisa hakika maslahar tsarin da ke shugabanci ne. Daga sifofin wannan ra’ayin har wala yau akwai baudar da hukunce-hukuncen Allah domin, ladan ‘yan dirhamomi.
Ra’ayin na Biyu:- Ra’ayi dan asali amintacce wanda ba ya ganin akwai wata maslaha mai daraja da daukaka da ta wuce bayyana ingantattun hukunce-hukuncen Ubangiji. Wannan ra’ayi ya kasance, ko an ki ko an so, yana cin karo da tsarin da yake shugabanci da kuma masu wa’azin fada, a duk wani taku da ya yi. Saboda haka tun farkon al’amari ya dauki mafuskanta irin ta talakawa tare da taka tsan- tsan da kiyayewa.
Fahimtar wannan zai sa mu gane da kyau cewa sabawan Fikihun Ja’afar da fukaha’un sarauta a zamanin Imam Sadik ba wai sabawa ce ta tunani da akida kadai ba, a’a ta hada har da abin da ya kunsa na hari irin wanda abokin hamayya yake yi.
Mafi muhimmanci daga kusurwowin wannan abin da ya kunsa shi ne tabbatar da cewa tsarin da ke shugabanci fanko ne kawai wanda ya rasa dukkan ma’anonin addini, ga kuma gajiyawarsa wajen gudanar da al’amuran tunani ga al’umma. Ko kuma mu ce rashin cancantarsa hawa mukamin “halifanci”. Wata kusurwa ita ce ayyana wuraren da aka baude cikin fikihun sarauta, wadannan baude-baude da aka gina kan tunanin “maslaha” wajen bayanin hukunce-hukuncen fikihu da sassautarwar malaman fikihu ga tsarin da ke shugabanci. Imam Sadik (a.s), da ayyukansa na karantarwa da kuma sabar nauyin bayyana hukunce-hukuncen fikihu da ilmomin musulunci da tafsirin Alkur’ani ta hanyar da ta saba da ta masu wa’azin fada, hakika, a’aikace, ya dauki matsayin hamayya da tsarin da ke mulki. Da wannan aikin, Imam ya iya watsi da duk tsarin sarauta a addini da fikihu wanda wani bangare ne na hukumar halifofi, ya kuma tube wa tsarin da ke mulki duk wata rigar addini.
Ba mu da wani tabbataceen isnadi mai bayyana lurar tsarin Umayyawa da wannan janibin hamayya, wanda Imam Sadik (a.s) ya aiwatar a fagen ilmi da fikihu. Sai dai abin da aka fi tsammani shi ne tsarin Abbasiyawa mai mulki-----musamman lokacin Mansur wanda yake mai wayo da gogewa da fahimtar halayyar duniya, abubuwan da ya koya a lokacin dambarwar siyasa mai tsawo sakaninsa da mulkin Umayyawa kafin shi kansa ya sami mulkin--wannan tsarin nasu yana kiyaye mas’alolin masu wuyar fahimta da ke tattare da ayyukan gidan Ali. Kuma tsarin Abbasiyawa mai mulki yana fahimtar muhimmiyar rawar da wancan aikin ulmi zai iya takawa ta bayan fage.
Barazana da kuntatawa da matsin lamba wadanda suke tattare da ayyukan Imam Sadik (a.s) na ilmantarwa wadanda kuma riwayoyi masu yawa na tarihi ke nakalto mana, sakamakon wannan luran ne da kasancewar mas’alar mai hadari ce. Kazalika muhimmancin da Mansur ya bayar wajen tara mashahuran fukaha’u daga Hijaz da Irak a helikwatarsa, kamar dai yanda nassoshin tarihi mayawaita suke nunawa, shi ma ya samo asali ne daga wancan lurar da ya yi.
A magarsa da koyarwarsa ga sahabbansa da mukarrabansa, Imam (a.s) yana kafa hujja da “yanayin holoko da jahilci na halifofi” kan cewa a ra’ayin musulunci basu cancantar shugabanci. Ana iya ganin wannan sigar suka kan tsari mai mulki a sarari da fayyacewa a darusansa na fikihu.
An ruwaito zancensa (a.s):- “Mu mutane ne wadanda Allah ua farlanta biyayya gare mu, kuma kuna koyi da wanda ba’a yi wa mutane hanzari saboda jahilcinsa”[38]
Abin nufi shi ne mutane sun baude saboda jahilcin mahukuntansu da shugabanninsu, sun dauki hata wanya bata Allah ba. Wadannan ba abin yi wa hanzari ba ne wajen Allah domin biyayyarsu ga wadannan mahukunta aiki ne na baudiya saboda haka ba zai wanke abin da ke biyo bayansa na abkawa cikin baude-baude ba.[39]
A koyarwar imamai ( a.s) kafin imam Sadik da bayansa kuna ganin karfafawa kan wajibcin gwama jagorancin siyasa da tunani da manufa (aidiyolojiyya). A wata riwaya daga Imam Ali ibn Musa Al Rida (a.s) daga kakansa Imam Muhammad Bakir (a.s) ya ce: Makami a gare mu tamkar akwati ne ga Bani Isra’ila, duk inda akwati ya juya, sai mulki ya juya, (ka yi tunani da kyau kan ma’ana irin ta alama (ramzu) da ke cikin maganar) duk kuwa inda makami ya juya a cikinmu ilmi can zai juya. A wata riwayar kuma duk inda makami ya juya a cikinmu, to can al’amarin (hukuncin) yake. [40] Sai mai riwaya ya tambayi Imam ya ce:- Shin makamin yana rabuwa da ilmi?
Imam ya ce:- A’a (watau jagorantar al’ummar musulmi wajibine ta zama a hannun wanda yake rike da makami da kuma ilmi gaba daya). Saboda haka Imam (a.s) yana ganin cewa ilmin addini da fahimtar Alkur’ani ingantacciyar fahimta daya daga sharudan imamanci ne. Ta wata fuska kuma ta hanyar aikinsa na ilmi da tara adadi mai yawa na masu kishirwa da begen ilmomin addini a gangarsa, da koyar da addini yanda ya saba cikakkiyar sabawa da hanyar da aka saba wajen malamai da masana hadisi da masana tafsiri masu alaka da tsarin halifanci. Wannan yana tabbatarwa, a aikace, da cewa janibin addini sifa ce ta asali a makarantarsa, da kuma cewa rigar addinin da tsarin halifanci da malaman fada masu daka rawarsu ke da shi ta boge ce. Da wannan hanyar hari mai tsanani mara yankewa kuma cikin tsanaki Imam yake baiwa jihadinsa wata sabuwar kusurwa.
Kamar yanda muka ambata a baya, mahukuntan Abbasiyawa na farko wandanda suka sami shekaru da dama kafin su karbi mulki, suna tare da jihadin Alawiyawa kuma mataimakansu suna da masaniya kan da yawa daga hanyoyi da sako-sakon kirar. Sun riski rawar da hari da fama da wannan aikin fikihu da hadisi da tafsiri ke takawa fiye da magabatansu, Umayawa. Hala wannan dalilin shi ya sanya Mansur, saboda tinkarar Imam Sadik (a.s) ya hana shi zama a halakar koyarwa na wani lokaci da hana mutane zuwa gare shi. Har Mufaddal ibn Umar yana cewa:- “ Hakika Mansur ya daura aniyar kashe Abu Abdillah ba ma sau daya ba ko yaushe ya aika a kira shi domin ya kashe shi, idan ya dube shi sai haibar Imam ta rufe shi kana ya bar shi-sai dai fa ya hana mutane zuwa gare shi, ya kuma hana shi zama saboda mutane, ya bincike shi bincike mai tsanani, har al’amar ya kai ga cewa waninsu zai bukaci samun haske a wata mas’alar addini kan batun aure ko shika ko wani abin daban, gashi basu da sanin ta, kuma basu iya isa gare shi. Sai mutum ya kaurace wa iyalinsa. Wannan abu ya kuntata wa shi’arsa ya kuma yi musu tsananin”[41]
3. Kafa tsari na sirri kan manufa da kuma siyasa
Ya gabata cewa Imam Sadik (a.s) a karshen zamanin Umayyawa ya jagoranci wani shirin sadarwa da sanarwa mai fadi wanda kuma manufarsa ita ce kira zuwa imamanci irin na Ali (a.s) da bayyana sha’anin imamanci a kan sahihiyar ma’anarsa. Wannan shirin sadarwa ya yi yunkurin tabbatar da aikin yada ma’anonin imamanci. Wannan yunkuri ya yi alfanu saboda irin tasirinsa a sassan duniyar musulunci masu nisa masamman a Irak da Kurasan.