CIKAKKEN MUTUM MAI KAMALA
 

Hafiz Muhammad Sa’id
Email: hfazah@yahoo.com

Ubangiji Madaukaki yana Cewa:
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Tsiran Allah Ya Tabbata Ga Manzon Rahama Da Alayensa Tsarkaka
"Kuma lalle hakika kana da ladar da ba ta yankewa. Kuma lalle hakika kana kan halayen kirki manya"[1].

Shimfida
Daga Allah ne muke neman taimako muna gode masa a cikin kowane hali muke na farin ciki da bakin ciki, kuma muna gode masa a kan rahamarsa da sakon da ya aiko annabawa da shi, musamman annabin karshe Muhammad (S.A.W) Dan Abdullah (A.S) Dan Abdulmudallib (A.S) tsira da amincin Allah su tabbata ga alayensa tsarkaka. Wanda shi ne aka aiko da kur’ani domin ya fitar da mu daga duhu zuwa haske, ya tseratar da mu daga bata, ya canja mana mafi munin al’adu da shiriya zuwa tafarki madaidaici. Sai muka bi shi muna masu mika wuya, muka yi koyi da shi, ya zama mana abin koyi kyakkyawa.
Saudayawa idan marubuta zasu yi rubutu game da tarihin rayuwar wani mutun sananne mai daraja da muhimmanci a tarihin rayuwar dan Adam, sukan fifita bincike game da bangaren rayuwarsa ta ilimi da kyawawan dabi’unsa daidai gwargwadon bukatun su da suke hankoron cim musu ta hanyar bincike game da wannan mutum, sai dai mu a wannan makala zamu yi bincike game da sirar mafi girman mutum, mafificin halitta, mafi tsarkin samammu, shi ne cikamakoin annabawa da manzanni da Kur’ani ya siffanta shi da cewa:
“Ba ya magana da son rai, sai dai shi wahayi ne da aka yi masa shi”.
Da fadinsa: “Ba mu aiko ka ba sai rahama ga talikai”.
Ya umarce mu da mu rike shi abin koyi, yana mai fadin: “Lallai kuna da abin koyi kyakkyawa ga manzo”.
Manufar da ake son kai wa gareta ita ce; sanin annabi Muhammad (S.A.W) domin mu dauki darussa da abin la’akari mu kuma yi koyi da shi, mu lizimci abin da ya zo da shi da umarni, mu koyi sadaukarwa saboda muusulunci daga gareshi, kuma kada mu yi gezau ko rauni gaban abubuwa masu rudarwa, sai ya zama mana alami kuma jagora mafi daukaka a wannan rayuwa.
Zamu yi kokarin yin bincike game da sirar annabi (S.A.W) da suka hada da bincike game da sanin annabi (S.A.W) da haihuwarsa, da tijararsa, da bishararsa, da annabta, da matansa, da wahayin manzanci, da kira a boye da fili, da hijirar annabi, da yakokinsa, zuwa bude Makka da hajjin bankwana, da halifan annabi (S.A.W) zuwa wafatinsa.
Muna rokon Allah ya sanya mu daga wadanda saka kari musulmi wajan sanin wani abu daga tarihin annabinmu, domin ya zama mana haske kuma ya karbi wannan dan kadan daga ayyukanmu ya yi mana gafara, domin shi ne mai karbar tuban muminai. Kuma ina rokonsa ya bayar da ladan ga wanda aka rubuta makalar game da shi (S.A.W) musamman da aka ambaci wannan shekarar da sunansa. Kuma muna rokon Allah madaukaki ya hada kan musulmi gaba daya musamman da gabatowar makon hadin kai.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
10 Rabi’ul awwal 1427
20 Parbardin 1385
9 Afrilu 2006


Jazirar Larabawa Kafin Musulunci
Idan muna son fahimtar musulunci da sanin girman annabin rahama mai shiryarwa Muhammad (S.A.W) Wanda da ikon Allah ya iya tseratar da dan Adam, ya sanya shi a kan tafarkin cigaba da daidaituwa a ayyuka, yana mai farawa da wadanda suke gefensa na larabawa. To yana kanmu da farko mu san wane hali ne larabawa suka kasance kafin musulunci domin mu san yanayin da, daga nan ne da’awa zuwa ga musulunci ta fara, daga cikin mafi kyawun magana a kan wannan al’amari ita ce maganar Sayyid Allama Tiba’tiba’i (K.S) da yake cewa:
“Hakika wannan kur’ani yana ambaton lokacin zamanin larabawa da yake tukewa har zuwa bayyyanar musulunci a lokacin jahiliyya, ba komai ba ne sai nuni daga gareshi zuwa cewa; abinda yake hukunci a cikinsu a wannan zamani shi ne jahilci ba ilimi ba, kuma abin da ya mamaye su a cikin kowane al’amari nasu ba komai ba ne sai barna ba gaskiya ba[2], sun kasance a kan hakan kamar yadda kur’ani ya ke ba mu labarinsu yana mai cewa: “Suna tsammani ga Allah abin da yake ba gaskiya ba zato na jahiliyya suna masu cewa shin mu na da wani makami na wani abu”. Ali imran: 154.
Madaukakin sarki ya ce: “Shin hukuncin jahliyya suke so waye yafi kyautata hunkunci fiye da Allah ga mutane masu yakini”. Al-ma’ida: 50.
Ya ce: “Yayin da wadanda suka kafirta suka sanya gaba a zuciyarsu irin gaban nan ta jahiliyya, sai Allah ya saukar da nutsuwarsa a kan manzonsa da kuma a kan muminai ya kuma lizimta musu kalmar takawa, kuma da man sun kasance su ne mafi cancanta da ita kuma su ne ma’abotanta, kuma Allah ya kasance masani da kowane abu”. Al-fath:26.
Ya ce: “Ku tabbata a gidajenku kada ku yi fita irin fitar jahiliyya ta farko, ku tsayar da salla, ku bayar da zakka, ku bi Allah da manzonsa”. Ahzab: 33.
Wannan ayoyi su ne mafificin madubi da yake nuna halin da larabawa da yanayinsu ya kasance, al’ummar larabawa musamman yankin hijaz ba ta da wata wayewa, kuma babu wani abu na wayewa da cigaba da ya rage a cikinta kafin bayyanar musulunci, kuma ga al’adu iri-iri da koyi da iyaye da ya yadu a cikinta da mafi shahararsu su ne:
1- Shirka da Allah a ibada, ta hanyar bauta ga gumaka da taurari.
2- Musun tashin kiyama, wato komawar mutum zuwa rayuwa a wata duniyar bayan mutuwarsa.
3- Yaduwar surkulle da kauce wa tafarki madaidaci da camfi, abubuwan da suke dakushe hankulan mutane, wadannan al’adu ne da suka yi karfi a suka kafu a cikinsu, kuma suka kasance dalili mai karfi na ci bayansu, kuma suka zama hani mai karfi a tafarkin cigaban da’war musulunci daga baya, abin da ya sanya annabi (S.A.W) yake aiki da dukkan karfinsa da kokarinsa wajan kawar da wadannan al’adu na jahiliyya, da gurbatattun akidu.
4- Fasadi da lalacewar dabi’a, kamar yaduwar caca, da giya, da zina, da luwadi, da karuwanci.
5- Binne ‘ya’ya mata, wannan wata al’adace mai muni da kur’ani ya yi magana game da ita a matsayin laifi mai muni da ba zai bari haka nan ba a lahira ba tare da ya yi hisabi a kai ba.
Ya ce: “Idan aka yi wa dayansu albishir da mace sai fuskarsa ta zama baka yana mai bakin ciki, yana boye kansa daga mutane daga munin aibin da aka yi masa albishir da shi, shin zai rike shi ne a wulakance ko kuma ya turbude shi a turbaya, hakika abin da suke hukumtawa ya munana”. Nahal: 58-59.
Ya ce: “Idan wacce aka binne ta aka tambaye ta. Da wane laifi ne aka kashe ta”. Takwir: 8-9.
Saboda haka ne mace ta zama an haramta mata dukkan hakkokin zamantakewar al’ umma har da gado, namiji ya zama yana auren matar babansa idan ya sake ta ko bayan wafatinsa, da yawa daga ‘ya’ya suka yi fasin-fasin da matar babansu daya bayan daya, kamar yadda namiji yake gadon matar dan’uwansa idan ya mutu ya bar ta tamkar yadda yake gadon kayan gida, hada da cewa su ba sa ba wa ‘ya’ya mata gado kamar yadda suke ba wa ‘ya’ya maza.
6- Shan jini, da cin mushe, da cin naman alade, da cin naman sauran dabbobi da suke kashewa ta hanyar rashin tausayi.
7- Cin riba, wannan kuma yana zaman kashin bayan cinikayya a tattalin arzikinsu.
8- Kwace da karfi, kwace abin da yake hannun mutane da kai hari, da kisa, da kashewa, yana daga al’adu masu karfi a wajansu, har ma ya zama yana daga abubuwan alfahari gun maza.
9- Amma a janibin ilimi da wayewa, mutanen hijaz sun siffantu da rashin iya rubutu da karatu, wadanda suka san karatu da rubutu a Makka gaba dayanta adadinsu bai wuce mutane goma sha bakwai ba daga kuraishawa kafin zuwan musulunci.
10- Daga cikin munanan al’adunsu a wancan zamani akwai abin da Ja’afar Dan Abi Talib (A.S) ya fada yayin da ya yi huduba a gaban Najashi sarkin Habasha yana mai cewa: “Ya kai sarki! Mu mun kasane mutane ne na jahiliyya, muna bauta wa gumaka, muna cin mushe, muna zo wa alfasha, muna yanke zumunci, muna munana wa makwabci, mai karfi a cikinmu yana cin mai rauni, mun kasance a haka…”[3]. Wannan ita ce hakikar larabawa kafin musulunci.

Wane ne Muhammad (S.A.W)
Muhammad shi ne annabin da Allah a aiko shi a matsayin annabin karshe domin shiryar da dukkan halitta gaba daya.
A lokacin da aka haife shi Makka da Dakin Allah sun kasance a cike da daudar bautar gumaka, sannan kuma Yahudawa da Kiristoci suna rayuwa a Jazirar larabawa.
Daular Farisa tana mallakar gabashin jazirar larabawa, kuma ga daular Rumu a yammacinta maso arewa, kuma da daula ta uku ta Habasha a yamma, kuma a kudu akwai Daular Yemen da ta kasance karkashin mulkin mallakar Habasha a lokacin haihuwar annabi, da kuma Tekun Indiya.
An ambaci shekarar haihuwarsa da “Shekarar giwa”, saboda harin da Habasha ta kai wa Ka’aba domin rusa ta a wannan shekarar. Kuma abubwan mu’ujiza sun wakana yayin haihuwarsa (S.A.W) da suka hada da:
1. Faduwar gumaka akan fusakunsu
2. Rushewar katangun kisira da suke Shiraz
3. Mutuwar wutarsu da suke bautawa
4. Kafewar kogin Sawa
a. Dukkan wadannan abubuwa sun faru ne a shekarar miladiya ta 571 ne.
Babarsa ita ce Amina ‘yar Wahabi (A.S)
Babansa kuma Abdullahi Dan Abdulmudallib (A.S)
Kakansa ya ambace shi da Muhammad, kuma ya yi walima, ya yanka tumaki, kuma ya soke rakuma ya ciyar da mutane har kwana uku[4].
Wadanda suka shayar da shi:
1. Babarsa a kwana uku na farko
2. Suwaiba a wata hudu
3. Halimatus’ Sa’adiyya, wacce ta dauke shi kuma ta rene shi. Ta kasance tana da ‘ya’ya kamar haka:
1. Abdullahi
2. Anisa
3. Shaima’u
Ta samu albarka mai yawa sakamon renonsa da shayar da shi:
1. Daukewar fari da ya same su da su da mutanensu
2. Aminci a cikin al’ummarsu gaba daya
3. Yalwar arziki da hayayyafar dabbobinsu
Babarsa ta rasu yana dan shekara shida, sannan sai kakansa Abdul mudallabi ya cigaba da renonsa, shi ma ya rasu yana dan shekara takwas, wanda a sakamakon haka ne baffansa Abu Talib (A.S) da kuma matarsa Fatimatu ‘Yar Asad (A.S) suka dauki nauyin renonsa.

Kasuwancinsa
Kasancewar gidan Abu Talib yana da karancin yalwa wannan ne ya sanya manzo (S.A.W) ya motsa domin ganin ya dauki nauyin wannan gida, ta hanyar karbar kwadagon kasuwanci na fatauci kamar yadda yake al’amari sananne a wannan zamani.
Manzo ya yi fatauci da dukiyar Khadiza (A.S) da shawarar Abu Talib (A.S), kuma wannan ya samu alheri da yawa da albarka da ba ta lissafuwa.
Sai ya yi fatauci zuwa Sham da dukiyarta ya dawo yana mai cike da hannu mai albarka da kuma amana da ba ta taba gani ba. Musamman daga labaru da ta samu daga mutane daban-daban kamar bawanta Maisara.
Annabi mai girma ya bayar da dukkan ribar da ya samu na hakkinsa na fatauci ga amminsa Abu Talib gaba daya domin yalwatawa ga iyalansa, wannan al’amari ya sanya shi farin ciki mai yawa da abin da dan dan’uwansa Muhammad (S.A.W) ya yi masa na kyauta[5].

Aurensa
Manzon Allah (S.A.W) ya auri mace mafi kamala a cikin larabawa da mafi yawa daga manyan Makka sun so aurenta amma ta ki amincewa da su saboda kamalarta da kuma yanayinsu na ba tsararrakinta ba ne su a halaye.
Musamman ma wasu suna sonta ne domin wani abu na duniya da take da shi kamar kyawunta ko dukiyarta, wasu kuma ma’abota dukiya maras misali ne amma duk da haka taki amincewa, sai ta yarda da neman da Abu Talib (A.S) ya yi daga gareta na aure da dan dan’uwansa Muhammad, kuma ta amsa masa abin da ya nema, domin kamalarsa da kuma darajar gidansu a cikin larabawa da kuma kamewar Manzo (S.A.W) da rikon amanarsa.
Khadiza (A.S) ta auri Manzo (S.A.W) tana budurwa a lokacin ba ta taba aure ba, tana ‘yar shekara goma sha takwas, shi kuma yana dan shekara ishirin da biyar.
Abu Talib (A.S) ya tafi wajan amminta Amru Dan Asad ya nemi aurenta ga manzo (S.A.W), domin an kashe babanta kafin wannan lokacin.
Abu Talib (A.S) yana cewa a yayin da ya tafi neman aurenta ga Manzo (S.A.W): “Godiya ta tabbata ga ubangijin wannan daki (na ka’aba), wannan da ya sanya mu daga tsatson Ibrahim (A.S) da kuma zuriyar Isma’il (A.S)… sannan dan dan’ uwana… -yana nufin manzon Allah- ba a auna shi da wani mutum daga kuraishawa a sikeli daya sai ya yi rinjaye, kuma ba a kwatanta shi da wani mutum sai ya fi shi daukaka, … ga shi yana son Khadiza (A.S), mun zo muna neman aurenta a wajanka, da yardarta da kuma umarninta, kuma sadakin yana kaina a dukiyata da zaku nema hannu-da-hannu ko kuma ajalan –na rantse da ubangijin wannan Dakin na Ka’aba- (wannan aure) rabo ne mai girma, addini mai yaduwa, kuma ra’ayi cikakke”.
Sai Muhammad (S.A.W) ya tashi domin ya tafi tare da Abu Talib (A.S) gida, sai Khadiza (A.S) ta ce da shi: ina zaka tafi, ai gidana gidanka ne kuma ni mai hidimarka ce.
Haka nan ne ya aure ta (A.S) aka kafa gida mai haske cike da shiriya. Manzo (S.A.W) yana fadi game da ita: Khadiza (A.S) ta yi imani da ni yayin da mutane suka kafirta da ni, ta gaskata ni yayin da mutane suka karyata ni, ta taimake ni da dukiyarta yayin da mutane suka hana ni, kuma Allah ya arzuta ni ‘ya’ya da ita ya hana ni ‘ya’yan mutane (ta wata matar)[6].