A nan za mu yi ishara ga kadan daga wannan al’amari. Sha’anin tsaren-tsaren sirri a rayuwar siyasa ta Imam Sadik (a.s) da sauran imamai yana daga cikin al’amura wadanda suka fi muhimmanci kuma suka fi tsanani ko hadari a lokaci guda kuma shi ya fi komai zama dishi-dishi da rashin bayyana a rayuwarsu. Kamar yanda muka ambata ba zai yiwu mu sami bayani wannani al’amari a fayyace ba tun da ba mu tsammanin Imam ko wani daga sahabbansa zai yi furuci da cewa akwai wadannan tsare-tsaren siyasa da tunani a fili.
Wannan abu ne wanda ba za’a iya gano shi ba. Abin da hankali zai kama shi ne Imam ya tabbatar da rashin samuwar irin wannan tsari na sirri, tare da musantawa mai tsanani, haka nan ma sahabbansa, kuma sun dauka wannan wata tuhuma ce da mugun zato da tsarin hukuma zai nemi su ba da bayani kan wannan lamari. Wannan ita ce sifar da aikin sirri ya kebanta da ita, kuma shi ma mai bincike yana da damar rashin gamsuwa da samuwar irin wanna tsarin idan ba da dalili mai gamsarwa ba. Idan haka ne to ya zama wajibi mu bincika da shaidu da abubuwan da suka auku wadanda ga alama ba bakin komai suke ba kuma basu daukar hankalin mai karatu mara lura, saboda mu yi binciken manuniyar da suke da ita a kan wannan batu. Da irin wannan bin diddigi a rayuwa imamai (a.s) cikin karni biyu da rabi, mai bincike zai iya natsuwa da samuwar irin wadannan tsare-tsare masu aiki karkashin jagorancin imamai (a.s).
Me ake nufi da tsari? Ba fa tsari a nan yana nufin wata jam’iyya tsararra bisa irin manufar da take da ita a yau ba. Ba kuma samuwar wasu dakaru tararru masu jagorantar larduna, masu dangantaka tamkar tsarin dala ba. Babu wannan, kuma bai yiwuwa a same shi. Abin nufi da tsari shi ne samuwar wata jama’a ta bil Adama mai tarayya kan wata manufa, masu aikace-aikace daban-daban wadanda cimma waccan manufa shi suka sa gaba, masu alaka da matattara daya da zuciya mai bugawa guda daya da kwakwalwa mai tunani guda daya, sannan daidaikunta suna tarayya a alakar soyayya.
Wannan jama’a, a zamanin Imam Ali (a.s) (watau cikin shekara ishirin da biyar tsakanin wafatin Manzon tsira da mubaya’ar Ali a matsayin halifa) ta kasance imani da hakkin Imam Ali na halifanci yana hada ta. Ta kan bayyana cika alkawarinta ga Imam ta hanyar tunani da ta siyasa, sai dai ita tana koyi da Imam Ali (a.s) kan rashin ta da abin da zai girgiza jaririyar al’ummar musulunci. Haka kuma suna yunkurawa kan abin da a wadancan shekaru Imam Ali yake yunkuri saboda shi kamar nauye-nauyen sako da zimmar kare musulunci da yada shi da kokarin takaita baude-baude. Saboda wilayar ta wannan jama’a ta dauki sunan ‘Shi’ar Ali’.
Wadanda suka shahara daga cikinsu akwai Salman da Ammar da Abu Zarri da Ubayy ibn Ka’ab da Mikdadi da Huzaifa da sauransu, daga manyan sahabbai.
Muna da shaidun tarihi masu tabbatar da cewa wadannan suna yada tananinsu kan al’amarin imamancin Ali (a.s) cikin mutane tare da hikima. Wannan aiki nasu ya zama gabatarwa ga dafifin da mutane suka yi kan Imam Ali (a.s) da kafa hukumarsa.
Bayan Imam Ali (a.s) ya karbi ragamar mulki shekara ta talatin da biyar bayan hijira mutane iri biyu suke tare da shi. Na farko sun san Imam da matsayinsa, sun fahimci ma’anar imamancin sun kuma gaskata shi. Wadannan su ne shi’arsa wadanda suka yi tarbiyya a gabansa ko dai kai tsaye ko kuma ta hanyar wadansu. Kashi na biyu ya kunshi jama’a baki daya wadanda suka rayu cikin yanayin tarbiyyar Imam da tafarkinsa amma basu da alaka ta tunani ko ta ruhi da jama’ar da Imam ya yi wa tarbiyya ta musamman.
Saboda haka ne za ka sami mabiya Imam iri biyu ne na mutane, tsakaninsu da fifiko mai yawa. Kashi guda ya hada da Ammar da Malik Ashtar da Hujr ibn Adiy da Sahl ibn Hunaif da Kais ibn Sa’ad da tamkarsu. Daya kashin kuwa ya hada da Abu Musa AlAsh’ari da Ziyad ibn Abih da ire-irensu.
Bayan sulhin Imam Hassan (a.s) muhimmin matakin da Imam ya dauka shi ne yada tunanin mazhabin Ahlulbaiti da daidaita tsakanin masu wilaya da wannan tunanin, tun da an sami faragar motsawa mafi yalwa sabili da danniyar mulkin Umayyawa. Da’iman haka al’amarin yake, danniya tana kawo hadin kan wadanda ake dannewa ya sa su sajewa da kafuwa a maimakon watsewa da rarraba. Dabarun Imam Hassan sun fuskanci tara karfi mai wilaya dan asali waje guda da kare shi daga rabkar tsarin Umayyawa, da kuma yada tunanin musulunci dan asali a tsakanin wata takaitacciyar kungiya, sai dai an zurfafa koyar da su wannan tunanin. Sauran ayyuka sun hada da neman masu shigowa safun wilaya da dakon damar da ta dace da yin tawaye wa tsarin zalunci: da yin bindiga da ginshikansa da kuma aza hukumar Alawiyya a gubinsa. Wannan dabarar aiki ita ta bar Imam Hassan (a.s) da zabi daya kadai, wanda shi ne sulhu.
Wannan shi ya sa muke ganin wani gungun ‘yan shi’a karkashin jagorancin Musayyib ibn Najiyya da Sulaiman ibn Sard Alkhuzai, ya tafo gurin Imam Hassan (a.s) a Madina bayan sulhu, yayin da ya dauki birnin ya zama sansanin aikinsa na tunani da siyasa bayan dawowarsa daga Kufa. Wadannan mutane suna gabatarwa Imam da shawarar sabonta karfinsu da tsare-tsarensu na soji da mamayar Kufa da yin tafo-mu-gama da rundunar Sham. Imam ya yi kiran wadannan mutane biyu daga cikin gungun, ya kebance da su, ya kuma tattauna da su kan abin da ba mu san me ya kunsa ba. Mutanen nan biyu sun fito a karshen wannan tattaunawa tare da cikakken gamsuwa da rashin alfanun daukar wannan mataki. Yayin da wadannan biyun suka koma ga wadanda suka zo tare da su sai suka fahimtar da su a takaice cewa an yi watsi da batun tawaye ta hanyar daukar makami, kuma dole ne a koma Kufa domin a sake sabon aiki a can.[42]
Wannan muhimmin al’amari ya kunshi ma’anoni masu girma wadanda suka sa sashen malaman tarihi na wannan zamani daukar wancan zama a matsayin tushen da aka kafa tsare-tsaren shi’a a kansa.
Hakikan al’amari shi ne idan dai matakin farko na tsare-tsaren shi’a an dauke shi ne a wancan zama tsakanin Imam Hassan (a.s) da mutane nan biyu wadanda suka tafi daga Irak to ai Imam Ali (a.s) ya yi wasici da irin wannan matakin a lokacin da ya yi wasici ga sahabbansa mukarrabai da cewa:- “Idan kun rasa ni lallai za ku ga a bayana abubuwan da dayanku zai yi burin mutuwa saboda zalunci da gaba da son kai da rikon sakainar kashi da za’a yi wa hakkin Allah da kuma tsoron abin da zai sami ransa. Idan haka ya faru :-
-Ku yi riko da igiyar Allah gaba dayanku, kuma kada ku rarraba…..
-Na hore ku da dauriya da kuma salla.
-Da kuma takiyya.
Kuma ku sani Allah Mai girma da daukaka yana kin bayinsa su zama masu fuska biyu. Kada ku gusa daga gaskiya da mutanenta domin duk wanda ya musanya mu da wani ya halaka, kuma duniya ta kubuce masa, zai kuma fita daga cikin ta yana mai sabo)[43]
Wannan nassi mai zana yanayin bala’i da ya wanzi a zamanin Umayyawa a fayyace, mai fuskantar da muminai kan wajibcin taimakekeniya da daidaitawa da sajewa da juna yana furuci da mafi hasken shaida kan shirin tsare-tsare a harkar Ahlulbaiti (a.s). Wannan shirin tsare-tsare ya fito fili da siffarsa ta aikace a zaman nan da Imam Hassan (a.s) ya yi da biyu daga cikin shi’arsa makusanta. Kuma babu shakka cewa ba duka mabiyan Ahlulbaiti suke da masaniya kan wannan shiri mai zurfi ba. La’alla wannan yana iya zama wani hanzari kan abin da yake fitowa daga sahabbansa wanda ya danganci suka. Masu sukan kuwa sun kasance suna fiskantar maganar Imam sa’ar da ya yi masu bayani. Ga abin da ta kunsa: “……wa ya sani, ko wannan jarrabawa ce a gare ku, kuma amfani mai gushewa ga abokan gabarku……” A cikin wannan amsa akwai wata ishara boyayya ga siyasa da tsare-tsaren Imam[44]
A tsawon shekaru ishirin wadanda Mu’awiya ya yi mulki, farfaganda mai tsanani wanda ake gudanarwa da zimmar muzanta gidan Ali, wanda ya kai ma ana tsine wa Amirul Muminina Ali bisa mimbarorin musulmi da kuma janyewar Imam Hassan da Imam Hussain (a.s) daga fagen bayyannanar haraka wacce ake iya ganinta a fili, wannan yanayi ya sa babu wani musabbabin yaduwar tunanin Ahlubaiti da fadadar farfajiyar shi’a a Hijaz da Irak da za’a iya gani face samuwar wannan shirin tsare-tsare. Bari mu leka mu ga yanayin da fagen tunani ya ke ciki a wadannan wurare shekar ishirin bayan sulhun Imam Hassan (a.s).
A Kufa za ka samu cewa mazajen shi’a suna daga cikin mashahuran mutane. A Makka da Madina, kai da ma larduna masu nisa za ka ga mabiuya Ahlulbaiti tamkar wata sarka, sashinta yana sane da abin da yake samun daya sashen.
Bayan wasu shekaru, da daya daga mazajen shi’a watau Hujr ibn Adiy ya yi shahada sai ka ji suka da nuna rashin yarda a wurare da dama na kasashen musulunci duk da razanarwar da aka kakaba a ko ina.
Bakin ciki da takaicin ya kai ma wani sanannen mutum a Kurasan ya mutu saboda tsananin bakin ciki bayan ya bayyana suka cikin fushi.[45]
Bayan mutuwar Mu’awiya dubban wasiku suka zo wa Imam Hussaini (a.s) suna kiran sa da ya taho Kufa ya jagoranci juyi. Bayan shahadar Imam gomomin dubbai suka shiga kungiyar “ Tawwabun” ko suka shiga safun rundunar Muktar da Ibrahim ibn Malik masu adawa da mulkin Umayyawa.
Wajibi ne mai binciken tarinin musulunci ya yi tambaya kan musabbabin yaduwar wilaya ga Ahlulbaiti (a.s). Shin yana yiyuwa hakan ta tabbata ba tare da samuwar wani aiki mai yawa da tsari, wanda aka auna shi, wanda kuma hadadde ne wajen tafarki da manufa ba?
Amsa a’a, bisa dabi’a wannan ba zai yiwu ba. Gagarumar farfa-gandar da mulkin Umayyawa suka dana ta hanyar daruruwan alkalai da hakimai da masu huduba ba za ta rushe kuma ta ci tura ba idan ba wani zayyanannar farfaganda mai hamayya da waccar, wacce wani tsari hadadde, daidaitacce, boyayye ya yunkura da ita ba. Dab da mutuwar Mu’awiya aikace-aikacen wanna shirin Alawiyyawan ya ci gaba, saurinsa kuma ya karu. Lamarin ya kai ga hakimin Madina ya rubuta wa Mu’awiya abin da ya kunshi wannan: “Bayan haka, Umar ibn Usman (dan leken asirin hakimin Madina wanda ya sa ido kan Imam Hussain (a.s)) ya ba mu labarni cewa wadansu mazaje daga Irak da sashen manyan mutanen Hijaz suna yawan zuwa wajen Hussain Ibn Ali, suna kuma tattauna batun daga tutar tawaye …….ku rubuto mana ra’ayin ku.”[46]
Bayan waki’ar Karbala da shahahar Imam Hussain (a.s) aikin tsare-tsare na shi’a a Iraki ya karu sakamakon girgizar da ta sami zukatansu saboda kisan Imam Hussain (a.s) inda wannan babban laifi wanda ya kwace musu daman shiga ayarin Hussain da mutanen gidansa a Karbala ya zo musu ba zata. Wannan motsawa tasu tana kewaye da jin zafi da tabewa da takaici.
Dabari ya ce : Mutanen ba su rabu da tara kayan yaki da shirya masa da kiran jama’ar shi’a da ma waninsu, a asirce, kan daukar fansar jinin Hussain ba. Mutane sun amsa kiransu jama’a na bin jama’a, birni na bin birni, ba su rabu da haka ba har Yazid ibn Mu’awiya ya mutu.[47] Abin da littafin Jihadu Shi’a yake fadi gaskiya ne, inda ya yi taliki wa zancen Dabari da cewa:-
“Bayan kashe Imam Hussaini, jama’ar shi’a ta bayyana a matsayin wata jama’a mai tsari, ra ayoyin addini da alakar siyasa suna dinke ta, tana gudanar da tarraki tana da shugabanni, kana tana da karfin soji. Jama’ar “Tawwabun” ita ce farkon mai bayyana dukkan wanna.
Bincike kan al’amuran da suka auku a tarihi da ra’ayin marubuta tarihin kan wancan zamani, ga alama, yana nuna cewa shi’a suna daukar nauyin jagoranci da shirye-shirye, sai dai farajiyar fusata da sukar Banu Umayya ta fi tsararriyar jama’ar shi’an nan fadi. Wannan farfajiyar tana haduwa da kowace haraka mai rinin shi’a .
Za mu gane cewa masu motsawa da hamayya kan Banu Umayya ko da sun yi amfani da taken shi’a ba dai dai ne mu dauka cewa dukkansu suna cikin adadin shi’a ba, watau adadin tsararren shirin nan na imaman Ahlulbaiti (a.s)
Bayan bayanin da ya gabata, ina son in yi ta’akidi kan cewa bayan shahadar imam Hussaini wadanda kadai ake kiransu shi’a su ne jama’ar nan da take da alaka mai karfi da imamin gaskiya, tamkar yanda lamarin yake a zamanin Amirul Muminina (a.s). Wannan jama’a ita ce bayan sulhun Imam Hassan (a.s) ta fuskanci kafa tsarin shi’a da umarnin Imam, kuma ita ce ta yi kokarin jawo mutane zuwa wannan tsarin da kuma kange mafiya yawa wadanda basu kai matuka a tunani ba kuma basu yi kwari a fagen aiki ba balle su kai matsayin shiga tsarin, wanda yake da zimmar samar da wata babbar harakar shi’a.
Riwayar da muka kawo a farkon wannan bahasi wacce aka rawaito daga Imam Sadik (a.s) mai cewa adadin muminai bayan waki’ar Ashura bai wuce uku ko biyar ba, abin da take nufi shi ne ‘yan wannan kebantacciyar jama’a. watau mutanen nan da suke iya rawar gani, a matsayinsu na madugu mai wayewar kai a kokarin kaiwa matuka cikin al’amarin juyin Alawiyyawa.
Sakamakon aikin da Imam Sajjad (a.s) ya yi a cikin sirri da tsanaki, turakun wannan ‘yar jama’a sun fadada kuma da wannan Imam Sadik (a.s) yake ishara a riwayar da muka ambata…… “sannan mutane suka risko su suka yawaita”. Za mu gani cewa zamanin Imam Sajjad da Imam Bakir da Imam Sadik ya ga motsawar wannan jama’a, wanda ta jefa tsoro da firgici a zukatan azzaluman mahukunta, al’amarin da ya sa du mai da martani mai tsanani.
A takaice, a karnin farko da na biyu bayan hijira da ma tsawon zamanin imamai (a.s) ba’a kiran wadanda suke kaunar Ahlubaiti da imani da hakkinsu da gaskiyar kiransu kadai ba tare da yin tarayya a tafiyar harakarsu ba da sunan shi’a. Su shi’a suna bambanta da saura ne ta hanyar wani tabbatanccen sharadi na tushe, wanda shi ne alaka da Imam wajen tunani da aiki da tarayya a aikin tunani da siyasa kai da ma ta fuskar aikin soji wanda yake jagoranta saboda dawo da hakki ga mai shi da kafa tsarin Alwawiyyawa na musulunci. Wannan alaka ita ake kira “wilaya” a kamus na shi’a.
Bisa hakika jama’ar shi’a suna ne wanda ake baiwa ‘yan jam’iyyar imamanci, jama’iyyar da take motsawa karkashin jagorancin Imam (a.s) take kuma daukar boyewa da takiyya a matsayin mafaka, tamkar duk wata jam’iyya ko shiri mai rayuwar cikin tsoro da danniya. Wannan shi ne takaitaceen bayani kan dubi na hakika kan rayuwar Imamai (a.s) musamman Imam Sadik (a.s) kuma kamar dai yanda muka ambata tun farko ba zai yiwu a sami hujjoji bayyanannu kan irin wannan al’amarin ba, tun da ba za mu yi tsammanin za’a kafa wa wani gidan sirri alama mai cewa: “wannan gidan sirri ne” ba! Kazalika ba zai yiwu mu natsu da sakamakon (bincike) ba, ba tare da samuwar wasu tabbatattun shaidun yanayi ba. Saboda haka ya kamata mu bi biddigin wadannan shaidu da isharori.
Daga cikin kalmomi masu zufafan ma’anoni wadanda suke jan hankalin mai bincike mai bin diddigi a riwayoyin da rayuwar imamai (a.s) ko kuwa wadanda ake kawowa a maganganun masu talifin karnin musulunci na farko akwai kalmomin “kofa” da “wakili” da “ma’a bocin sirri” wadannan kalmomi ne da ake kiran wasu sahabban imami da su. Alal misalim mashaurin malamin hadisi dan shi’a yana fada dangane da rayuwar Imam Sajjad (a.s) cewa :- “ Yahya ibn Ummu Dawil shi ne kofarsa” a kan ta Imam Bakir ( a.s) kuwa ya ce: “Jabir ibn Yazid Alju’fi shi ne kofarsa”, batun rayuwar Imam Sadik (a.s) kuwa ya ce:- “Muhammad Ibn Sinan shi ne kofarsa”. A cikin littafin “Rijalul Kashshi” ana kiran Zurara da Buraid da Muhammad ibn Muslim da Abu Basir da lakabin “ma’ajin sirri”. A cikin littafan hadisi ana ruwaito kalmar “wakili” daga Imam Sadik (a.s) a kan batun Mu’alla ibn Kunais. Ko wani daya daga cikin wadannan kalmomi imma dai ya fito ne daga Imam, wa imma sakamakon bincike ne mai yawa kan rayuwar imamai, wanda magabatan marubutan shi’a suka gudanar. Ko ma yaya ta kasance zabar wadannan kalmomi masu zurfafan ma’anoni ya samo asali ne daga wadansu fitattun alamomi a rayuwar Ahlulbaiti (a.s). Idan muka yi tunani da kyau kan wadannan kalmomi za mu tarar cewa ko wacce daga ciki tana nuni da cewa karkashin ayyukan zahiri wadanda imamayi (a.s) suke gudanarwa, akwai wani rayayyen shiri na boye.

Ma'ajin Sirri
Idan mutum ba shi da wani “sirri” to ba shi da ma’ajin sirri. To mene ne wannan sirrin a rayuwar imamai? Me ne abin da sahabban imami a game ba za su iya rikewa ba sai wata jama’a da bata wuce a kidaya ta ba take da dacewa da cancantar rike shi? Kuma da haka ta sami darajar “ ma’ajin sirri”?
Hankula na baya-bayan nan manisanta daga ainihin abubuwan da suka auku a tarihi da rarrabe su suna fassara wannan sirrin da cewa shi ne sirrorin gaibi da iko kan ababen da suka keta al’ada da kuma mu’jizoji.
Ni ina imani da ikon wannan sifa tsarkakka ta Ahlulbaiti wadanda Allah ya zabe su domin ci gaba da nauyin rungumar sako da iyar da shi bayan kaurar Manzon Allah, na yarda suna dauke da irin wannan iko da irin da wadannan ilmomi. Kamar yanda nake imani da cewa adon da suka yi da wannan karfin da kuma wadannan ilmomi ko kadan ba ya karo da dubin da musulunci ke yiwa bil Adama da ka’idojin dabi’a da kuma dabi’ar kaunu. Amma fa wanna kari da ilmomi ba su ne “ sirrin imam” ba. Ai irin wannan karfi da kuma ilmomi su ne mafi bayyanar dalilai mai tabbatar da imamanci da gaskiyar da’awar imani. To me zai sa imami ya boye wadannan al’amura ya kuma yi wasici ga sahabbansa da boyewa, a riwayoyi mayawaita, wadanda yawansu da karfafa juna ya kai littafan shi’a na hadisi suna kebe babi mai suna “babin boyewa”? Dole ne wannan sirri ya zama cewa idan ya yadu zai zame wa Imam da sahabbansa wani hadari mai girma, wannan kuma ba zai zama al’amuran gaibi da masu keta al’ada ba.
Shin sirrin shi ne ilmomi da ma’arifar Ahlubaiti? Shin shine irin ganinda mazhabin Ahlulbaiti yake yi wa musulunci da fikihunsa da kuma hukunce-hukunce sa? Ba mu musun cewa ilmomi Ahlulbaiti ana yada su a zamanin danniyar Umayyawa da Abbasiyawa ta hanyar hikima da dabara domin kada ko wani sususu da shashasha ya kutsa cikinsu, amma wadannan ilmomi ba zai yiwu a ce su ne sirrin Imam ba. Duk da kebantar da take tattare da wadannan ilmomin ana karantar su a daruruwan makarantin fikihu da hadisi a wadansu manyan biranen lardunan musulunci a wancan lokacin. ‘Yan shi’a sun kasance suna nakalta wa juna wadannan ilmomin tare da sharhinsu. Muna iya cewa wadannan ilmomi da ma’arifa kebantattu ne amma ba na sirri ba. Kebantuwarsu tana nufin cewa yaduwarsu ta takaita ga haular ‘yan shi’a, amma a halaye na musamma suna isa ga wadanda ba shi’a ba ma. Sam ba masu takaita da kadan daga sahabban imamai, boyayyu ga wanin su ba ne.
Gaskiyan al’amarin shi ne sirrorin su ne al’amuran da suke ta’allaka da bayanan da suka danganci shirin tsare-tsaren imami,……….shirin da yake kutsawa cikin filin daga a siyasance da zimmar cimma manufar juyi,…… ko wadanda suka danganci dabarun da shirin ya haifar, ko ayyukan da zai aiwatar, ko suka danganci sunaye da nauye-nauye mambobin shirin ko hanyoyin kudi ko labarai, da rahotannin da suka ta’allaka da muhimman ababen da suke faruwa. Wadannan da ire-irensu sirrori ne wadanda ba dama wani ya tsinkaya idan ba jagora ba ko mataimakan da suke rike da ayyuka daban daban. Tana yiwuwa a sami yanayin da ya dace da bayyana wadannan sirrori a kwaye lulubinsu, ko a kusa ko kuwa tare da jinkiri, sai dai kafin wannan lokaci ba dama wani ya sami masaniya kan wadannan sirrori face wanda aikinsu yake da dangantaka da su kai tsaye, su ne kuwa “ma’ajin sirri”. Duk wani zarcewarsu zuwa ga makiya (shi kuwa laifi ne mai girma wanda ba’a yafewa) laifi ne wanda ka iya janyo rushewar jihadi da ayyuka da kuma tsararrar jama’an nan. Wannan zai fahimtar da mu abin da Imam (a.s) yake nufi da cewa: “ Jidalin da mai gaba da mu (nasib) yake janyo mana baya wuce wanda mai baza sirrinmu zuwa wanda ba ahalinsa ba yake jawowa. Mai baza sirrinmu ba zai bar duniya ba sai makami ya ci shi”[48]

Kofa Da Wakili
A alakar sirri tsakanin Imam (a.s) da shi’a ta yiwu a bukaci isar musu da wasu bayanai ta hanyar “ mai shiga tsakanin” ko kuma sila. Wannan kuwa dabara ce mai ma’ana, abin da aka saba bisa alada. Yan leken asiri masu lababawa da zimmar gane alakokin Imam (a.s) su kan faki zaman ganawarsa da mabiyansa a lokacin aikin haji a Makka da Madina yayin da ayarai daga nisan duniya suke zuwa. Fakon wadannan zama ya kan kai ga ganowa bakin zaren babban shirin tsare-tsaren Imam. Saboda haka kake ganin Imam (a.s) wani lokaci yana nisanta wasu mutane daga gare shi da kalami mai taushi, a wani lokacin kuma da lafazin suka. Alal misali Imam ya ce da Sufyan Sauri:- “Kai mutum ne abin nema, sarauta kuma tana da ‘yan leken asiri a kanmu, saboda haka ka fita amma ba korar ka aka yi ba”[49]
Wani lokaci sai ka ga Imam (a.s) yana rokon jinkai ga mutumin da ya yi kicibis da shi a kan hanya amma ya kau da kai kamar bai gan shi ba, a wani zubin kuwa yana laifanta wani wanda ya gan shi a makamancin wancan yanayin ya kuma yi wa Imam sallama tare da karramawa da girmamawa.[50]
Irin wadannan yanayi na bukatar samuwar wani mutum da zai zama sila taskanin Imam da mai neman bayanai masu iso shi daga wajen Imam, to wanna silan shi ne “kofa” kuma wajibi ne ya zama daya daga mafiya amincin mabiyan Imam, wadanda suka fi kusaci da shi, kuma suka fi wadatuwa wajen sanin bayanai da hanyoyin sadarwa. Dole ne ya zama tamkar kudan zuma wacce da muggan kwari za su san zumar da take dauke da ita da sun sassare ta sun kuma kai hari kan gidanta.[51] Ba banza ba muke ganin wadannan “kofofi” galibi ana farautarsu ana kamawa ana dira kansu da mafi munin nau’in azaba.
Yahya ibn Ummi Dawil, “Kofar” Imam Sajjad an kashe shi, mummunan kisa.[52] Jabir ibn Yazid Alju’fi kuwa dole ta sa ya sa rigar hauka kuma wannan labarin ya watsu ya zama dalilin tsirarsa daga kisan da halifa ya riga da ya bayar da umurninsa ‘yan kwanaki kadan kafin yaduwar labarin haukacewarsa. Muhammad ibn Sinan kuwa ‘kofar’ Imam Sadik (a.s) korarsa Imam ya yi, kora ta zahiri duk cewa Imam ya bayyana yardarsa gare shi da yabonsa a wasu wuraren. Ba don komai aka yi masa haka ba sai domin shigarsa irin wadannan hadura, kamar yanda sanarwar Imam cewa ba shi da wani sananne mashahurin marawaici wanda kuwa ya rabauta da sanarwar yarda daga Imam. Sau da dama yana ishara, bisa ra’ayi mai karfi, cewa dabara ce ta tsare-tsare.
Irin wannan makoma tana fuskantar “wakili” shi ma. “Wakili” shi ne mai nauyin tara dukiyoyin da suke da alaka da Imam da kuma rarraba su. Shi ma ya san sirrori masu yawa, alal akalla, sunayen masu bayar wa da na masu karba. Wadannan bayanan, makiya Imam basu raina su. Mafificin hujja kan haka shi ne makomar Mu’alla ibn Kunais, wakilin Imam Sadik (a.s) a Madina da kalmomin Imam game da Mufaddal ibn Umar, wakilinsa a kufa, wadanda ya fade su bisa takiyya.
Lakabin nan guda uku: kofa da wakili da ma’abocin sirri, wadanda muke samun cewa masu su wadansu wanyan mutane ne daga mazajen shi’a suna bayar da haske kan halin da shi’a ke ciki da alkarsu da Imam da kuma harakar tsare-tsare ta shi’a.
Da wannan dubi muna iya fahimtar cewa shi’a su ne jama’ar mutane masu sajewa da junansu, jama’a mai manufa, mai himma, mai matattara a kan wani ginshiki mai tsarki wanda yake watsa haske kan mataimakan sa ta hanyar umurce-umurce da shiriyarwarsa. Su kuma mataimakan suna da alaka da shi, suna kawo masa bayanai, suna kame motsin rai suna kuma fin kafin zuciyarsu albarkacin wasice-wasicensa na hikima. Suna kuma lizimtar salon sirri wajen aiki, kamar kiyaye sirrori da karancin magana da rashin shiga mutane da aikace –aikacen jama’a da kuma nisantar al’amuran kawo juyi.