Bayan Hisham ya gama sai jama’a suka karba, suka ci gaba da maimata wadannan tuhumce-tuhumce da soke-soke. A tsawon wannan lokaci Imam uffan bai ce ba, yana sunkuye da kai cikin natsuwa, yana jiran damar ba da amsa. Yayin da mutanen nan suka kare duk abin da ke gare su, wuri ya yi tsit, sai Imam ya mike ya fuskanci jama’a, ya yi yabo ga Ubangiji ya yi salati ga Manzonsa (s.a.w.a) kana ya yi jawabi.
Wannan jawabin ya kunshi kalmomi ne matakaita masu kwankwasa tare da bayyana rauni da kuma sakar akala tamkar kumaki wanda wadancan ‘yan amshin Shatan suka yi. Kazalika ya nuna matsayi da daukaka da Ahlulbaiti suke da shi, kamar yanda ma’aunan musulunci suka tabbatar, ya kuma wulakanta duk abin da halifa da jama’arsa suka mallaka na kazamar dukiya da kuma iko. Ya ce:- ‘Ya ku mutane ina kuke tafe ne? Ina aka nufa da ku? Da mu Allah ya shiryi na farkonku kuma da mu ne zai cikata (shiryar da) na karshenku. Idan abin gaggautawa na mulki naku ne to (ku sani cewa ) abin da aka jinkirtar na mulki namu ne sannan kuma babu wani mulki bayan namu saboda mu ne ma’abota kyankkyawan karshe. Allah mai girma da daukaka yana cewa: “Kuma kyakkyawan karshe ya tabbata ga masu takawa”[21].
Wadannan kalmomi matakaita wadanda suka kunshi wawaitarwa da kokowa da zalunci, da albishiri da bazarana, da tabbatarwa da kuma raddi duk a lokaci guda, ba shakka masu girgizawa ne tare da sa mai sauraro yin imani da cewa mai fadarsu shi ne ma’abocin hakki. Sakamakon haka, Hisham sai ya ga babu abin da zai yi face umarni da a jefa Imam kurkuku. Imam Bakir ( a.s ) ya ci gaba da aikinsa na gyara hatta a cikin gidan kaso, al’amarin da ya yi tasiri matuka kan fursunoni. Da labari ya kai ga Hisham,sai ya ji tsoron cewa irin wannan farkawa za ta faru a hedkwatarsa wacce aka kiyaye daga tasirin Alawiyyawa. Sai ya yi umarni da fitar da wannan fursunan (Imam Bakir) tare da wadanda suka dauki ra’ayinsa da kuma aika su da daggawa zuwa Madina wanda shi ne mazaunninsa. Umarnin ya hada da cewa idan sun kama hanya kada kowa ya yi wata hulda da wannan ayari wanda halifa yake fushi da shi. Kada a ba su guzurin abinci ko ruwan sha.
Bayan kwana uku ana tafiya ba kakkautawa abinci da ruwan da yake tare da su sai ya kare, a wani birni da ake kira Madin. Saboda umarnin Hisham, mutanen sun kulle kofifin birnin suka kuma ki sayarwa wadannan bayin Allah da komai. Yunwa da kishi suka yi wa mabiya Imam tsanani. Sai Imam ya haura kan wani tudu wanda daga bisan shi ana iya hangar cikin birnin ya daga murya da kyau ya ce:- “Ya ku mutan garin da mutanensa suka yi zalunci! Ni ne falalar Allah mai wanzuwa Allah yana cewa”:- Falalar Allah mai wanzuwa (bakiyyatul lahi ) ita ce mafi alheri a gare ku idan kun kasance muminai, kuma ni ba mai tsaro ne a kanku ba”.
Mai riwaya ya ci gaba da cewa: Akwai wani tsoho tukuf a wannan birni, wanda ya ce da su: ‘Mutanena, wallahi wannan kira ne irin na Annabi Shu’aibu ( a.s). Na rantse da Allah idan ba ku fita kuka sayar wa wannan mutumin (abin da yake bukata) ba za’a kama ku daga birbishinku da kuma karkashinku. To lallai ku gaskata ni kuma ku bi maganta, domin ni mai nasiha ne a gare ku’.
Mutanen garin sai suka amsa kiran dattijon nan, suka fita da gaggawa suka sayar wa Abu Ja’afar (Imam Bakir (a.s)) da sahabbansa da abin da suke bukata.[22]
Karshen wannan ruwaya yana nuna mana irin dirar da halifan Abbasiyawa yake yi kan mutane da kuma jabberancinsa. Bayan mutanen birnin sun budewa Imam da sahabbansa kofofin gari sai aka rubuta dukkan abin da ya faru aka aike wa Hisham. Sai ya aiko da takarda zuwa hakimin Madin da umarnin cewa ya kama wancan dattijon ya kashe. Allah ya ji kansa da rahama![23]
Tare da wannan hali, Imam yana nisantar duk wani matsanancin fito-na-fito da yin gaba da masu mulki. Ba ya daukar takobi ba ya kuma yardarwa masu garaje zare tokobi, yana dai shiryar da su ta hanyar hikima. Takobin harshe ma Imam ba ya zarewa idan ba aikinsa na gyara da sauyi daga tushe ya bukaci hakan ba. Kuma bai yardar wa dan uwansa Zaid, wanda fushi da motsin rai ya kai masa iya wuya, yin tawaye ba. A ‘a, shi dai aikinsa yana ba da karfi ne wajen shiryarwar da wayar da kai da tunani, hakan kuma gina tushen manufa (aidiyoloji) ne tare da kula da takiyya a siyasance.
Sai dai wannan salon bai hana Imam ya bayyana wa mabiyansa “harakar imamanci” ba, kamar dai yanda muka yi nuni da shi, bai kuma hana shi karfafa musu babban burin shi’an nan na kafa sahihin tsarin siyasa mai bin tafakarkin Imam Ali (a.s) ba. Wani lokaci ma yana tunzura zukatansu gwargwadon bukata saboda raya wannan burin.
Daya daga hanyoyin da Imam Bakir (a.s) yake kwadaitar da mabiyansa ita ce ishara ga zamanin mai haske wanda zai zo nan gaba. Wannan kuma yana nuna yanda Imam (a.s) ya kwatanta zangon da yake raye a harakar imamanci. Hakam ibn Uyaina yana cewa: wata rana ina tare da Abu Ja’far (a.s) alhali gidan na cike makil da mutanen gidansa sai ga wani dattijo ya tafo yana tokarawa da mashinsa har ya tsaya bakin kofa ya ce:
Aminci da rahamar Allah da albarkarsa su tabbatar gare ka ya dan Manzon Allah (watau ya yi sallama). Sannan ya yi shiru. Sai Abu Ja’far ya amsa masa: Aminci ya tabbata gare ka da rahamar Allah da albarkarsa. Sai dattijo ya fuskanci mutanen gidan ya ce: assalam alaikum, sannan ya saurara har jama’a suka amsa sallama gaba dayansu. Sai ya fuskanci Imam ya ce: “Ya dan Manzon Allah ka kusantar da ni gareka, Allah Ya sanya ni fansarka. Wallahi ni ina kaunarku, ina kuma kaunar mai kaunarku. Kuma wallahi ba na son ku tare da son mai son ku saboda kwadayin abin duniya. Kuma ni ina kin mai gaba da ku ina kubuta (bara’a) daga gare shi. Kuma wallahi ba na kin shi ina kubuta daga gare shi domin wata kullalliya da ke tsakaninmu. Wallahi ni ina halatta abin da kuka halatta shi, ina haramta abin da kuka haramta shi ina sauraron umarninku. To shin kana mini tsammanin (alheri ),Allah ya sanya ni fansar ka? Sai Imam ya ce: “ Taho nan, taho nan” ya zaunar da shi gangarsa sannan yace:-
‘Dattijo! Lallai wani mutum ya zo wa babana Ali bin Hussain (a.s) ya tambaye shi tamkar abin da ka tambaye ni sai babana (a.s) ya ce da shi:- Idan ka mutu za ka zo ga Manzon Allah (s.a.w.a) da Ali da Hassan da Hussain da Ali ibn Hussaini, kuma za’a sanyaya zuciyarka, za ka ga farin ciki, za’a tarbe ka da hutawa da kyakkyawan abinci tare da Masu daraja, Marubuta ( kiramun katibuna ). Idan kuma ka rayu za ka ga abin farun cikin da Allah zai sanya ka ciki za ka kasance tare da mu cikin kololuwar daukaka”.
Cikin gigicewa saboda girman wannan albishiri,dattijo sai ya ce:`Ta yaya,ya kai Abu ja’far? Sai Imam ya maimaita masa maganar da ya yi. Sai tsohon nan ya ce:Allahu akbar! Ya Abu Ja’far idan na mutu zan zo wa Manzon Allah (s.a.w.a) da Ali da Hassan da Hussain da Ali ibn Hussaini, kuma zan ga abin farin ciki, a kuma sanyaya min zunciya, a tarbe ni da hutawa da kyakkyawan abinci tare da Masu daraja, Marubuta idan na cika? Idan kuma na rayu zan ga abin da zai faranta mini rai, kuma in zama tare da ku a kokoluwar daukaka?” Sai tsoho ya kama kuka sai da ya kai kasa. Yayin da mutanen gidan Imam suka ga yanayin da dattijon nan ya shiga sai su ma suka kama kuka. Sai dattijo ya daga kai ya nemi Imam ya mika masa hannunsa. Sai ya sumbanci hannun ya sanya shi kan idanu da kumatunsa sanan ya yi ban kwana ya fita. Imam yana kallonsa yana cewa:- Wanda ya so ganin wani mutum daga mutanen aljanna to ya dubi wannan (mutumin).[24]
Irin wannan fayyacewa tana karfafa ruhin buri a zukatan da suke rayuwa cikin yanayin zalunci da danniya, ta kan wanzar da tunkudawa zuwa ga manufar da ake bida wacce ita ce kafa adalin tsari na musulunci.
Shekara goma sha tara na imamanci Imam Bakir (a.s) aka yi aiki na gudana bisa wannan mikakken layi mabayyani. Shekara goma sha tara na koyarwa kan manufar gini da dabarun kare kai da tsare-tsare da kare haraka da takiyya da karfafa ruhin sa-rai da sauransu.
Shekara goma sha tara ana gudanar da wannan tafiya mai tattare da kaya da munin hanya wanda yake bukatar kokari da ijtihadi mai yawa. Lokacin da wadannan shekaru suka kawo karshe, ranar rayuwarsa mai albarka ta zo faduwa, sai abokan gabansa suka yi ajiyar zuciya domin a zatonsu idan wannan jagora mai shiryarwa ya tafi za su huta da tushen farkarwa da izawa wanda ya dade yana hana su hutu da barci.
Amma hakan bai yiwu ba domin Imam ya tabar da burinsu ya kuma sa wannan dama ta kubuce musu saboda ya sanya wafatinsa ya zama tushen shiryarwa, musabbabin farkawa sannan kuma hanyar wayar da kai mai dorewa. Imam ya umarci dan sa Sadik(a.s) a karshen rayuwarsa, ya umarce shi da wani aiki wanda samfuri ne mai gwanin ban sha’awa daga samfur-samfur na takiyya da kuma salon kira wadanda Imam Bakir (a.s) ya yi amfani da su a zangon zamani wanda ya kebance shi . A cikin ruwaya daga Abu Abdillah Sadik (a.s) ya ce: ‘Babana ya ce da ni: Ka ware abu kaza daga dukiyata saboda a mini zaman makoki na tsawon shekara goma a Mina a ranakun Minan”.[25] ..Ita wannan ruwaya , wadanda suka yi bincike kan rayuwar Imam Bakir basu dube ta da kyau ba kuma sun gafala ga barin ma`anoni masu girma wadanda ta kunsa. Imam ya rasu ya bar dirhami dari takwas, yayi umarni da aware wani abu daga ciki a baiwa masu kukan mutuwarsa a Mina. Yin kukan rasuwar Imam a Mina ya kunshi ma`ana mai girma .Lallai shi aiki ne na raya tushen nan da ya kasance a ko yaushe yana watsa hasken wayar da kai da farkarwa da kuma sanya ruhin kamuji da gwagwarmaya.
Zaben Mina kuwa yana nufin wanzar da aikin a tsakiyar taron jama`a masu tahowa daga dukkanin sassan duniyar musulunci a dai dai lokaci guda daya tak da ake zaune wuri guda yayin aikin haji. Saboda dukkan ayyukan haji ana gabatar da su ne cikin halin motsawa ba tare da sararawa ba idan ba a Mina ba, inda ake kwana biyu ko uku, saboda haka alhazai suna samun isashshen lokaci domin sauraro da ganin kukan rasuwar Imam a wannan wuri zai kuma sa a yi tambaya kan ko wane ne wannan mamacin? Za’a kuma sami jawabi wajen mutanen Madina wadanda suka yi zamani da shi. Za su ce shi daya daga ‘ya’yan Manzon Allah ne, kuma shi ne malamin fukaha`u da masana hadisi. Za’a kuma tambayi dalilin da ya sa ake makokinsa a wannan guri, shin mutuwarsa ta bambanta da ta saura ne? To wane ne ya kashe shi ko ya sanya masa guba? Shin ya kasance wata barazana ga mulkin Umayyawa ne? Da dai sauran su. Gomonin tambayoyi aka yi ta jefowa yayin da ake kukan rasuwar Imam a wannan wuri, sannan masu tambaya suna samun amsa. Kuma labarin ya yi ta watsuwa cikin garuruwa, sako sako, bayan komawar alhazai kasashensu. Akwai kuma masu zuwa daga Kufa da Madina takanas saboda amsa wadannan tambayoyi da yada ruhin shi’a suna daukar damar taron musulmi, damar da ba’a samun tamkar ta a wancan lokacin.
Haka Imam ya rayu, haka kuma ya tsara al’amura domin abin da zai zo bayan wafatinsa. Tsira ta tabbata gare shi ranar da aka haife shi da ranar da ya yi jihadi da ranar da ya yi shahada a tafarkin Allah da kuma ranar da za’a tashe shi rayayye.
Imam Bakir (a.s) ya rasu yana da shekara hamsin da bakwai a duniya, a zamanin Hisham bin Abdulmalik, wanda yake daya ne daga sarakunan Banu Umayya wadanda suka fi iko. Duk da matsaloli da wahalhalun da suka addabi sarautar Banu Umayya a wancan zamanin wannan bai hana su aikata makida ga zuciyar shi’an nan mai bugawa, watau Imam Bakir, ba. Hisham ya yi ishara ga barorinsa cewa su sanya wa Imam guba, da haka ne kuma ya cimma burinsa na hallaka mafi hadarin abokan gabansa.

Jagorancin Imam Sadik (a.s)
Imam Sadik (a.s) ya dauki nauyin ci gaba da wannan tafiya a cikin yanayi mai tsananin sarkakiya da wahala. Bore ya kunno kai a ko ina a daular musulunci, hakimai sun shagaltu da tara kazamar dukiya alhali ga annoba da fari sun aukawa yanki mai yawa wanda ya hada da Kurasan da Irak. Masu mulki kuwa suna tursasawa da zalunci ba tare da rahama ba ko kankani, da haka suke jefa mutane cikin halin kaskanci da mika wuya. Kuma galibi hadarin masu shagaltuwa da ilmomin musulunci kamar fikihu da hadisi da tafsiri bai kasa na ‘yan siyasa da mahukunta ba. Alhali kuwa su ake tsammanin zamansu mafaka ga mutane. Yawa yawan wadannan malamai na kawata fatawowi saboda dadada wa sarki da hakimansa. Da yawa daga cikinsu suna shagaltar da kansu da ma mutane da mas’alolin da basu taka kara sun karya ba, suna ta da jayayyar da ba bakin komai take ba cikin mas’alolin ilmul kalam kuma babu abin da ya danganta ta da musulunci ko wahalhalun da al’umma ke ciki.
Nauyin da ya rataya a wuyan Imam Sadik (a.s) a wannan yanayi mai duhu shi ne abin da muka ambata kan sha’anin nauyin imamanci.A takaice shi ne bijiro da ingantaccen tunanin musulunci, watau bayyana musulunci kamar yanda ya zo cikin Alkur’ani dasunnarMa’aiki(s.a.w.a) gami da yaki da dukkanin baude-baude da gurbatarwar jahiliyya mai bin son rai. Haka nan kuma da shirya dabarun kafa tsarin adalcin musulunci da kuma kare wannan tsarin yayin kafa shi.Duk wannan nauye-nauye guda biyu watau nauyin wanzar da tsarin tunani da nauyin tsarin siyasa suna matsayin wani hadari mai girma ne ga tsarin da yake mulki. Ba nauyin siyasa kadai yake tunzura fushin sarauta ba, a’a shi ma nauyin tsarin tunani wanda yake jifa da baudaddun tunane-tunane da manufofin da sarki da masu wa’azinsa ke gabatar wa al’umma da sunan addini, yana fusata ta. Wannan ya nuna cewa aikin kyautata tunani abin fifitawa ne domin yana kawar da karkatarwa da sunan addini wacce tsarin sarauta ke dogaro da ita wajen wanzarda zaluncin da yake yi wa jama’a. Ta wata fuska kuma yanayin da ake cikinsa a shirye yake ya saurari tunanin shi’a mai neman sauyi, domin yaki da talauci da danniya sabubba ne masu habaka ruhin sauyi, ga kuma share fage da ayyukan Imam Bakir (a.s) suka yi a yankuna dabam-dabam. Dabarar cimma manufar Imamanci a game ita ce yunkurin sauyin tauhidi irin na Imam Ali. Bukatunta su ne:-Na farko: Samarda wata jama’a wacce za ta dauki tunanin imamanci, ta yanda zai saje da ita, sannan ta zama mai begen aiwatar da shi.
Na biyu: Samar da wata jama’a tsararriya mai jihadi da sadaukarwa. Shi kansa cimma wadannan bukatu yana bukatar yada kiran gaskiya a sassan duniya da shirya zukata domin karbar tunanin musulunci mai ra’ayin sauyi a dukkanin wurare. Har ila yau yana bukatar wani kiran daban wanda zai tanadi daidaiku masu sadaukarwa da fana’i, wadanda za su zama mambobin shirin tsare-tsaren kiran na sirri.Wannan shi ne sirrin wahalar kira bisa tafarkin imamancin gaskiya. Saboda kira mai dauke da sako, mai zimmar kawar da dagutu da fir’aunanci da jabberanci da dagawa da zalunci a cikin al’umma tare da cewa tana riko da ma’aunan musulunci wajen ayyukanta dole ne ta yi dogaro da zabin (irada) talakawa da karfinsu da imaninsu da nunarsu. Sabanin kiraye-kirayen da suke dauke da taken yaki da masu dagawa alhali su ma suna aikata irin ayyukan dagutai da azzalumai, basu lura da dokokin kyawawan dabi’u da na halin zaman jama’a. Irin wadannan kiraye-kiraye basu fuskantar wahalhalun da kira mai dauke da sako, mai manufa, take fuskanta. Wannan shine sirrin rashin tabbatar manufofin harakar Imamanci cikin gaggawa, shi ne kuma sirrin samun nasara nan take na harakokin da suka yi hannun riga da harakar imamanci, kamar ta Banu Abbas.
Yanayin da ake ciki da shirin da ayyukan imamin da ya gabata (Imam Bakir) bai shafi takwabi ba. A’a shi yana tsayawa ne ta hanyar suka mai tsanani, sawa’un da salon aikin gyaran tunani ko na tsare-tsare ko kuma ta wata fuskar dabam, da nufin kwankwasar azzalumai da yakar su. A nan Imam Bakir (a.s) yana karfafawa kan ma’anar yukurin da Imam Sadik zai yi saboda aiwatar da babban nauyi wajen fuskantar mulki mai ci, kuma ba ya karfafawa kan sakamakon da ka iya biyowa baya. Kai a wata riwayar ma maganarsa kusan tana yanke kaunar samun nasarar harakar imamanci ne a cikin wannan yanayin siyasar da ake ciki.Daga cikin riwayoyin da a cikin su Imam Bakir (a.s) yake karfafawa kan rawar da Imam Sadik (a.s) zai taka akwai abin da Abu Sabah Alkinani ya ruwaito, ya ce: “Abu Ja’afar ya dubi dansa Abu Abdillah sai ya ce: ‘Kana ganin wannan? Wannan yana cikin wadanda Allah Ta’ala ya ce (game da su :Kuma muna nufin Mu yi falala ga wadanda aka raunanar a cikin kasa kuma Mu sanya su shugabanni, kuma Mu sanya su magada.[26]
La’alla wadannan fayyace-fayyacen Imam Bakir su ne suka yada tunanin yunkurin Imam Sadik (a.s) da halifancinsa a tsakanin ‘yan shi’a, ya kuma sanya sahabban Imam Bakir da Imam sadik(a.s) sauraron wata faraga daga lokaci zuwa lokaci. Akwai wata riwaya cikin Rijal na Shaikh Kashshi wacce a cikinta ana iya fahimtar wannan yanayi mai wanzuwa a tsakanin mabiya Ahlulbaiti a wancan lokacin. Ibn Miskan ya ruwaito daga Zurara cewa ya tambayi Abu Abdillah (a.s) batun wani mutum cikin abokanmu wanda yake buya saboda gudun tara. Ya ce: Allah ya kiyaye ka! Akwai wani mutum cikin abokanmu yana buya saboda gudun tara, idan wannan al’amari kusa yake zai hakura har ya fito tare da mai tsayawa, Idan kuma akwai jinkiri zai yi sulhu ( da mahukunta ) saboda gudun tara. Sai Abu Abdillah (a.s) ya ce: Zai kasance. Sai Zurara ya ce : Zai kasance nan da shekara? Sai Abu Abdillah ya ce: Zai kasance insha’allahu. Sai Zurara ya ce: Zai kasance nan da shekara biyu? Sai Abu abdillah ya ce: Zai kasance insha’allahu. Sai Zurara ya fita, sai ya kwallafa ransa kan cewa zai kasance nan da shekara biyu. Amma bai faru ba. Sai ya ce : Ban kasance ina ganin Jafar ba face ya fi haka sani.[27]
Kalamar ‘wannan al’amari’ a sanin mabiya Ahlulbaiti kinaya ce kan zamani mai zuwa wanda aka yi musu alkawarinsa, watau karbar ragamar mulki ko kuma tabbatar da abin da zai kusanta su da wannan, kamar juyin juya hali ta hanyar daukan makami. Kuma ‘Mai Tsayawa’ shi ne zai jagoranci wannan aikin.
A wata riwaya Hisham Ibn Salim wanda shi ma wani babba ne kuma sananne daga cikin shi’a, ya ambaci cewa Zurara ya ce da shi: “Ba zaka ga wani kan karagar shugabanci ba face Ja’afar.” Ya ce: Yayinda Abu Abdillah ya yi wafati sai na zo na ce masa (Zurara): Kana tuna labarin da ka bani? Na ambata masa shi, ina mai tsoron kada ya yi musun cewa ya fada mini. Sai ya ce: “Wallahi ni ban fadi waccar maganar ba face dama nawa ra’ayin ne(watau dama ba ya ruwaito maganar Imam ba ne)”.
Daga jumlar abin da ya gabata muna fahimtar cewa a ra’ayin babansa da na jama’a Imam Sadik (a.s) shi ne mai tabbatar da burin imamanci da shi’anci. Kuma silsilar imamanci ta riga ta yi tanadinsa domin tabbatarda kokarin Imam Sajjad da Imam Bakir(a.s) . Kamar dai shi ne ya wajaba a kansa ya dawo da ginin hukumar Alawiyya da tsari irin na tauhidi,watau ya wajaba ya aiwatar da wani sabon yunkurin musulunci. Imaman nan biyu da sauka gabata sun riga sun ci zango-zango masu wahala da kunci a kan wannan gwadabe, shi kuma sai ya ji da zangon karshe. Kamar yanda muka ambata, yanayi ya daidaita ga Imam kuma ya yi amfani da wannan dama wajen yukurin gabatar da sakonsa mai girma.
Tun lokacin da ya karbi nauyin shugabaci har zuwa wafatinsa, Imam ya dauki shekara talatin da uku yana jihadi maras yankewa. Cikin wadannan shekarun yanayi ya kasance yana sa kyakkyawar fata, wani lokacin kuma matsin lamba yana hawa da kuma sauka;wani zubi ya dace da maslahar mazhabin Ahlulbaiti, wani zubin kuwa yanayin ya juya akasin hakan. Wani lokaci halin yana sa kyakkyawar fata, wani lokacin kuma matsin lamba yana tsanani, har sahabban Imam su zaci cewa dukkan buri ya tarwatse. A duk wadannan halaye Imam Sadik(a.s) yana rike da ragamar jagoranci kyam tare da azama da jajircewa. Yana keta fagen nan mai rudani, mai tattare da tsammani da kuma yanke kauna, ba ya damuwa da komai sai tafiyar da ke gaba yana wanzar da kokari da karfin gwiwa da imani wa mabiyansa domin kaiwa ga tsira.
A nan ya zama wajibi mu yi nuni da wani al’amari mai ban takaici wanda dukkan masu bincike kan rayuwar Imam Sadik(a.s) suke fuskanta .
Wannan kuwa shi ne halin rashin tabbas wanda ya lullube shekarun farkon imamanci Sadik(a.s) wadanda suka yi muni daidai da karshen zamanin Banu Umayya. A lokacin rayuwa ba ta san natsuwa ba tana kuma cike da aukuwar manya-manyan al’amura,muna iya fahimtar alamunsu cikin daruruwan riwayoyi. Sai dai malaman tarihi da hadisi basu kawo mana labarin wannan lokacin a jere tare da sajewa da daganta wannan bayani da wancan ba. Saboda haka ya zama dole ga mai bincike ya yi dogaro da kuma lura da al’amura da suke baiyana cikin abinda yake karantawa (kara’in), ya lura da kungiyoyi da ra’ayoyi a game na wancan zamani sannan ya kwatanta ko wace riwaya da bayanan da ya riga ya sani domin ya ga abin fahimtar(mafhumi) abinda riwayar ta kunsa da rabe-raben ta.
La’alla daya daga dalilan wannan rikitarwa shi ne kasancewa harakar Imam da mabiyansa an yi ta cikin sirri, domin shiri na siri wanda ya kafu bisa ingantattun ginshikai dole ne bayanan da suka dangance shi su wanzu cikin sirri da boyewa, kuma wajibi ne kada wanda yake waje da wannan shiri ya tsinkaye su. Wadannan bayanai ba su watsuwa sai bayan tabbatar harakar da kuma nasararta. Saboda haka ne muke samun cikakkun bayanai dalla-dalla kan sadarwa ta sirri a harakar Abbasiyawa domin harakarsu ta yi nasara. Babu shakka da an kaddara wa harakar Ahlulbaiti kaiwa ga nasara da karbar ragamar mulki da a yau mun riski sirrin tsare-tsarenta masu fadi.
Akwai wani dalilin daban wanda zai iya janyo wannan rashin baiyana dangane da harakar Ahlulbaiti, cewa murubuta tarihi, bisa al’ada suna rubuta abin da yake dadada wa sarakuna ne. Domin haka muke ganin bayanai filla-filla kan rayuwar halifofi da wasanninsu da hirarrakinsu da wuraren holewarsu amma bamu ganin bayanan kirki kan masu neman juyi da wadanda aka zalunta da wadanda aka murkushe. Domin samun irin wadannan bayanan mai bin diddigi na bukatar dogon bincike da kirkado da tsananin biyawa. Amma rayuwar halifofi bayani ne tanadadde, tsuntsu daga sama gasashshe, yana kawo yardarsu da tarin kyaututtuka.
Marubuta tarihi masu rusnawa ga halifofin Abbasiyawa sun ci gaba da rubutu bisa wannan hanya na tsawon shekara dari biyar bayan rayuwar Imam Sadik (a.s). Saboda haka ba za mu yi tsammanin samun wani abin kirki na bayanai kan rayuwar Imam Sadik (a.s) ba, da ma na ko wani imamin shi’a cikin wadannan littafai.
Hanyar kadai da za ta iya shiryar da mu kan layin da rayuwar Imam Sadik ta duka ita ce gano muhimman alamu na rayuwar Imam ta hanyar ka’idoji, a game, na salon tunanin Imam da dabi’unsa. Kana mu yi bincike kan abubuwan tarihi da suka danganci wannan rayuwa da hujjojin tarihi da suke warwatse da kuma irin wadancan abubuwa masu dangantaka da rayuwar Imam wadanda ba na tarihi ba har mu kai ga rarrabewar al’amarin filla-filla.

Alamomi a Rayuwar Imam Sadik (a.s)
Muhimman alamomi wadanda suke fitattu a rayuwar Imam Sadik (a.s) idan muka lura da mahangar bahasinmu, suna iya tattaruwa cikin wadannan:-
1. Bayyana sha’anin imamanci da kira zuwa gare shi.
2. Sharhi kan hukunce-hukunce da tafsirin Alkur’ani dai-dai da abin da mazhabin Ahlulbaiti ya gada daga Manzon Allah (s.a.w.a)
3. kafa tsari na sirri kan manufa da kuma siyasa.
Hanyar da bahasinmu zai dauka ita ce yin bincike kan kowani daya daga wadannan alamomi sannan daga karshe mu sanya wani jadawalin ayyukan Imam (a.s) Duk wannan zai kasance da salon masu tarihi ba na masu hadisi ba, gwargwadon iyawarmu.
1. Bayyana sha’anin imamanci da kuma yin kira zuwa gare shi.
Wannan maudu’i yana daukar masayin mafi bayyanan alamomin kiran imaman Ahlulbaiti (a.s) tun shekarun farko bayan kaurar Annabin rahama (s.a.w.a). Mas’alar tabbatar da imamancin Ahlulbaiti ita ce al’amari na kan gaba wajen kira a dukkan zamunnan imamanci. Muna iya ganin wannan mas’alar a yunkurin Imam Hussain ibn Ali (a.s) da kuma yunkurin ‘ya‘yan imaman Ahlulbaiti kamar Zaid ibn Ali. Kirar Imam Sadik ita ma ba ta fita daga wanna fagen ba.
Kafin mu bijiro da hujjoji kan wannan maudu’i ya zama wajibi tukun mu fara da bayanin ma’anar (imama) ‘imamanci’ a tunanin musulunci. Kuma mene ne kira zuwa ga imamanci? Kalmar imamanci a asalinta tana nufin jagoranci sake ba kaidi. A tunanin musulunci kuwa galibi ana amfani da ita ne a kebance. Wannan wurin kuwa shi ne jagoranci a sha’anin halin zaman jama’a walau wajen tsarin tunani ne ko kuwa tsarin siyasa.
Kalmomin da aka tsago daga ita kalmar ‘imama’kamar su ‘imam’ da ‘a’imma,’ duk inda suke a cikin Alkur’ani abin da ake nufi da su shi ne kebantaciyar ma’anarsu watau jagorancin al’umma. A wadansu wurare abin da ake nufi da ita shi ne jagorancin tunani a wadansu kuwa jagorancin siyasa ko kuma biyun gaba daya.
Bayan kaurar Ma’aiki da bayyanar rarrabuwar salon tunani da siyasa tsakanin jama’ar musulmi, kalmar imamanci, da imama, ta dauki wani kebantaccen masayi, saboda mas’alar jagorancin siyasa ita ce jigon sassabawar musulmi. Da farko, kalmar tana da manufar siyasa fiye da kowace manufa wacce ba ta siyasa ba. Daga bisani wadansu ma’anonin sun riske ta sannu a hankali, har aka wayi gari a karni na biyu mas’alar ‘imama’ ta zamo mas’ala mafi muhimmanci wajen makarantan ilmul kalam masu baiyana ra’ayoyinsu kan sha’anin sharuddan imam da sifofinsa, watau sharuddan mai hukunci a al’ummnar musulunci; wannan kuwa shi ne ma’anar imamanci a siyasance.