Zango Na Biyu
Zangon rike ragamar shugabanci. Wannan zangon ya dauki shekaru hudu da wata tara na halifancin Amirul Muminina Ali (a.s) da kuma wasu watanni na halifancin dansa Hassan (a.s). Duk da wahalhalu da matsaloli da damuwa da tsanani da yake tattare da wannan zangon, kamar yadda duk wata hukuma mai ra’ayin juyi take fuskanta, mafi haske da ban sha’awan shafuffukan tarihi ne suka kunshi bayanin aikace-aikacesa, kamar su mu’amala mai cikakkiyar dan Adamtaka da adalci da tsananin lizimtar hukunce-hukuncen musulunci ta fuskoki dabam-dabam wajen gudanar da al’ummar musulunci da kuma rikon magana daya da fayyacewa da jaruntaka wajen aiwatarwa da kuma daukan matsayi.
Wannan zango na tarihin imamanci ya zama abin koyi wanda Imaman Ahlulbaiti (a.s) suka yi kira domin aiwatar da shi a rayuwar siyasa da zamantakewa, tsawon karni biyu. Mabiya Ahlulbaiti suna kankame da son wancan yanki na tarihin musulunci, suna neman dawo da shi, suna kuma auna tsare-tsaren da suke rayuwa cikinsu da wancan zamani mai ban sha’awa. Da wannan ma’aunin ne suke tuhumar tsare-tsaren da suka baude wa turbar musulunci. Mai ra’ayin sauyi a al’ummar wacce da bidi’a da baudiya suka addaba. Wannan halin da al’umma take cikinsa ya dorawa Imaman da suka biyo baya nauyi mai tsanani da mas’uliya mai girma.

Zango Na Uku
Shi ne wanda ya dauki shekara ashirin,tsankanin sulhun Imam Hassan (a.s) a shekara ta 41 H zuwa shahadar Imam Hussain (a.s) a shekara ta 61 H. Bayan sulhun Imam Hassan (a.s) an soma wani nau’in aiki mai kama da sirri wanda kuma manufarsa ita ce maido da jagorancin musulunci wa ma’abotansa na gaskiya tun da lamarin yana bukatar dako har sai mulkin Mu’awiya ya kare. Cikin wannan gajeran lokaci an fuskantar da kokarin kyautata yanayi wajen yin shimfida ga zango na gaba.

Zango Na Hudu
A nan ya kamata mu yi bayani mai dan dama, tun da wannan zangon shi ya shafi laccarmu domin a ciki Imam Sadik (a.s) ya rayu. Cikin wannan zangon da ya dauki kusan karni biyu, tafiyar Imamanci ta ci gaba kan wani dogon layi domin canja al’umma har ta dace da ra’ayin musulunci a dukkanin fagage wadanda suka hada da jagorancin siyasa. Tafiyar sashe ta yi galaba sashe kuma ta gamu da ci baya; tana tattare da nasara mai girma a fagen tunani da akida, tana cudanye da salo daban daban na dabarun gudanar da kira, abin adonta kuwa shi ne ikhlasi da sadaukarwa da fana’i da girman dan adamtaka a idon musulunci, halayen da suka kai kololuwa da kuma matukar kyau.Wannan marhala ko zango ya fara daga watan Muharam shekara ta 61 bayan hijira, bayan shahadar Imam Hussain bin Ali (a.s). Kamar yanda muka ambata, cikin wannan zangon, al’umma ta kara motsawa kwarai da gaske a fagen manufa (watau aidiyolojiyya) da tinkarar baude-baude ba jirkice-jirkice, wadanda matattarar iko da kuma kwakwalen jahiliyya suka wanzar. Waccar motsawa manufarta gudanar da aiyuka tsawo lokaci domin kafa hukumar musulunci mai tafiya bisa turbar Alkur’ani da sunnar Ma’aiki (s.a.w.a) kamar yanda Imam Ali (a.s) ya misalta.
A sarari yake cewa zartarda manhajar sauyi ‘yar asali a cikin al’ummar da ta sami shekaru da dama cikin karkacewar tunani da aiki yana bukatar kwararan dabaru da shiri mai tushe. A wancan lokacin, al’ummar Annabi ta rayu karkashin hukumar Mu’awiya mai cike da karkata gaskiya da musanya ta da wata fuska ta jabu, halin da ya jefa jama’a cikin wani barci mai nauyi tare da nisanta tunanin mutane daga ruhin jagoranci mai bin ka’ida. Wannan baudewa ta kai har lamarin ya janyo kashe badadin Manzon Allah (s.a.w.a) a Karbala, al hali wannan al’umma tana ji tana gani, al’ummar da take fama da halin fargaba da rauni da fatattaka a hannun razanarwar banu Umayya.
Saboda haka sai an yi aiki tukuru kafin a iya maido wa wannan al’umma ruhinta rasashshe da mutuntakarta wanda aka tattake, hakika aiki ne mai girma wanda al’umma take bukatarsa domin sake cancantar daukar sakon Islama da kama yunkurin ciccibar nauyin rike shi. Ba makawa ga wani sauyi tamkar wanda Manzon Allah (s.a.w.a) ya fuskanci al’ummar jahiliyya da shi, sannan daga bisani a karbi jagorancin jama’a.
Babu shakka dawo da rayuwa irin ta sauyi da sabonta ta aiki ne wanda bai kasa samar da ita tun farko wajen tsauri da muhimmanci ba. Tajdidi irin na juyi yana bukatar imani mai karfi da azama tabbatatta da hankali mai tsarawa da tunani farkakke, wayayye mai motsawa. To wane ne mai daukar wannan nauyin?! Waccar jama’ar da ta kasa tafiya tareda Imam Hassan (a.s) ta kuma kasa kai matsayin taimakawa Imam Hussain (a.s) lallai ba ta iya wannan aikin raya al’ummar musuluncin. Saboda haka dogaro ga wanna jama’ar babu abin da zai haifar illa cin tura da tabewa. Hakika motsin da Tawwabin suka jarraba da tawayen Mukhtar da Ibrahim bin Malik hujja ce babba kan abin da muka fadi.

Matsayin Imam Sajjad (a.s)
Bayan waki’ar Ashura Imam Zainul Abidin Ali bin Hussain (a.s) yana da zabi biyu,su ne:- Imma dai ya sa sahabbansa shiga wata harka sakamakon motsawar rai da tausayi ya jefa su cikin wani garaje wanda wutarsa ba badewa ruruwarta zai yi sanyi, ya bice (saboda ba su da sifofin masu jihadi), sannan daga bisani a bar wa Banu Umayya filin ci gaba da danniya da babakere kan makomar al’umma wajen tunani da siyasa, ko kuma ya rinjayi tausayi da biri---bokon fushi da tunzura, kana ya tanadi share fage wa wani babban aiki wanda zai kai ga dawo da rayuwa irin ta musulunci. Bukatun share fagen su ne tunani mai jagorantan aiki da samar da wata salihar jama’a domin ta zama iri ga juyi da sauyi nan gaba, ya kuma nisanci idanun Banu Umayya, ya ci gaba da aiki haikan wanda manufarsa ita ce gina tunani da kuma dai-daikun matane. Da haka ne zai yi tafiya mai yawa kan manufar kira, Imamin da zai gaje shi kuwa zai zama ya kara kusanto cimma manufar.
To wani zabi ko hanya zai fifita? Ko shaka babu, hanyar farko ita ce ta sadaukarwa da daukar fansa, sai dai jagoran da yake shiri saboda harakar tarihi da kuma zamanin da tsawonsa ya zarce tsawon rayuwar Imam nesa ba kusa ba, sadaukar da rayuwarsa kawai ba ta isa. Dole ne ya zama mai zurfin tunani, mai yalwar zuciya, mai hangen nesa mai dabara da hikima cikin al’amuransa. Wadannan sharrudda sun wajabtawa Imam zabar hanya ta biyun.
Imam Ali bin Hussain (a.s) ya zabi ta biyun duk da dauriya da wahal-halu da juriya da kuncin da ke tattare da wannan hanya. Ya ba da rayuwarsa kan wannan tafarki (a shekara ta 95 bayan hijira).
Imam Sadik (a.s) ya sifanta mana yanayin da imami na hudu ya rayu a kai da kuma rawar da ya taka ta jagaba, ya ce:-“Bayan Imam Hussain (a.s) mutane sun juya baya banda mutum uku, Khalid Alkabuli da Yahya ibn Ummi Dawil da Jubair bin Mud’im. Daga bisani sai mutane suka dawo suka yawaita. Yahaya Ibn Ummi Dawil ya kan shiga masallacin Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce:- “Mun fita batunku kuma kiyayya da jiyewa juna sun bayyana a tsakaninmu …..”(Mumtahina aya 4.)
Wannan riwaya tana nuna halin da al’ummar musulmi take ciki bayanan kashe Imam Hussaini (a.s). yanayi ne mai ban tsoro, na fatattaka da raunin zuciya wanda ya game al’ummar musulunci a lokacin da waccan waki’ar ta faru, abin takaicinda ya auku a Karbala al’ummar har ma shi’ar Ahlulbaiti, ya fadi warwas. Wadannan ‘yan shi’an da suka gamsu da alaka da Imamai a zuci kawai amma a aikace sun karkata wa duniya da jin dadinta da kelkelinta. Irin wadannan suna nan tsawon tarihi hatta a zamanin nan namu, ba kuma kadan suke ba.
Daga cikin dubban masu da’awar shi’a a zamanin Imam Sajjad (a.s) mutum uku kadai suka rage bisa tafarki, mutum uku ne razanarwar Ummayawa da kamun da hukuma ke yiwa mutane bai sa su firgita ba, kuma son kubuta daga neman zaman lafiya bai girgiza azamarsu ba. Sun ci gaba da amsa kira da fama bisa wannan tafarki da cikakkiyar azama da tabbata. Guguwar da ta kwashi al’umma tamkar wasu zauna gari-banza suka kuma bi manufar azzalumar hukuma, ba ta kwashi wadannan mutanen ba. Dayansu watau Yahya ibn Ummi Dawil ya kan mike a masallacin Madina ya yi huduba wa masu da’awar wilaya ga Ahlulbaiti yana mai baiyana bara’a gare su, kamar yanda ya gabata, yana kafa hujja da abin da Annabi Ibrahim (a.s) da mabiyansa suka fada wa masu bijirewan zamaninsa “ Mun fita batunku kuma kiyayya da jiyewa juna sun bayyana a tsakaninmu.” Ibn Ummi Dawil ya karanta wannan aya mai girma gaba ga masu da’awar wilaya ga Ahlulbaiti ne domin ya baiyana cikakken rabewa tsakanin sassan guda biyu:sashen ma’abota sako masu lizimta da kuma sashen masu zaman dirshan da sassautowa zuwa burace-buracen da basu taka kara sun karya ba da kuma rudi da abin duniya mara kima. Wannan rabewa tana tare da dukkanin kiraye-kirayen addini. Imam Sadik ya sifanta wannan rabewa na sassan biyu da cewa:- (Wanda ba ya tare da mu, to yana adawa da mu). Watau wanda duk ba ya sashen tauhidi to yana bangaren dagutu, babu wata ma’ana ga zama dan ba ruwanmu domin kuwa ba wani yankin tsaka-tsaki.
Wannan musulmi mai wilayar gaskiya ga Ahlulbaitin Manzon Allah (s.a.w.a) watau Yahaya bn Ummi Dawil, da wannan kiran nasa ya baiyana rabewa tsakanin masu gamsuwa da wilayar da ta takaita ga motsin rai alhali suna kwanto cikin abubuwan amfanin kansu, suna nitse cikin dattin kuntataccen zatinsu,da masu lizimtar Imam a tunani da kuma aiki. Bisa dabi’a wannan rabewa tana nufin wuce gaban cewa batattun masu rinjaye su janye mutum, amma ba tana nufin watsi da batattun ba. Da wannan fikira ne wannan salihar jama’a ta fuskanci aikin tsamar da duk wani mai iya ‘yantuwa daga wahala da kangi. Sannu a hankali, sai wannan jama’a mai jihadi da dauriya ta yawaita, kuma da wannan ne Imam Sadik (a.s) yake ishara yayin da ya ce: “…… daga bisani sai mutane suka dawo suka yi yawa” Ta haka ne Imam Sajjad ya ci gaba da ba da himma kan aikinsa. Wannan aikin da wadansu matsayin da Imam ya dauka, wadanda za mu ambato nan gaba yana daga cikin abubuwan da suka janyo shahadarsa da ta wasu daga mukarrabansa.
Ban ga wani bayyanannen sa-in-sa da hukuma a rayuwar Imam Sajjad (a.s) ba. Kamar yanda muka ambata, hakan shi ne abin da ya dace da hikima. Domin da ya dauki irin matsayin da muke gani a rayuwar Imam Musa ibn Ja’afar (a.s) da imaman da suka biyo bayansa dangane da mahukuntan zamaninsa da bai iya ciyar da aikin sauyi gaba har ya samar wa Imam Baqir (a.s) damar mayalwacin aiki ba. Da yayi haka da an hallaka shi da salihar jama’ar da take tare da shi.
Ba mu iya tsinkayar ra’ayin Imam na hakika dangane da masu iko illa nadiran, ko a nan ma bai kai matsayin fito-na fito ba. Iyaka dai yana tabbatar da wani matsayi wa tahiri yana kuma fadakar da jama’ar da take kusa da shi kan abin da ya shafi aikinsa da harakarsa gwargwado. Irin wadancan matsayi sun hada da takardar suka mai tsanani da Imam da aikewa wani malami mai alakar kut-da-kut da Banu Umayya watau Muhammad bin Shihab Azzuhri. Muna iya fahimta a takardar cewa Imam yana magana ne da tsararraki masu zuwa tsawon zamani, ba da Azzuhri ba saboda Azzuhri ba mutumin da zai iya yantuwa daga kangin liyafar Banu Umayya da wasanninsu da mukamansu da al’farmarsu ba ne.Tahiri ya tabbatar da hakan, domin kuwa Azzuhri ya gama rayuwarsa ne cikinsa hidimarsu tare da rubuta littafi da kuma kirkirar hadisai saboda neman kusanci da su [9]
Saboda haka takardar Imam tana bayyana matsayinsa kan yanayin zamaninsa ne. Nassin wannan wasika yana nan cikin littafin Tuhaful Ukul.[10]
Akwai kuma wasikar da Imam ya aikewa Abdulmalik ibn Marwan a matsayin jawabi kan wata wasikarsa wacce take dauke da aibantawa ga Imam saboda ya auri wata baiwar da ya yanta. Abin da Abdulmalik yake son baiyanawa Imam (a.s.) shi ne yana sane da duk abin da yake aikatarwa hatta al’amuran da suka kebance shi. Kazalika yana nufin tunatar da Imam (a.s) da dangantakarsa da shi da zimmar jan hankalinsa.
A jawabin da ya rubuta, Imam ya baiyana ra’ayin musulunci a kan wannan mas’ala yana mai takidin cewa fifikon imani da musulunci ya kore kowani fifiko. Sannan ta hanyar kinaya, mai gwanin kyau, imam yayi ishara da hali rin na jahiliyya wanda iyayen halifa suka rayu a kai, la’alla ya hada har da rayuwar halifan shi kan shi. Ya ce: “ Babu karanta ga musulmi, karantar jahiliyya ce kawai karanta”.
Da halifa ya karanta kalmomin Imam (a.s) ya fahimci ma’narsu,cikakkiyar famta,kamar yanda dansa Sulaiman ya tsinkayi ma’anar yayin da ya ce da mahaifinsa: “Ya Shugaban Muminai alfaharin da Ali bn Hussaini ya yi hakika ya yi tsanani!” Saboda gogewarsa ta siyasa,halifa sai ya amsa wa dansa da abin da zai nuna masa cewa ya fi shi sanin abin da karo da imamin shi’a zai hafar. Ya ce da shi: “Da na kada ka fadi haka,domin wadannan harsunan Bani Hashim ne masu tsaga dutse, masu kamfata daga teku. Da ma ai Ali ibn Hussaini yana bayyana daukakarsa a yanayin da sauran mutane suke fankamar mika wuya.”
Wani misali mai nuna matsayin da Imam ya dauka shi ne yin watsi da wata bukatar Abdulmalik bin Marwan. Abdulmalik ya sami labarin cewa akwai takwabin Manzon Allah (s.a.w.a) wurin Imam sai ya aiko yana neman ya ba shi kyautarsa ya kuma yi barazanar yanke abin da ake baiwa Imam daga baitul mali.Sai Imam (a.s) ya rubuto masa:-
((Bayan haka, Lallai Allah ya lamunce wa masu tsoronsa mafita ta inda suke ki, da arziki ta inda basu tsammani. Mai girman ambato ya ce (Lallai Allah ba ya son duk wani mai tsananin ha’inci mai yawan kafirci), sai ka duba ka gani wane ne daga cikinmu ya dace da wannan aya?[11]))
A wasu wurare muna ganin Imam Sajjad (a.s) yana motsawa cikin natsuwa da kuma garkuwa da tarbiyar dai-daiku da gina mutumtaka ta musulunci bisa karantarwar mazhabin Ahlulbaiti da yaki da baude-baude da sauransu. Da wannan aikin ne bisa hakika, ya dauki matakin asasi na farko a kan tafarkin tabbatar da manufar mazhabin Ahlulbaiti wanda ita ce kafa jama’ar musulunci karkashin inuwar salihar hukumar musulunci bisa misalin hukumar Manzon Allah (s.a.w.a) da Ali bin Abi Talib (a.s). Kuma kamar yanda muka ambata Imam (a.s) da mabiyansa basu nemi daidaitawa da hukuma mai kamu da azabtarwa ba duk da cewa sun bi hanyar da a zahiri tana daidaitawa da hukuma.
Daga cikin mabiyansa akwai wadanda aka kashe ta kazamar hanya, wasu an daure wasu kuwa an kore su nesa da mutanensu da gidajensu. Imam da kansa a kalla sau daya an tusa keyarsa a cikin kangi a cikin halin torartawa da wahala daga Madina zuwa Sham, sau da yawa kuma ya fada cikin nau ‘o’ in cutarwa da azabatarwa. Daga karshe halifan banu Umayya, Walid bin Abdulmalik ya ciyar da shi guba. Imam (a.s) ya yi shahada a shekara ta 95 bayan hijira.

Rayuwar Imam Bakir (a.s) Zarcewar Irin Rayuwar Imam Sajjad
An wayi gari mabiya Ahlulbaiti sun zama wata jama’a fitacciya mai dogaro da kai, kirar Ahlulbhaiti kuwa wacce ta dan tsaya ta kuma boye bayan shamaki mai kauri a dalilin waki’ar Karbala da waki’o’in da aka zubar da jini da suka biyo bayanta kamar waki’ar Harra da tawayen Tawwabun wadanda fir’aunancin Umayyawa ya haifar ta zama samamma ce mai yaduwa ta kuma bayyana cikin da yawa daga yankunan daular musulunci, musamman a Iraki da Hijaz da Kurasan. Tare da wannan samuwa, ta haifar da tsari na tunani da kuma aiki. Kwanakin da Imam Sajjad (a.s) ya sifanta da cewa : “ mabiyansa ba su wuce ashirin ba” sun kau sai ga Imam Bakir (a.s) yana shigo masallacin Ma’aiki (s.a.w.) a Madina jama’a mai yawa daga mutanen Kurasan da sauran lardunan duniyar musulmi suna kewaye shi, suna tambayarsa hukuncin musulunci kan al’amuran rayuwa dabam-dabam. Mutane kamarsu Dawus Yamani da Katada ibn Da’ama da Abu Hanifa da wadansu daga shugabannin mazhabobin fikihu suna tahowa domin su sha daga ilmin Imam ko kuma su yi jayayya da shi kan al’amura dabam-dabam.
A wannan zamanin an sami mawaka masu kare mazhabin Ahlulbaiti da bayyana manufofinsa. Daga cikinsu akwai Kumait wanda ya sauwara mafi kyan surar da kwararru ke zaiyanawa a kan wilaya ta tunani da kauna ga mutanen gidan Manzon Allah (s.a.w.a) cikin kasidarsa mai suna hashimiyya. Hakika harsuna basu gushe ba suna nakaltar wadannan gwalagwalan wake yayin da zukata suke kiyaye su.
Ta wata fuska kuwa halifofin Banu Marwana cikin wannan dan lokacin, sun sami wata natsuwa da tabbatar mulki bayan Abdulimalik ibn Marwan (m.86H) cikin shekara ashirin da ya yi mulki, ya murkushe dukkan masu ja da mulkinsu, kuma yiwuwa cewa sansancewar aminci da natsuwa da halifofin Marwaniyawa na wannan lokacin ya samo asali ne daga kasancewar sun sami mulki tamkar wata ganima, sabanin magabatansu wadanda suka yi jan aiki kafin su kai ga mulki. Wannan natsuwa ta sa halifofin baya shagaltuwa da wasanni da jin dadin duniya, tadodin da galibi suke tare da mai jin iko da alfarma da kuma girma. Ko mene ne ma dai, damuwar halifofin Banu Marwan da lamarin mazhabin Ahlulbaiti ta ragu a wancan lokacin, sai ga Imam da mabiyansa suna rayuwa kusan a ce cikin aminci daga farautar hukuma. Bisa dabi’a, Imam zai ci tafiya mai yawa kan tafarkin tabbatar da manufofin mazhabin Ahlulbaiti a irin wannan yanayi ya kuma kai shi’anci wani sabon zango. Wannan kuwa shi ne ya bambanta rayuwar Imam Bakir (a.s) da ta saura. Ana iya takaita abin da rayuwar Imam, cikin shekaru goma sha tara na imamancinsa (95-144H) ta kunsa kamar haka:-
Yayin da mahaifinsa Imam Sajjad (a.s) ya zo cikawa ya yi wasici da cewa dansa Muhammadu ya zama Imami bayansa, gaba ga sauran ‘ya’yansa da danginsa, ya kuma ba shi wani akwati. Riwayoyi sun ce akwatin cike yake da ilmi, sun kuma ce akwai makamin Manzon Allah (s.a.w.a) a ciki. Imam Sajjad (a.s) ya ce:- “Ya kai Muhammadu wannana akwati ka tafi da shi gidanka” Sannan ya ce:- “Hakika babu dinari ko dirhami a ciki, sai dai cike yake da ilmi”[12]
La’alla wannan akwati wata alama ce mai muna cewa Imam Sajjad ya mikawa dansa jagorancin tunani da ilmi (tunda yana cike da ilmi) ya kuma mika masa nauyin jagorancin juyi (tun da yana kunshe da makamin Annabi (s.a.w.a)).
Gami da farawar Imam da mabiyansa faffadan aikinsu na yada koyarwar Ahlubaiti (a.s) farfajiyar yaduwar kiran ta kara fadi, ta sami sababbin fuskoki wadanda suka zarce fagenta daya gabata a Madina da Kufa. Sai ga ta tana yaduwa cikin larduna manisanta daga cibiyar mulkin Umayyawa. Lardin Kurasan na daga cikin wadancan wurare kamar yanda riwayoyin tahiri suka nuna.[13]
Yanayin tunani da zamantakewa mai kaskanta mutane ya zaburar da Imam da mabiyansa wajen haraka mai dorewa ba tare da gajiya ko kosawa ba domin sauya wannan mummunan yanayi da tabbatar da abinda Ubangiji ya wajabta na kawar da wannan baudiyar.
Suna ganin mafiya yawan mutane sun rusna wa gurbatanccen yanayin da Banu Umayya suka yada, suka nitse cikin kazantar abin duniya iya wuya har suka wayi gari tamkar mahukuntan nasu,basu fahimtar zance, kunnensu bai jin nasiha. “Idan mum kira su ba sa amsa mana”.[14]
Ta wata fuska kuwa, Imam da jama’arsa suna ganin bincike-binciken fikihu da ilmul kalam da hadisi da tafsiri na karkata ne wajen dadada wa fir’aunancin Umayyawa da bin sonransu. Saboda haka duk hanyoyin dawowar jama’a kan katari da sun toshe, ba don zaburar mazhabin Ahlulbaiti wajen bayar da wajibinsa ba idan kuwa muka kyale su ba za su shiriya ta hanyar waninmu ba[15]
Mazhabin Ahlulbaiti ya yi Allah wadai da malamai da mawaka da suka sayarda kansu. An yi wannan sukan ne saboda kokarin farkarda zukatan wadancan malaman ko kuma zukatan mabiyansu. Imam yana fadawa Kumait, sha’irin Ahlulbaiti, da lafazin suka:- yabon Abdulmalik kayi?
Ya ce:- Ban ce da shi ‘ya shugaban shiriya’ ba, abin da na ce shi ne ‘ya zaki’ zaki kuma kare ne, ‘ya rana’ rana kuwa jamadatu ce, ‘ya kogi’ kogi kuwa mataccen abu ne, ‘ya maciji’ maciji kuwa kwaro ne mai wari, ‘ya tsauni’ tsauni kuwa kurman dutse ne. Sai Imam ya yi murmushi. Kumait sai ya rera wannan baitin gaban Imam:-
Zuciyar da so ya tsare ya aure?
Ban da yaranta tasa har da guri,
Wannan mimiyar ta kafa mararraba tsakanin alkiblar Alawiyya da ta Umawiyya a daraja da kuma halaye ta hanyar dawwamammar zaiyanawa mai kyan gaske.
Wata rana Ikrima almajirin ibn Abbas wanda yake sananne ne, mai matsayin ilmi a cikin al’ummar wancan zamanin ya je yin mukabala da Imam sai haibarsa da natsuwarsa da ruhinsa da tunaninsa suka kama Ikrima. Abin da kadai ya iya fada shi ne:- “Ya dan Manzon Allah hakika na zauna gaban Ibn Abbas da waninsa sau da yawa amma irin abin da ya same ni yanzu bai taba samu na ba”. Sai Imam ya amsa masa da cewa:- “(Kai kana gaba ga gidaje wadanda Allah ya yi wa daukaka kuma ake ambaton sunansa a cikinsu)[16]
Ta wandansu fuskoki daban na ayyukan mazhabin Ahlulbaiti a wannan zangon kuwa, akwai jerin zalunci da fir’aunanci da kisa da azabtarwa da kora, da suka kewaye Ahlulbaitin Manzon Allah da mabiyansu ba don komai ba sai domin kokarin da suke yi na iza matacciyar zuciyar mutane da girgiza rayukansu wadanda suka yi sanyi da zaburar da kwantacciyar azamarsu da shiryar da su zuwa harakar juyi.
Alminhal bin Umar ya ruwaito cewa:- “Na kasance ina zaune tare da Muhammad bn Ali Albakir (a.s) sai wani mutum ya taho ya ce da shi: Yaya kuke? Sai Imam Bakir(a.s) ya ce:- “Lokaci bai yi ba da za ku san yanda muke? Misalinmu a wannan al’umma tamkar Bani Isr’a’ila ne a da,ana yanka ‘ya‘ya maza ana barin (raya )mata. Ka saurara! Lallai wadannan suna yanka ‘ya‘yanmu maza suna barin ‘ya ‘yanmu mata. Larabawa sun yi da’awar fifiko bisa baibayi. Sai baibayin suka ce: ‘Mene ne dalilin haka?’ Sai suka ce: “Muhammadu balarare ne daga gare mu” Sai suka ce da su: “Kun yi gaskiya.” Kuraishawa kuwa suka yi da’awar cewa suna da wani fifiko bisa sauran larabawa. Sai sauran larabawa suka ce “Mene ne dalili?” Sai suka amsa da cewa: ‘Muhammadu bakuraishe ne’. Suka ce da su: ‘Kun yi gaskiya’. Idan mutanen nan sun yi gaskiya, to muna da fifiko bisa mutane domin mu zuriyar Muhammadu ne, mutanen gidansa kuma makusantansa masu kebanta da shi, waninmu ba ya tarayya da mu a wannan” Sai mutumin ya ce da Imam; “Wallahi ni ina son ku, ku Ahlulbait”. Sai ya ce da shi: “To ka dauki bala’i a matsayin riga, domin kuwa wallahi shi (bala’i) ya fi kusa da mu da kuma shi’armu bisa ga gudanar igiyar ruwa a cikin kwari. Da mu bala’i zai fara sanan ku”[17]
Da ganin alamar cewa mutumin ya girgiza saboda zaburarwar da ya ji sai Imam ya yi maza ya zana masa tafarkin kiran, ya fayyace.Shi dai tafarki ne wanda aka shimfida shi da jini da kwalla, Imam kuwa shi ne madugun tafiyar, bala’i yana samunsa da farko kafin ya kai ga shia’rsa.
A tsakanin shi’arsa alakar Imam tana da wadansu sifofi kebantattu. Za ka gan shi cikin mabiyansa tamkar yanda kwakwalwa take a tsakanin gabban jiki yana ciyar da ruhinsu yana karfafa masu haraka da himma ba tare da yankewa ba. Akwai hujjoji a hannunmu wadanda suke bayyana wannan alaka mai ba wa mabiya manufofi da karantarwa mabayyana da kuma tsara al’amuransu bisa tafarki hadadde, lasaftacce.
Misali; A farkon haduwar Jabir Alju’fi da Imam Bakir(a.s) sai ya masa wasiyya da kada ya fada wa kowa cewa daga Kufa yake ya kuma yi fita irin ta mutanen Madina .Da wannan Imam yake koyar da darasin rike sirri ga wannan sabon dalibi wanda ya ga alamun iya rike sirri tattare da shi. Wannan dalibi mai cancanta sai ya zama ma’abocin sirrin Imam. Tsakaninsa da hukuma kuwa lamarin ya kai ga abin da Nu’man bin Bashir ya ce:-
“Ina mai lizimtar Jabir bin Yazid Alju’fi yayin da muke Madina sai ya shiga wurin Abu’far (a.s) ya yi masa bankwana ya fito yana farin ciki. (Muka kama hanya) har muka isa Al’ukairaja, daga kewayen Madina, a ranar Juma’a. Muka yi salla. Mun kama tafiya kenan sai ga wani mutum dogo mai duhun fatar jiki da wasika a hannunsa. Sai Jabir ya karbe ta ya sunbace ta yasanya ta kan idanunsa. Sai ga shi a rubuce(( Daga Muhammad bin Ali ( Bakir) zuwa ga Jabir bin Yazid)), ga kuma danyen bakin yumbu a kanta. Sai ya ce da shi: ‘Yaushe rabonka da shugabana?’ Sai mutumin ya ce: ‘Dazun nan; sai ya ce: ‘kafin salla, ko bayan salla? Sai ya ce : ‘Bayan salla.’ Sai ya warware hatimin ya ci gaba da karantawa, yana daure fuska har ya kai karshenta, sannan ya nade ta. Daga nan ban sake ganinsa yana dariya ko farin ciki ba har muka isa Kufa”.
Numan ya ci gaba da cewa: “Mun isa kufa cikin dare, kashegari sai na tafi wajen Jabir Alju’fi saboda girmama shi, sai gashi ya fito bisa dokin kara yana rataye da wadansu kulle-kulle, tamkar yanda mahaukata ke yi, yana rerawa kamar haka:
‘Na san Mansur mutumin mutane;
Mai umurni ba’a umurtansa’
da wasu baitoci irin wannan. Sai ya kalli fuskata na kalli tasa amma bai ce da ni komai ba, ni ma ban ce masa komai ba. Sai na juya ina kuka saboda abin da na gani. Sai jama’a, babba da yaro, suka kewaye mu. Sai ya tafo har ya shigo dandali, ya kama zagawa tare da yara mutane na cewa Jabir bin Yazid ya haukace. Wallahi bayan ‘yan kwanaki sai ga takardar Hisham Ibn Abdulmalik an aiko ta gare ni kan batun shi. Tana cewa: ‘Ka binciki wani mutun mai suna Ja’bir Ibn Yazid Alju’fi ?’sai mutane suka ce: ‘Allah ya kiyaye ka’. Da mutun ne mai ilmi da daraja da sanin hadisi, ya yi aikin haji sai ya haukace. Shi ne wancan a dandali bisa dokin kara yana wasa da yara. Sai na ce: “Godiya ta tabbatar ga Allah wanda ya hutar da ni kisansa’.[18]
Wannan misali ne na alaka tsakanin Imam da mabiyansa na kusa. Yana bayyana tsananin tsari sa alaka kazalika yana nuna wani misali na matsayin hukuma kan mabiyan Imam. Wannan yana tabbatar mana cewa, masu iko ba cikin cikakkiyar gafala dangane da alakar Imam da mabiyansa na kusa suke ba, a’a, suna sa ido kan wadannan alakoki, suna kokarin gano su da kuma yin fito-na-fito da su.[19]
Sannu a hankali bangaren fito-na fito a rayuwar Imam Bakir (a.s) da ta shi’a yana tabbatar da wani fasali na rayuwar Ahlulbaiti (a.s).
Nassoshin tarihi da riwayoyin hadisi wadanda suke hannunmu basu faiyace samuwar wata matsananciyar harakar fama a siyasance wacce Imam yake aiwatarwa ba. Wannan rashin bayyanannar fama yana da dalilai, kamar su wanzuwar wani yanayi na jabberanci da azabtarwa mai mamaye da rayuwar al’umma, abin da ya tisalta wa mabiyan Imam wadanda su kadai ne masu masaniya kan rayuwarsa ta fuskar siyasa da su yi riko da takkiya. Sai dai martani matsananci wanda magabta (hukuma) suke mayarwa yana nuni da aikin jihadi mai zurfin tasiri da ake yi. Yayin da karfin mulki iri na Abdulmalik Ibn Marwan,wanda ake daukarsa a matsayin mafi karfin sarakunan Umayyawa, yayin da yake daukar mafi tsanani da tsaurin mataki kan Imam Bakir, ba wata tantama, wannan yana nuna cewa halifan yana jin tsoron hadarin da harakar da Imam da mabiyansa ke gudanarwa take tattare da shi ne. Da a ce Imam ya shagaltu ne da aiyukan ilmantarwa kadai ba tare da ya ba da himma kan gina tunani da tsare-tsare ba, to da sai mu ce ba maslaha ce ga masu mulki ba su matsawa Imam din lamba domin wannan mataki yana iya sa wa shi da mabiyansa su dauki matsayin fushi matsananci tamkar wanda mai tawayen nan ba’alawe Shahidin Fakh, watau Hussain bin Ali ya dauka.
A takaice, ana iya fahimtar matsanancin matsayin da hukuma ta dauka dangane da Imam Bakir (a.s) ta fuskar mayar da martanin da take yi kan aiyukan Imam masu sabawa da ra’ayin masu iko.
Daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a karshen rayuwar Imam Bakir (a.s) akwai kiransa da aka yi zuwa hedkwatar halifancin Umayyawa watau Sham (Dimashka). Halifofin Umayyawa sun yi niyyar bincikar matsayin Imam kan hukuma. Wannan ya sa suka yi umurni da kama shi da kuma kai shi Sham cikin cikakken tsaro. A wasu riwayoyi an ce wannan umurni ya hada har da dansa matashi watau Ja’far Sadik.
An kawo Imam fadar halifa. Kafin haka Hisham ya yi wa jama’arsa shiftar yanda za su fuskanci Imam yayin da yake shiga. Abin da ya shirya shi ne, shi halifa zai fara bijiro da tuhumce-tuhumce kan Imam sannan jama’a su ci gaba.
Abubuwa biyu yake da niyyar cimmawa: na farko shi ne raunana azamar Imam da sanya masa rashin yarda da kai. Na biyu: Kokarin sukar Imam a cikin taron da ya hada jagaban jama’ar halifanci da kuma na Imamanci a waje guda, sannan daga bisani a yada wannan cin zarfin ta hanyar kakakin fada kamar masu jawabi da masu wa’azin sarki da kuma ‘yan laken asiri, kuma da haka ne Hisham yake fatar samawa kansa nasara kan abokin hamayyarsa.
Da Imam ya shigo fadar halifa, sabanin yanda masu shigowa suka saba da yin gaisuwa ga halifa da sunan shugaban muminai, sai ya fuskanci dukkan mahalarta yana mai nuni ga ilahirinsu, ya ce: assalamu alaikum. Sannan ba tare da jiran izinin zama ba sai ya yi zamansa.
Wannan abin da Imam ya aikata ya cinna wutar hasada da kufe a zuciyar Hisham. Nan take sai ya fara jefa muggan maganganu yana cewa: ‘ Ya Muhammad Ibn Ali ba’a gushe ba wani daga cikinku yana rarraba kan musulmi, yana kiran mutane da su bi shi, yana kuma da’awar shi ne Imami (shugaba ) saboda wauta da karancin sani ………[20]Ya dai ci gaba da sukar sa.