kowane daya, ba tare da la'akari da jinsinsa (namiji ko mace) ba, yana yin kokarinsa da abin da zai iya wajen biyan bukatun al'umma, don shi ma ya sami tashi biyan bukatar ta hanyar aikin musayar abin duniya da hidima a cikin al'umma. Manomi na gabatar da kayan noma, injiniya da masanin fanni suna sana'anta na'ura, likita na bayar da lafiya, malami na yin aikinsa na karantar da manyan gobe, dan kasuwa na samar da kayayyakin masarufi a kasuwa, soja na kare kasa, mai gadi na maganin barayi da dai sauransu.
Darasi da nazarin hukunce-hukuncen Musulunci dukkansu, za su tabbatar mana da cewa Musulunci bai haramta wani nau'i na aiki ko ilimi ga mace bayan ya halalta shi ga namiji ba; mace na iya yin kowane irin aiki, kamar noma, sana'a, likitanci, injiniyanci, gudanarwa, ayyukan siyasa, tela, tukin jirgin sama da sauransu.
A musulunci babu wani aiki na samar da wani abu ko hidima da aka halalta ga namiji alhali kuma an haramta shi ga mace; kowa a shari'ar Musulunci daya ne a kan haka; bambancin kawai da ke tsakanin namiji da mace a wasu wajibai ne da aka kallafa wa namiji ko mace ko wasu maslahohi da suka ginu a kan asasan ilimi da aka yi la'akari da yanayin halitta ta rai da ga66ai ga kowannen su, da wajibcin tsara rayuwar zamantakewa da gudanar da ita.
Abin da yake asali a shari'ar Musulunci shi ne halaccin aiki, kai! wajibcin shi ma a wasu halaye; in banda abin da shari'a ta haramta ko abin da ke haifar da fadawa cikin abin da aka haramta.
Idan kuwa har akwai wata hayaniyar haramta aiki ga mace daga wajen wasu, to wannan na bukatar dalili, babu kuwa dalili na shari'a a kan wannan haramci.
Lura na ilimi ga bin diddigin malamai game da wajibai, da kasa su zuwa wajibi na Aini (shi ne irin wajibin da ya hau kan kowane mutum, wani ba ya daukewa wani; kamar sallolin wajibi) da na Kifa'i (shi ne wajibin da ya hau kan mutane a matsayin su na jama'a, idan wasu suka yi shi ya fadi a kan sauran; kamar sallar gawa), za ta bayyana gare mu, ta hanyar nazarin wajibin Kifa'i, cewa tsarin Musulunci ya wajabta wa daidaiku, ba tare da iyakance jinsin mace ko namiji ba, ya wajabta musu samar da bukatun al'umma da duk kashe-kashensu; kamar likitanci, injiniyanci, karantarwa, noma, kasuwanci, sufuri, tsaro da wasunsu na daga ayyukan da al'umma ke bukata; kai! wajibin Kifa'i ma na sauyawa ya zama wajibi Aini a kan mutum ko wasu mutane da ikon aiwatar da wannan wajibi ya kebanta da su; ba kuwa tare da la'akari da jinsin namiji ko mace ba.
Daga wannan za mu fahimci cewa kasa ayyukan hidima cikin al'umma da aiwatar da su, ya ginu ne a bisa asasai biyu: na mutum shi kadai da na tarayya; kuma a cikin dukkan halayen biyu, Musulunci bai bambanta tsakanin namiji da mace ba, maimakon haka, a wasu fagagen wajibcin Kifa'i, kamar wajibcin aikin likita da ya kebanci mata da karantar da su, yana fuskantar da wajibcin ne zuwa ga jinsin mace.

Mace Da Harkokin Siyasa
Daga cikin al'amurra na asasi da aka sanya a teburin tattaunawa da muhawara ta tunani da wayewa a karni na ashirin, akwai al'amarin hakkokin mace, daga ciki kuwa har da shigar ta cikin rayuwar siyasa da harkokin siyasa.
Abin da ke ba da mamaki shi ne cewa wadannan masu kira ga hakkokin mace na siyasa, suna fuskantar da tuhumarsu ga tunanin Musulunci da akidunsa, suna siffanta su da cewa tunane-tunane da akidu ne da suka haramta wa mace shiga cikin rayuwar siyasa, kuma su ke hana ta aiwatar da ayyukan siyasa; suna dogara da abin da suke ikirari da yanayin zamantakewa da siyasa wadanda suke shaidawa a garuruwan Musulmi, ba tare da sun tantance Musulunci a matsayinsa na tsari, shari'a da dokoki; da masu bin Musulunci wadanda ke misalta shi a cikin halayyarsu ta siyasa da zamantakewa ba; da cewa abin da suke shaidawa a kasashen Musulmi ya sabawa yadda ya kamata ya kasance cikin al'ummar Musulmi ba; domin surar mace a wadannan kasashe na Musulmi da hanyar yin mu'amala da ita da kimarta a cikin al'umma, a yanayin da yake na sabawa Musulunci, ya samo asali ne daga wasu tunane-tunane da al'adu da ayyuka na zamantakewa da ba sa misalta Musulunci, masamman ma matsayin mace a fagagen aiki, al'adu, zamantakewa, siyasa da alakarta tare da namiji.
Siyasa a yanayin Musulunci na nufin lura da sha'anonin al'umma a dukkan fagagensu na rayuwa, da ja-gorancin tafiyar da suke yi a hanyar Musulunci; don haka ita (siyasa) wani nauyi ne na zamantakewa baki daya da aka kallafa wa Musulmi baki daya. Wannan nauyi malamai sun kira shi da Wajibi na Kifa'i; wato game da shi ake horo da magana da dukkan Musulmi, ba tare da la'akari da kasancewarsu maza ko mata ba, in banda wanda aka toge (saboda wani dalili) daga cikinsu; misali fad'ar Allah Madaukaki: "..Cewa ku tsayar da addini kuma kada ku rarraba". Surar Shura, 42:13.
Da irin fadarSa Madaukaki: "Allah kuma Ya yi wa wadanda suka ba da gaskiya daga cikinku suka kuma yi aiki na gari alkawarin lalle ba Zai sanya su masu mayewa a bayan kasa kamar yadda Ya sanya wadanda suka gabace su masu mayewa..." Surar Nuri, 24:55.
Da fadarSa Madaukaki: "..ku bi Allah kuma ku bi ManzonSa da kuma majibinta al'amurranku (wato Imamai Ma'asumai).." Surar Nisa'i, 3:59.
Cikin dukkan wadannan ayoyin ana fuskantar da magana ne ga dukkan Musulmi maza da mata; ashe ke nan tsayar da addini da akidunsa da dukkan tsare-tsarensa na siyasa, zamantakewa, ibada da sauransu, nauyi a kan dukkan Musulmi, haka nan horon yin biyayya ga Majibinta al'amurra da ya zo a cikin wannan aya ana fuskantar da shi ne zuwa ga dukkan baligai; haka nan alkawarin mayewa ana fuskantar da shi ne ga dukkan wadanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka na gari maza da mata.
Fadar Allah Madaukaki: "Ya kai Annabi idan muminai mata suka zo maka suna mubaya'a gare ka a kan ba za su hada wani da Allah ba, ba za su yi sata ba, ba za su yi zina ba, ba za su kashe `ya'yansu ba, ba za su zo da wata karya wadda za su kage ta da tsakanin hannayensu ko da kafafuwansu ba, kuma ba za su saba maka cikin abin sarari na shari'a ba; to sai ka yi mubaya'a da su, kuma ka nema musu gafarar Allah, hakika Allah Mai yawan gafara ne Mai jin kai". Surar Mumtahanati, 60:12.
Wani aikatau ne kuma dalili na Alkur'ani da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya aikata shi cikin rayuwarsa ta isar da sako da siyasa, a kan kar6ar bai'ar mace ga Maji6incin AI'amari; kai! wajibcin haka ma, domin mubaya'a a wannan aya ita ce bai'ar biyayya ga Majibincin Al'amari, a kan lizimtar hukunce-hukuncen shari'a da dokokinta, da ikrari da shugabancinsa. Mubaya'a kuwa tana misalta mafi girman ma'anonin hakkokin siyasa a cikin al'ummar dan Adam.
Watakila daga cikin mafi bayyanar dalili a kan gudummawar mace ta siyasa da hakkokinta na siyasa a Musulunci, akwai abin da ya zo cikin ayar `Horo da aikin kirkidahanidamummuna', da ayoyin Wilaya da gamammen shugabanci wadanda suka hada maza da mata.
Hakika babban malamin furu'a nan, gawurataccen manazarcin Musulmi Shahid Sayyid Bakir Sadar (r.a) ya kafa dalili da wannan aya a kan cewa Mumini da Mumina sun cancanci shugabancin siyasa, da cewa namiji da mace a kan wannan daya ne; ya zo cikin nassin abin da ya fada cewa:
"AI'umma na taka rawarta wajen Khalifanci a tsaikon shari'a, da dalilin ka'idoji biyu na AIKur'ani masu zuwa: 'AI'amurransu shawara ne tsakaninsu' da `Muminai maza da muminai mata kuwa, majibinta al'amarin juna ne; suna umurni da aikata alheri kuma suna hani daga mummunan aiki...' Domin nassi na tarko yana ba al'umma damar aiwatar da al'amurranta ta hanyar shawara ne matukar wani nassi na musamman bai zo da abin da ya sa6a da haka ba. Nassi nabiyu kuwa yana magana ne a kan ji6intar al'amari; da cewa kowane mumini majibincin al'amarin saura ne, saboda dalilin horo da aiki da alheri da hani da mummuna da ya biyo baya. Wannan nassi zahiri ne a kan gudanar wannan jibintar al'amari tsakanin dukkan muminai maza da muminai mata daidai wa daida. Daga nan za a iya fitar da ka'idar shawara da bin ra'ayin mafi yawa a yayin sabani. "[20]
Hakika mace Musulma ta shiga fagen siyasa a zamanin Manzon Allah (s.a.w.a.), kamar yadda ayar Bai'a ta tabbatar da haka; hakika sun shiga fagen siyasa sun kuma yi tarayya a rayuwar siyasa. Haka nan mace Musulma ta shiga kuma ta bayyana ra'ayinta game da Imamancin siyasa da Khalifanci bayan rasuwar Manzon Allah (s.a.w.a.); mafi girman dalili a kan haka shi ne matsayin Fadimatu `yar Manzon Allah Muhammadu (s.a.w.a.) kuma matar Imam Aliyu dan Abi dalibi (a.s.), wadda ta shiga fagen siyasa bayan rasuwar mahaifinta, ta kasance a gefen Aliyu cikin harkokinta da matsayinta na siyasa; har wasu taro mutane daga Muhajirai da Ansar suka hadu tare da ita; wannan ne ma ya samar da wannan kungiya ta akida da siyasa mai hamayya da bai'ar Sakifa, kuma mai kira zuwa ga sake yin mubaya'a ga Aliyu (a.s.). Hakika ta kasance tana ganawa da Ansar (mutanen Madina) a gidajensu tana neman su da su yi mubaya'a ga Aliyu (a.s.) alhali tana mai hamayya da bai'ar Sakifa.
Ya zo cikin wasu hanyoyin tarihi cewa: "Sai Aliyu ya fita yana dauke da Fadimatu 'yar Manzon Allah (s.a.w.a.) a kan dabba da daddare zuwa mazaunan Ansar, tana neman taimakonsu; su kuwa sun kasance suna cewa: Ya 'yar Manzon Allah, hafcika bai'armu ta gudana a kan wannan mutum, da mijinki kuma dan baffanki ya riga zuwa wurinmu kafin Abubakar da ba mu kauce daga gare shi ba".[21]
Haka nan tarihi ya rubuta muhawarori da matsayin siyasa na hamayya da ya gudana tsakanin Fadimatu (a.s.) da Khalifa Abubakar (r.a.) da Umar bin Khaddabi (r.a.). Ta hanyar lura da ayoyin nanbiyu (ayar Shawara da ayar Wilayar Muminai), kamar yadda bayanin fassarar su ya bayyana daga Sayyid Sadar, za mu same su a matsayin asasi na tunani mai fadi kan hakkokin siyasa; kai! wajiban siyasa ga al'umma da dukkan mutanenta maza da mata daidai wa daida.
Wata aya kuma wadda ke wajabta aikin siyasa da wajibcin Kifa'i a kan maza da mata, kamar yin tawaye wa mahukunta masu dagawa, tsayar da daular Musulunci, wayar da kan mutane ta fuskar siyasa da wasun wadannan, ita ce fadar Allah Madaukaki:
"A sami wasu mutane daga cikinku, suna kira zuwa aikata kyakkyawan aiki da hani da mummuna, wadannan su ne masu babban rabo."
AIKur'ani Mai girma a wannan aya, yana wajabta samun wasu jama'a daga Musulmi da suke kira da kyakkyawan aiki suke kuma hani da mummuna; wadannan jama'a sun hada maza da mata daidai wa daida, da dalilin fadar Allah Madaukaki:
"Muminai maza da muminai mata kuwa, majibinta al'amarin juna ne; suna umurni da aikata allied kuma suna hani daga mummunan aiki, wad'annan su ne masu babban rabo." Surar Taubati, 9:71.
Bayyanannen abu ne a tunanin Musulunci cewa fagen siyasa shi ne fage mai fadi da ya hada horo da aikin kirki da hani da mummunan aiki, wadanda suka kunshi kira zuwa tsayar da tsarin Musulunci, kalubalantar azzaluman shugabanni da karakatattun tsare-tsare na zalunci, kamar yadda suka kunshi shiga cikin gudanar da shugabanci, tsarin siyasar al'umma, wayar da kan mutane a fagen siyasa, shawara da mubaya'a kamar zaben shugaba da wakilin al'umma, shiga cikin wakilcin al'umma a majalisu da muke kira da 'majalisun wakilai', wadanda ke aikin horo da aikin kirki da hani da mummuna ta fuskar siyasa da sauran irin wadannan.
Ta hanyar nazarin yanayin zamantakewa da siyasa wadanda ya wajaba ayi aiki a tsaikonsu, za mu iya fitar da cewa wannan al'umma (ko mutane) da Alkur'ani ya yi kira da a same su da cewarsa: "A sami wasu mutane daga cikinku.." ba za su iya aiwatar da aikin su a matsayin su na mutane kamar yadda AIKur'ani ke so ba sai sun zama mutane tsararru, wadanda ke gudanar da ayyukansu ta wayayyun hanyoyi wadanda suka dace da yanayi da marhalar tarihi da Musulmi ke raye a ciki.
Wannan na nufin wajibcin shigar mace yadda ya kamata cikin jama'a da ayyukan siyasa, da cikin kungiyoyi, jam'iyyu da mu'assasosin tunani da kawo gyara dabam-dabam, matukar aiwatar da wannan wajibi kamar yadda ake bukata ya ta'azzara ba tare da haka ba.
Daga wadannan asasai na AIKur'ani za mu fahimci cewa rayuwar siyasa a Musulunci a bude take ga mace kamar yadda take bude ga namiji a dukkan matsayinsu -na wajibi Aini da Kifa'i- ko halaccin shiga cikin rayuwar siyasa da dukkan fagagenta.

Kalma Ta Karshe: Karin Bayani
A karshe: mace ba ta da hakki ko karimci sai a Musulunci, wanda ya tabbatar da ka'idojin hakkoki da karama ga daidaikun nau'in dan Adam baki daya da fadarsa:
"Hakika Mun karrama bani Adama, Muka kuma dauke su a tudu da ruwa, Muka kuma fifita su a kan da yawa daga abubuwan da muka halitta da fifita wa mai yawa."
"..kuma suna da hakkoki a kan mazajensu kamar (yadda mazajensu ke da hakkoki) a kansu da kyautatawa.."
Da fadar Manzon Allah (s.a.w.a.): "Daga cikin dabi'un Annabawa akwai son mata".[22] don haka ba abin da ya rage ga mace sai ta nemi hakkokinta kamar yadda AIKur'ani ya tanadar mata, ta kuma lizimci abin da ya wajaba a kanta kamar yadda AIkur'ani ya iyakance mata; a matsayinta na uwa, 'ya, kuma mata; kuma a matsayin ta na mutum da ke da hakkin wilaya da kauna a cikin al'umma; da ke amfani da iyawarsa na tunani, rai da jiki a wuraren alheri, tsarki da kawo gyara. Bayan ta jarabci dacin rayuwa a rudun rayuwar sha'awe-sha'awe munana a duniyar wayewar duniyanci watsattsiya.
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.

[1] Dabrisi ya I;ida n cikin Majma'al F3avan, a lokncnn da vakc fassara wannan ava, ccwa: "Waun su na mn w:asu hoclim;v"'Sai dayansu ya amfana da aikin da dayan v_ a vi mishi, d. haka sai tsavuwar duniva ta rama bisa tsari.'
[2] Darihi cikin Tafsirul-Kur'anil-Karim, da Allama Dabadaba'i cikin Tafsir al-Mizan.
[3] Wurarcn da aka ambata a sama.
[4] Ma'ajam al-Wasid.
[5] Inda aka ambata a sama.
[6] Bukhari, littafin Ladubba, babi na 27.
[7] Dokta Anwar Suldan, cikin littafin `Mabadi'ul-Kanuniyya al-Ammah', shafi na16.
[8] Hurrul Amili, cikin Wasa'ilul-Shi'ah, littafin Salla, babin hukunce-hukuncen tufafi, babi na13.
[9] Inda aka ambata a sama.
[10] Bukhari, juz'i na7, shafi na 55.
[11] Dokta Nadim Ada al Yas, cikin littafin `Sayakharul-Ma'i Thummal-Hajar, shafi na 42.
[12] Inda aka ambata a sama.
[13] Inda aka ambata a sama.
[14] Inda aka ambata a sama.
[15] Inda aka ambata a sama.
[16] Littafin da aka ambata a sama, shafi na 15.
[17] Is'aful-Ragibin, wandaaka buga a hamishin Nurul-Absar, na Shabalanji, shafi na 96.
[18] Sahih Muslim, juz'i na1>, shafi na 201, bugun Darul-lhv [19] Sunan al-Tirmiri, da Masnad Ahmad bin Hambali, juz'i na 4, shafi na s; da Khasa'is na Nasa'i, shafi na 25.
[20] Dabari, cikin Dakha'irrul-Ukba, shafi na 37.
[21] Bukhari, juz'i na3, shafi na 196.
[22] Al-Kulaini, cikin Furu'ul-Kafi, juz'i na 5, shafi na 320, bugu na 3.