Hakkokin Kawukanmu A Kanmu
Kawukanmu da gabobinmu suna da nasu hakki a kanmu[57] saboda haka haramun ne mu cutar da kanmu cutarwa ta Lahira kamar mu yi sabo da su wanda zai jawo musu azaba, haka ma cutarwa ta Duniya kamar kin cin abinci da shan ruwa, da kin shiga inuwa, da shan guba. Don haka ne ma wasu malamai suka haramta shan taba don tana cutarwa. Kodayake malamanmu suna cewa: Ba ta zama haramun da farko amma in ta kai matsayin in mutum ya sha tana cutar da shi to a nan ta zama masa haramun[58].
Mafi munin zaluntar kai shi ne hana kai sanin Allah da manzanninsa da Ilimin aikace-aikace da suka shafi Sanin Duniya da Lahira na dan Adam, idan mutum bai san Allah ba sai ya kamanta shi da halittu sai ya bauta wa Allah (S.W.T) yana mai shirka da shi.
Masu hikima suna cewa: Sanin kawukanmu ya dogara kan amsar wadannan tambayoyi ne kamar haka: Ni wanene? Daga ina nake? A ina nake yanzu? Kuma Ina za ni?.
Rayinmu tana bukatar irin nata abincin da abin shan kamar yadda jiki yake bukata, mafi dadi a ciki shi ne sanin Allah da ganawa da shi ta hanyar addu'o'i da sauran ibadoji, amma babban asasi shi ne saninsa da farko, domin in ba sanisa yaya za a gana da shi?[59] Rashin sani ko wane iri ne yana daidai da sanya rai a kurkuku ne.
Haka nan ba ya halatta ga mutum ya halakar da ransa ta kowace hanya, kamar ta hanyar ganganci da mota ko babur da kowane irin abin hawa da zai iya kaiwa ga cutar da jiki, ko kin shan magani ga maras lafiya.
Haka nan ji da gani, da hannu, da ciki, da kafa, da farjinmu, duk suna da hakki a kanmu na kada mu yi sabo da su, kuma mu nemi Duniya da Lahira da su, kuma mu nemi Ilimi da su ta hanyar gani, da ji, da tafiya wajan neman Ilimi ko neman halal, haka nan kada mu taba haram ko daukarta ko kallonta da su. Wani lokaci ana zaluntar kai ne da zaman banza har ma kana iya ganin mutum ya shantake yana ta barci wai hutawa yake yi saboda lalacewa alhali bai yi aikin komai ba. Wani kuwa yana alfahari ne da cewa babansa yana da dukiya mai yawa, sai ya zalunci kansa ba zai je ya nemi abin da zai mutunta kansa ba.

Hakkin Kiyaye Harshenmu
Ya zo a ruwayoyi cewa harshe mai dadi da kalma ta alheri sadaka ne[60], kuma ya zama wajibi a kare shi daga maganganu na karya, da hada husuma, da giba, da annamimanci. Kalma mai dadi da harshe mai hada sulhu tsakanin mutane[61] shi ne wanda Allah ya ke so. An karfafa yin hakan musamman tsakanin ma'aurata da abokan zamantakewa a matsayin al'umma.
Wani lokaci a kan samu wasu mata suna gaya wa mazajensu "Me ka taba yi mini" wato duk alherinsa maimakon godiya sai su kushe. Haka nan wasu matan idan suna magana da mazajensu kamar suna magana da wani azzalumi babu wata kalma ko magana mai dadi. Haka nan ta bangaren mazaje akwai irin wadannan mutane masu jahiltar rayuwa da manufa da hadafin yin aurensu.
Harshe ya fi komai hadari, saudayawa masu kin kasashen musulmi da masu ganin hada husuma tsakanin musulmi da 'yan'uwansu na zaman kasa daya sukan yi amfani da harshe da yada jita-jita don ganin sun kawo husuma da yaki. Kuma saudayawa irin wannan ya faru a kasashenmu da biranenmu kuma ya jawo kashe dubunnan mutane! mu sani babu wani abu da ya fi harshe santsi da hadari don haka sai a kiyaye shi.

Hakkin Kiyaye Jinmu
Ya wajaba a kiyaye ji daga sauraron haram da jita-jita musamman ga mai maganar da an san ba ta da tushe, da yawa mutanen da aka saurare su maganarsu ta zama bala'i ga al'umma da kuma ga mai sauraron. Haka nan ana son sauraron magana mai amfani kamar ta Ilimi da sauraron karatun Kur'ani (musamman ga mai ciki), kuma mai magana da kai yana da hakkin ka saurare shi idan ya gama maganarsa sai ka yi taka.

Hakkin Kiyaye Ganinmu
Ya wajaba a kiyaye gani daga haram[62] musamman kallon namiji ga mace, Musulunci ya hana kallo mai tayar da sha'awa ko kuma da nufin tayar da sha'awa, kamar yadda ya hana kallon jikin mace ajnabiyya in banda fuska da tafuka koda ba tare da nufin sha'awa ba. Haka nan yana hana mace kallon abin da maza bisa al'ada sukan rufe shi na daga jikinsu, amma in ba haka ba, ba ya zama haramun. Amma idan ya zama a matsayi na dole kamar a matsayi na magani da ba wani mai iyawa sai ajnabi to a bisa lalura ya halatta idan zai yiwu ta madubi ko ruwa, idan ba zai yiwu ba to a lokacin yana halatta da idanu[63].
Haka nan akwai abubuwan da ya halatta da wanda bai halatta ba a gani a telebijin da satalayet da bidiyo da hoto kamar tsaraici. Haka nan yana da kyau ga iyaye su kayyade wa yara lokacin kallonsu domin yakan hana su karatu, a wannan kwanaki an samu lissafi mai yawa a kasashen Yammacin duniya na kallon telebijin da ya sanya karatun yara ya yi rauni sosai.

Hakkin Yin Aiki Ga Dukkan Musulmi
1-Shari'ar Musulunci tana daukar yin aiki don samun biyan bukatun rayuwa ga mutum ko ga wanda daukar dawainiyarsa ta zama dole a kansa a matsayin wajibi, kuma ta wajabta wa wanda ake bi bashi kuma yake da ikon yin aiki da ya yi aiki don biyan bashin da yake kansa.
2-Haka nan Shari'ar Musulunci tana daukar yin aiki don yalwatawa cikin ciyarwa, samar da jin dadin rayuwa, da ayyukan alheri, a matsayin mustahabbi da take kwadaitar da mutum a kan yin su.
3-Shari'ar Musulunci ta haramta yin ayyukan da aka haramta, kamar sana'anta giya, miyagun kwayoyi, raye-raye, zina, caca, riba, da wasun wadannan, kamar yadda ta haramta duk wani aiki da yake jagora zuwa aikata haram ko da kuwa shi a kansa halal ne.
4-Shari'ar tana daukar wasu ayyuka a matsayin makaruhai a kashin kansu ko saboda wani abu daban, kamar sayar da likkafani.
5-Asalin da shari'ar musulunci take tabbatarwa game da aiki shi ne halacci, don haka yin aiki don tara dukiya ko kara kudi wani al'amari ne na halal matukar yana gudana a kan hanyar da shari'a ta halatta.
Yayin nazari da bin diddigin ma'anonin ayoyi da nassosi, a cikinsu ba zamu sami abin da ya hana mace yin aiki ba, ko ya kebe halaccin haka ga namiji, duk kuwa da cewa kwadaitar da namiji a kan aiki ya zo a cikin wasu nassosi.

Hakkin Yin Aiki Ga Matar Aure
Shari'ar Musulunci ta tanadi wasu hukunce-hukunce da suka kebanci aikin matar aure kamar haka:
1-Yana daga hakkin mace ta shardanta wa miji cewa ba zai hana ta yin aiki ba a lokacin daura aure.
2-Miji ya amince a kan aikin matarsa ta hanyar fahimtar juna tsakaninsu, wannan kuwa idan ta so yin aiki ba tare da wani sharadi da ya gabata ba kenan. Idan kuwa miji ya ki amincewa da matarsa ta yi aiki a irin wannan hali, ba yana nufin cewa shari'ar musulunci ce ta hana mace aiki ba.
3-Idan mace ta yi aure alhali ta riga ta yi yarjejeniyar aiki na wani ayyanannen lokaci da wasu to yarjejeniyar aikin ba ta baci ba koda kuwa ya sabawa hakkin miji.
4-Idan matar aure ta kulla yarjejeniyar aiki ba tare da izinin mijinta ba to ingancin wannan yarjejeniya ta dogara ne a kan yardar mijin idan aikin ya sabawa hakkokinsa, idan kuwa bai saba wa hakkokinsa ba, to yarjejeniyar tana zartuwa.
5-Hukuncin duk wata yarjejeniyar aiki da mace ta kulla tana gudana ta hanyar nazarin hukunce-hukuncen shari'a, ba zamu taba samun wani nassi da yake haramta yin aiki ga mace ba.
Masu haramta aikin mace suna bayar da dalili ne da kasancewarsa a wajen gida wanda fita yana bukatar izinin mijinta, wasu kuwa ba su amince da aikin mace cikin ma'aikatun da ake cakuda maza da mata ba saboda hakan yana haifar da fasadi da fadawa cikin abubuwan da aka haramta.
A nan ya kamata mu yi nuni da cewa aikin da yake haifar da aukawa cikin haram, haram ne ga dukkan jinsosin biyu namiji da mace, don haka matsayi na iya tilasta hana cudanyar da kuma kokarin sanya aiki a hannun jinsin namiji ko mace kamar yadda nau'in aikin yake bukata, ko samar da yanayin da zai hana kai wa ga haram. Sannan mu sani aikata haram ba ya kebanta da yin aiki idan masu aikata haram sun kasance fasikai ne.
Sa'annan ta hanyar wannan aya: "Kuma muka daukaka darajojin sashensu a kan wani sashe don wani sashen ya riki wani mai yi masa hidima.."[64]. muna iya gani cewa; bamabancin iyawa, kwarewa, da karfin aiki, yana sabawa daga wani mutum zuwa wani ba tare da la'akari da kasancewarsa namiji ko mace ba, kuma alkar musayar amfanoni da biyan bukatun rayuwa da hidima suna cika ne tsakanin daidaikun al'umma baki daya. Kuma kowane daya ba tare da la'akari da jinsinsa (namiji ko mace) ba, yana yin kokarinsa da abin da zai iya wajen biyan bukatun al'umma wanda da haka ne shi ma zai sami tashi biyan bukatar. Manomi yana gabatar da kayan noma, injiniya da masanin fanni suna sana'anta na'ura, likita yana bayar da magani, malami yana yin aikinsa na karantar da manyan gobe, dan kasuwa na samar da kayayyakin masarufi a kasuwa, soja yana kare kasa, mai gadi yana maganin barayi, da sauransu.
Darasi da nazarin hukunce-hukuncen Musulunci dukkansu zasu tabbatar mana da cewa musulunci bai haramta wani nau'i na aiki ko ilimi ga mace ba bayan ya halatta shi ga namiji, mace tana iya yin kowane irin aiki kamar noma, sana'a, likitanci, injiniyanci, gudanarwa, ayyukan siyasa, tela, tukin jirgin sama, da sauransu.
A Musulunci babu wani aiki na samar da wani abu ko hidima da aka halatta ga namiji amma aka haramta shi ga mace, kowa a shari'ar Musulunci daya ne. A kan haka bambancin kawai da yake tsakanin namiji da mace a wasu wajibai ne da aka kallafa wa namiji ko mace, ko wasu maslahohi da suka ginu a kan asasin ilimi da aka yi la'akari da yanayin halittar gabobi ga kowannensu, da kuma wajibcin tsara rayuwar zamantakewa da gudanar da ita.
Asali a shari'ar Musulunci shi ne halaccin aiki, ko wajibcinsa a wasu halaye, in banda abin da shari'a ta haramta, ko abin da yake haifar da fadawa cikin abin da aka haramta. Idan kuwa har akwai wani ra'ayin haramta aiki ga mace daga wajen wasu, to wannan yana bukatar dalili. A tsarin musulunci da abin da ya dora shi a kan musulmi na wajibai aini[65], ko kifa'i[66], ya wajabta su ne a kan maza da mata ba tare da iyakance jinsinsu ba, ya wajabta musu samar da bukatun al'umma gaba daya kamar likitanci, injiniyanci, karantarwa, noma, kasuwanci, sufuri, tsaro da sauransu na daga ayyukan da al'umma suke bukata. Kuma wajibin kifa'i yana iya sauyawa ya zama wajibi Aini a kan mutanen da ikon aiwatar da wannan wajibi ya kebanta da su ba tare da la'akari da jinsin namiji ko mace ba. Sai dai wani lokaci shari'a tana fuskantar da wajabci ga wani jinsi idan aikin ya shafe shi ne kamar aikin likita da ya kebanci haihuwa (unguwar zoma) da al'amuran da suka shafi mata.

Hakkin Harkokin Siyasa Ga Mace
Daga cikin al'amura na asasi da aka sanya a teburin tattaunawa da muhawara na tunani da wayewa a karni na ishirin akwai al'amarin hakkokin mace, daga ciki kuwa har da shigarta cikin harkokin siyasa, abin da yake bayar da mamaki shi ne, cewa wadannan masu kira ga hakkokin mace na siyasa suna fuskantar da tuhumarsu ga tunanin musulunci da akidunsa, suna siffanta su da cewa akidu ne da suka haramta wa mace shiga cikin rayuwar siyasa, kuma suke hana ta aiwatar da ayyukan siyasa. Suna dogara da yanayin zamantakewa da siyasa wadanda suke gani a garuruwan musulmi ba tare da sun tantance musulunci a matsayinsa na tsarin shari'a da dokoki ba, da kuma masu bin musulunci da suka cakuda shi da al'adunsu a a siyasa da zamantakewa[67] ba.
Sun dauka abin da suke gani a kasashen musulmi shi ne ainihin musulunci alhalin ya saba wa yadda ya kamata ya kasance cikin al'ummar musulmi. Domin mace a wadannan kasashe na musulmi da yadda ake yin mu'amala da ita da kimarta a cikin al'ummar musulmi duk sun doru bisa al'adu ne a zamantakewa, da fagagen aiki, da siyasa, da alakarta tare da namiji.
A musulunci siyasa tana nufin lura da sha'anonin al'umma a dukkan fagagensu na rayuwa da jagorancin tafiyar da su ta hanyar Musulunci. Don haka ita wani nauyi ne na zamantakewa da aka dora wa musulmi baki daya, wannan nauyi an dora shi a kan dukkan musulmi ba tare da la'akari da kasancewarsu maza ko mata ba.
Misalin fadinsa Madaukaki: " ku tsayar da Addini kuma kada ku rarraba". Surar Shura, 42:13. Da fadinsa Madaukaki: "Allah kuma ya yi wa wadanda suka bayar da gaskiya daga cikinku kuma suka yi aiki na gari alkawarin lallai zai sanya su masu mayewa a bayan kasa, kamar yadda ya sanya wadanda suka gabace su masu mayewa..." Surar Nuri, 24:55. Da fadinsa Madaukaki: "Ku bi Allah kuma ku bi Manzonsa kuma da majibanta al'amuranku (Imamai Ma'asumai)" Surar Nisa'i, 3:59.
Cikin dukkan wadannan ayoyin ana magana ne ga dukkan musulmi maza da mata, ashe kenan tsayar da Addini da Akidunsa da dukkan tsare-tsarensa na siyasa, zamantakewa, ibada da sauransu, nauyi ne a kan dukkan Musulmi, haka nan umarnin yin biyayya ga majibanta al'amura da ya zo a cikin wannan aya ya doru a kan dukkan baligai, kuma alkawarin mayewa ana fuskantar da shi ne ga dukkan wadanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka na gari maza da mata.
Fadinsa Madaukaki:"Ya kai Annabi idan muminai mata suka zo maka suna mubaya'a gareka a kan ba zasu hada wani da Allah ba, ba zasu yi sata ba, ba za su yi zina ba, ba zasu kashe `ya'yansu ba, ba zasu zo da wata karya wadda zasu kage ta tsakanin hannayensu da kafafuwansu ba, kuma ba za su saba maka cikin wani kyakkyawa ba, to ka yi mubaya'a da su, kuma ka nema musu gafarar Allah, hakika Allah Mai yawan gafara ne Mai jinkai". Surar Mumtahannati, 60:12.
Wannan wani abu ne da ya faru a aikace, kuma dalili ne na Kur'ani da Manzon Allah (S.A.W) ya aikata shi cikin rayuwarsa ta isar da sako da siyasa game da karbar bai'ar mace, kuma mubaya'a a wannan aya tana nufin biyayya ga majibancin al'amari a kan lizimtar hukunce-hukuncen shari'a da dokokinta, da ikrari da shugabancinsa. Mubaya'a kuwa ita ce mafi girman hakkokin siyasa a cikin al'umma, kuma wannan dalili ne a kan gudummawar mace ta siyasa da hakkokinta na siyasa a Musulunci.
AyatulLahi Shahid Sayyid Bakir Sadar (R.A) ya kafa dalili da wannan aya a kan cewa mumini da mumina sun cancanci shugabancin siyasa, da cewa namiji da mace a kan wannan daya ne. Ya zo cikin nassin abin da ya fada cewa: "AI'umma tana taka rawarta wajen halifanci a tsayar da shari'a, da dalilin ka'idoji biyu na Kur'ani masu zuwa: "AI'amuransu shawara ne tsakaninsu" Surar shura: 38. da ayar "Muminai maza da muminai mata kuwa, majibanta al'amarin juna ne, suna umurni da aikata alheri kuma suna hani daga mummunan aiki...' Surar Tauba: 71.
Nassi na farko yana ba wa al'umma damar aiwatar da al'amuranta ta hanyar shawara ne matukar wani nassi na musamman bai zo da abin da ya saba da haka ba.
Nassi na biyu kuwa yana magana ne a kan jibintar al'amari da cewa kowane mumini majibancin al'amarin saura ne, saboda dalilin horo da aikin alheri da hani da mummuna da ya biyo baya. Wannan nassi dalili ne na zahiri a kan gudanar wannan jibantar al'amari tsakanin dukkan muminai maza da muminai mata daidai wa daida.
Daga nan za a iya fitar da ka'idar shawara da bin ra'ayin mafi yawa a yayin sabani." Musulma ta shiga fagen siyasa a zamanin Manzon Allah (S.A.W) kamar yadda ayar bai'a ta tabbatar da haka, sun shiga fagen siyasa sun kuma yi tarayya a rayuwar siyasa.
Haka nan mace Musulma ta shiga kuma ta bayyana ra'ayinta game da jagorancin siyasa da halifanci bayan rasuwar Manzon Allah (S.A.W), mafi girman dalili a kan haka shi ne matsayin Fadimatu 'yar Manzon Allah Muhammadu (S.A.W) kuma matar Imam Aliyyu dan Abi Dalibi (A.S) wacce ta shiga fagen siyasa bayan rasuwar mahaifinta, ta kasance a gefen Aliyyu cikin harkokinta da matsayinta na siyasa har wasu taron mutane daga Muhajirai da Ansar suka hadu tare da ita. Wannan ne ma ya samar da bangaren siyasa mai hamayya da bai'ar Halifa na farko ta Sakifa, kuma mai kira zuwa ga sake yin mubaya'a ga Imam Ali (A.S).
Ta kasance tana ganawa da Ansar (mutanen Madina) a gidajensu tana neman su da su yi mubaya'a ga Imam Ali (A.S), tana mai hamayya da bai'ar Sakifa. Ya zo a cikin tarihi cewa; Sai Aliyyu ya fita yana dauke da Fadima 'yar Manzon Allah (S.A.W) a kan dabba da daddare zuwa Ansar tana neman taimakonsu, su kuwa sun kasance suna cewa: Ya 'yar Manzon Allah hakika bai'armu ta gudana a kan wannan mutum, da mijinki kuma dan baffanki ya riga zuwa wurinmu kafin Abubakar da ba mu kauce daga gare shi ba.
Haka nan tarihi ya rubuta muhawarori da matsayin siyasa na hamayya da ya gudana tsakanin Fadima da halifa Abubakar da Umar Dan Khaddabi.
A musulunci fagen siyasa fage ne mai fadi da ya hada da horo da kyakkyawan aiki da hani daga mummunan aiki wadanda suka kunshi kira zuwa tsayar da tsarin musulunci, da kalubalantar azzaluman shugabanni, da karkatattun tsare-tsare na zalunci, kamar yadda suka kunshi shiga cikin gudanar da shugabanci, da tsarin siyasar al'umma, wayar da kan mutane a fagen siyasa, shawara da mubaya'a kamar zaben shugaba da wakilan al'umma, shiga cikin wakilcin al'umma a majalisu da muke kira da 'majalisun wakilai, wadanda suke aikin horo da kyakkyawa da hani daga mummuna ta fuskar siyasa.
Wannan yana nufin wajibcin shigar mace yadda ya kamata cikin jama'a da ayyukan siyasa, da kungiyoyi, da jam'iyyu, da cibiyoyin tunani, da kawo gyara, matukar aiwatar da wajibai kamar yadda ake bukata ya ta'azzara.
Daga wadannan asasai na Kur'ani zamu fahimci cewa rayuwar siyasa a musulunci a bude take ga mace kamar yadda take bude ga namiji a dukkan matsayinsu na wajibi Aini da Kifa'i, ko halaccin shiga cikin rayuwar siyasa da dukkanin al'amura na zamantakewar al'umma.
Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai

Masdarorin Madogarar Wannan Littafin:
Kur'ani mai girma
Sharhu risalatil hukuk
Tauhid, saduk
Al'intisar, amuli
Ma'asatuz Zahara, murtadha amuli
Alwilayatut takwiniyya alhakkud dabi'I lilma'asum, jalal sager
Nahajul balaga
Aka'idul imamiyya
Usulul kafi
Biharul anwar, Allama majlisi
Hudubar imam khomaini 15 sha'aban 1400
Mikyalul makarim, Muhammad taki al'asfahani
Namazijun min karamatil ayimma wa mu'ujizatihim, markazul musdapha
Ruzgare rahayi
Ba'adhu ma warada min siratil imam Hasan Askari (A.S)
Murkazul musdapha, min zulamatihim fi a'hdi banil Abbas
Asshabus sawakib, Muhammad Ali Abduljabbar
Nahajul imani, Ibn hajar
Masharikul yakin
Assiradul mustakim
Misbahul mutahajjid, shaikh Dusi
Minhajul karama, allama hilli
Muhadharatun fil ilahiyyat, bahasu fi as'ilatin haulal mahadi, subhani
Sharhu ihkakul hakk, mar'ashi najafi
Salim bn Kais
Sharhu Risalatil hukuk
Muniyyatus sa'il, almasa'ilul mutafarrika, sayyid Khu'I
Siradun najat, Mirza Jawad tabrizi
Masharikul anwaril yakin
Markazul musdapha, minal a'amalil lati tujibul janna wannari
Raudhatul wa'izin, al'fitalin naisaburi
Masnad Ahmad bn Hambal
Al'baharur ra'ik, ibn Najimul misri
Takmilatu hashiyati raddil mukhtar, Ibn Abidin (Ala'ud din)
Almabsud, shaikh Dusi
Al'mu'utabar, muhakkikul hilli
Al'wasa'il
Munyatut dalib, na'ini
Wilayatul fakih, musdapha khomaini
Nahajul balaga, ibn abil hadid
Tazkiratul fukaha', allama hilli
Fikihus Sunna, sayyid sabik
Al'majmu'u, nawawi
Sharhin akhbar, alkali Nu'uman almagribi
Al'amali, Shaikh Dusi
Raushatul wa'izin, al'fitalun naishaburi
Zubdatul bayan, muhakkikul ardabili
Al'hada'ikun nadhira, baharani
Kitabul hajj, sayyid Khu'I
Tafsirul kur'anil karim, sayyid musdapha
Samarud dani, Azhari
Al'intisar, sharif murtadha
Makatibur rasul, ahmadi miyanji
Markazur risalatil hukukul ijtima'iyya
Tafsirul Ayashi
Kanzul ummal
Hashiyatu majma'ul fawa'id wal burhan, bahbahani
Kitabuddahara, ansari
Jawahirul kalam, jawahiri
Mizanul hikima, Raishahari
Tahrirul wasila, imam khomaini
Raddi Kan Sukan Auren Mace Fiye Da Daya.