Hakkokin Mutane Game Da Arzikin Kasa
Haka nan talaka ba ya ganin ma yana da hakki a arzikin kasa, in banda 'yan kwanakin nan da wasu 'yan kadan suka san hakan, al'amarin har ya kai ga wasu daga masu tafiyar da al'amarin al'umma suna neman jahiltar hakan. Saudayawa mai mulki ba ya kiyaye hakkin wanda yake mulka game da arziki da albarkatun kasa, idan kuwa ka ce zaka yi magana kan sauran kayan rayuwa a nan kam sai dai ka mutu da bakin ciki. Duba ka ga wutar lantarki, da ruwan famfo, da man fetur da kasar nan take ita ce ta biyar a duniya a yau. Kuma duba ka ga wasu kasashe da mun fi su karfin tattalin arziki amma ba su da wata matsalar irin wadannan abubuwan rayuwa, man fetur kuwa a wajensu kusan mafarki ne wani ya ce ya ga dogon layi ko babu, kuma a gidaje akwai wuyarin na wutar lantarki da fayef na famfo da na Gas, wannan kuwa duk sun yi shi ne cikin shekaru kadan. Kuma mutanensu suna biyan kudi kankani ne domin duk talaka yana iya biyan kudin. Haka ma a gidaje akwai kayan sanyaya gida a lokacin zafi kuma da abin dumama daki lokacin sanyi, amma wadannan abubuwan a kasarmu a gun talaka wani kayan masu jin dadi ne.
Wani abin kunya da dan Nijeriya yake sha a duniya shi ne; ga shi kasar a waje tana da kima saboda suna jin labarin tana da arziki, amma hatta da gasar kwallon kafar da aka yi a kasar sai ana yi ana dauke wuta. Irin wannan al'amarin ya faru wata rana yayin da muka isa tashar jiragen sama ta Kano, ga fankokin kansu suna bayar da zafi ne amma duk wannan bai isa ba sai aka dauke wuta, wani mutum (ba dan Nijeriya ba ne) ina ji ya ce: Kai ka ga Air port sai ka ce kango. Haka nan ake tara wa 'yan kasar abin kunya a kasashen waje kai ka ce masu mulki ba sa zuwa wasu kasashe suna ganin abin da yake faruwa.

Hakkokin Mutane A Kotuna
Idan kuwa ka waiwaya kotu abin ya yi muni sosai, amma akwai ma'auni na gane kotun zalunci da kotun adalci, Idan ka ga kotu mai kudi da sarki suna jin tsoronta to ana adalci ne kuma ana bin gaskiya ne, amma idan ka ga talaka kawai ne yake tsoron kotu to ka sani ana zalunci ne. Wani lokaci akan ja shari'a da ya kamata a yanke ta a sati ko awowi kadan amma sai ta yi watanni da shekaru har ma mai hakki ya ce ya yafe, ko ya gaji ya bari don kansa. Wani lokaci hakkin yana rutsawa da kudin marayu ne amma sai ka ga kotu ta ajiye a banki tana samun kudin ruwan, wani lokaci ma ba ya isa sai an diba daga hakkin maraya an sa a aljihu. Wani lokaci kuma akan iya mirgide gaskiya ko jifa da hauka ga wani don wani ya kubuta, da haka ne hakkoki masu yawa na mutane suke salwanta.

Hakkin Malami A Kan Dalibi
Malami yana da hakki a kan dalibi, a takaice muna iya cewa: a girmama shi, da sauraronsa idan yana magana, da barinsa ya amsa tambayar da wani ya yi masa, da kaskantar da kai a gare shi, da kare shi daga mai sukansa, da rufa asirinsa ko aibinsa, da yada kyawawansa da alherinsa, kada ka zauna da makiyinsa, kada ka yi gaba da masoyinsa.

Hakkin Dalibi A Kan Malami
Malami ya tausaya wa dalibai kuma ya san cewa su 'ya'yansa ne don haka yana neman tsiransu ne, kada kuma ya taba yi musu gori ko kausasa musu hali. Kuma ya rika yi musu nasiha, ya nisantar da su daga miyagun halaye, kada ya muzanta musu wani ilimi da ba a wajansa suke koyonsa ba, kamar idan shi malamin nahawu ne to kada ya rika kushe musu Ilimin mandik, ya rika yi musu magana daidai fahimta da kwakwalwarsu, kada ya yi musu rowa ta Ilimi.

Hakkin Mace A Kan Mijinta
Daga cikin hakkin mace a kan mijinta shi ne ya girmamata, kuma ya tausaya mata da tausasawa, ya ciyar da ita, idan ta yi laifi ya yafe mata, kada ya la'ance ta ko ya zage ta ko ya doke ta, kada ya muzanta ta ko ya kunyata ta ko ya daidaita mata asiri.
Haka nan akwai hadisai da dama da suka zo game da falalar mutumen da yake taya matarsa aikin gida, don haka bai kamata ba al'ada ta rinjayi Addini, don wasu sukan ki hakan saboda wani dalili maras ma'ana na al'ada.
Dole ne miji ya yi adalci ga matarsa da tsakanin 'ya'yansa da matansa, kamar yadda yake wajibi a kansa ya nuna mata soyayyarsa, kuma ya nuna mata wannan a fili ta yadda zata zama abokiyarsa a komai. Kuma ya rika yi mata maganganu irin na soyayya da nuna kauna ga juna, bai isa ba ya ba ta kudi kawai don yana da shi, wannan ba ya isa ga bukatun mace. Shi ya sa Allah (S.W.T) ya fada a cikin littafinsa cewa: "Ya sanya soyayya (kauna) da tausayi (rahama) a tsakaninku"[39].
Haka nan ba shi da kyau ga miji ya munana zato ga matarsa, ko ba komai munana zato ga musulmi haramun ne, idan mace ta san mijinta yana munana mata zato alhalin tana mai kame kanta wannan yana iya rusa alakar soyayya da girmama juna da ke tsakaninsu har ya kai su ga rabuwa.

Hakkin Miji A Kan Matarsa
Daga cikin hakkin miji a kan matarsa shi ne: Kada ta ki shimfidarsa in ya neme ta, kada ta bayar da izinin shiga gidansa ga wanda ba ya son shigarsu, kada ta yada sirrinsa ko ta yi masa barnar dukiya, ta kula da yaransa da kuma ayyukansa na gida da suka shafeta, kada ta kausasa masa harshe, ta yi kokarin faranta masa rai. Sannan ta rika ba shi uzuri a kan wasu al'amuran, kada ta yi abin da zai sa shi ya ji baya son zama da ita a gida ko abin da zai sanya shi nisantar hira da ita ko kaurace mata.
Wasu ruwayoyi sun kawo hakkin miji kan matarsa kamar haka: Yayin da wani sahabi ya ba wa Manzon Allah (S.A.W) labari cewa: Yana da mata da idan ya kalle ta sai ta faranta masa rai, idan ya shiga gida da bakin ciki sai ta yaye masa shi, idan kuwa ba ya nan tana kare shimfidarsa ba ta ha'intarsa, kuma ta kare dukiyarsa da kula da tarbiyyar 'ya'yansa. Sai Manzon Rahama (S.A.W) ya ba shi amsa da cewa: "Allah yana da ma'aikata, kuma wannan matar tana daga cikin masu aikin Allah, kuma tana da rabin ladan shahidi"[40]. Haka nan wata ruwaya ta nuna cewa: "Mace mai aiki a gidan miji daidai take da wanda yake Jihadi a tafarkin Allah"[41].
Haka nan dole ne ta yi biyayya a gare shi[42] domin shi shugaba ne a gida babu kuma yadda mutane biyu zasu hadu a wuri ba tare da shugaba ba, ta sani rashin biyayya a gare shi yana rusa masa ruhinsa da karya masa zuciya, sai ya fara tunanin daukar fansa sai gaba ta faru, kuma zamansu ya gurbace, ko kuma wannan fushin ya tura shi ga miyagun halaye da kuma yawan fusata da fada.
Kada wata mata ta rika gasa da wasu mata ta ce: An saya wa kawata kaza kai ma sai ka yi min kaza wannan ko kadan ba shi da kyau. Yana da kyau mata su dauki samfurin rayuwar zamantakewa daga Imam Ali (A.S) da sayyida Zahara (A.S), ga wani misali daga irin wannan; Wata rana Imam Ali (A.S) ya shiga wajan Fadima (A.S) sai ya tambaye ta ko tana da wani abu sai ta ce: "Wallahi kwana uku ke nan ya Dan Ammina ba mu da komai". Sai ya ce: "Me ya sa ba ki gaya min ba" Sai ta ce: "Manzon Allah ya hana ta tambayarsa, ya gaya mata cewa: Kada ki tambayi Dan Amminki (Imam Ali) komai, idan ya kawo, in ba haka ba, kada ki tambaye shi".[43]
Duba ki ga irin wannan rayuwa ta gidan Ahlul Bait (A.S) wacce hatta abin da yake wajibi a kan miji ba ta tambaya sai idan ya kawo, saboda haka yana da kyau mata su kamanta daidai gwargwado, kamar yadda maza su kuma su kiyaye ba kwauro ba barna.

Hakkokin Iyaye A Kan 'Yaya
A nan saboda girma da muhimmancin hakkin iyaye a kan 'ya'yansu babu wani abu da zamu ce sai dai; duk abin da kasan zaka yi in dai bai saba wa shari'a ba don faranta masu rai to wannan abin ka yi shi, idan kana da da zaka iya gano sirrin haka, duba ka ga danka da wahalar da kake sha a kansa, wannan kuwa bai kebanta da mai da ba domin hankali yana iya fahimtar wahalar rayuwa da iyaye suke sha a kan 'ya'ya.
Akwai hadisai masu yawa da suka zo game da girmama iyaye da kuma biyayya a gare su kamar haka;
1-Wanda ya yi kallo zuwa ga iyayensa kallo na rahama Allah zai rubuta masa ladan aikin Hajji[44].
2- Wanda ya kalli iyayensa kallo na wulakanci Allah ba zai karbi sallarsa ba koda kuwa sun kasance suna masu zaluntarsa ne[45].
3- Umarnin iyaye ana gabartar da shi a kan wajibi kifa'i[46].
4- Kada a daga sauti kan sautin iyaye ko gabata gaba gare su[47].

Hakkokin 'Ya'ya A Kan Iyaye Daga nasihohi tattararru da suke cikin wasu hadisai su ne; Kada ka fusata danka ba tare da hakkin shari'a ba, wannan yana iya sanya masa jin haushi, da son barna, da daukar fansa, da nisantar gida ta hanyar kusantar mutanen banza. Haka nan an yi wa uba da yake tura dansa cikin biyayyar iyaye saboda kyawawan dabi'unsa rahama [48]. Game da tausasawa cikin mu'amala wannan ya zo cewa, sauki shi ne yake kawata komai[49], tsanantawa ita ce take bata komai, haka nan mata da 'ya'ya ana son a biyar da su daidai yadda zasu iya da gwargwadon karfinsu, kuma a yarda da dan kadan da zasu iya ba kausasawa ko tsanantawa. Game da girmama 'ya'ya a mu'amala ya zo cewa; Manzon Rahama (S.A.W) idan Fadima (A.S) ta shigo Gidan yakan tashi daga wajansa, ya kama hannunta, ya sumbance ta, ya zaunar da ita kan shimfidarsa[50].
A daidaita tsakanin 'ya'ya hatta a kallo: Da uba zai rika yi wa wannan kallon wulakanci ba dalili, amma wancan kuma ana lallashinsa to ba abin da wannan zai haifar sai kaiwa ga tarwatsawa da rarraba tsakanin 'ya'yan[51]. Annabi Ya'akub (A.S) ya kasance a aikace ba ya rabawa tsakanin 'ya'yansa, ba ya fifita wani a kan wani a aiki da mu'amala, amma ya kasance yana nuna wa Yusuf (A.S) soyayya domin Allah ya zabe shi, Sannan shi ne salihi a cikinsu da shi da dan'uwansa, kuma shi ne karami yana da hakkin soyayya da akan nuna wa yara. Amma da yake 'yanuwansa mujrimai ne sai wannan ya sanya haushi ya rike su suka nemi kashe Annabin Allah su huta saboda soyayyar da yake da ita ta musamman wajan Annabin Allah Ya'akub (A.S), Sannan suka zo suka yi karya da kyarkeci don cimma mugun kaidinsu. Wannan mun kawo shi ne domin kare Annabi Ya'akub (A.S) da barrantar da shi daga zunubi ko laifi da wasu suke jinginawa gareshi.
Kyautata sunan 'ya'ya da sanya musu sunan Annabawa da wasiyyansu; kamar Muhammad da Ibrahim da Ali, ko kuma sunan da aka danganta zuwa ga Allah kamar Abdullahi da AbdurRahman, ko sunan salihan bayi kamar Fadima da Maryam da Khadija ko Lukman. Haka nan tarbiyyar 'ya'ya tana daga wajibi na farko a kan iyaye kamar yadda ya zo a Hadisai.

Hakkokin Dan'uwa A Kan Dan'uwansa
Da farko muna iya cewa musulmi duka 'yan'uwan musulmi ne saboda haka hakkin da yake hawa kan dan'uwa yana hawa tsakaninsu amma dan'uwa na jini yana da kari kan dan'uwa na musulunci da kamar wajabcin sadar da zumuncinsa. Daga cikin hakkokin dan'uwa a kan dan'uwansa su ne: Yi masa nasiha da kare shi daga wahalhalun da zaka iya taimaka masa wajan maganinsu kamar taimakonsa wajan sana'a, da samun magani, da kudin makaranta, da biyan bukatunsa, da kokarin kawar masa da talauci, da taimakonsa a kan makiyinsa.
Malam Muzaffar a Littafinsa yana cewa: Daga cikin mafi girma da kyawun abin da Musulunci ya yi kira zuwa gareshi shi ne 'yan'uwantaka tsakanin musulmi a kan duk sassabawarsu da martabobinsu da mukamansu. Kamar yadda mafi munin abin da musulmi suka yi a yau da kuma kafin yau shi ne, sakacinsu wajan riko da wannan 'yan'uwantaka ta musulunci.
Domin mafi karancin koyarwar wannan 'yanuwatakar ita ce "Ya so wa dan'uwansa musulmi abin da yake so wa kansa, kuma ya ki masa abin da yake ki wa kansa, kamar yadda zai zo a hadisin Imam Sadik (A.S).
Ka duba ka yi tunani a kan wannan dabi'a mai sauki a mahangar Ahlul Baiti (A.S), za ka samu cewa yana daga mafi wahalar abin da zaka iya samu wajan musulmi, da musulmi zasu yi wa kansu adalci su san addininsu sani na hakika, su yi riko da wannan dabi'a ta so wa dayansu dan'uwansa abin da yake so wa kansa, da ba a ga zalunci daga wani ba ko ketare iyaka, ko sata, ko karya, ko yi da wani, ko annamimanci, ko zargi da mummuna, ko suka da karya, ko wulakanci, ko girman kai.
Idan da musulmi sun tsaya sun fahimci mafi karancin ma'anar hakkin 'yan'uwantaka a tsakaninsu kuma suka yi aiki da ita, da zalunci da ketare iyaka sun kau daga bayan kasa, kuma da ka ga 'yan Adam sun zama 'yan'uwa suna masu haduwa da juna cikin farin ciki, kuma da mafi daukakar sa'adar zamantakewa ta cika garesu, kuma da mafarkin malaman falsafa na da na samar da mafificiyar hukuma ya tabbata, da sun kasance masu musayar soyayya a tsakaninsu, da ba su bukaci wasu hukumomi da kotuna ba, ko 'yan sanda, ko kurkuku, ko dokokin laifuffuka, da dokokin haddi da kisasi ba, kuma da ba su rusuna wa 'yan mulkin mallaka ba, kuma da dawagitai ba su bautar da su ba, kuma da kasa ta canja ta zama aljannar ni'ima kuma gidan sa'ada.
Bugu da karin cewa, da dokokin soyayya sun jagoranci rayuwar 'yan Adam kamar yadda Addini yake so na koyarwar 'yan'uwantaka, to da kalmar neman adalci ta bace daga harsunanmu da ma'anar cewa, ba za mu zamanto muna bukatar adalci da dokokinsa ba ballantana har mu bukaci amfani da kalmarsa, saboda dokokin soyayya sun isar mana wajen yada alheri, da aminci, da sa'ada, da murna, domin mutum ba zai bukaci amfani da adalci ko dokoki ba, sai idan ya rasa soyayya daga wanda ya wajaba ya yi masa adalci, amma a wajan wanda yake nuna masa kauna da soyayya, kamar da, da dan'uwa, sai dai ya kyautata musu ya hakura da dama daga abubuwan da yake so, duk wannan sakamakon so da kauna ne daga yardar zuciya, ba don adalci ko masalahar kansa ba.
Sirrin haka kuwa shi ne cewa mutum ba ya so sai kansa da kuma binda ya dace da kansa, kuma mustahili ne ya so wani abu ko wani mutum da yake wajen ransa, sai dai idan yana da alaka da shi, kuma ya shiga ransa. Kamar kuma yadda yake mustahili ne ya sadaukar da zabin kansa gareshi a cikin abin da yake so yake kuma kauna saboda wani mutum da ba ya sonsa, ba ya kuma kaunarsa, sai dai idan yana da wani imani mai karfi da ya fi karfin son ransa, kamar imani da kyawun adalci da kyautatawa, a yayin nan yana iya sadaukar da dayan abubuwan da yake so, ya yi fansa da shi saboda son wani.
Farkon madaukakan darajoji da suka wajaba musulmi ya siffantu da su, su ne; ya kasance yana jin hakkin 'yan'uwantaka ga sauran mutane, idan kuwa ya kasa wannan, to zai gaza aikata mafi yawa da haka saboda galabar son ransa, saboda haka yana wajaba a kansa ya cusa wa kansa akidar son adalci, da kyautata biyayya ga shiryarwar musulunci, idan kuwa ya gaza hakan to bai cancanci ya zama musulmi ba sai dai a suna, kuma ya fita daga soyayyar Allah (S.W.T), kuma Allah ba ya da wani buri a kansa kamar yadda zai zo a hadisi mai zuwa.
Saudayawa sha'awar mutum takan yi galaba a kansa, sai ya zamanto mafi wahalar abin da yake fama da shi, shi ne, ransa ta yarda da adalci, balle kuma ya samu imani cikakke da ya fi karfin sha'awarsa.
Saboda haka ne ma kiyaye hakkin 'yan'uwantaka ya zama daga mafi wahalar koyarwar addini idan babu imani na gaskiya game da 'yan'uwantaka. Don haka ne imam Abu Abdullah (A.S) ya ji tsoron yi wa sahabinsa "Almu'ula Bn Khunais" bayanin tambayarsa game da hakkin 'yan'uwantaka sama da abin da ya kamata ya bayyana masa, domin tsoron kada ya koyi a bin da ba zai iya aiki da shi ba.
Sai Mu'ula ya ce[52]: Menene hakkin musulmi a kan musulmi?
Sai Abu Abdullahi ya ce: yana da hakkoki bakwai wajibai, babu wani hakki daga cikinsu sai ya wajaba a kansa, idan ya tozarta daya daga ciki to ya fita daga soyayyar Allah da biyayyarsa, kuma Allah ba shi da wani buri a gareshi.
Sai na ce masa: A sanya ni fansa gareka! Mecece?
Sai ya ce: Ya Mu'ula ni ina mai tausasa wa gareka, ina tsoron ka tozarta ba zaka kiyaye ba, ko kuma ka sani ba za ka aikata ba.
Na ce: Babu karfi sai da Allah.
Yayin nan sai Imam (A.S) ya ambaci hakkoki bakwai, bayan ya fada game da na farkonsu cewa: "Mafi saukin hakki daga cikinsu shi ne ka so wa dan'uwanka kamar yadda kake so wa kanka, ka kuma ki masa abin da kake ki wa kanka".
SubhanalLahi! Wannan shi ne hakki mai kankanta, to yaya wannan hakkin mafi kankanta yake a garemu yau mu musulmi? Kaicon fuskokin da suke da'awar musulunci amma ba sa aiki da mafi kankantar abin da ya wajaba na daga hakkokinsa. Abu mafi ban mamaki kuma shi ne, a dangata wannan rashin ci gaban da ya samu musulmi ga musulunci, alhalin laifi ba na kowa ba ne sai na wadanda suke kiran kansu musulmi amma ba sa yin aiki da mafi karancin abin da ya wajabta musu da su yi aiki da shi na koyarwar addininsu.
Domin tarihi kawai, kuma don mu san kawukanmu da takaitawarta zamu ambaci wadannan hakkoki bakwai wadanda Imam (A.S) ya bayyana su:
l- Ka so wa dan'uwanka musulmi abin da kake so wa kanka, kuma ka ki masa abin da kake ki wa kanka.
2- Ka nisanci fushinsa, ka bi yardarsa, kuma ka bi umarninsa.
3- Ka taimake shi da kanka, da dukiyarka, da harshenka, da hannunka, da kafarka.
4- Ka zamanto idonsa, dan jagoransa, kuma madubinsa.
5- Kada ka koshi, shi kuma yana cikin yunwace, kada ka kashe kishirwarka shi kuma yana jin kishirwa, kada ka zama a suturce shi yana tsirara.
6- In kana da mai hidima shi kuma dan'uwanka ba shi da mai hidima, to wajibi ne ka tura mai hidimarka, sai ya wanke masa kaya, ya dafa masa abinci, ya gyara masa shimfida.
7- Ka kubutar da rantsuwarsa, ka amsa kiransa, ka gaishe da maras lafiyarsa, kuma ka halarci jana'izarsa. Idan kuwa ka san yana da wata bukata sai ka yi gaggawar biya masa ita, kada ka bari har sai ya tambaye ka, sai dai ka gaggauta masa.
Sannan ya rufe maganarsa da cewa: "Idan ka aikata haka to ka hada soyayyarka da soyayyarsa, kuma soyayyarsa da soyayyarka".
Akwai hadisai da yawa da suka kunshi ma'anar da ta zo a wannan hadisi daga imamanmu (A.S), wasunsu daga littafin Wasa'il a babobi daban-daban.
Tayiwu wasu su yi tsammanin cewa abin nufi da 'yanuwantaka a hadisin Ahlul Baiti (A.S) ya kebanci tsakanin musulmi ne wadanda suke daga mabiyansu a kebance, amma komawa ga ruwayoyinsu yana kawar da wannan zato, koda yake sun kasance ta wani bangare suna tsananta musantawa ga wanda ya sabawa tafarkinsu kuma ba ya riko da shiriyarsu. Ya wadatar ka karanta hadisin Mu'awiya Dan Wahab da ya ce[53]:
Na ce masa[54]: Yaya ya kamata gare mu mu yi tsakaninmu da mutanenmu, da kuma wadanda muke cudanya da su na daga mutane wadanda ba sa kan al'amarinmu".
Sai Ya ce: "Ku duba Imamanku wadanda kuke koyi da su ku yi yadda suke yi, na rantse da Allah! su suna gaishe da maras lafiyarsu, suna halartar jana'izarsu, suna ba da shaida garesu da kuma a kansu, kuma suna bayar da amana garesu".
Amma 'yan'uwantakar da Imamai suke son ta daga mabiyansu, tana saman wannan 'yan'uwantaka ta musulunci, Kuma ya isar ka karanta wannan muhawara tsakanin Abana Bn Taglib da Imam Sadik (A.S) daga hadisin[55] da Abana ya rawaito da kansa yana mai cewa: Na kasance ina dawafi tare da Abi Abdullah (A.S) sai wani mutumi daga cikin mutanenmu ya bujuro mini wanda ya riga ya tambaye ni in raka shi wata biyan bukatarsa, sai ya yi mini ishara, sai Abu Abdullahi (A.S) ya gan mu.
Sai ya ce: Ya Abana kai wannan yake nema?
Na ce: Na'am.
Ya ce: Shin yana kan abin da kake kai?
Na ce: Na'am.
Ya ce: Maza ka tafi zuwa gare shi ka yanke dawafin.
Na ce: Koda ya kasance dawafin wajibi?
Ya ce: Na'am.
Abana ya ce: Sai na tafi, bayan nan -wani lokaci- sai na shiga wajansa (A.S) na tambaye shi game da hakkin mumini. Sai ya ce: Bari kada ka kawo wannan! Ban gushe ba ina sake tambaya har sai da ya ce: Ya Abana ka raba masa rabin dukiyarka, sannan sai ya kalle ni ya ga abin da ya shige ni, sai ya ce: Ya Abana ashe ba ka san Allah ya riga ya ambaci masu fifita wasu a kan kansu ba?
Na ce: Haka ne!
Ya ce: "Idan ka ba shi rabin dukiyarka ba ka fifita shi ba, kana fifita shi ne kawai idan ka ba shi daya rabin!
Na ce[56]: hakika a yanayinmu mai ban kunya bai dace ba mu kira kanmu muminai na hakika. Mu muna wani waje ne, koyarwar Imamanmu (A.S) tana wani wajen. Kuma abin da ya Shigi zuciyar Abana zai Shigi zuciyar duk mai karanta wannan hadisin, sai dai ya juya fuskarsa kawai yana mai mantar da kansa shi kamar wani ake wa magana ba shi ba, kuma ba ya yi wa kansa hisabi irin na mutumin da yake abin tambaya.