Hakkin Imami (Shugaban Zamani) A Kannu
Sanin Imamin lokacinmu yana daga cikin hakkokin Allah a kanmu, domin duk wanda ya mutu bai san Imamin zamaninsa ba ya yi mutuwar Jahiliyya[18], haka nan ya zo a Kur'ani mai girma cewa a Ranar Lahira kowace al'umma za a kira ta tare da imaminta ne[19]. Wadannan imamai Allah bai bar mu mun zabe su da kanmu ba sai da ya shelanta su ta hannun Manzonsa (S.A.W)[20] wanda ya sanar da mu cewa su goma sha biyu ne: Na farkonsu Ali (A.S) na karshensu Mahadi (A.S) wanda yake shi ne imamin wannan zamanin.
Sanin Imam ba wai kawai sanin sunansa ba ne, saninsa ya hada da binsa kuma da koyi da abin da ya bari na wasiyyarsa kuma da bin koyarwarsa da malaman da suke shiryarwa zuwa ga abin da ya bari da kin makiyansa[21]. Al'amarin ba wasa ba ne kamar yadda wasu suke dauka domin ko Salla da Azumi da duk wata ibada idan babu mika wuya ga Imami Allah ba ya karba. Manzon tsira (S.A.W) ya ce: "Wanda ya mutu bai san Imaminsa ba ya yi mutuwar Jahiliyya"[22]. Domin zai tashi a Ranar Lahira kamar wanda ya yi zamani kafin a aiko Annabi ba shi da komai da Allah (S.W.T) ya karba daga gare shi.

Hakkokin Littafin Allah A Kanmu
Karanta littafin Allah da saninsa suna daga cikin hakkokinsa a kanmu, amma sanin littafin ba yana nufin mu san sunansa ba kawai domin hakan ko kadan ba shi da wata ma'ana, amma abin nufi shi ne ya zama mun siffantu da Kur'anin a aikace. Idan ba haka ba a ranar lahira akwai kara da zai shigar a kotun Allah[23] wacce ba a zalunci a nan kuma ba a iya boye gaskiya. Kuma dole a bi shi kamar yadda Manzo da wasiyyansa goma sha biyu daga Alayensa suka fassara domin su ne ya ce: "Idan an yi riko da su ba za a taba bata ba har abada". kuma "Da Su da Littafin Allah ba sa rabuwa har sai sun riske shi a tafki"[24].
Haka nan al'amarin yake a matsayin al'umma, dole ne Littafin Allah ya yi iko da rayuwarmu a matsayin al'umma, in ba haka ba, ba mu sauke nauyin da yake kanmu ba. Kuma dole ne mu siffantu da shi, in ba haka ba, yana da hakkin karar cewa musulmi sun bijire masa.

Hakkokin Addini A Kanmu
Addinin Musulunci yana da hakki na kare shi a kan kowane musulmi da bakinsa da basirar da Allah ya ba shi, da wajabcin saninsa da taimakawa wajan yada shi a aikace[25] da baki da kyawawan dabi'u, da kokarin hada kan mabiyansa, da raddi cikin hikima ga masu gaba da shi, da girmama fahimtar ma'abotansa don ba ka sani ba ta yiwu shi mai waccan fahimtar da ta saba da taka shi ne yake a kan daidai.
Kada mutumin da bai fahimta ba ko bai sani ba ya tsoma baki da jayayya a kan mas'alolin Addini[26] wannan na malamai ne, kamar yadda shehu Usman dan fodiyo (R.A) ya yi nuni da haka yayin da yake nuni da bidi'oin da aka farar cikin Addini da cewa: Shi malami kada ya sa mutane cikin rikicin Addini haka ma maras Ilimi kada ya sanya kansa cikin rikicin Addini, bayyana ra'ayi kan mas'aloli abu ne na malamai.

Hakkokin Garuruwa Ne A Tsaftace Su
Rashin kula da tsafta daga bangaren gwamnati da kuma al'umma yana daga cikin mummunan al'amari da addabi birane da kauyuka, ta yadda zaka ga duk ko'ina ana iya zuba shara[27]. Ga mummunan tsarin da garuruwa suke fama da shi, sai a sayar da hanyoyi har da hanyar ruwa ta yadda damina da kwararar ruwa zasu wahalar da talaka, ga karancin manyan hanyoyi da matsattsun kananan lunguna[28]. Idan kuwa damina ta zo talakawa suna fargaba ne, ga miyagun lunguna da kududdufai marasa hanya, amma ba za a rushe gidaje a fadada hanyoyin ruwa da na motoci da yin kwatami don samar da magudanar ruwa ba.
Mafi girman abin takaici shi ne abin da na gani a Jami'ar Bayaro da na dade ban ga irinsa ba, sai na ga takardu a ko'ina a kasa, matattakala duk da tabo ta yi bakin kirin, muna tsaye muna hira sai wani ya watso ruwa daga sama duk ya kusa bata mu, idan kuwa ka wuce wasu wurare wari yana tashi. Sai na fara tunanin Jam'iar Tehran da wuri ne kodayaushe kamar ka sanya abincinka a kasa ka ci, na rika tunanin cewa a yanzu da wani zai zo daga abokanmu daga Jami'ar ya ga wurin kwanan dalibai kawai da an ji kunya. Kuma da zaka tambaya a kan me aka gina imani? Daya daga mafi muhimmancinsu ita ce tsafta: Hatta ma wasu hukunce-hukuncen Allah yakan sanya su ne domin kai wa ga cimma samuwar tsafta a cikin al'umma.
Ba ma jami'a ba, a irin wadannan kasashe a cikin gari duk wani yanki a kowane dare yana da motoci na musamman wadanda da dare sukan wanke titinan yankin. Amma wani abin takaici a kasarmu ba ma kawai tsaftar gari ba, kana iya ganin yanki da miliyoyin mutane suke rayuwa ba tare da wani isasshen ruwan sha ba.

Hakkokin Da Suke Tsakanin Mutane
Kowane mutum yana da hakkoki masu yawa a kan dan'uwansa mutum musamman abokin zamantakewa na kasa ko gari, ko makaranta, da duk wani waje da alaka ta kan hada juna kamar wajan aiki. Babban ma'auni na hakkin junanmu a kanmu shi ne wanda ya zo a cikin Hadisai na cewa: "Mu duba duk abin da muke so a yi mana sai mu yi wa mutane shi, mu kuma duba duk abin da muke ki a yi mana shi sai mu guji yi wa mutane shi"[29]. Misali kana kin a wulakanta ka, kuma kana son a girmamaka, to a nan sai ka ki wulakanta mutane kuma ka girmama su.
Wannan hadisi da za a yi aiki da shi, da Duniya gaba daya ta zauna cikin aminci, da ta juya ta zama kamar aljanna, da so ya game tsakanin mai kudi da talaka, da mai ilimi da maras ilimi, da miji da mata, da 'ya'ya da iyaye, da malami da dalibi, da mai mulki da wanda ake mulka, da dukkanin nau'i na mutane gaba daya.
Wannan hakkoki kuwa sun hada nisantar cutar da waninmu ta kowace hanya kamar duka ko da kuwa dalibinmu ne, amma a kasashenmu duka wani abu ne mai sauki. Kai a makarantun Furamare da na Allo har yakan yi muni kwarai; mai dukan ba ya neman izinin Shugaban musulmi, ko uban da, sai a yi ta jibga ko mai kankantar abu.
Duka ba ya halatta koda kuwa uwa ce ga danta sai da izinin uba[30], ko dukan uba ga dansa ko wanda Shugaban musulmi ya ba wa izini. Shi ma uban a matsayin tarbiyyantarwa da ya zama sai ta hakan, kuma ba mai cutarwa ba. Ko kuma miji ga mace mai nushuzi[31], shi ma a mataki na uku na karshe[32] kuma ba mai cutarwa ba, sai kuma Shugaban musulmi ga mai laifi kamar a haddi ko ladabtarwa.
Daga cikin hakkin mutum a kan waninsa shi ne ya shiryar da shi abin da zai amfanar da shi, kamar hakkin mutane a kan likita na ya nuna musu hanyar tsafta da kare lafiya, da yadda zasu tsara abinci da abin sha mai sanya lafiya, da magunguna, musamman ta hanyar Gidan Radio da Talabijin; Da maras lafiya zai tafi wajan likita sai ya cutar da shi to dole ne ya biya shi diyya, amma idan da gangan ne sai a yi masa kisasi.
Kamar yadda yake wajibi ne a kan malami ya shiryar da al'umma kuma ya ilmantar da ita, mai kudi kuwa ya yi odar abin da yake tattalin rayuwa na al'umma kuma ya sanya farashi da talaka zai iya saya cikin sauki, haka ma injiniya ya kyautata mota ta yadda ba zata zama hadari ga mai hawanta ba, mai gini kuwa ya kyautata shi.
Haka nan yana kan mai sayan kaya ya girmama mai sayarwa shi ma mai sayarwa ya mutunta mai saya, likita da marasa lafiya, mai kudi da talaka, malami da marasa sani, mai haya da dan haya, mai aiki da shugaba. Bai kamata ba shugaba a ma'aikata ya rika kallon masinja kallon wulakanci, hakki ne a kansa ya girmama masinja, ya tuna shi ma dan kasa ne kamarsa kuma ma'aikaci da bai fi shi da komai ba a wajan Allah sai dai idan ya fi shi takawa domin ita ce ma'aunin fifiko. Haka ma dan hayar mota kamar Taksi da Bos (hayis) kada ya zama idan ya ga fasinja yana ganin naira goma ne ko biyar ko ishirin, hakki ne a kansa ya ga mutum yake kallo kafin ya ga Naira ishirin, kuma ya yi mu'amala da shi ta mutunci da girmamawa tsakanin juna.
Haka nan alakar na kan mota da na kan jaki, da na jirgin sama da na kasa[33], duka daya ne a wajan Allah kuma ba mai fifiko sai da takawa, rashin kiyaye wannan da mantawa da Allah ya sanya rashin kiyaye hakkin juna.
Wani misali a kan haka shi ne; wata rana wani mai kudi shahararre ya taba kade wani almajiri da mota a kan titi, maimakon mutane su nemi ya bayar da kudin magani a kai almajirin kyamist tun da shi ba shi da mutuntaka domin ba ya ganin almajirin mutum ne kamarsa don ko taba shi bai yi ba, sai suka zo suna ba shi hakuri. Har da cewa: Ai da ma haka almajirai suke ba sa jin magana. Haka mutakabbirin ya hau mota ya wuce! Shi kuwa bawan Allah yana ta nishi har ya samu da kyar ya taka. Su kuwa mutanen ba mai ji a jikinsa cewa an ji wa wani mutum daga cikin mutane masu hakki kamar kowa ciwo! Wallahi da dabba ce aka kade da sun fi ba ta muhimmanci!.
Daga cikin hakkin mutun a kan dan'uwansa mutum taya shi bakin ciki idan wani abu ya same shi musamman ma dan'uwa na jini ko na Addini da makwabci, kamar idan an yi masa mutuwa to ya kamata ne bisa koyarwa ta Manzo (S.A.W) a yi abinci kwana uku daga makwabta ana kai musu kamar yadda ya koya mana kyawawan dabi'u da fadinsa: "Ku yi wa iyalan Ja'afar abinci hakika wani al'amari da ya shagaltar da su ya same su"[34]. Amma abin sai ya zama bisa akasi, maimakon a kai gidan mutuwa, sai ya zama su ne kuma za a shagaltar da su da ciyar da masu taruwa.
Idan muka waiwayi alakar mai kudi da yaronsa al'amarin ya kai ga ana iya samun yaron Alhaji da rashin lafiyarsa bai fi a kashe kudi kankani a kansa ba ya warke amma yana iya mutuwa alhali Alhajin da ya yi wa hidima a gida, da shago, da kanti, shekaru masu yawa yana gani sai dai ya mutu. Wani kuma yana aiki karkashin uban gidansa amma canja riga mai tsada yana iya tayar da mugunyar tsatsar nan ta hassada a zuciyar uban gidan, sai ya ce da shi: Ka tattara naka ka yi gaba kuma ka bar min shagona.
Akwai wata kabila da galibinsu ba ma musulmi ba ne amma har bikin yaye yaron shagonsu suke da shi. Idan kuwa ka duba bangaren kere-kere to a nan sun yi nisa, sannan wasu abubuwan idan kana nemansu ranar lahadi to lallai ka wahala domin sun kulle shaguna. Don haka idan ana son mafita da ci gaba ya zama dole ne a siffantu da siffa ta gari a bar hassada da kyashi, a cire duk wata dauda daga zuciya. Idan wani ya ci gaba ta hanyarmu sai mu gode wa Allah, amma rashin kishin kai da son ci gaban juna, da rashin kyawawa dabi'un musulunci ya sanya ana danne hakkin juna, kuma mu sani cewa dukkan ayyukanmu suna da hisabi a Lahira.

Hakkokin Mai Mulki Da Wanda Ake Mulka
Wannan yana iya bayyana ne ta hanyar sanin wanene shugaba da siffofinsa, domin idan mun san siffofin mai mulki to muna iya gane wannan alaka ta hakkokin mai mulki da wanda ake mulka: Daga cikin siffofin shugaba su ne; ya zama mai karfin tafiyar da mulki da Iliminsa da basirarsa, mai karfin zartarwa, kuma amintacce, wanda ba ya cin amanar al'ummar kasarsa.
Mai neman maslaha ga al'ummarsa, mai daukarsu a matsayin 'yanuwansa, maras tsanantawa a kan mutanensa. Kuma mai sakin fuska, mai hankali, da ilimi, da adalci, mai karbar shawara daga mutanensa wajan gudanar da al'amuranta, mai daidaitawa tsakanin mabiyansa ba tare da son kai ba ko fifita wasu kan wasu.
Haka nan ya kasance mai kwarjini, mai kyawawan dabi'u da son gyara, mai hidima ga mutanensa, masanin siyasar Duniya da al'amarin tafiyar da al'umma, mai karbar nasiha daga talakawansa ko wakilansu, mai saukin hali. Ya kasance ba ya daukar fansa kan abokan hamayya, kuma mai kyauta ba marowaci ba, mai kaifin basira da yakan iya mayar da makiyi masoyi saboda kyawawan halaye da basirarsa, mai tausasawa ba mai tsanantawa ba.
Duba wasikar da Imam Ali (A.S) ya rubuta wa Malik Ashtar yana cewa da shi: "Ka nisanci fushin al'ummarka domin fushinsu yana tare da fushin Allah"[35]. Mu sani cewa idan shugaba zai kalli kansa ne to lallai zai fada cikin fushin al'umma domin su ba su da abin da yake da shi, wasu shugabannin sukan kara kudin kaya ba ruwansu da talaka, sai ka ga al'ummar ta koma tana kinsa ba ta ganinsa daya daga cikinta, da zai wuce tana iya jifansa.
Amma a tsari na adalci dole ne shugaba ya ji cewa shi daya ne daga cikin 'ya'yan al'ummarsa, wannan zan sanya idan ta gan shi ta nuna shaukinta da kaunarta gareshi, idan ya mutu tana nuna bakin cikinta kamar yadda a wannan zamani namu ya faru ga Imam khomaini da mutane sama da miliyan ishirin suka zo jana'izarsa, mutanen kasarsa suka yi kwanaki suna kuka, kasar gaba dayanta ta shelanta zaman makoki na kwanaki. Ta haka ne a kan gane waye ya yi wa al'ummarsa adalci? Waye kuma ya zalunce ta?
Akwai wanda ya taba rike babban mukami a kasar nan amma da ya mutu mutane da yawa sun yi bukukuwan murnar mutuwarsa, aka hole aka yi annashuwa, a kan titina. Akwai kuma wadanda suka mutu amma har yanzu al'umma tana bakin cikin rashinsu, wannan kuwa ya isa wa'azi ga na yanzu rayayyu.

Hakkin Shugaba A Kan Al'umma
Daga cikin hakkokin shugaba su ne; a yi masa biyayya ga abin da bai saba wa Allah (S.W.T) ba. Kuma wasu bayanai sun zo game da cewa; yana daga hakkin shugaba a kan al'umma a ba shi shawara da nasiha, idan kuwa zai kauce hanya sai a tuna masa, sannan a taimaka masa domin ci gaban addini da al'umma gaba daya[36].
Dan kasa na gari shi ne wanda yake kiyaye doka koda kuwa ta kan titin mota ce. Wani malamin Ilimin tafiyar da al'amuran al'umma ya taba ba mu labari cewa: Wata rana ya dauko wani dalibinsa suna tafiya, sai suka isa wata danja ba mota ko daya amma bangarensu ba a bayar da hannu ba sai ya wuce. Sai dalibinsa ya ce: Amma da an kiyaye. Sai ya ce da shi: Ai ba mota. Sai dalibin ya ce: Amma da ka girmama dokar da kuma wadanda suka sanya dokar, don sun yi tunani kafin kafa ta, kuma don maslahar kanka da ta sauran 'yan kasa ne. Ya ce: Sai ya yi kwana ya koma ya sake jira sannan ya wuce. Tun ran nan ya amfana da nasihar dalibinsa kuma ya yi masa godiya.

Hakkokin Dan Kasa A Kan Shugaba
Yana daga cikin hakkokin dan kasa a samar masa da aminci, da kariya, da lafiya, da ilimi, da hakkin fadin ra'ayinsa, da hakkin zamantakewa, da na walwala, da dukkan abin da ya shafi ci gaban rayuwarsa ta Duniya da Lahira. Haka nan yana da hakki kan masu tsaron kasa, amma wani abin haushi shi ne; samun tazara mai yawa tsakanin masu tsaron kasa da al'umma, ta yadda al'umma ba ta ganinsu wani bangare nata. Wannan kuwa yana faruwa ne sakamakon ba sa ji ko kadan cewa suna aiki don al'ummarsu ne kamar suna aiki don shugaba ne.
Wannan mummunan kuskure ya sanya masu kare doka sai su yi zalunci babu tausayi, har ma takan kai ga lahantawa ko salwantar da rai, kuma ga karbar cin hanci da ya zama ruwan dare. Koda yake a ciki akwai mutane masu hankali da kula da aiki da son taimakon al'umma kuma ba sa karbar cin hanci, irinsu ne suke iya mutuwa wajan kare mutanensu, amma da yawa ba haka suke ba sai dai kokari wajan neman na aljihunsu kawai sun manta da manufarsu. Wani lokaci kamar suna cike da jin haushin mutane ne, ta yadda da sun kama mai laifi sai duka da azabtarwa, alhali shi mai laifi koda kuwa barawo ne da makamancinsa mai kare doka ba shi da hakkin yi masa wani abu sai dai ya kai shi kotu ta yanke masa hukunci.
Ban taba sanin cewa al'umma tana da tazara mai yawa da 'yan doka ba sai ranar da na samu nawa rabon, har ma wani yana jinginamu da wata kasa kai ka ce su ba mutane ba ne. Wani daga cikinsu ya ce: Irin wannan ku rika guduwa tun da ku ba ma su laifi ba ne! Kai ka ce su makafi ne da ba sa ganin mai laifi!. A ofishinsu ne na ga wani ana ta dukansa wai ya yi taurin kai a shiga mota, ana buga kansa da kasa, shi kuwa yana ta la'antar duk wani uba ko uwa na dan sanda.
Kuma a nan ne na yi mamakin yadda wani tsararre yake la'antar uwar ma da ta haifi dan sanda, har ma ya ce: Babansa ya taba cewa da shi tun da ya rasa aiki ya yi aikin dan doka. Sai ya ce: Ai baba gwara ka tsine mini in san ni tsinanne ne da in yi wannan aiki, ya kara da cewa: Wallahi in gawa ta kai dubu to shi zai iya gano ta dan sanda a ciki don fuskarsa ba ta cikawa da imani.
A lokacin ne na san cewa lallai akwai tazara mai yawa sosai tsakanin 'yan sanda da al'umma, amma ra'ayin mutane da yawa ya tafi a kan cewa: Zafin zalunci da take hakkin dan Adam shi ya jawo haka, ta yadda mai tsaron kasa yake ganin yana yi wa shugaba aiki ne ba al'ummarsa ba, kuma yana ganin hadafinsa shi ne ya huce haushinsa kan al'ummarsa, sai ya cire wa al'umma jin cewa shi daga cikinta yake.
Haka al'amarin yake game da soja, kamar yadda dan sanda yake da hakkin kare cikin kasa da samar da aminci, haka ya zama wajibi a kansa ya kare kasa daga waje kada wani ya kai farmaki kanta. Amma wani abin takaici al'umma ba ta jin su nata ne haka su ma ba sa jin al'umma ta su ce. A misali da za a yi rigima tsakanin wani dan kasa da soja, da zaran sojoji sun isa wurin ba sa tambaya, a wurinsu mai gaskiya shi ne mai kaki na soja. Wannan rashin ganin juna a matsayin abu daya ya shafi har matsayin auratayya, domin na sha jin soja (ladani ne) yana nasiha a masallacin Barikin Bukabu da yake Kano yana cewa: Me ya sa ba a zuwa daga gari a auri 'ya'yansu? Ko su ba kamar sauran mutane suke ba. Haka nan aka jahilci hakkin juna tsakanin mai tsaro da wanda ake tsaro har ya zama kamar al'umma daban-daban ce a cikin al'umma daya.
Duba ka ga me Imam Ali (A.S) yake cewa game da mai tsaron kasa: "Runduna: Ita ce kariyar al'umma da izinin Allah, kuma adon shugabanni, izzar Addini, hanyoyin aminci, al'ummar kasa ba ta tsayuwa daram sai da su"[37]. A wani wurin yana cewa: "Ka sanya wa rundunarka jagora wanda ya fi su nutsuwa da biyayya ga Allah da Manzonsa a ganinka. Wanda ya fi sirri na gari (wato mai dabi'u masu kyau), wanda ya fi su hakuri, da ilimi, da sanin tafiyar da al'amuran al'umma, da rashin saurin fushi, kuma da karbar uzurin mutane. Mai tausayawa talakawa, maras bayar da dama ga masu karfi. Wanda takurawa ba ta harzuka shi, rauni (karayar zuci) ba ya dunkufar da shi[38]. A cikin wannan akwai nuni da cewa: Cin hanci shi ne abin da yake kawo ba wa mai karfi dama ya taka doka. Kuma akwai nuni da cewa: Bin hakkin dan kasa wajibi ne a kan hukuma a ko'ina ne yake, al'amarin da ya yi karanci a kasashenmu ko ma ba a san da shi ba.
Yana daga cikin hakkin dan kasa a samar masa da wurin shakatawa da walwala da wuraren hutawa da na wasanni da shi da iyalinsa da yaransa. Wani abin takaici irin wadannan filayen da ake warewa unguwanni domin wasanni saudayawa maciya amanar al'umma suka sayar da su al'umma tana gani, mafi ban haushi da muni shi ne mafi yawa ba su san ma cewa wannan hakkinsu ba ne.