Hanyar Da Ake Bi Wajen Tafsirin Kur'ani
Yayin da tafsiri yake bayanin ma'anar kalmomin Alkur'ani da jumlolinsu da kuma fito da ma'anoni a sarari, sannan kuma sashen kalmomin Alkur'ani da jumlolinsa ana iya fassara su da tafsirin zahiri wanda mai yiyuwa ne ya kasance ya yi nisa da manufa ta hakika ga Alkur'ani, shi kuwa tawili shi ne aikin fito da ma'anar da ake nufi, hakan kuwa ta hanyar mayar da ma'anoni da ke ajiye cikin ayar - bayan jujjuya su tsakanin fuskoki biyu ko fiye([111]) - ya zuwa ga makomarsa. Burin da muke so mu cimma a nan shi ne daidaiton tawili da tafsiri a matsayin sakamako. Shi ne kuwa fayyace ma'anonin Alkur'ani da bayanin abin da Allah Madaukakin Sarki Yake nufin bayaninsa ga bayinSa.
Duk wanda ya yi bitar littattafan tafsiri da tafarkin masu tafsiri, zai samu cewa akwai tazara mai fadi da ramuka masu hadari, wadanda sashin masu fassara suka fada, sai suka karkace daga manufar tafsiri domin hanyoyin tafsirin wadanda suka bi da bayanin tawilin da suka yi wa ayoyin Alkur'ani. Wani lokacin a samu sun dogara da raunanan ruwayoyi da aka sossoka, wani loton kuwa a samu sun bi son zuciya sai su tankwarar da Alkur'ani zuwa ra'ayoyin kungiyoyin da suke bi, da kuma son zuciyarsu kebantacciya. Sai ka ga suna kokarin sa ayoyin Alkur'ani su dace da abubuwan da suka auku a tarihi kuma danganta su ga wadansu daidai-kun mutanen da Alkur'anin ba su yake nufi ba. Kai sun ma nemi su sa ayoyin Alkur'ani su dace da girmama ra'ayoyinsu da karkatar su kebantattu.
Misalin karkata cikin tawili shi ne fuskartar da ayoyin Alkur'ani da sashen masu falsafa da ilimin kalami suka yi bayan sun riga sun yi imani da tunani da mazhabobin kalami da falsafa sannan suka tankwara ma'anonin ayoyin zuwa wadannan mazhabobin.
Misali kuma shi ne cewa akwai abin da sashen marubuta da masu tafsiri ke yi na fuskantar da ayoyin Alkur'ani domin su dace da nazarce-nazarcensu na ilimin kimiyya da tunaninsu na tattalin arziki da zamantakewa da siyasa wadanda marubuta da amsu nazari suka bijiro da su suka kuma yadu a zamanin wadannan masu fassara. Suna bin fadar masu nazarce-nazarcen nan ba tare da akwai wata dangantaka ta hakika ko dacewa ta gaskiya ba. Haka nan muke samun yadda ake murda ayoyi zuwa son zuciya, ko ka ga mai tafsiri ya yarda da wasu ra'ayoyi sannan daga baya ya karkata ayoyin Alkur'ani zuwa ra'ayoyi da halaye da dama, tun da can da kuma ma yanzu.
Hakika masu tafsiri da yawa sun fada cikin wannan kuskuren, kuma daga mazhabobi daban-daban, na Ahlussunna ne ko na Shi'a ko kuma waninsu. Bayan sun yi wannan kuskuren sai su dora kawo hujjoji da dalilai don kare wadannan ra'ayoyi nasu.
Idan muka koma ga tafarkin Musulunci na asali wajen tafsiri za mu ga cewa ya yi watsi da wannan tafarki da muka fadi a baya da kuma tabbatar da asasai ingantattu na tafsiri.
Don kuwa tafsiri kamar yadda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya fadi, kuma tafarkin Ahlulbaiti (a.s) da duk wanda ya bi tafarkinsu ba tare da karkata ba da malaman tafsiri masu lizimta, yana da asasai da ginshikansa wadanda suke shiryar da mai tafsiri da mai bincike zuwa dacewa mayalwaciya.
Bari mu kawo bayanin da ya zo daga Manzon Allah (s.a.w.a.) da Imamai Masu shiryarwa (a.s.) da malaman al'umma kan batun sanya ginshikai wadanda ba su da wata karkata, domin tafsiri da tabbatar da ma'aunai da kuma dokoki masu kiyaye wannan ilmi mai daraja, domin shi ilmi ya ba da gudummawarsa tare da cikakkiyar kula da kubuta daga karkatarwa. Kuma domin wannan ilmi ya wadatar da duniyar dan'Adamtaka da ma'anoni da tunani da fahimce-fahimcen da za a iya riska da kuma hukumce-hukumce, ba tare da wata tawaya ko kirdado ko jidali ko bin ra'ayi ko kuma tankwara tafsirin domin ya bi son zuciya ba.
Allama Dabrisi ya ambata cewa: "Ya inganta daga Annabi (s.a.w.a), ta hanyar Ahlulbaiti (a.s) cewa: "Tafsirin Alkur'ani ba ya halatta sai da asari (wato hadisi) ingantacce da kuma nassi bayyananne([112])".
Lalle Ahlulbaiti (a.s) sun kasance suna bin wannan hanyar, suna kuma watsi da yi wa Alkur'ani tafsirin da ya yi nisa daga wadannan ginshikai guda biyu, wato:
1. Tafsirin Alkur'ani da Alkur'anin, wato wasu ayoyi su yi wa wasu tafsiri.
2. Tafsirin Alkur'ani da ruwayoyi da kuma hadisai ingantattu.
Don haka ne ya wajaba cewa dole tafsirin ya lizimci wadannan ginshikai biyu, cikakkiyar lizimta. Sannan kuma wajibi ne kada mu gafala kan cewa hankali yana da fagensa na asasi da ja-goranci wajen fahimtar Alkur'ani da tafsirin ma'anoninsa da fuskantar da zahirinsa, bisa sharadin cewa shi hankali zai lizimci iyakokin Littafin Allah da Sunnan Ma'aiki (s.a.w.a.), ba zai kuma sabawa tsarinsu ba. Hakika Manzo Mai girma ya ba wa hankali fage fitacce wajen tafsirin Alkur'ani, inda ya ce: "Alkur'ani mai saukin korawa ne, mai fuskoki da yawa; to ku dauki fassarar da ta fi kyau([113])". Har ila yau ya ce: "Ku bayyana Alkur'ani kuma ku nemi kebantattun abubuwansa([114])".
Alkur'ani mai girma ya bayyana irin rawar da hankali zai taka cikin tafsiri, ya kuma yaba wa ma'abota hankula masu fitar da hukumce-hukumce daga Alkur'ani, yayin da yake cewa: "Da masu istinbadinsa daga cikinsu sun san shi". (Surar Nisa'i, 4: 83)
Alkur'ani ya yi suka ga wadanda suka bar tunani da lurar hankali cikin ayoyin Alkur'ani mai girma, da gano ma'anoninsa da abubuwa da ya kunsa, da cewa: "Shin ba su lura da Alkur'ani ne, ko kuwa da kemare ne bisa zukata" (Surar Muhammadu, 47:24). Daga nan za mu san cewa a mazhabar Ahlulbaiti (a.s) tafsiri yana dogara ne da asasai uku:
1. Tafsirin Alkur'ani da Alkur'ani.
2. Tafsirin Alkur'ani da Sunna.
3. Tafsirin Alkur'ani da hankali mai lizimtar Alkur'ani da Sunna.
Haka nan muke samun cewa tafsiri yana da asasai da dokoki, kuma abin da ya tafo na tafsirai wanda za a cewa ra'ayin mutum ya shige shi, ko kuwa an dauki wasu nazarce-nazarcen ilmi wadanda mai tafsirin ya yi zamani da su, ko ra'ayoyin falsafa da ilmin akida, ko abin da aka danganta shi da ruwayoyi raunana ko ma wadanda sanadinsu yashashshe ne, ko kuwa masu karo da ayoyin Alkur'anin da suke a sarari ko kuma sunna tabbatatta, ko kuwa tafsirin da mai tafsirin ya daidaita shi da ra'ayinsa da karkatarsa da kuma sauran irin wadannan, dukkansu ababan yarfarwa ne a tafarkin Ahlulbaiti (a.s) da kuma malamai da masu tafsiri wadanda suka bi shiriyarsu. Sau da yawa kuma ana samun cikin tafsiran musulmi, sunna da shi'a, ra'ayoyi da tafsirai wadanda ba su lizimci wannan hanyar ta Musulunci ba, wadanda kuma ba su bayyana ruhin Alkur'ani.
Don haka, ba wa irin wadannan tafsiran kima ba ya inganta, ba za mu kuma rike su mu yi aiki da su ba, sai dai wanda ya tabbatar wa kansa da ingancinsu.
Mai tafsiri kuwa ko wane ne shi, Alkur'ani hujja ce akansa, ba shi ne hujja a kansa ba. Kuma ba zai zamo hujja kan musulmi ba face da gwargwadon abin da ya dace da katari da abin da ya gano na hakika kawai.
Hakika hani ya zo daga wajen Imamai (a.s.) kan magana ba da wani ilimi ko hujja ba. An ruwaito Imam Bakir (a.s.) yana cewa:
"Abin da kuka san shi to ku fade shi, abin da kuwa ba ku sani ba to ku ce "Allah Shi Ya fi sani". Lalle mutum yana tuzgo aya daga Alkur'ani ya fadi cikin tuzgowar da ya yi, faduwar mai nisan fiye da tsakanin sama da kasa([115])".
Imam Sadik (a.s.) ya ce: "Ko wane abu ana komar da shi zuwa ga Littafin Allah da Sunna([116])".

Sunnar Annabi (s.a.w.a) A Mazhabar Ahlulbaiti (a.s)
"Allah Ya ni'imta bawan da ya ji maganata sannan ya haddace ta ya kiyaye ta ya kuma bayar da ita (ga wasu) kamar yadda ya ji ta. Sau da yawa ana samun mai daukar ilmi, amma ba malami ba, sannan kuma sau da yawa ana samun mai daukar ilmi ya zuwa wanda ya fi shi sani([117])".
Baicin Littafin Allah, Sunna ita ce mabubbuga ta biyu daga mabubbugan shari'a, wadanda musulmi suke dogara da su wajen fitar da hukumce-hukumce da dokoki da ka'idojin Musulunci. Ita Sunna tana daukar nauyin bayani da faiyacewa da kuma tafsirin Littafin Allah da furuci da abubuwan da ya kunsa da kuma abubuwan da ya tattara na shari'a da tunani da kuma tarbiyya. Shi nassi na Alkur'ani yana dauke da wata wadata da arziki na tunani da shari'a, mai girma kuma dauwamammiya, ita sunna kuwa ta dauki nauyin bayyana wannan arziki da gamar da shi. Lalle hankula ba za su iya riskar Littafin Allah tamkar yadda Sunna take riskar shi tana bayyana shi ba. Manzon Allah (s.a.w.a.) shi aka yi wa zance da wahayi, shi ne kuwa masanin abin da ke cikin Littafin Allah mai girma na daga abin da suka shafi hukumce-hukumce da ababen fahimta daga ciki da kuma manufofin da yake da su.
Don haka ne ita Sunna mabubbuga ce wacce ba ta kafewa, kuma gaskiya ce wacce barna bata taho mata a bayanta ko a gabanta. Sunna ita ce amintacciya mai ayyana dokokin rayuwa da kuma tsarin jin dadin dan'Adam, kuma ita madawwamiya ce dawwama irin ta Alkur'ani mai girma. Allah Ta'ala Ya ce: Abin da Manzo ya zo muku da shi, ku karba, abin da kuma ya hane ku, to ku hanu...". (Surar Hashr, 59: 7)
"Hakika abin koyi mai kyau ya kasance muku daga Manzon Allah, da duk wanda yake kaunar Allah da kuma ranar lahira...". (Surar Ahzab, 33: 21) "Idan kuka yi jayayya a wani abu to ku mai da (hukumcinsa) ga Allah da Manzo...". (Surar Nisa'i, 4:59)
Babu shakka, Ahlulbaiti (a.s) da wadanda suka dauki tafarkinsu wajen tafsiri da hadisi da fikhu da shari'a da akida, sun lizimci wannan hanyar, sun kuma yi gwagwarmaya, sadaukarwa, daurewa cutarwa, shiga kurkuku, kisa, azabtarwa da kuma kora duk a dalilin kare sunna mai tsarki da kira zuwa ga dacewarta da Littafin Allah mai girma.
Hakika an bijirar da Sunna tsarkakakkiya ga coge da karkatarwa da jirkitarwa wanda masu yi wa Musulunci dasisa, karya da kiyayya suke yi domin muzanta wannan dawwamammen sako na Ubangiji, domin kuma su karkatar da tafarkin al'ummar Musulunci.
Ahlulbaiti (a.s) sun kasance suna fagen kan gaba wajen kiyaye Sunna tsarkakakkiya da daukar ta da kuma isar da ita da gaskiya da amana, da kuma bayyana abubuwan da ta tattara na bayani mai zurfi.
Don aka ne suka yaki bidi'oi da bata, suka yi kira da a lizimci Littafin Allah da Sunna da sanya Littafin Allah ya zama shi ne ma'aunin Sunnar Annabi (s.a.w.a). Sun yi hakan ne domin Littafin Allah abin kiyayewa ne daga karkatarwa da jirkita - Alhamdu lillahi - kiyayye ne kamar yadda Jibrilu (a.s.) ya isar da shi ga Annabi Amintacce Muhammadu (s.a.w.a). "Lalle Mu muka saukar da Ambato (Alkur'ani) kuma lalle Mu Masu kiyaye shi ne".
Saboda haka, babu hannun jirkitawa ko coge ko wasa da ya taba shi. Domin haka ne ma muke samun Amirul Muminina (a.s) yana cewa: "Ya ku mutane! Farkon aukuwar fitinu (na daga) son zuciya wadanda ake bi da hukumce-hukumce fararru (wato na bidi'a) wadanda ake sabawa Littafin Allah wajen binsu, mutane suna jibintar wasu mutane wajen bin wadannan hukumce-hukumce. Da dai ita bata tsantsarta take, da ba ta buya ba ga mai hankali, da kuma gaskiya tsantsarta take, da sabani bai samu ba. Amma ana daukar wani abu a nan, a dauki wani a can, sai a cudanya su, sannan su zo tare. A nan ne Shaidan ya rinjaye majibantansa, wadanda kuwa kariya ta gabata gare su daga Allah suka tsira([118])".
Abu Basir, daya daga cikin sahabban Imam Sadik (a.s.) ya ruwaito cewa: "Na ce da Abu Abdullahi (a.s.) cewa: Wadansu abubuwa suna taho mana, mu ba mu san su cikin Littafin Allah ko Sunna ba, to za mu dube su? Sai ya ce: "A'a, amma kai ko ka dace ba za a sakanta maka ba, idan kuwa ka yi kuskure to ka yi wa Allah Mai Girma da Daukaka karya([119])". Sannan ya ce (a.s.): Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Dukkan bidi'a bata ce, kuma dukkan bata cikin wuta take".
Abdullah bn Abi Ya'afur ya ce: "Wata rana na tambayi Abu Abdullah (a.s.) game da sassabawar hadisai, wadanda muke amincewa da wadanda ma ba mu amince musu suna ruwaitowa", sai ya ce:
"Idan hadisi ya zo muku kuma kuka sama masa wata shaida daga Littafin Allah ko wata magana ta Manzon Allah (s.a.w.a.), (to ku karba) idan kuwa ba haka ba to wanda ya kawo muku hadisin ya fi cancanta da shi([120])".
An samu daga Ayyub bn Al-Hurr ya ce: "Na ji Abu Abdullah (a.s.) yana cewa: "Duk wani abu ana iya masa raddi in ban da Littafin Allah da Sunna, to duk hadisin da bai dace da Littafin Allah ba, to kyalkyali ne kawai([121])".
An samu daga Ayyub bn Rashid daga Abu Abdullah al-Sadik (a.s.) ya ce: "Abin da bai dace da Alkur'ani ba daga cikin hadisai kyalkyali ne kawai([122])".
An samu daga Imam Sadik (a.s.) cewa: Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Wanda ya yi riko da Sunnata yayin sassabawar al'umma, yana da ladan shahidai dari([123])".
Wani mutum ya taho wa Amirul Muminina (a.s) ya ce: "Ka ba ni labari (mece ce) Sunna da bidi'a da jama'a da kuma rarraba", sai Amirul Muminina (a.s) ya ce da shi:
"Sunna ita ce abin da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya sunnanta, bidi'a kuma ita ce abin da aka fare shi a bayansa. Jama'a ita ce wadanda suke tare da gaskiya ko da su kadan ne, rarraba kuwa ita ce wadanda suke tare da bata, ko da kuwa suna da yawa([124])". Har ila yau, Imam Ali (a.s) yana cewa:
"Sunna biyu ce: Sunna ta wajibci, riko da ita shiriya ce, barinta kuwa bata ce. Da kuma Sunna cikin abin da ba wajibi ba, riko da ita falala ce, barinta kuwa kure ne([125])". Imam Bakir (a.s.) yana cewa:
"Ita Sunna ba a yi mata kiyasi, to ya ya za a yi kiyasin Sunna alhali mace mai haila tana rama azumi, amma ba ta rama salla([126])".
An samu daga Abu Abdullah, Imam Sadik (a.s.) daga Mahaifansa, daga Imam Ali (a.s.) cewa: "Kowace gaskiya tana tare da wata hakika, kuma kowace dacewa tana tare da wani haske. To abin da ya dace da Littafin Allah ku karbe shi, abin da kuwa ya saba da Sunnar Manzon Allah, to ku bar shi([127])". Sannan kuma yana cewa: "Allah Ya ji kan mutumin da ya kawo hadisi daga Manzon Allah (s.a.w.a.) ba tare da ya yi masa karya ba, ko da kuwa mutane sun guje shi([128])".
Sannan Amirul Muminina Ali (a.s) ya ce: "Na ji Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: "Idan hadisi ya taho muku (sashinsa) yana daidaita, (sashi kuma) yana sassabawa, to abin da sashinsa yake karyata sashe ba daga gare ni yake ba, kuma ban fade shi ba, ko da an ce na fada. Idan kuma hadisi ya taho muku, sashensa yana gaskata sashe, to shi daga gare ni yake, kuma ni na fade shi. Wamda kuwa ya ganni bayan rasuwata, kamar wanda ya ganni a raye ne, wanda kuwa ya ziyarce ni to zan kasance masa mai shaida a ranar kiyama([129])".
An samu daga gare shi (a.s.) ya ce wa Muhammad bn Muslim cewa: "Ya Muhammad! Abin da ya taho maka na wata ruwaya daga mutumin kwarai ko na banza, idan ya dace da Alkur'ani to ka dauke shi, abin da kuwa ya taho maka na ruwaya daga mutumin kwarai ko na banza, idan ya saba da Alkur'ani to kada ka karbe shi([130])".
Haka nan ake sanya iyakoki wa abin da ake daukarsa Sunnar Manzon Allah (s.a.w.a.) ne a mazhabar Ahlulbaiti (a.s) da tafarkinsu da kuma alakar wannan Sunna mai tsarki da Littafin Allah, da kuma rawar da take takawa cikin shari'a da sanya dokoki da gina rayuwar zamantakewa da ta ibada, wa al'ummar Musulmi. Muna iya tsamo wadansu abubuwa daga wannan tsarin mazhabi kamar haka:
1. Cewa kowane fadi ko aiki ko tabbatarwar da aka danganta ga Manzon Allah (s.a.w.a.), to wajibi ne a gwada su da Alkur'ani, a tabbatar da ingancinsu bisa hasken Alkur'ani, abin da ya dace da Littafin Allah, to daga Sunnar Manzo (s.a.w.a) yake, abin da kuwa ya saba da shi to ba kome yake ba wajen Sunna.
2. Alkur'ani da Sunna su ne tushen shari'a da doka, su ne ma'aunin hukumce-hukumce da halaye da tsarin rayuwa. Abin da duk muka samu na hukumce-hukumce na fikihu ko ma'anonin da ake riska na akida, to wajibi ne mu tabbata sun dace da Littafin Allah da Sunna. Duk abin da muka samu daga cikinsu ya dogara bisa asasin Littafin Allah da Sunna da shari'a, to doka ce ta Allah, mu yi aiki da shi, mu rike shi da karfi. Abin da kuwa ya saba da Littafin Allah da Sunna to shi bidi'a ce, bata ce.
3. Idan aka samu Sunna tabbatacciya, wacce an tabbatar da fitowarta daga Manzon Allah (s.a.w.a.) tana kuwa yin daidai da Litttafin Allah, to wajibi ne mu dauke ta a matsayin ma'auni kuma abin da za a yi amfani da ita wajen ruwayoyi da hadisan da muke shakkar su, ko muka sami rikitarwa wajen ingancinsu. Sai mu tabbatar da abin da ya dace da Littafin Allah da tabbatacciyar Sunna, mu yarfar da abin da ya saba da su. Ta wannan hanyar ne mazhabar Ahlulbaiti (a.s) ta ke iyakance tafarkin da za a bi wajen mu'amala da Sunnar Ma'aiki (s.a.w.a.).

Rabe-Raben Sunnar Annabi (s.a.w.a)
Malamai suna raba Sunnar Annabi (s.a.w.a) zuwa gida uku:
1. Maganganu: Su ne dukkan abin da suka taho daga Manzon Allah (s.a.w.a.) na daga zantattuka, hudubobi, wasiyyoyi, wasiku da dai sauransu.
2. Ayyuka: Abin nufi shi ne duk wani aiki da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi wajen mu'amalarsa da mutane, ko wajen yin ibadoji, ko wanin wannan daga abin da yake bayyana halalci. Duk aikin da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya aikata to za mu gane halalcinsa a tushen al'amarin domin Ma'aiki (s.a.w.a.) abin tsarakake-wa ne daga aikata haramun.
Saboda haka muna iya cewa abin da ya fito daga Ma'aiki (s.a.w.a.) na aiki ya kasu kashi biyu:
· Wajibci: Sashin abin da ya fito daga Manzo (s.a.w.a) kamar salla, hajji, adalci tsakanin mutane da dai sauransu, yana bayyana wajibcin wannan aiki, da kuma cewa shi takalifi ne kuma farilla ne, wadda lizimtar su yana wajaba a kanmu, kuma dole ne mu gudanar da hukumce-hukumcensu.
· Akwai wasu ayyukan Manzon Allah (s.a.w.a.) wadanda ba su nuna wajibci, suna nuna halalci ne. Dukkan wannan yana karkashin halal, wanda aikatasu ja'izi (ya halalta) ne.
Don haka, aikin Manzo (s.a.w.a.) yana bukatar tafsiri domin mu gane wajibi da mustahabi da kuma ja'izi. Malamai wadanda suka kebanta da wannan fannin suna rarrabewa cikin fahimta da tafsirin 'aiki' a cikin Sunna, ta hanyar hujjoji da alamomi da tafarkin bincike na ilmin Usulu.
3. Yarda (Takriri): Shi ne yin shirun Manzo (s.a.w.a) kan wani aikin da sahabbansa suka aikata, ya gani kuma bai hana su ba, kamar mu'amalolin zamantakewa da aikin mutum shi kadansa. To hakan ikirari ne da kuma yarda daga wajen Manzon Allah (s.a.w.a.), yana kuma shiga karkashin Sunna.
To kamar haka ne mazhabar Ahlulbaiti (a.s) ta iyakance yadda ake mu'amala da Sunna mai tsarki da tafarkin tabbatar da ingancinta da tafsirinta.

Tafarkin Bincike da Tabbatarwa
Malaman mazhabar Ahlulbaiti (a.s) suna da hanyar bincike da tabbatar da Sunnar Annabi (s.a.w.a) wacce Imaman Ahlulbaiti (a.s) suka iyakance kuma suka bayyana tushenta da alamominta. Mun riga mun yi nuni ya zuwa ga ruwayoyin da suka zo kan hakan a baya.
Bisa wannan tushen malaman fikhun mazhabar Ahlulbaiti (a.s) suka kafa tafarkin gyara (nakdi) cikin aikin bincike na ilmi. Babu wata sunna da suke mika wuya wajen ingancinta tun farko, sai dai su dauki matakin shakka kan ingancin sunnar, sannan su ci gaba da kokkofi da binciken ruwayar da tabbatar da ingancinta, idan har ingancinta ya tabbata sai su yi riko da ita da kuma daukanta a matsayin hujja da kuma fitar da hukumce-hukumce daga cikinta. Idan kuwa rashin ingancinta ya tabbata musu, sai su yi jifa da ita, ba za su yi aiki da ita ba. To kamar haka ne tafarkin binciken ruwayoyi da tabbatar da ingancin Sunna yake.
Bisa ga wannan bayani, malaman mazhabar Ahlul-baiti (a.s) ba su yi ikrari da samuwar wasu littattafan hadisai masu inganci, sake ba tare da wani kaidi ba. Sai dai kowane littafi dole ya rusuna wa bincike da gwaji kafin a tabbatar da ingancinsa. Misalin littattafai mashahurai a ruwaya wadanda suka tattara abin da ya taho ta hanyar Ahlulbaiti (a.s) su ne:
1. Al-Kafi na Shaikh Kulayni.
2. Al-Istibsar na Shaikh Dusi.
3. Al-Tahzib na Shaikh Dusi.
4. Man la Yahdhuruhul Fakih na Shaikh Saduk.
5. Wasa'il al-Shi'a na Hur al-Amuli.
6. Biharul Anwar na Allama Majlisi.
Da dai sauran littattafan hadisi.
Babu shakka malaman Imamiyya wadanda kuma suke lizimtar tafarkin Ahlulbaiti (a.s) a fikihu da shar'antawa da ilmomin Musulunci sun sanya hadisan da suka zo cikin wadannan littattafa a bisa ma'aunin bincike wanda ya kubuta daga son rai, inda bayan binciken suka zubar da adadi mai yawa na hadisan saboda rashin ingancinsu.
Kamar yadda wadannan malumma suka binciki wadannan littattafa na hadisi, haka kuma suka gudanar da bincike kan wasu littattafan kuma, kamar su Sahih Bukhari, Sahih Muslim, Sunan Abi Dawud, Kanzul Ummal da dai makamantansu daga cikin littattafan hadisai da ruwayoyi, suka kuma auna su da wannan ma'auni na ilmi, kamar dai yadda suka gudanar akan wadancan, suka dauki na dauka da kuma zubar da ba zubarwa. Su wadannan malamai kuwa, su kan yi wannan bincike nasu ne a bisa wadannan asasai:
(A). Bincike Kan Isnadi: Abin nufi da isnadi kuwa shi ne silsilar maruwaita wadanda suke ruwaito hadisi. A nan malaman su kan tsaya tsayin daka wajen tabbatar da gaskiyar maruwaitan, suna masu dogaro da ilmul Rijal, wanda yake gabatar musu da sanarwar abin da ya jibinci mutanen da suke maruwaita ne, yana shaidar gaskiya ko rashin gaskiyarsu, ba tare da la'akari da mazhabar da maruwaicin ya fito ba. Idan ya zama abin dogaro kuma gaskiya, sai su karbi ruwayarsa, idan kuwa an yi suka cikin al'amarinsa sai su ture ruwayar tasa. Su ba sa duba kome sai gaskiyar mai ruwaya da kubutarsa a bisa ginshikai tabbatattu.
(B). Binciken Matani: Abin nufi da matani shi ne asalin nassi. A nan malamai suna bincike ne kan luggar matani da ma'anarta, kuma suna bincike domin su tabbatar da cewa abin da ya taho a hadisin bai sabawa Littafin Allah ko tabbatacciyar Sunna ko wata hakika tabbatacciya wacce Mai shar'antawa Matsarkaki (Allah) Ya tabbatar da ita a matsayin tabbatacciyar hakika a hankalce ba.
Yayin da ingancin isnadi da na matani suka tabbata wajen malamai sai su karbi ruwayar, idan kuwa ba haka ba sai su ture ta, ba ruwansu da cewa a wani littafi daga cikin littattafan hadisi ta zo.
Saboda haka a tafarkin malaman fikihu da malaman mazhabar Ahlulbaiti (a.s) Imamiyya ba a samun:
1. Rikon wani littafi na hadisi a matsayin sahihi daga dayansa ko kuma kore shi gaba dayansa.
2. Su suna karbar ruwayar maruwaici ne bisa sharadin gaskiyarsa da amincinsa ba tare da lura da mazhabarsa ko bangaren da ya fito ba. Wanda duk yake bitar littattafan Usulu da fikihu da Ilmul Rijal , zai samu wannan hakikar a bayyane.
Da haka ne wannan hanyar bin diddigi ta ilmi ta kiyaye asalin shari'a da tsarkin ta, da kuma hadin kan musulmi da nisantar nuna bangaranci, jahilci da ganin girman wani tun da ba a ba da dama wa wadannan abubuwa a tafarkin bincike, don kuwa a yayin bincike kowa daya ne.
Kuma da wannan tafarkin bincike da ilmin bin diddigi, wanda ya kafu a bisa asasin neman gaskiya da bincike a aikace, da rashin mika wuya da yarda da ingancin kowace ruwaya ba tare da lura da kowane ne maruwaicin ta ba, ko littafin da aka ruwaito ta ba, ne ake gudanar da binciken hadisi.<

Imaman Ahlulbaiti (a.s) Maruwaita Manzon Allah (s.a.w.a)
Imaman Ahlulbaiti (a.s) ba su kasance masu Ijtihadi ko fitar da hukumci ba, sai dai sun kasance masu ruwayar Sunna ne, don haka, duk abin da ya fito daga gare su Sunna ce. Su kan ruwaito Sunnar ce da daga mahaifinsa, daga kakansa….daga Manzon Allah (s.a.w.a.). A saboda haka ne Imam Sadik (a.s.) ya ke cewa: "Hadisina hadisin babana ne, hadisin babana hadisin kakana ne, hadisin kakana hadisin babansa ne, hadisin babansa kuwa hadisin Aliyu bn Abi Talib ne, hadisin Aliyu kuwa hadisin Manzon Allah (s.a.w.a.) ne, hadisin Manzon Allah (s.a.w.a.) kuwa fadar Allah ce Mai girma da Daukaka([131])".
Daga Kutaiba, ya ce: "Wani mutum ya tambayi Abu Abdullah al-Sadik (a.s.) wata mas'ala, sai ya ba shi amsarta, sai mutumin ya ce: mene ne ra'ayinka in ya kasance kaza da kaza, mene ne hukumcinsa? Sai Imam ya ce masa: "Saurara! Abin da na baka jawabinsa, to daga Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ke, mu ba mu daga cikin wadanda a ke ce da su mene ne ra'ayinka a kowane abu([132])".
A saboda haka ne Shaikh al-Baha'i yake cewa: "Dukkan hadisanmu idan ba 'yan kadan ba suna komawa ga Imamanmu goma sha biyu (a.s.), daga nan kuma suna komawa zuwa ga Annabi (s.a.w.a). Domin ilminsu abin haskaka ne daga waccar fitilar([133])".
Da wannan ne Imaman Ahlulbaiti (a.s) suka zama mabubbugar hadisi da ruwaya da bayanin hukumce-hukumcen shari'a da kuma bude boyayyun al'amurranta.
Lalle rayuwarsu mai albarka, rayuwa ce da ke danfare da juna, babu rabewa a cikinta, babu wani bako wanda ba sananne ba da ya shamakance saduwarsu da Manzon Allah (s.a.w.a.), to wannan rayuwa tana zaman wata makaranta ce da kuma gwaji rayayye mai nuna Musulunci da tabbatar da hukumce-hukumcensa da kiyaye tushensa. Dukkan wannan yana karfafa mana amincewa da tsarkin mabubbugar da tsabtar baiwar da kuma cewa abin da ya taho daga gare su (a.s.) mai asali ne.
Yayin da muka san dukkan hakan, za mu iya gane yanayin da mazhabar ilmi wanda mabiyan Ahlulbaiti (a.s) suka taso daga ciki suka kuma dauki iliminsu, sannan za mu gane cewa mazhabarsu na hadisi da tafsiri da ilmin akida da tauhidi da dai sauransu suna da aminci kuma hanya ce tsabtacciya mai sadarwa zuwa ga masaniyar annabci da tsarkin shari'a da asalin tushen Musulunci.
Daga nan ya dace mu fito da daidaikun silsilar nan mai albarka ta Imaman Ahlulbaiti (a.s) maruwaita daga Manzon Allah (s.a.w.a.) sannan kuma mu sanar da al'ummarmu matsayinsu na ilmi a shariance. Su Ahlulbaiti (a.s) yayin da suke zancen silsilarsu ta maruwaita hadisin Manzon Allah (s.a.w.a.), suna zancen wannan silsilar ne, ga ta nan kuwa:
1. Aliyu bn Abi Talib (a.s.), an haife shi shekara ta 30 bayan Shekarar Giwaye, ya kuma yi shahada ne a shekara ta 40 bayan hijira.
2. Hasan bn Ali (a.s.), an haife shi shekara ta 3 bayan hijira, ya yi shahada kuma a shekara ta 50 bayan hijira.
3. Husaini bn Ali (a.s.), an haife shi a shekara ta 4 bayan hijira, ya yi kuma shahada ne a shekara ta 61 bayan hijira.
4. Imam Ali bn Husain (Zainul Abidin) (a.s.), an haife shi a shekara ta 38 bayan hijira, ya yi shahada a shekara ta 95 bayan hijira.
5. Imam Muhammad bn Ali al-Bakir (a.s.), an haife shi a shekara ta 57 bayan hijira, ya yi shahada a shekara ta 114 bayan hijira.
6. Imam Ja'afar bn Muhammad Sadik (a.s.), wanda ake danganta mazhabar Ja'afariyya Imamiyya gare shi, an haife shi a shekara ta 83 bayan hijira, ya yi shahada a shekara ta 148 bayan hijira.
7. Imam Musa bn Ja'afar al-Kazim (a.s.), an haife shi a shekara ta 128 bayan hijira, ya yi shahada a shekara ta 183 bayan hijira.
8. Imam Aliyu bn Musa al-Ridha (a.s.), an haife shi a shekara ta 148 bayan hijira, ya yi shahada a shekara ta 203 bayan hijira.
9. Imam Muhammad bn Ali al-Jawad (a.s.), an haife shi a shekara ta 195 bayan hijira, ya yi shahada a shekara ta 220 bayan hijira.
10. Imam Aliyu bn Muhammad al-Hadi (a.s.), an haife shi a shekara ta 212 bayan hijira, ya yi shahada a shekara ta 254 bayan hijira.
11. Imam Hasan bn Ali al-Askari (a.s.), an haife shi a shekara ta 232 bayan hijira, ya yi shahada a shekara ta 260 bayan hijira.
12. Imam Muhammad bn Hasan al-Mahdi (a.s.), an haife shi a shekara ta 255 bayan hijira, yana kuma raye a boye gwargwadon abin da ruwayoyi suka kawo.
Mun riga da mun yi magana kan guda uku na farko (wato Aliyu, Hasan da Husaini), mun san matsayi da mukaminsu cikin Alkur'ani da Sunnar Annabi (s.a.w.a), wadanda suke nuni da wajibcin yin musu da'a da kuma karba daga gare su.
To yanzu kuma bari mu yi bibiyar zantuttukan malamai dangane da sauran da suka saura daga cikin wadannan taurari masu albarka na gidan Annabci.
4- Imam Aliyu bn Husain (Zainul Abidin) (a.s.):
Shaikh Mufid ya nakalto cikin littafinsa Al-Irshad daga Zuhri cewa: "Ban riski wani mutum daga mutanen wannan gida - wato gidan Annabi (s.a.w.a) - wanda ya fi Aliyu bn Husaini (a.s.) ba([134])".
An nakalto daga Sa'id bn Musayyab, dangane da Imam Aliyu bn Husain (a.s.) yana cewa: "Wannan Shugaban masu ibada, Aliyu dan Husain dan Aliyu dan Abi Talib (a.s.) ne([135])".
Ibn Hajar cikin littafinsa Sawa'ikul Muhrika ya siffanta Imam Aliyu bn Husain (a.s.) da cewa: "Zainul Abidin shi ne halifan babansa (Imam Husain) wajen ilimi da zuhudu da ibada([136])".
An samu daga Abi Hazim da Sufyan bn Uyaina, ko wani dayansu yana cewa: "Ban taba ganin wani Bahashime wanda ya fi Aliyu bn Husain daraja ko ilmi ba([137])".
Hakika irin wadannan mutane daidaiku masu daraja wadanda suke kan mukamin Imamanci su ne malaman al'umma kuma su ne mafifita wajen ilmi, to lallai sun cancanca da malamai su siffantasu da irin wadannan siffofi, kuma sun cancanci karkatowar musulmi zuwa gare su wajen karbar hadisi da fikihu da tafsiri da akida da dai sauran ilmomin shari'a matsarkaki.
Hakika Imam Husaini bn Ali (a.s.) ya yi wa dansa Imam Ali Zainul Abidin alamar imamanci, ya kuma bayyanar da Imamanci da shugabancin addini ga dan nasa. Akwai dalili mafi bayyana, cikin yin hakan, dalilin da ya nuna mukamin wannan Imamin (Zainul Abidin) da karbar abin da ya fito daga gare shi na ilmomi da masaniyya da ruwayoyi da sauransu.
An ruwaito hadisi daga Imam Ja'afar Sadik (a.s.) cewa: "Lallai yayin da Husaini (a.s.) ya yi tafiya zuwa Iraki ya yi ajiyar littattafai da wasiyya wajen Ummu Salama (r.a.). Da Aliyu bn Husaini ya dawo (daga Iraki bayan shahadar babansa) sai Ummu Salama ta mayar da ajiyar zuwa gare shi([138])".
5- Imam Muhammad bn Aliyu al-Bakir (a.s.):
Amma dansa, Muhammad bn Ali, wanda ake masa lakabi da al-Bakir saboda fadadawarsa cikin ilmomi da masaniyya, to shi kamar mahaifinsa yake, shi ne mafi shahara da musulmi suka sani da tsantsaini da zuhudu da ilmi da masaniyya, malamai da maruwaita da malaman hadisi sun shaida hakan. Sahabin nan mai daraja Jabir bn Abdullah al-Ansari ya ruwaito cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ba da labarin cewa shi (Jabir) zai riski dansa Muhammad al-Bakir ya kuma umurce shi da ya isar masa da gaisuwarsa.
Wannan sahabin ya ruwaito cewa: Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce da shi: "Za ka rayu har ka hadu da wani da nawa daga Husaini, ana ce da shi Muhammadu, yana tsaga ilimi tsagawa. To idan ka hadu da shi ka isar masa da gaisuwa daga gare ni([139])".
Wannan sahabi kuwa ya riski Imam Bakir (a.s.) alhali yana yaro, sannan kuma ya isar da wannan gaisuwa ta Manzon Allah (s.a.w.a.) gare shi.
Lallai a cikin wannan shaida ta annabta da wannan sanarwa, akwai wadatarwa wajen bayyanar da mukamin wannan Imami da dogaro da shi da komawa zuwa gare shi da karbar hukumce-hukumce daga gare shi. Lokacin rayuwarsa, Imam Bakir (a.s.) da dansa Imam Sadik (a.s.) su ne yanki mafi wadata daga dukkan tarihin Musulunci wajen hadisi da ruwaya da kuma sanar da ilmummukan Musulunci.
Hakika malamai da maruwaita da malaman tafsiri da masu neman ilmummukan Musulunci daban-daban a wancan yanki zamanin suna yi wa Imam Bakir kallon kololuwar da tafi kowacce, kuma ilmin da ba wani ilmin da daukakarsa ta kusaci nasa.
Ibn Ahmad al-Hanbali ya siffanta shi da cewa: "Abu Ja'afar, Muhammadu al-Bakir ya kasance daga malaman Madina kuma ana ce da shi bakir ne domin ya tsaga ilmi wato ya tsaga shi ya sanar da asalinsa ya kuma fadada cikinsa([140])".
Ibn Jawzi ya nakalto daga wani shugaban Tabi'ai, Ada, wata maganar da ya yi kan Imam Muhammad al-Bakir (a.s.) cewa: "Ban taba ganin malamai suna kaskantar da kai cikin ilminsu kamar yadda na gani a gaban Abu Ja'afar al-Bakir ba([141])".
6- Imam Ja'afar bn Muhammad al-Sadik (a.s.):
To batun dansa, Ja'afar al-Sadik (a.s.) kuwa, hakika malamai sun yawaita yabo gare shi da kuma mahaifansa da kuma girmama matsayinsu. Za mu ambaci kadan daga cikin wadannan maganganu, kamar haka:
Allama Muhakkik Sayyid Muhsin Amin ya nakalto cewa: "Lallai Hafiz bn Akd al-Zaidi a cikin littafinsa na Rijalu, ya kawo mutum dubu arba'in daga magaskatan da suka ruwaito daga Ja'afar bn Muhammad (a.s.), ban da kuma wadanda ba a tabbatar da gaskiyarsu ba. Ya kuma ambaci rubuce-rubucensu([142])". Ibn Shahr Ashub ya kawo a cikin littafinsa, Manakib Aali Abi Dalib daga littafin Hilyatul Awliya' na Abu Nu'aim cewa: