A-Sanadin Wannan Hadisi
Maruwaitan wannan hadisi su ne kamar haka: 1-Waki 2-Sufyanus sauri 3-Habib bn Abi sabit 4-Abu wa’il 5-Abu hayyaj Asadi.
Dangane da maruwaici na farko kuwa abin da Ahmad bn Hambal wanda malamin hadisi ne yana cewa dangane da shi ya wadatar da mu inda yake cewa: Waki yayi kuskure a cikin hadisai guda 500, [80]Sannan ya cigaba da cewa: Ya kasance yana ruwaito hadisi da ma’ana (ba tare da kiyaye lafuzzan da aka yi amfani da su ba) Sannan ba shi da cikakkiyar masaniya a harshen larabci. [81]
Dangane da maruwaici na biyu kuwa (Sufyanu sauri) Ibn hajar Askalani ya ambace shi da cewa yana yin "Tadlis"a cikin hadisi. An ruwaito daga Ibn Mubarak cewa, Sufyanus Sauri ya kasance yana ruwaito hadisi yana yin "Tadlis"a lokacin da na iso sai ya ji kunya a kan abin da yake yi.[82] duk kuwa yadda aka fassara ma’anar tadlis ba ya dacewa da adalci.[83]
Dangane da maruwaici na uku kuwa, Habib bn abi Sabit, Ibn Hibban ya ruwaito daga Ata yana cewa: Ya kasance yana tadlis a cikin hadisi, don haka ba a bin hadisinsa, [84]
Amma mai ruwaya na hudu kuwa, wato Abu wa’il wanda sunan shi Shakik bn Salma Asadi Kufi, ya kasance abokin adawar Ali bn Abi Dalib ne, Ibn Abil Hadid yana cewa: Ya kasance daga cikin masu sabani da Imam Ali (A.S) Lokacin da aka tambaye shi Ali kake so ko Usman, Sai ya ce: wani lokaci na kasance Ali amma yanzu Usman.[85]
Sai dangane da maruwaici na biyar wato Abu Hayyaj Asadi wanda sunansa Hayyan bin Husain, Tirmizi yana kauce wa ruwaito hadisi daga gare shi, haka nan Ingantattun littattafan hadisai guda biyar ban da wannan ruwayar ba su ruwaito komai daga gare shi. [86]

B-Dangane Da Ma’anar Wannan Hadisi
Dangane da kirkirar wannan hadisi na Abu hayyaj kuwa kamar yadda muka gani a sama a fili yake abin, domin kuwa maruwaita wannan hadisi ta yadda ake tuhumar su yin tadlis da kuskure wajen ruwaya. Saboda haka ba za a iya dogara da shi ba wajen kafa dalili na shari’a. Koda an runtse ido daga raunata maruwaita wannan hadisi, ma’anarsa ba tabbatar da wannan ma’ana. Saboda haka: domin bayyanar da wannan al’amari ta hanyar bayyanar da wasu kalmomin don fahimtar ma’anar wannan hadisi.
1-"Kalmar: Kabran musharrafan"
2-"Illa sawwaitahu"
Wadannan kalmomin sune suka zo a cikin wannan hadisi;
Dangane kalma ta farko zamu yi bayani ne a kan kalamar "musharraf" wadda take da ma’anar daukaka wato abu madaukaki. Don haka ne wadanda suke daga babban gida kamar iyalan Manzo ake kiransu da sharifai, Sannan tozon rakumi saboda kasantuwarsa yana da daukaka a kan sauran jikinsa ana kiransa da "Sharaf".
Ya zo a cikin Tajul Arus cewa: Sharaf ma’anarsa shi ne wani wuri mai tudu, wato madaukaki. Sannan ana kiran tozon rakumi da sharaf, Sannan wurare masu bisa kamar gidajen sarakuna ana kiransu da Sharaf, Haka nan akan kira tudun da yake a kan bangaye da wannan kalma.[87] Saboda haka wannan kalma tana nufin abu mai daukaka ko kuwa kawai tana nufin tozon rakumi ko bayan kifi?.
Tare da kula da ma’anar kalmar "Sawwaitahu" kamar yadda zamu yi bayanin a kanta zamu fahimci cewa wannan kalma ta Sharaf a cikin wannan hadisi tana nufin ma’ana ne ta musamman.
Dangane da kalma ta biyu kuwa muna iya bayani kamar haka: Kalma ta Sawwaitahu da ta zo da ma’anar aiki wato baje wani abu ko dai-daita shi, ana mafani da ita a cikin harshen larabci da ma’anoni guda biyu.
1-Daidaita wani abu da wani abu daban ta hanyar tsawo ko girma ko makamancin haka. Saboda haka idan da wannan ma’ana kalmar sawwa ta zo tana da aikau guda biyu (maf’ul) wanda a cikin harshen larabci wannan maf’ul na biyu yana bukatar harafin jarra wanda zai dai-daita wannan abin da waninsa.[88]
2-Ma’ana ta biyu kuwa shi ne baje wani abu ta yadda zai daidaita babu tudu da kwari, saboda haka a nan wannan fi’ili na sawwa yana bukatar maf’uli guda daya, ba shi bukatar na biyu. Saboda haka duk lokacin kafinta ya daidaita wani katako, kawai zai ce na goge katako, (wato sawwaitul khashab). [89]
Saboda haka bambanci wannan ma’anoni guda biyu a bayyane yake, wato a ma’ana ta farko siffa ce ta abubuwa guda biyu, amma a ma’ana ta biyu kuwa siffa ce ta abu guda (wato daidaita wani abu ba tare da an hada shi da waninsa ba kamar yadda muka gani). Saboda haka yanzu mun fahimci ma’anonin wadannan kalmomi guda biyu: wato "Sawwaitahu da musharrafan".
Saboda haka muna iya fahimtar cewa wannan hadisi yana magana ne dangane da yadda wannan kabari yake domin kuwa yana magana ne a kan abu guda, ba wai kabari ba da kasa (wato ba a daidaita shi da kasa ba wato a daidaita shi kansa kabarin) Domin da haka ake nufi sai a ce "sawwaitahu bil ard". Saboda haka abin da Imam yake nufi a cikin wannan hadisi shi ne, duk inda ya ga wani kabari yana da tudu da kwari kamar tozon rakumi ya dai-daita shi ya gyara shi ya zama kamar dakali. Saboda haka wannan hadisi yana nuna mana yadda za a yi kabarin musulmi ta yadda za a baje samansa ba a yi masa tulluwa ba kamar bayan rakumi ko kifi.
Domin kuwa wannan zamani a kan yi kaburbura ne da tudu kamar yadda bayan rakumi yake, don haka ne Imam ya ba Abu hayyaj umarni da ya daidaita duk kabarin da ya gani a haka. Saboda haka wannan hadisi wace alaka yake da shi wajen rusa shi kansa kabari ko ginin da aka a samansa?!
Kuma cikin su maruwaitan wannan hadisi da masu sharhinsa sun bayyana ma’anar wannan hadisi kamar yadda muka yi bayani a sama.
1-Muslim ya ruwaito wannan hadisi karkashin babin "Amr bi taswiyatul kubur" wato ruwayoyin da suke magana a kan daidaita saman kabari, saboda haka muna iya cewa shi ma muslim abin da ya fahimta da ma’anar wannan hadisi kenan (wato kasantuwar kaburbura kamar yadda dakali yake ba kamar yadda bayan rakumi yake ba).
2-Muslim a farkon wannan babi ya ruwaito cewa: Fudhala tare da wasu mutane sun kasance a Rom, Sai wani daga cikin mutanensa ya rasu sai ya rufe shi ya yi kabarinsa kamar yadda ake dakali (Rectangle) sai ya ce haka na ji daga Manzo (S.A.W). ya ce: Ku yi kaburbura kamar haka wato samansu a baje ba tare da tudu ba.
Saboda haka dukkan wadannan hadisai suna bayyanar mana da ma’anar Kalmar Musharrafan da ta zo a cikin hadisi, ba tana nufin kasancewar kabari ya yi bisa ba daga kasa ko kada ya yi, tana nufin shi kansa kabarin kada ya kasance yana da tudu kamar bayan rakumi.
3-Nabawi kan sharhin wannan hadisi yana cewa: Bai kamata ba kabari ya yi bisa da kasa ba ko kuma ya zamana ya yi tudu kamar bayan rakumi. Ya cigaba da cewa dole ne bisansa ya kasance kamar kamun hannu guda sannan samansa ya zamana a baje ba mai tudu ba. [90]
4-Kurdabi a cikin tafsirinsa ya ruwaito wannan hadisi da aka ambata yana cewa: Wannan hadisi abin yake nunawa shi ne baje kabari shi ne Sunna, sannan yi masa tulluwa bidi’a ne.[91]
5-Ibn Hajar askalani bayan ya yi bayani a kan mustahabbancin baje saman kabari yan rubuta cewa: Hadisin Abi Hayyaj ba yana nufin cewa ba a baje ya zama daidai da kasa, abin da yake nufi shi ne a baje saman kabari ta yadda za a daidaita shi babu wani tudu a samansa, duk da yake cewa ya dan yi sama da kasa.[92]
Kamar yadda wasu ba su ba wannan bayani muhimmanci ba, (mu dauka ma wannan hadisi yana nufin cewa a baje kabari ta yadda zai zama daya da kasa babu wani tudu) kafa hujja da shi a kan rusa gine-ginen da aka yi a kaburburan bayin Allah, zai fuskanci matsaloli guda biyu:
1-Baje kabari ta yadda zai zama daya da kasa babu wani tudu ya sabawa dukkan ra’ayin fukaha domin kuwa dukkansu sun tafi a kan haka din cewa mafi karanci tashinsa ya kai kamun hannu guda.[93]
2-Idan muka dauka cewa wannan hadisi yana nufin cewa a baje kabari ta yadda zai zama daidai da kasa, to dole ne mu rusa kabari ta yadda zai zama daya da kasa, ba wani gini da aka yi ba a saman kabarin. Saboda haka sam wannan hadisi ba yana magana ba ne a kan ginin da yake kan kabari yana magana ne a kan shi kansa kabarin!.
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya yi umarni da girmama annabawa da wasiyyansu.