Amma wannan fahimta ba daidai ba ce, domin kuwa ana aiwatar da sallar wajibi ne kawai a cikin masallatai, sannan mustahabbi ne a gabatar da sauran sallolin mustahabbi a cikin gidaje. Sannan ya kamata ma mutum ya kasa ibadarsa zuwa gida biyu, wato wani bangare na farilla ya aiwatar da su a cikin masallaci, sannan bangaren nafiloli ya gabatar da su a cikin gida.
Mai yiwuwa wasu suga wannan bai inganta ba, amma hakikanin al’amarin haka yake domin kuwa ruwayoyi da dama sun karfafa hakan. Muslim a cikin sahih dinsa, ya kawo babi mai zaman kansa wanda yake nuna mustahabbancin sallar nafila a cikin gida. A kan haka ya ruwaito ruwayoyi da dama, amma a nan kawai zamu kawo wasu a matsayin misali:
Manzo mai tsira da aminci yana cewa: "Fiyayyar sallar mutum a cikin gidansa, sai dai sallolin wajibi"[66].
Wannan ruwaya tana nuna mana cewa Manzo (S.A.W) da sauran sahabbansa suna yin sallolinsu na nafila a cikin gidajensu, sakamakon haka ne gidajen annabawa da na salihan bayi suka zama wurin zikirin Allah da tsarkake shi. Sannan kuma dalilin wannan ne Allah ya ba da izini a kan daukaka su.
A yanzu dole ne mu ga me ake nufi daga matsayin wadannan gidaje! me ake nufi da daukaka wadannan gidaje?
A baya mun yi bayanin cewa, kafa hujja da wannan aya yana bayyanar da abubuwa guda biyu ne. Abu na farko kuwa shi ne, bayyanar da ma’anar "buyut" wanda muka yi cikakken bayaninsa a baya, yanzu lokaci ya yi da zamu yi bayani a kan abu na biyu wanda shi ne daukaka wadannan gidaje da Allah yake horo da shi.
Hakika kalmar "Rafa’a" cikin Kur’ani tana zuwa ne da ma’anar daga gini kamar yadda ta zo a cikin wannan ayar: "Shin halittar su ita ce tafi wahala ko kuwa sama wadda ya gina ta?! Sannan ya daga rufinta ya kuma daidaita ta?![67]
Amma kalmar "rafa’a" a cikin wannan aya ba yana nufi yin gini ba, domin kuwa an dauka cewa akwai gida ne, Kur’ani yana magana a kan siffofin wannan gida ne. saboda haka abin da ake nufi da wannan kalma a cikin wannan aya shi ne daga matsayinsu da girmama su, mafi yawan masu tafisiri sun dauki wannan ma’ana duk da cewa wasu daga ciki sun tafi a kan ma’anar da muka ambata a baya. [68]
A bayyane zamu iya cewa: Wuraren da Allah yake ambatar "Buyut" yana nufin gidajen da bayin Allah suke kwana suna yin tasbihin ubangiji kuma suna tsarkake shi. Saboda haka daukaka wadannan gidaje ba ya nufin daga gininsu ko rufinsu ba ne, abin da ake nufi shi ne daga matsayi da martabarsu. Daya daga cikin wannan girmamawa da daga matsayinsu kuwa shi ne ya zamana an tsarkake su daga dukkan wata kazanta, sannan duk inda suka dan lalace a gyara su.
Dukkan wannan aiki za a yi shi ne saboda girmama wadanda suka kasance a cikin wadannan gidaje suna tasbihin ubangiji suna salloli kuma ba su kin fitar da zakka, domin girmama wadannan mutane ne Allah ya yi horo da a girmama wadannan gidaje, sannan a kare su daga rushewa.
Kowa ya san cewa an rufe Manzo (S.A.W) a cikin gidansa, wato a wurin da ya kasance yana ambaton Allah da yabonsa. Saboda haka tare da bin hukuncin wannan aya gidan Manzo ya cancanci girmamawa da daukaka matsayinsa, sannan a kiyaye shi daga kowane irin rushewa da lalacewa. Sannan kuma a kaurace wa sanya masa duk wani nau’i na kazanta, kai da yawa daga bangarorin Madina kaburburan manyan bayin Allah ne. Kamar yadda ya zo a cikin ingantattun ruwayoyi sayyida Fadima (A.S) ita an rufe ta ne a cikin gidanta[69]
Haka nan Imam Hadi da Imam Askari (A.S) an rufe su a gidajensu wadanda suka kasance suna ibada da zikirin ubangiji a cikinsu. saboda haka wadannan gidaje bisa la’akari da wannan aya sun cancanci a daukaka su, sannan dole ne a kauce wa rusa su domin ya saba wa wannan aya. A unguwar Bani Hashim a garin Madina shekaru kadan da suka gabata gidan Imam Hasan da Husain (A.S) da makarantar Imam Sadik (A.S) sun kasance a wadannan wurare, Marubucin wannan littafi shi kansa ya ziyarci wadannan wurare, amma abin bakin ciki tare da fakewa da fadada masallacin Manzo duk an rusa wadannan wurare masu dimbin tarihi da albarka. Duk da cewa ana iya yin wannan aiki na fadada masallacin Manzo (S.A.W) ba tare da rusa wadannan wurare ba.

Soyayyar Manzo (S.A.W) Da Iyalansa
Ayoyi da hadisai da dama sun zo domin bayani a kan soyayya ga Manzo da ‘yan gidansa (A.S). Kur’ani ya nuna mana cewa imanin abin ceta shi ne ya kasance yana tare da wanda yake son Manzo da jihadi a tafarkin Allah fiye da komai a cikin zuciyarsa: "Ka ce idan iyayenku da ‘ya’yanku da matanku da ‘yan’uwanku da dukiyoyinku wadda kuka tara, da kasuwanci da kuke tsoran ku fadi a cikinsa, da gidajenku da kuke kaunarsu, idan sun kasance sun fi soyuwa a gareku daga Allah da manzonsa da jihadi a tafarkin Allah sai ku saurara har al’amarin Allah ya zo, Allah ba ya shiryar da mutane fasikai".[70]
Ayar sama tana magana ne a kan abubuwa guda uku wadanda mafi yawa soyayyar mutum takan ta’allaka da su, wato Iyalai da dukiya da gidaje da saye da sayarwa. Amma mumini na hakika shi ne wanda Allah da mazonsa da jihadi a tafarkin Allah ya fi soyuwa a gare shi fiye da wadancan abubuwa da aka ambata. Amma a wata aya ana bayani ne a kan soyayyar iyalan gidan Manzo ga abin da take cewa: "Ka ce ban nemi wani abu a kan sakon manzancin da na zo da shi ba a matsayin lada sai soyayya ga iyalan gidana". [71]
Sannan Manzo yana bayyana wasu abubuwa guda uku wadanda suke nuna dandana zakin imanin mutum, daya daga cikinsu shi ne soyayya ga Allah da shi manzon: Abubuwa guda uku ne duk wanda yake da su to ya dandana zakin imani, daya daga cikinsu kuwa shi ne ya kasance a wajan mutum son Allah da manzonsa ya fi komai a wajensa… Ruwayoyi da suka zo dangane da son Manzo da iyalansa sun wuce gaban mu kawo su a cikin wannan littafi, saboda haka a nan zamu takaia da wasu ruwayoyi a matsayin misali dangane da wannan al’amari, muhimmin abu a nan shi ne mu san ta yaya wannan soyayya zata tabbata, domin mutum ya isa zuwa ga wannan hadafi akwai hanyoyi guda biyu:
1-Mutum ta hanyar magana da ayyukansa ya yi koyi da koyarwar Allah da manzonsa, ta yadda zai kasance a rayuwa ya yi kokari ya ga bai kauce wa koyarwarsu ba, domin kuwa idan mutum ya zamana yana tsananin soyayya ga wani ba zai taba saba masa ba. Saboda haka ne ake cewa "soyayya ita ce biyayya". Wato sonka da abu yana lizimta maka da yi masa biyayya.
Sannan Imam Sadik (A.S) a wasu baituka yana bayyana bambanci tsakanin soyayya ta gaskiya da nuna soyayya da ba ta hakika ba, Inda yake bayani akan cewa: Kana sabon Allah alhali kana nuna soyayya gare shi, Wannan ba zai taba yiwuwa ba, Domin da sonka ya kasance a gaskinya ne, to da ka yi biyayya a gare shi, Domin kuwa masoyi yana bin abin da abin so yake so. [72]
2-Bayyana soyayya ta hanyoyi daban-daban kamar haka:
A- Nuna farin cikin yayin da masoyi yake cikin farin ciki, da nuna bakin ciki yayin da masoyi yake cikin bakin ciki;
B-Gabatar da buki na farin cikin a lokacin haiwuwar Manzo ko lokacin tayar da shi a matsayin ma’aiki;
C-Yada maganganunsa da abin da ya rubuta;
D-Kiyaye kayan tarihin da suka shafe shi;
D-Girmama Kabarinsa da yin gini domin kiyaye shi daga lalacewa;
Aikata wadannan abubuwa da makamantansu wadanda suke sun halasta a musulunci, yin su ga Manzo da iyalan gidansa ya nuna kauna ne a gare su.
Tirmizi yana ruwaitowa a cikin sunan dinsa: "Manzo (S.A.W) ya kama hannun Hasan da Husain sai ya ce: Duk wanda yake so na ya kuma so wadannan yara guda biyu da babansu da mamansu, to zai kasance a matsayina a ranar kiyama[73].
Kowannenmu ya san da cewa babban jikan Manzo yana rufe ne a "bakiyya" Sannan mai biye masa yana rufe a Karbala, Sannan wadannan wurare kodayaushe suna ganin al’ummar musulmi masu ziyara, Saboda haka duk wani gini kowane abu wanda za a yi domin kiyaye wadannan wurare, nau’i ne na nuna soyayya ga wadannan jikoki na Manzo kuma bin umarnin Manzo ne a kan soyayya gare su, kamar yadda muka yi bayani a ruwayar da ta gabata.
A yau al’ummu da dama suna kokari wajen tunawa da manyan tarihinsu (kamar sojoji da ‘yan siyasa da wadanda suka yi wasu ayyuka na gyara) ta hanyoyi daban-daban, sakamakon haka ne suke halarta jana’izarsu yadda ya kamata. Sannan su rufe a wani wuri na musamman a karkashin gini mai kawatarwa, ta yadda wadanda zasu zo a nan gaba kamar yadda na yanzu suke kulawa ta musamman a kan su, suma su yi kulawa da girmamamawa ta musamman a kan wadannan manyan mutane. Don haka mu ma musulmi dole mu yi kokari don yin gine-gine da zasu kare kabuburan manyan mutanemmu.

Kaburburan Manzanni Da Tarihin Magabata Ma’abota Tauhidi
Tafiye-tafiye domin bude ido zuwa wuraren da aka rufe annabawa da ‘ya’yansu wani abu ne wanda yake ba sabo ba a cikin al’umma. Wannan kuwa yana nuna cewa mabiya annabawa suna nuna kulawa ta musamman dangane da wadannan wurare, tare da gina gine-gine a kan kaburburansu suna kare su daga rushewa. A yanzu a kasashen Iraki, Palasdin, Jordan, Misra da Iran, akwai kaburburan annabawa (A.S) wadannan aka yi gine-gine masu kawatarwa ta yadda kodayaushe mutane suna zuwa wurin domin ziyara. Sannan dakarun musulunci da su kai hare-hare don bude garuruwan Sham, sam ba ruwansu da wadannan kabuburan annabawa, ba ma haka ba kawai sun bar mutanen da suke hidima a wadannan wurare don su cigaba da aikinsu a wajen kamar yadda suke a da. Sannan ba su nuna rashin amincewarsu a kan hakan ba ko kankani. Idan da yin gine-gine a kan kaburburan annabawa wani aiki ne da ya haramta kuma ya shafi shirka, da wadannan dakaru da suka zo da umarnin khalifa domin bude wadannan garuruwa duka sun rusa wadannan gine-gine, amma koda wani dan karamin canji ba su yi ba ga wadannan kaburbura an cigaba da tafiyar da su kamar yadda suke kafin wannan lokaci. Sannan har zuwa yanzu wadannan gine-gine suna nan kamar yadda suke ta suke jawo hankalin al’ummar musulmi da ma duk mai bin addinan da Allah ya aiko da su. Sannan a farkon zuwan musulunci ma musulmai sun rufe annabinsu a cikin dakinsa, kuma babu wani daga cikin wadannan musulmai da yake tunani cewa yin gini a kan kabarin Manzo haramun ne.
Sannan binciken littattafan tarihi da labaran tafiye-tafiyen masana addinin muslunci yana bayar da shedar cewa akwai daruruwan kaburbura a kasar da wahayi ya sauka da sauran kasashen musulmi:
1-Mas’udi wanda ya rasu 345Bh. wanda yake shahararren masanin tarihi ne, ga abin da yake cewa dangane da kaburburan imamai (A.S) da suke a "bakiyya" yana cewa:
"A bisa kaburburansu a akwai dutse wanda aka rubuta: Da sunan Allah mai rahma mai jin kai, godiya ta tabbata ga Allah wanda yake kashe al’umma yake kuma raya matattu. wannan shi ne kabarin Fadima "yar manzon Allah (S.A.W) wadda take ita ce shugabar matan duniya. Da kabarin Hasan bn Ali bn Abi Dalib da kabarin Ali bn Husain bn Ali bn Abi Dalib da kabarin Muhammad Bn Ali Bn Husain bn Ali Bn Abi Dalib da Kabarin Ja’farus Sadik Bn Muhammad". [74]
Mas’udi ya kasance daga cikin masana tarihi na karni hudu Bayan hjira. ’Yan salafiya wadanda suke da kankamo sun tafi a kan cewa, wannan karni da karnonin da suke kafinsu su ne fiyayyun karnonin tarihin musulunci, sannan ayyukan da suka yadu a tsakanin musulmi a wannan zamani suna nuna kasantuwar abubuwan da shari’a ta yarda da su. Amma abin bakin ciki wannan babban dutse wanda Mas’udi yake fada wanda aka yi wannan rubutu a kansa, sakamakon rushewar da wahabiyawa suka yi wa "bakiyya" yanzu babu shi a samuwa. Saboda haka yanzu wadannan kaburbura ba a iya bambance su.
Ibn jubair[75] (540-614) shahararren mai yawo bude ido ya ziyarci kaburburan annabawa da bayin Allah a kasashen Misra, Makka, Madina, Iraki da Sham, yayin tafiye-tafiyensa kuma ya yi bayani a kan kowane daya daga cikinsu a cikin littafinsa na tafiye-tafiye, ta yadda dukkammu zamu iya samun wannan a cikin wannan littafin nasa. Ta hanyar karanta wannan littafin musulmi suna samun masaniya a kan tarihin gina hasumiyoyi da gine-ginen kaburburan annabawa da waliyyan Allah. Dangane da abin da ya zo a cikin wannan littafin tafiye-tafiye nasa shi ne: Tarihin gina manya-manyan gine-gine a kan kaburburan Imamai da waliyyai da shahidai a tafarkin Allah, wanda yake komawa zuwa ga zamanin sahabbai da tabi’ai. Wanda yake nuna yadda a wancan zamanin da musulmai suke nuna kauna da kulawarsu dangane da shugabanni da manyan addini, ta yadda suka tashi domin gina wurare masu kawatarwa domin girmamawa gare su. Sannan babu wani daga cikin sahabbai wanda ya nuna cewa wannan aiki yana komawa ne zuwa ga shirka ko kuma ya saba wa tauhidi da kadaita ubangiji. Kamar yadda Ibn Jubair ya fara tafiyarsa daga gaban duniyar musulunci (Andulus) zuwa yammacinta ta yadda kasar Misra ta kasance wuri mafi kusa gare shi, Sai ya fara da wuraren tarihin da suke a Misra musamman Alkahira. Zamu kawo wasu daga cikin abin da ya rubuta daga cikin wadannan gine-gine na musulunci a wannan kasa:

Gini Mai Girma Na Kan Imam Husain (A.S) A Alkahira
Wasu sun tafi a kan cewa an rufe kan Imam Husain (A.S) a garin Alkahira, saboda haka suka gina wani wuri da sunan "Ra’asul Husain" inda mutane suke zuwa ziyara daga cikin gida da waje. Masu sabon aure a wannan gari sukan je Masallacin Husain (A.S) wanda yake a wannan wuri sukan yi dawafi.. [76]
Ibn Jubair yana cewa: Daya daga cikin wurare masu tsarki a Alkahira shi ne Wurin da aka rufe kan Husain, an kawata wannan wuri da azurfa, wannan gini yana da girma da daukaka ta yadda harshe ba zai iya siffanta shi ba. A kan wannan gini akwai wani dutse na alfarma kai kace madubin Indiya ne, ta yadda yake haske yana dauko hotunan abubuwan da suke a gabansa. Yace: Da idanuna na ga masu ziyarar Husaini (A.S) yadda suke kuka suna sumbatar yadin da aka dora a kan abin da aka rufe kabarinsa da shi suna neman tabarraki suna addu’a, ta yadda kwallarsu kamar ta rufe wannan kabari.
Ibn Jubair ya ambaci wani wuri da ake kira "Karafa" inda yake cewa yana daga cikin wurare masu ban al’ajabi kamar yadda ya bayyana akwai kaburburan annabawa da iyalan Manzo da sahabbansa da tabi’ai da sauran kaburburan manyan malamai da aka rufe a wannan wuri. Dan Annabi Salih (Raubil) dan Annabi Yakub (Ishak) da matar Fir’auna dukkansu an rufe su ne a wannan wuri. Haka nan daga cikin iyalan Manzo akwai dan Imam Ja’afar mai suna kasim da dansa Abdullah bn Kasim da dansa Yahya bn Kasim, sannan da kabarin Ali bn Kasim bn Abdullah bn Kasim da dan’uwansa Isa bn Abdullah.
Ibn Jubair ya ambaci da yawa daga cikin ‘ya’yan Ali (A.S) wadanda aka rufe su a can. Haka nan akwai kaburburan Sahabbai tabi’ai ba shugabanni kamar Imam Shafi’i ta yadda yake magana a kan girma da matsayin haraminsa, kamar yadda yake cewa: Salahuddin Al’ayubi shi yake biyan kudin da ake bukata domin gabatar da bukukuwa a wannan harami na Imam Shafi’i.

Hasumiyoyi Masu Tsawo A Garin Makka
Ibn Jubair yana bayyana yadda garin Makka ya kasance da hasumiyoyi masu daukaka a kan kaburbura a garin Makka, wanda ambatonsu a nan zai janyo mu tsawaitawa. Akwai wurare kamar Maulidin Nabi, Maulidin Zahara da Darul Khaizaran (wurin ibadar Manzo na sirri). Sannan ya ambaci wurare masu girma na sahabbai da tabi’ai a Madina, A cikin wannan kuma yake ambatar Raudhar Abbas bn Ali bn Hasan bn Ali (A.S) wanda yake da gini mai tsayi a garin Madina, sannan ya cigaba da bayyana yadda wadannan wurare suke.
Idan muna so mu fadi duk abubuwan da Ibn Jubair ya gani a garuruwan Sham da Iraki na sahabbai da manyan bayin Allah zai janyo mu tsawaita a cikin hakan. Don haka muna iya wadatuwa da wannan. Saboda haka wanda yake so ya samu karin bayani sosai a kan haka sai ya koma zuwa ga wannan littafi nasa.[77]
IBn Najjar (578-643) [78]: Muhammad bn Mahmud wanda aka fi sani da Ibn Najjar wanda yake shi ma shahararren musulmi mai yawon shakatawa ne a cikin littafinsa "Madinatur Rasul" yana cewa: "Akwai wata dadaddiyar hasumiya mai tsawo a farkon makabartar "bakiyya" wadda take da kofofi guda biyu wanda kowace rana ake bude daya daga cikinsu domin masu ziyara.[79]
Wadannan suna daga cikin littattafan tafiye-tafiye da muka dauko daga cikinsu, sannan ana iya komawa zuwa ga wasu littattafai na tafiye-tafiye wadanda suke tabbatar da yin gine-gine a kaburburan annabawa da bayin Allah wani abu ne da yake sananne kuma wata Sunna ce mai tsawon tarihi a tsakanin masu kadaita Ubangiji.
Ibn Hajjaj bagdadi (262-392) wanda yake mawaki ne shararre a iraki ya yi wata kasida ta yabon Imam Ali (A.S), sannan ya yi wannan kasida ne a haramin Imam Ali (A.S) a cikin taron mutane, a farkon wannan kasida ga abin yake cewa: "Ya kai ma’abocin wannan hasumiya fara a garin Najaf duk wanda ya ziyarce ka kuma ya nemi ceton Allah daga gareka to Allah zai karbi cetonsa". Wannan baiti yana nuna cewa kabarin Imam Ali (A.S) a farkon karni na hudu ya kasance yana da hasumiya.
Abin mamaki a nan shi ne a mahangar ilimin Usulul fikh haduwar mutane a kan hukuncin wani abu har zuwa karnoni da dama yana nuna ingancin wannan abin ne. Amma musulmi sun hadu a kan ingancin gine-gine a kan kabarin annabawa da waliyyan Allah tsawon karnoni masu yawa, amma mahangar wasu wannan bai isa ya zama dalili ba, ta yadda kowane lokaci suna kokarin kaucewa a kan yarda da wannan al’amari.

Gineginen Tunawa Da Bayin Allah Da Dalilai Masu Sabani A Kan Haka
Mun yi bincike a kan dalilan da suke nuni da ingancin ziyar da girmama kaburburan bayin Allah daga Kur’ani da Sunna da tarihin magabata, amma yanzu lokaci ya yi da zamu yi bincike a kan dalilan masu inkarin hakan. Wanda sukan yi riko da hadisin Abil Hayyaj Asadi ne a kan hakan, yanzu zamu auna wannan hadisi ta yadda zamu ga kimarsa ta hanyar ma’aunin da ake gane ingancin hadisi.
Muslim a cikin sahih dinsa yana ruwaitowa daga Abil Hayyaj kamar haka: "Ali bin Abi Dalib ya ce da ni: Ba na aike ba a kan abin da Manzo ya aika ni a kansa ba, kada ka bar wani hoto sai ka lalata shi, ko wani kabari mai tudu sai ka daidaita (baje) shi."
Masu adawa da wannan al’amari suna kafa dalili ne da wannan hadisin a kan haramcin gina haramin wani Imami daga cikin Imamai (A.S) sakamakon haka ne a shekara ta 1344Bh suka rusa makabartar "bakiyya" a wannan rana ne kuma a cikin jaridar "Ummul kura aka sanya tambaya da amsa dangane da dalilan da suka sanya aka rusa wannan makabarta, domin mu gane ta yadda aka kafa hujja da wannan hadisi yana da kyau mu yi bincike a kan ma’ana da kuma dangane wannan hadisi: