Ziyarar Masallatai Guda Bakwai
A sassa daban-daban na garin Madina akwai wasu masallatai guda bakwai wadanda mahajjata sukan ziyarta yayin da suka je Madina, Idan ma muka kara da (masallacin Raddi shams, da na Bilal da na Ijaba) Yawansu zai wuce bakwai. Mahajjata suka yi salla raka’a biyu a wadannan masallatai musamman sukan fi ba da muhimmanci a kan masallacin Imam Ali (A.S) Yanzu tambaya zata iya zuwa cewa: Idan har yin salla a wadannan masallatai ba shi da wani fifiko a kan sauran masallatai, to me ya sa mahajjata suke zuwa ziyarar wadannan masallatai sannan su yi salla a cikinsu? alhali kuwa wannan bai zo ba a cikin shari’a, saboda haka wannan zai zama "Bidi’a" kenan a cikin addini.
Amsar wannan tambaya kuwa a fili take:
Tafiya domin ziyarar wadannan msallatai ba wai don yazo a cikin shari’a ba ne, ko kuma yin salla a cikin wadannan masallatai yana da wani fifiko na musamman, sam ba haka ba ne manufar tafiya zuwa wadannan wurare sai daya daga cikin biyu ne kamar haka:
1-Tunawa da musulman farko wadanda suka kasance cikin mawuyacin halin yakin Khandak amma a cikin wannan hali ne suka gina wadannan masallatai don su yi salla kuma suka cigaba da yakinsu. Domin kuwa wasu daga cikin wadannan masallatai suna wuraren da aka gwabza tsakanin sojojin tauhidi da na shirka yayin da aka kashe gwarzon shirka (Amru bn Abdu wud) kuma sakmakon haka ne gwamnatin dagutu ta kawo karshe.
Halartar musulmi a wadannan wurare tana tuna musu da wadannan abubuwa da suka faru a wannan wuri, sannan yana kara karfafa alakarsu da wadancan musulman farko.
2-Amma ma’ana ta biyu kuwa da zata iya zama dalilin da ya sa musulmai suke zuwa wadannan masallatai ita ce, domin neman tabarraki daga wadannan wurare, domin jinanan shahidai a kan hanyar tauhidi a wadannan wurare ne ya zube, Saboda haka wannan wurare sun sheda kai da kawon shahidan musulunci, sannan kuma wuri na kai-da-kawon manyan musulmai.
Wadannan manufofi su ne suke sanya musulmi suna tafiya zuwa wadannan wurare da makamantansu, kamar wurin da aka yi yakin khaibar da Fadak, duk sun samo asali ne daga wadannan manufofi guda biyu.
Amma yin salla a wadannan wurare bayan musulmi sun shiga wadannan masallatai domin aiwatar da umarnin ubangiji cewa duk yayin da mutum ya shiga wani masallaci to ya gabatar da salla raka’a biyu a matsayin gaisuwa ga shi masallacin. Saboda haka ba wannan ba ne hadafinsu na zuwa wadannan masallatai ba domin su gabatar da salla a wajen. Wannan niyya tana zuwa ne bayan sun shiga masallatan.

Girmama Kaburbura Masu Tsarki
Al’ummun da suke raye a kasashen da suka cigaba a duniya zaka ga suna kokari wajen kare kayan tarihi kuma suna nuna soyayyarsu ga wadannan abubuwa na tarihi. Sannan suna iya kokarinsu da su kare wadannan kayan tarihi don kada su bata ko su lalace. Domin kiyaye wadannan kayan tarihi kuwa wadanda suke nuna cigabn su a tsawon tarihi har ma’aikatu na musamman suka samar da ma’aikata kwararru domin kawai wannan aiki. Sakamakon haka ne ba su ba da wata dama da zata sanya wani guntun abu daga cikin wadannan kayan tarihi da suka hada da wani allo wanda aka yi wani rubutu a kai ko guntun jirgin ruwa da ya bata. Domin sun yi imani da cewa wadannan kayan tarihi suna ba da wata sheda ce ta musamman ta su wadannan al’umma. Mutanen da suka yanke daga al’ummarsu da manyan tarihinsu da suka gabata suna da hukuncin yaro ne wanda ya bata daga hannun iyayensa. Cigaban musulunci wani cigaba ne wanda yake mai girman gaske wanda a karnonin tsakiya shi ne kawai cigaban da babu kamarsa.
Sakamakon koyarwar da Musulmai suka samu daga littafinsu na sama, sun kafa cigaban da ba a taba yinsa ba a tarihi. Wanda ya kai kololuwarsa a cikin karni na hudu, ta yadda gabas da yammacin duniya suka shaida haka, kamar yadda ya gina Tajmahal na kasar Indiya da Kasar (Spain) sauran gine-gine masu ban al’ajabi, wanda ta hanyar kaitsaye ko kuma ba kaitsaye ba. Kamar yadda masana na yamacin duniya suka tabbatar da cewa cigaban yammacin duniya ya samu asali ne ta hanyar Andulus ko kuma ta hanyar yakin da ya auku tsakanin musulmi da kiristocin yammacin duniya.
Cigaban musulunci ya fara ne da aiko manzon Musulunci (S.A.W) ko kuma da wata ma’ana ya fara ne da haihuwar shi manzon, Sannan da taimakon mabiyansa ya cigaba ta kafuwa da yaduwa a sauran sassan duniya. Gine-ginen da suke dangane da Manzo ko kuwa wasu daga cikin sahabbansa suna daga cikin wannan cigaba na musulunci. Sannan kuma wannan ba mallakin wani ba ne ta yadda zai yi abin da ya ga dama da su, wannan na dukkan al’ummar musulmi ne. Saboda haka babu wata hukuma ko wasu mutane da zasu yi abin da suka dama da wannan kayan tarihi da cigaban musulunci ba tare da izinin sauran musulmi ba. Ta yadda ta hanyar yaki da bidi’a da tsayar da tauhidi su kawar da wadannan kayan tarihi.
Tarihin musulunci yana gaya mana cewa: An haifi manzon musulunci ne a shekara ta 570 bayan haihuwar Annabi Isa (A.S) Sannan bayan ya kai shekara 40 da haihuwa aka aiko shi a manzanci. Bayan aiko shi da manzanci ya yi shekara 13 a garin Makka yana isar da wannan sako. Bayan wannan ne tare da umarnin ubangiji ya bar inda aka haife shi zuwa garin Madina, Inda a can ne ya yi shekara 10 yana isar da wannan sako na musulunci kuma ya yi fito na fito da mushrikai makiya musulunci, sakamkon bayar da shahidai da ya yi a wannan hanyar ya samu damar daga tutar musulunci a dukkan yankin kasashen Makka da kewayenta (yanki mai girma daga cikin Jaziratul Arab) A shekara ta 11 bayan hijara ne ya koma zuwa ga rahamar Ubangijinsa. Sannan bayan wafatinsa Sahabbansa suka cigaba da wannan aiki na yada musulunci a sassan duniya daban-daban.
Wannan kuwa ya shafi rayuwar da kokarin Manzo da iyalansa da da mabiyansa ne (kamar yadda muka fadi cewa shi ne tushen wannan cigaba) Saboda haka dole mu yi kokari wajen kare wannan asali.

Kaburburan Shugabannin Addinin Musulunci Suna Nuna Tarihin Musulunci
Dole ne mu kula da cewa duk wani abu da zai faru a wani zamani yana kore duk wani shakku ga wadanda suke rayuwa a wannan zamani. Amma tare da gushewar zamani sakamkon ko-in-kula na mutane zai sanya wannan yakini da tabbas da yake ga mutane ya ragu. Ta yadda a hankali zai zama ana shakku da tararrabi a kan faruwar wannan abin, ta yadda wani lokaci ma zai koma kamar wata tatsunniya. Abubuwan da suka faru ga addinan da suka gabata a lokacin da suka faru babu wani shakku ko taraddudi a kan faruwarsu, amma sakamakon rashin kulawa a yau sun zama kamar tatsunniya.
Maimaita wannan mummunan al’amari dangane da musulunci yana da matsala fiye da yadda ya faru a sauran addinan da suka gabata. Domin kuwa addinin musulunci addini ne wanda har zuwa ranar tashin kiyama dukkan mutane dole ne su yi biyya a gare shi, ta yadda zasu sadu da haske ta hanyar hakan. Mutanen da zasu zo nan gaba kuwa zasu iya biyayya ga wannan addini yayin da suka kasance sun samu yakini dangane da hakikaninsa.
Babu shakka daya daga cikin hanyar kiyaye wannan tabbaci na hakikanin addinin musulunci kuwa shi ne kiyaye abubuwan da suka shafi rayuwar Manzo da sauran shugabannin addinan musulunci.
Magabatanmu Allah ya rahamshe su, sun yi hidima mai yawa dangane da al’ummar yanzu, ta yadda suka kiyaye mana abubuwan da suka zo tun farkon zuwan musulunci. Sakamakon haka ne kai tsaye muke kiran sauran al’umma zuwa ga wannan addini wanda yake hakikaninsa bai samu wani canji ba, ta yadda muke cewa: Karni goma sha hudu ne da suka gabata shugaban Bani Hashim ya ta shi da manzanci daga Allah ya kuma kira mutane zuwa ga Tauhidi da kaurace wa bautar gumaka da kafirci, bayan Mu’ujizozin da ya zo da su. Sannan ya zo da littafi mai girma wanda ya karya makiyansa da shi. Sannan har zuwa yanzu wannan Mu’ujizata har abada tana nan ba tare da wani canji ba.
Wanda kafin ya fara bayyana kiransa ya kasance yana tafiya kogon hira domin yin ibada ga Allah madaukaki. Bayan cika shekara arba’in da rayuwarsa ya fara kiransa. Wasu mtane daga cikin mutanen Makka suka yi imani da shi, yayin da wasu mafi yawa suka kaurace masa, har ma suka yi nufin su hallaka shi, amma Allah da ikonsa ya boye shi a wani kogo da ake kira (Thaur) wanda yake kudancin garin Makka, ta yadda ya tsira da makiya. Bayan nan kuma ya yi hijira zuwa garin Madina, a wannan gari ne mutane Aus da Khazraj (wadanda ake kira da Ansar) suka amsa kiransa suka taimake shi. Manzo a tsawon zamansa a garin Madina ya gwabza yaki mai tsanani tsakaninsa da mushrikai da Yahudawa, Ta wannan hanyar ne ya gabatar da shahidai da dama a tafarkin Allah ta yadda suka ba da jinansu a yakin Uhud, Khaibar da Hunain. Manzo (S.A.W). Ta hanyar aika mabiyansa zuwa sassa daban-daban na wannan nahiya ta kasashen larabawa ya samu damar isar da sakonsa zuwa ko’ina a wannan lokaci. A shekara ta 11 ne bayan hijira ya koma zuwa ga ubangijinsa kuma ya yi umarni da rufe shi a cikin dakinsa. Bayan wafatinsa mabiyansa suka cigaba da hanyar da ya bari, ta yadda ba tare da bata lokaci ba, ya yada wannan addini tare da al’adun da Kur’ani ya zo da su a dukkan sassan duniya.
Wannan shi ne wani yanki na tarihimmu wanda bayan wucewar karni 14 ake maimaita shi. Saboda haka dole mu yi kokarin wajen kare wannan tarihi na mu da duk abin da ya shafi hakan, ba wai ta hanyar wasu dalilai ba marasa tushe mu ruguza wannan tarihi namu!.
Kamar yadda ya kasance mu shagala game da kiyaye wadannan kayan tarihi, ta yadda babu bambanci a wurin dangane da samuwarsa da rashinsa duk daya yake, (abin da ma ya fi muni shi ne yadda ake ganin cewa rusa wadannan abubuwa yaki ne da yaduwar shirka) Ta yadda a cikin kankanin lokaci an manta da wasu abubuwa na tarihin musulunci, don ha ka bayan wani lokaci zai yiwu a fara shakku dangane da wasu abubuwa na hakikanin wannan kira da Manzo ya zo da shi. Ta yadda kamar su Salman Rushudi maimakon canza addini sai ya yi kokarin inkarin addinin da tarihinsa baki daya.

Daukar Darasi Daga Tarihi
Mutum kodayaushe yana kokari ne ya kalli kowane al’amari ta hanyar idanu ko makamancinsu, domin kuwa ilimin da yake samuwa ta wannan hanya mutum ya fi dogara a kansa. Cikinsa a babban hanyar da ake bi domin tabbatar da wani abu dangane da abin da ya shafi rayuwar zamantakewa, kuma wanda aka fi dogara da shi domin yana ba da sakamakon da ake samun yakini, shi ne tarihi, Kur’ani mai girma yana ba da tarihin magabata ne domin daukar darasi. [55] Dangane da shari’un da suka zo daga sama muna iya daukar shari’ar Annabi Isa (A.S) a matsayin misali. A akidar musulmi Annabi Isa matsayin annabin Allah yake, wanda yake mai albishiri ne ga zuwan Manzo Muhammad (S.A.W), sannan ya zo da littafi mai suna "Injil" wanda yake dauke da haske a cikinsa, amma muna samun tabbas a hakan ne ta hanyar Kur’ani mai girma.
Amma sakamakon matashin da yake yammacin duniya ba shi da imani da Kur’ani ta yadda zai kalli Annabi Isa ta wannan fuskar, a yau dangane da zuwan Annabi Isa da littafinsa yana da shakku a kansu. Domin kuwa ba shi da wata alama ta wannan kira a hannunsa ta yadda zata taimaka masa ya samu yakini a kan hakan. Domin kuwa Masih ba shi da kabari ko mahaifiyarsa da sahabbansa da zasu tabbatar da zuwansa. Sannan littafinsa an hakaito shi ta hanyoyi daban-daban ta yadda zai yi wahala mutum ya gane gaskiyar al’amarin. A takaice babu wani abu wanda zai tabbatar wa matashin yammacin duniya gaskiyar zuwan Annabi Isa da littafinsa. Saboda haka sabanin magabatansa yana shakku a kan hakikanin wannan al’amari.
Saboda haka mu musulmi dole mu dauki darasi daga wannan abin da yake faruwa daga kiristanci. Ta yadda zamu kiyaye duk wani abu wanda yake ya zo daga Manzo kuma yana matsayin sheda ne ga da’awar da shi Manzo ya zo da ita, (duk yadda ya kasance abu dan karami ne) Ta yadda zamu kare duk wani abu wanda zai sanya wadanda zasu zo bayammu su yi shakku a kan gaskiyar addinin musulunci, kamar yadda matashin yammacin duniya yake shakkun gaskiyar Annabi Isa da Injila.
Muna iya amfana daga ayoyin Kur’ani da suke nuni da cewa: Al’ummun da suka gabata sun kasance suna kiyaye duk wani abin da manzonsu ya zo da shi, ta yadda suke tafiya da shi yayin wani kwami mai zafi da yake a gabansu. Ta yadda ta hanyar neman albarkaci da wannan abin daga annabawansu don neman samu cin nasara daga mushrikai abokan gabarsu. A matsayin misali Bani Isra’il sun kasance suna tsaron wani akwati wanda duk abin da musa da iyalansa suka bari yana cikinsa, sannan suna neman tabarruki daga gare shi kuma yayin karo da makiya suna daukar shi domin neman cin nasara.[56]
Kasantuwar albarkar da muhimmancin wannan akwati ya zamana mala’iku suke daukarsa. Idan har ya kasance kiyaye wasu abubuwa na magabata (kamar wannan akwatin) wani abu ne marar kyau, to me ya sa Kur’ani mai girma yake ambaton wannan al’amari da harshe na yabo, kuma me ya sa mala’iku suke daukarsa, sannan me ya sa bayan dauke wannan akwati daga "Amalika" a cikin wannan aya ya zama wata alama ce da take nuna wanda zai jagoranci wannan runduna ta yaki?! Yara wadanda ba su balaga ba, su ne suke wasa da kayan da iyayensu suka bar musu, ta yadda cikin sauki suna iya batar da su. Amma magadan da suke da hankali kuma sukan amfani da matsayin wannan abin da iyayensu suka bar musu, suna rike wadannnan kaya ne iya karfinsu. Al’ummar musulmi ma sakamakon cigaban da suka samu bayan wafatin Manzo (S.A.W), su kiyaye duk wani abu da ya bari, wannan kuwa har da kwarar gashinsa sun kasance sun sanya ta wani wuri na musamman suka ajiye ta.

Matsayin Gidajen Annabawa A Cikin Kur’ani
Gidajen annabawa da manyan bayin Allah suna da wani matsayi na musamman, wannan kuwa a fili yake matsayin da suke da shi bai shafi wani abu na duniya ba ne, domin idan da haka ne, gidajensu ba su da wani bambanci da sauran gidajen mutane domin an gina su ne da yumbu da tubali kamar na kowa. Wadannan gidaje suna da wannan matsayi ne sakamakon mutane masu matsayi da suka zauna a cikinsu.
Kur’ani mai girma[57] yana siffanta hasken ubangiji da fitila mai haske ta yadda yake haske kamar tauraruwa. A ayar da take biye ma wannan aya kuwa ya nuna cewa wurin wannan haske yana gidajen wasu mutane masu girma wadanda suke ambaton Allah a ciki safiya da yamma.[58]
A cikin wannan aya jimlar da take cewa "Ana tasbihinsa safiya da yamma, tana nuna dalilin da ya sa aka daukaka wadannan gidajen wadanda aka ambata a cikin ayar da ta gabata. A ayar da take biye mata kuwa an siffanta masu yin ibada a cikin wadannan gidaje ne, inda yake cewa: "mutane ne wadanda kasuwanci ba ya shagaltar da su daga ambaton Allah da tsayar da salla, domin suna jin tsoron ranar da zukata da idanu suke jujjuyawa suna tsorata.[59]
Wannan aya tana bayani ne a kan girma da daukakar gidajen da ake zikirin Allah ake kuma tsarkake shi a cikinsu. A nan dole ne mu yi bayani a kan abubuwa guda biyu kamar haka:
1-Me ake nufi da gidaje a cikin wannan aya?
Masu tafsiri sun yi sabani a kan ma’anar wannan ayar ta yadda kowane ya dauki daya daga cikin ma’anonin kansa:
A-Ana nufin gidaje a cikin wannan aya da masallatai guda hudu
B-Ana nufin dukkan masallatai ne a cikin wannan aya
C-Ana nufin gidajen Manzo ne
D-Masallatai da gidajen Manzo
A cikinwadannan ma’anoni da aka ambata a kasa ma’ana ta uku ce kawai zata iya dai-dai kamar yadda zamu kawo dalilai da suke karfafa hakan.
1-Ta fuskar lugga kalmar Buyut jam’i ne na bait wato gidan kwana. Ibn manzur ya tafi a kan cewa bait yana nufin gidan mutum. Ragib kuwa yana cewa bait shi ne inda mutum yake fakewa da dare. Amma mawallafin "almunjid kuwa cewa ya yi, ma’anar bait tana nufin wurin zama wanda ya hada da hema da gidan da aka gina kasa da tubali.
Saboda haka fassara kalmar bait da masallaci wanda yake wurin ibada na kowa da kowa bai inganta ba, domin kuwa ba wurin da mutum yake fake wa ba ne da daddare. Saboda haka idan ma har ya inganta, amma abin zai zo ga kwakwalwar mutum shi ne gidan kwana, don haka idan har yana nufin masallaci ne ana bukatar abin zai nuna hakan. Ba tare da hakan ba, ba za a karbi wannan ma’ana ba.
Da wani kalamin ma Bait ya samu asali ne daga baituta wato mutum ya tsaya wani wuri har zuwa safe. Idan har ana mabata gidan mutum da bait saboda mutum yana kwana a cikin wannan gida ne har zuwa safe. Tare da kula da wannan ma’ana ta kalamar bait, fassara ta da ma’anar masallaci yana bukatar abin da yake nuna hakan, ba tare da wannan ba ba za a karbi wannan fassara ba.
2-Kur’ani duk lokacin da zai yi magana a kan wurin da al’umma suke bauta yana amfani ne da kalmar "masjid" ko "Masajid" ne. Sakamakon haka ne wannan kalma an yi amfani da ita sau 28 acikin Kur’ani mai girma. Amma duk lokacin da za a yi nagana a kan wurin da mutane suke kwana a kan yi amfani da kalmar "Maskan, Ma’awa" ne. Sannan an yi amfani da kalmar bait ta fuskar jam’i ko tilo. Saboda haka wannan kalma ta zo sau 66 a cikin Kur’ani da wannan manufa, sakamakon haka muna iya fahimata cewa a cikin Kur’ani kalmar "Masjid" da "bait" ba suna nufin ma’ana guda ba ne. saboda haka idan aka nemi fassara su da ma’ana guda zai zama da’awa ba tare da dalili ba.
Idan Kur’ani ya kira masallacin Ka’aba da "baitullahi"[60] ba don yana wurin bautar Allah ba ne, domin kuwa mun san cewa Ka’aba alkibla ce ta masu bautar Allah ba wurin da ake ibada ba. Saboda haka hada sunan Allah da wannan wurin kawai yana nuna girmamawa ne, kai ka ce wannan gida na Allah ta yadda za a girmama shi girmamawa ta musamman.
3-Akwai muhimmin bambanci tsakanin masallaci da gida, Bait ana nufin bangaye guda hudu da aka yi wa rufi, amma masjid kawai bangaye guda hudu ne, wato rufi ba sharadi ba ne kafin ya zama masallaci. Da yawan akan gina masallatai a wuraren da suke da zafi ba tare da rufi ba, wanda daya daga cikinsu shi ne masallacin ka’aba, alhalin kuwa gidan da mutum yake kwana yana bukatar rufi.
Wannan aya da zata zo a kasa tana bayar da sheda a kan bukatar gida daga rufi:
"Ba don hikimar Allah ta yi rigaye ba akan cewa komai zai kasance bai daya, da mun sanya gidajen wadanda suka kafirce wa Ubangiji mai rahama masu rufi da azurfa da tsanin da suke amfani zuwa sama".[61]
Wannan aya tana bayyana cewa "bait" sabanin "Masjid" yana da rufi, sannan ba don wata maslaha ba da Allah madaukaki ya bambanta gidajen kafirai da na muminai ta yadda zai sanya gidajen Kafirai rufinsu ya zama na azurfa, amma sai bai yi hakan ba.
4-Jalaluddin Suyudi ya ruwaito daga Anas bn Malik Yana cewa: Yayin wannan aya wadda take cewa "A cikin gidajen da Allah ya yi Umarni da a daukaka….". Sai ya karanta a cikin masallaci, sai wani daga cikin sahabban Manzo ya mike ya tambayi Manzo me ake nufi da wadannan gidaje?
Sai Manzo ya amsa masa da cewa: Ana nufin gidajen Annabawa, a wannan lokaci sai Abubakar ya mike ya ce: Ya nuna gidan Ali da Fatima (A.S) ya ce wadannan gidajen suna cikin wadanda Allah ya yi izini da daukaka su?. Sai Manzo (S.A.W). ya amsa masa da cewa: E, suna ma daga cikin mafi daukakarsu.[62]
Imam Bakir (A.S) yana cewa: Abin da ake nufi da gidaje a cikin wannan aya shi ne, gidajen Annabawa da gidan Ali (A.S)[63]
Bisa dogaro da wadannan dalilai muna iya fahimtar cewa abin da ake nufi da gidaje a cikin wannan aya ta cikin Suratun Nur shi ne gidajen annabawa da waliyyan Allah, sakamakon tasbihi da tsarkake Allah da ake yi a cikinsu yake da wani matsayi na musamman, kuma Allah ya yi izini da yin kokari wajen a daukaka su.
5-Sannan dalili wanda yake a fili a kan cewa abin da ake nufi da gidaje a cikin wannan aya su ne, ayoyi guda biyu da suka zo kamar haka: Allah madaukaki yana yi wa Annnabi Ibrahim da matarsa magana kamar haka:
A-"Rahmar Allah da albarkarsa ta tabbata a gare ku ya ku ma’abota gida[64];
B-Allah Kawai ya yi nufi ya tafiyar muku da kazanta yaku Ahlul Bait, ya kuma tsarkake ku tsarkakewa[65]; Kai ka ce wadannan gidaje su ne cibiyar hasken ubangiji.
Tare da kula da wadannan dalilai guda biyar da muka kawo muna iya cewa: Masati da daukakar wadannan gidaje sakamakon wadanda suke zaune a cikinsu ne, suna tasbihin ubangiji suna tsarkake shi. A hakikanin gaskiya wannan aya tana magana ne dangane da gidaje irin gidajen Annabi Ibrahim da Manzo (S.A.W). Wannan kuwa sakamakon tasbihi da tsarkake ubangiji da ake yi a cikinsu. Shi ne ya sanya Allah madaukaki ya daga martaba da darajarsu.
Mai yiwuwa a ce: Karkashin wannan aya ana cewa: "Yana tasbihinsa a cikinsu safiya da yamma": wato abin da ake nufi da "Buyut" Masallatai, domin kuwa musulmin farkon zuwan musulunci sun kasance suna halarta sallar jam’i baki dayansu. saboda haka tasbihi da tsarkake ubangiji ana yin sa ne a cikin masallaci.