4-Imam Sadik (A.S) yana cewa Manzo. (S.A.W) yana cewa: "Duk wanda ya ziyarce ni zan zama mai cetonsa a ranar tashin kiyama". [43]
Ruwayoyin da dukkan bagarori guda biyu suka ruwaito ta fuskar ma'ana ba su da bambanci, saboda haka suna karfafa abubuwa guda biyu kamar haka:
A-Duk wanda ya je Makka bai ziyarci Manzo ba, to ya yi wa manzon jafa'i.
B-Duk wanda ya ziyarci Manzo, Manzo zai cece shi a ranar kiyama. Saboda haka don mu takaita wadannan ruwayoyi guda takwas daga Shi’a da Sunna sun wadatar wanda yake son karin bayani sai ya koma zuwa ga littfan da muka ambata.

Tattaunawar Imam Malik Tare Da Mansur Dawaniki
Kadhi Iyadh ya nakalto tattaunawar Imam Malik tare da Mansur Dawaniki kamar haka:
Mansur Dawaniki wanda yake khalifa ne mashahuri na Abbasiyya, wata rana ya shiga haramin Manzo yana magana da karfi. Malik a lokacin shi ne Fakih a Madina sai ya juya zuwa ga Mansur ya ce: Ya kai shugaban Muminai, kada ka daga muryarka a cikin wannan masallaci, Allah madaukaki ya koya wa wasu mutane ladabi inda yake cewa: "Kada ku daga muryarku saman muryar Annabi"[44] Sannan ya ya bi wasu gungu daga cikin mutane ya ce: Lallai wadanda suke kasa da muryarsu a gaban manzon Allah, su ne wadanda Allah ya jarabba zukatansu da takawa"[45] Sannan Allah yana cewa Wasu gungun mutane wadanda suke hayaniya a bayan gidan Manzo suna cewa: Ya Muhammad ka yi sauri ka fito daga cikin gida, Allah yana kaico da halinsu, yan cewa: "Lallai wadanda suke kiranka daga bayan gida mafi yawansu ba su da hankali".[46] Sannan ya cigaba da cewa girmama Manzo a lokacin da ba shi da rai kamar lokacin da yake da rai ne babu bambanci.
Lokacin da Mansur ya ji wannan magana sai ya zo da kansa wajen Malik ya ce: A lokacin da nake addu'a zan kalli kibla ne ko kuwa kabarin Manzo?
Sai Malik ya ba shi amsa da cewa: Me ya sa zaka juya wa Manzo baya alhali kuwa shi ne tsaninka kuma tsani ga babanka Adam har zuwa ranar tashin kiyama, don haka ka kalli kabarin Manzo ka nemi ceto daga gare shi Allah ya amshi cetonka. Allah yana cewa: A lokacin da suka zalunci kawunansu suka zo gare ka suna neman gafarar Allah manzon zai nema musu gafara..."[47]

Ziyarar Kabari Da Kiyaye Asali
A cikin wannan bahasi namu mai tsawo kawai mun yi amfani ne da ruwayoyin da suke nuni a kan wannan al'amari daga ruwayoyin Ahlus Sunna. Amma muna da ruwayoyi da dama daga maruwaitanmu na Shi’a da suka ruwaito daga Imaman Ahlul Bait (A.S). Wadanda ba mu yi nazari a kansu ba. Sdaboda haka idan aka duba littattafan hadisai na Shi’a za a tabbatar da wannan al'amari cewa, ziyarar Manzo da Ahlul Bait (A.S) yana daga cikin abin da yake karbabbe ga kowa a cikin wannan mazahaba ta Ahlul Bait (A.S) sakamakon haka ne aka rubuta littattafai? da dama a kan hakan wadanda a ka fi sani da suna "almazar" wato wurin ziyara, daga cikin wadannan littattafai? kuwa wanda duk ya fi shahara shi ne, "Alkamil Ziyarat" wanda shehin malamin nan mai suna Ja'afar bn muhammad bn kulawaihi ya rubuta. (ya yi wafati 367H).
A nan zamu kara da cewa, kiyaye abubuwan da suke na asali yana daya daga cikin ayyukan addinin musulunci. Abin da muke nufi da asali kuwa shi ne abin da yake bayyanar da gaskiyar musulunci da cigabansa har ya isa zuwa ga dukkan zamuna.
Addinin musulunci addini ne da yake na duniya baki daya, don haka har zuwa tashin kiyama zai kasance matsayin addini cikakke har karshen duniya. Saboda haka dole ne mu yi iya kokarinmu mu ga cewa mun kiyaye asalin wannan addini don ya isa kamar yadda ya zo zuwa ga wadanda zasu zo a nan gaba.
Saboda haka ziyarar kabarin Manzo da Ahlul Bait (A.S) yana daya daga cikin kiyaye asalin addini, don haka barin hakan bayan wani tsawon zamani sai ya zamana an manta da wannan babban aiki mai albarka. Saboda haka dangane da wadanda zasu zo nan gaba sai ya zamana wadannan wurare na musamman na manyan bayin Allah ya koma kamar wani abin tatsuniya.
Kasancewar zuwan Isa (A.S) a yau wani abu ne wanda ba abin shakka ba ga al'ummar musulmi, amma a yammacin duniya musamman ga matasa al'amarin Annabi Isa ya zama kamar wani abin tatsuniya, wannan kuwa ya faru ne sakamakon rashin wani abu wanda yake nuna gaskiyar samuwar shi Annabi Isa (A.S) a hannayen mutane. Wannan kuwa ya faru ne sakamakaon canza littafinsa da a ka yi, don haka dangane da shi kansa Masih da mahaifiyarsa da sauran manyan sahabbansa babu wani abu na hakika wanda yake tabbas daga garesu yake. Don haka sakamakon tsawon zamani a yau al'marin masihiyya ya zamana kimarsa ta rage kuma ya shiga cikin wani halin kokwanto da rashin tabbas. Kamar yadda a yau ziyarar Manzo wadda take daya daga cikin abu na asali a cikin addinin musulunci kuma mai nuna hakikanin matsayi da samuwar Manzo tana neman ta zama wani abu marar muhimmanci a cikin al'ummar musulmi, kuma ya zamana an ajiye ta a gefe guda. Don haka sakamakon tsawon zamani akwai yiwuwar abubuwan asali na addinin musulunci da waliyyan Allah, su shiga cikin wannan hadari mai girma.
Saboda haka al'ummar musulmi dole ne su tashi tsaye domin kare wannan hadari da ya fuskanto su, wannan kuwa yana samuwa ne ta hanyar kiyaye duk wani abu da ya shafi sakon manzanci da Imamanci, ta yadda za a rika tuna shi a kowane zamani. Saboda haka ziyarar wadannan manyan bayin Allah tana daya daga cikin hanyoyin kiyaye su daga bacewa da kuma yin tunani a kansu a kowane lokaci. Saboda haka sakamakon yin hakan ba za a taba watsi da matsayin wannan muhimmin al'amari ba, ta yadda za iya kulle kofar ganawa ta hanyar ruhi da wadannan manyan bayin Allah ga al'ummar musulmi. Saboda haka da ikon Allah a nan gaba zamu yi magana a kan kiyaye wadannan wurare masu tsarki.

Tafiya Domin Ziyarar Kabarin Manzo (S.A.W)
Ziyarar Kabarin dukkan musulmi da musamman ziyarar kabarin Manzo wani abu ne wanda yake mustahabbi mai karfi a cikin musulunci. Sannan malaman hadisi daga Sunna da Shi’a sun ruwaito hadisai da dama a kan mustahabbancin ziyarar kabarin Manzo wadanda wasu daga cikinsu sun gabata a cikin bahasin da ya gabata ta yadda babu wani malami daga cikin malaman musuluncin da ya ba kansa damar yin shakku a kan mustahabbancin ziyarar Manzo. Wannan kuwa ya hada har da Muhammad bn Abduh wanda yake da wasu masatlolin dangane da abin da ya shafi annabawa, a nan ba kawai ya yi shiru ba ne, sai dai ya yi magana a kan mustahabbcin ziyarar Manzo (S.A.W). Sannan mun kawo abin da yake cewa dangane da hakan a bahasimmu na baya. Tare da la’akari da kasantuwar mustahabbicn ziyarar Manzo, amma msulmi sun kasu a kan wannan kyauta ta ubangiji:
1-Mazauna Madina
Mazauna Madina sakamakon makwautaka da suke da ita da Manzo (S.A.W). Suna iya ziyartarsa ba tare wata wahala ba don aiwatar da wannan mustahabbi.
2-Mazauna sauran wurare a cikin duniya
Mazauna sauran sassan duniya dole ne su yi tafiya domin su damar yin sallama ga kabarin Manzo Su ce: "Amincin Allah ya tabbata a gareka ya manzon Allah".
A nan tambaya ita ce; menene hukuncin wannan tafiya a shari’a?
Jawabain wannan tambaya kuwa a fili yake domin wannan amsa tana matsayin gabatarwa ce domin aiwatar da aikin mustahabbi, saboda haka a akidar wasu malamai tana matsayin mustahabbi, wasu kuwa suna cewa tana hukuncin halal "Mubah" ne.
Duk yadda ta kama kasantuwar wannan tafiya domin aiwatar da mustahabbanci ce ba zata taba zama haramun ba. Domin kuwa ba zai inganta ba a hankali Allah madaukaki ya umurce mu da aikin mustahabbi na ziyartar Manzo sannan ya haramta abin da yake matsayin gabatarwa ne domin aiwatar da wannan aikin. Saboda haka daga nan muna iya gane cewa hukuncin wannan tafiya domin aiwatar da wannan aiki ta halitta. [48]
Kamar yadda yake a tarihi shi ne musulman da suke rayuwa a sauran sassan duniya wato ba wadanda suke rayuwa ba a garin Madina sukan daure kayansu domin tafiya zuwa ziyarar kabarin Manzo mai girma a nan ga wasu misalai a kan hakan:
Bilal wanda yake mai kiran salla ne na Manzo kuma Manzo ya kasance yana kaunarsa. Bayan tafiyar Manzo ya zabi ya tafi wani wuri yiwa musulunci hidima, sakamakon haka ne ya yi hijara daga garin Madina. Wani dare sai ya ga Manzo a cikin mafarki yana ce masa: Wannan wane irin rashin kulawa ne Bilal? Yanzu lokaci bai yi ba da zaka ziyarce ne?
Lokacin da Bilal ya tashi daga barci yana cikin bakin cikin da ya mamaye masa zuciya, sai kawai ya tanaji abubuwan bukata domin yin tafiya kuma ya tafi zuwa Madina. Lokacin da Bilal ya shiga a cikin Raudar Manzo yana kuka da murya mai karfi a wannan hali ya dinga goga fusakarsa a kan kabarin Manzo (S.A.W). A nan haka sai kwatsam abin kaunar? Manzo wato Hasan da Husain (A.S) sai suka yi wajensa sai ya kama su ya runguma, sai suka ce masa, Muna tsananin son mu ji muryar kiran sallarka, kiran sallar da kake yi wa kakanmu manzon Allah (S.A.W).
A lokacin sallar Asubahi sai Bilal ya hau wurin da ya kasance yana kiran salla a zamanin Manzo (S.A.W) ya kira salla. A lokacin da kiran sallarsa ya mamaye Madina Ya girgiza garin Madina a wannan lokaci, a lokacin da ya yi kalmar shahada a cikin kiran sallarsa sai duk mutane suka daga murya suna kuka, a lokacin da kuwa ya yi shahada a kan manzancin Manzo (Ashhahadu anna Muhammadar Rasulullah) ai sai duk mutanen Madina suka yi waje suna kuka. Kamar yadda ake rubutawa: Bayan ranar da Manzo ya yi wafati madina ba ta taba ganin irin kukan da ta gani ba a wannan lokaci.[49]
2-Umar bn Abdul Aziz ya kasance yana hayar mutane domin su zo daga Sham zuwa madina domin su yi masa sallama ga Manzo. Subki a cikin Futuhus Sham yana rubuta cewa: Lokacin Umar bn Abdul Aziz ya yi Sulhu da mutanen Kudus sai Ka’abul Akhbar ya shigo wajen kuma ya musulunta, a wannan lokaci Umar ya ji dadi kwarai da musuluntarsa. Sai Umar ya ce masa: Kana iya bi na mu tafi madina mu ziyarci kabarin Manzo ta yadda zamu fa’idantu da ziyararsa? Sai Ka’ab ya amsa wa khalifa abin da ya nema daga gareshi, ya yi shirin tafiya tare da khalifa. A lokacin da Umar ya shiga garin madina, farkon abin da ya fara yi shi ne ya shiga masallacin Manzo ne domin ya yi wa Manzo sallama.[50]
Duk da yake ba mu da bukatar mu kafa sheda a nan da irin wadannan misalai, domin kuwa al’ummar musulmi duk tsawon karnoni? sha hudu sun dauki wannan al’amari na ziyara Manzo a matsayin mustahabbi kuma suna tafiya Madina domin su aiwatar da wannan mustahabbi.
Subki dangane da tafiyar ayari-ayari zuwa ziyarar Manzo ya yi maganganu da dama a kan hakan, ya kara da cewa masu ziyara bayan sun gama aikin hajji sukan kama hanyar Madina ne domin su kai wa Manzo ziyara, ya kara da cewa: wata sa’a sakamakon fahimtar ladar da yake cikin yin hakan sukan dauki hanyar da tafi nisa zuwa Madina, domin su samu lada mai yawa a kan haka. Sannan ya cigaba da cewa, wadanda suke tunanin cewa dalilin da ya sa mutane suke tafiya madina shi ne domin su ziyarci masallacin Manzo kuma su yi salla a ciki wannan kuskure ne, domin kuwa abin masu ziyarar suke fada ya saba wa wannan tunanin. Domin manufarsu a kan wannan ziyara shi ne su ziyarci kabari Manzo, sannan wannan shi ne gurinsu na ziyarar Madina. Domin kuwa idan manufarsu a kan wannan tafiya shi ne ziyartar masallaci, me ya sa ba su tafiya Kudus domin su ziyarci masallacin baitil mukaddas wanda yin salla a cikinsa bai gaza wa yin salla a masallacin Manzo ba?
Kamar yadda yake haduwar malamai a kan wani hukunci yana nuna ingancin wannan hukunci a shari’a haka nan haduwar dukkan musulmi a kan wani aiki yana nuna mafi daukaka kasantuwan wannan abin a cikin shari’a.[51]

Masu Haramta Tafiya Don Ziyarar Manzo
Har zuwa karshen karni na bakwai malamai sun hadu a kan wannan al’amari cewa tafiya domin aiwatar da wani aiki na mustahabbi koda ba ta zama mustahabbi ba to alal akalla ta halasta. Amma a farkon karni na takwas, Sai Ibn Taimiyya ya yi riko da hadisin Manzo wanda Abu Huraira ya ruwaito ta yadda ya saba wa dukkan malamai da suka hadu a kan wannan al’amari. Wannan ruwaya kuwa da Ibn taimiyya ya yi mafani da ita, an ruwaito ta ne ta fuska guda uku, amma abin da yake iya tabbatar wa Ibn taimiyya da manufarsa ya zo da fuska biyu ne kamar haka:
1- Kada a yi nufin tafiya sai zuwa masallatai guda uku: Wannan masallaci nawa, masallacin ka’aba da Masallacin Kudus.[52]
2- Ana yin tafiya ne kawai zuwa ga masallatai guda uku[53], Ibn taimiyya ya yi riko ne da zahirin wannan hadisi domin tabbatar da manufarsa, ta yadda ya yi da’awar cewa domin aiwatar da ayyukan ibada masallatai uku ne kawai mutum zai iya zuwa domin yin hakan. Saboda haka ziyarar Manzo wanda yake matsayin ibada ba ya daya daga cikin wadannan abubuwa guda uku. Wannan kafa hujja ta Ibn Taimiyya kuwa idan muka lura da kyau zamu iya gane rashin ingancinsa, domin kuwa ba shi da kafafu masu karfi.
Domin kuwa mun san cewa jumlar da take kebewa tana ginuwa daga sassa guda biyu kamar haka:
1-Jumlar da ake kebewa daga gareta: "Ba wanda ya zo wurina".
2- Jumlar da a ka kebance "Sai Ali"
Hadisin da ya gabata ya ginu ne ta hanyar jumloli biyu ne:
1-jumla ta farko jumlar da aka kebance daga gare ta "Kada ku yi tafiya. "
2-Jumla ta biyu kuwa, wadda aka kebance: "Sai masallatai uku".
A jumlar ta farko abin da aka kebance bai fito ba a fili, bisa la’akari da ka’idar larabci a nan dole mu kaddara wata jumla, wadda zata iya zama daya daga cikin wadannan jumloli guda biyu kamar haka:
1-Mai yiwuwa ka iya cewa "masallaci" ne. (wato kada ka yi tafiya zuwa kowane masallaci sai masallatai guda uku)
2-Mai yiwuwa ana nufin "wuri" ne (kada ka yi tafiya zuwa wani wuri sai masallatai guda uku) Saboda haka bisa ga tsammani na farko, zai zama ma’anar jumla zai zama haka, wato kada ka yi tafiya zuwa kowane masallaci sai masallatai guda uku da aka ambata.
Saboda haka idan muka dauki wannan ma’ana zai zama cewa Manzo yana magana ne a kan masallatai, wato don mutum ya yi salla kada ya yi wahala don tafiya kowane masallaci sai masallatai guda uku da aka ambata. Saboda haka a nan ziyarar Manzo ba ta cikin abin da aka hana a cikin wannan hadisi domin ba a kansa ake Magana ba. Sannan dalilin da ya sa aka yi hani tafiya wani masallaci domin yin salla domin sauran masallatai hukunci guda garesu babu wani wanda ya fi wani daraja daga cikinsu, saboda haka yayin da mutum yake da damar yin salla a daya daga cikin masallatai me zai sanya ya sha wahala domin ya tafi waninsa.
Misali kamar idan akwai masallacin jumma’a a wani gari me zai sanya mutum ya tafi wani gari domin ya yi sallar jumma’a a can, domin kuwa ladar da zai samu a wancan masallacin ba ta dara wadda zai samu ba a wannan na garinsu.
Amma dangane da wadancan masallatai uku abin ba haka yake ba, domin salla a cikin daya daga cikinsu ya fi salla a cikin sauran masallatai, saboda haka tare da kula da cewa a cikin wannan hadisi an yi magana ne kawai a kana masallatai, don haka tafiya zuwa wasu wurare bai shafi wannan hani na hadisi ba, saboda haka ba ya magana a kan halasci ko haramcin yin hakan.
Amma idan muka dauki ma’ana ta biyu ma’anar wannan hadisi zata kasance kamar haka: kada ka yi tafiya sai zuwa wurare guda uku (masallatai guda uku da muka ambata).
Idan muka dauki wannan ma’ana dogaron Ibn Taimiyya yana iya zama dai-dai. Amma tare da lura da yadda tarihin musulmai ya tafi a kan mustahabbacin tafiya zuwa kabarin Manzo (S.A.W), domin ziyara tana nuna mana rashin ingancin wannan hadisi.
Na farko kamar yadda muka gani a cikin hadisin da ya gabata, ana iya tsammanin wata ma’ana daban, sakamakon wannan ma’ana kuwa ba za a samu wani fito na fito ba a hadisai da ayoyi da kuma tarihin musulmi da suke nuni a kan halascin ziyarar Manzo. Kuma tare da daukar ma’anar farko musamman kasantuwar mu dauki cewa kalmar da zamu iya kaddarawa ita ce masallaci, domin kasantuwar dacewarta da abin da ya zo a cikin jumlar, kuma shi ne abin da ya fi dacewa ya kuma fi karfi. Saboda haka wannan hukunci wanda Ibn Taimiyya ya dauka zai zama sam ba shi da ma’ana a nan.
Haka nan idan muka dauki ma’ana ta biyu wato muka dauka cewa ai a nan ana nufin "wuri" wato bai halitta ba mutum ya tafi wani wuri sai wadannan wurare guda uku, wannann kuwa zai bayar da ma’anar da ba ta dace ba, sannan fitowar wannan kalma daga mai hikima musamman Manzo ba zai yiwu ba. Wato ya zama an hana zuwa kowane wuri sai wadannan wurare guda uku (Masallacin ka’aba, Kudus da Masallacin Manzo). alhalin musulunci ya halatta wasu tafiye-tafiye da dama a cikin musulunci wasu daga cikinsu ma mustahabbi ne. Misali kamar tafiya domin neman ilimi, ko tafiya domin kasuwanci ko tafiya don sada zumunci, tafiya don yawon bude ido, tafiya domin jihadi da dai sauran tafiye-tafiye da suke halas wadansu ma mustahabbi a musulunci.
Saboda haka a nan dole ne mu dauki ma’ana ta farko wato masallaci, cewa kada mutum ya yi tafiya domin ya je wani masallaci sai masallatai guda uku, domin kuwa su ne su kafi sauran masallatai matsayi. Da wannan ne zamu fitar da batun tafiya domin ziyarar Manzo domin ba ita ake magana ba a cikin wannan hadisi.
Bayan dangane da ingancin wannan hadisi koda an dauki ma’ana ta farko, akwai shakku a cikinsa. Domin kuwa yana nufin wannan magana ta fito daga bakin Manzo inda take nuni da cewa tafiya zuwa kowane masallaci ba ta inganta sai masallatai guda uku. Alhali kuwa ruwayoyi sun zo a kan cewa Manzo (S.A.W). Wasu ranakun Asabar yakan tafi kasa, wata sa’a bisa abin hawa domin ya je masallacin "Kuba?" domin ya yi salla raka’a biyu a wajen. Wannan masallaci a zamanin da Manzo yake a raye yana da tazarar kilo mita 12 tsakaninsa da Madina.[54]