Amsar wasu tambayoyi guda biyu
Wasu sun haramta ziyarar mata zuwa kaburbura, suna kafa hujjarsu ne kuwa da wadannan hadisai guda biyu kamar haka:
1-“Allah ya la’anci mata masu ziyarar kabari”.
Amsa:
Wannan Hadisi ya rasa sharuddan da ya kamata ya kasance yana da su kafin a iya kafa hujja da shi. Domin bisa ga dogara da dalilai da aka ambata a baya dole ne mu dauka wannan hadisi an shafe shi, Sannan cikin sa’a wasu daga cikin malaman hadisi na Sunna sun dauki wannan hadisi matsayin shafaffe. Tirmiz maruwaicin wannan hadisi yana cewa: Wannan hadisi an shafe shi domin yana nuna lokacin kafin halasta ziyartar kabari ne, amma lokacin da manzo ya halasta ziyarar kaburbura wannan hukunci ya hade mace da namiji babu bambanci.
Kurdabi yana cewa: Wannan hadisi yana Magana ne a kan matan da suke bada dukkan lokacinsu a makabarta ne, ta yadda sakamakon haka ba su bayar da hakkokin mazansu da ya hau kansu. Kuma sheda a kan haka shi ne manzo ya yi amfani da kalmar “Zuwwar” wadda take da ma’anar kambamawa, wato wadanda suke yi yawaita ziyara.
2-Ibn maja yana ruwaito daga Ali bn Abi Dalib cewa: Manzo (S.A.W). Ya fito sai ya ga wasu mata a zaune, sai ya tambaue su me ya sa suke zaune? sai suka ce: Muna jiran jana’iza ne.
Sai ya ce zaku yi wa jana’izar wanka ne?
Suka ce: A’a.
Sai ya ce: zaku dauki gawar ne?
Suka ce: A’a.
Ya ce: zaku saka gawar kabari ne?
Suka ce: A’a.
Sai manzo ya ce: ku koma gida kuma su masu sabo ne ba masu neman lada ba.
Amsa:
Wannan hadisi ta fuskar ma’ana da isnadi ba a bin dogaro ba ne da za a iya kafa hujja da shi, saboda sanadin wannan hadisi (maruwaita hadisin) akwai Dinar bn Amru ya shiga a cikinsu, ta fuskar masu ilimin ruwaya suna cewa ba a san shi ba, kuma mutum ne mai karya mai sabo kuma wanda ake bari. Shin ana iya dogara wajen kafa hujja da irin wannan hadisi wanda maruwaicinsa yake da wadannan siffofi na rauni?
Mu dauka ma dangane wannan hadisi yana da inganci, sam ba shi da alaka da ziyarar kabari, domin kuwa Allah wadai din da manzo ya yi ya shafi matan da suka fito domin kallon janaza, ba tare da wani aiki da zasu yi ba wajen kai jana’zar, saboda haka wannan bai shafi batun ziyarar kaburbura ba.
A nan dole mu yi tunatarwa a kan wani al’amari shi ne, addinin musulunci addini ne wanda ya dace da halitta mutum, kuma mai sauki, manzo yana cewa: “Akidun musulunci akidu ne tabbatattu duk wanda zai shiga cikinsu ya shiga tare da dalilai na hankali”.
Mu dauka cewa mahaifiyar mumini sai ta rasa danta aka kuma rufe shi a karkashin kasa, sai ta damu a kan hakan, abin da kawai zata iya yi a nan shi ne ta ziyarci kabarinsa. A nan idan aka hana ta yin wannan aiki wanda ya dace da hankali kuma dukkan mutanen duniya sun tafi a kan hakan, wannan zai haifar da muguwar damuwa ga zuciyar uwa. Shin musulunci zai yi hani da irin wannan aiki sannan kuma ya zama addini mai sauki?
Kai asali ma ziyarar kaburbura wani darasi ne kuma mai sanya mutum ya rika tunawa da lahira wanda kuma ya kunshi karanta wa wadanda aka ziyarta fatiha. Ta yaya za a hana mata dangane da samun wannan falala?
Da wani kalamin kasantuwar hikimar ziyarar kaburbura tana kunshe da daukar darasi da tunawa da lahira, ta yaya za a kebance maza kawai ban da mata a ciki?
Kasantuwar ziyarar kaburbura ya nisanta da duk wani sabo, idan muka dauka haka kuma sai aka hana mata a wancan lokaci, to kila sakamakon cewa ba su kiyaye sharuddan da suka kamata ne.

Ziyarar Kabarin Manzo Mai Girma A Mahangar Malaman Hadisi Da Fikihu
Tare da bibiyar maganganun manyan malaman hadisi da malaman fikihu, zamu ga yadda kodayauhse malaman musulunci suke karfafawa a kan kasantuwar ziyarar kabarin manzo a matsayin mustahbbi mai karfi, Sannan suna kiran mutane zuwa ga ziyarar kabarin manzo mai tsarki.
Takiyyuddin Subki Shafi’i (ya rasu shekara ta 756) Wanda yake daya daga cikin manyan malaman karni na takwas. Yayin da yake kalu balantar akidun Ibn Taimiyya wanda yake inkarin ziyarar kabarin manzo (S.A.W), ya rubuta littafi mai suna (shifa’us sikam fi ziyarati khairil anam) a cikin wannan littafi ya yi kokari ya tattaro ra’ayoyin malaman Ahlus Sunna tun daga karni na hudu har ya zuwa lokacinsa a kan wannan al’amari, a cikin wannan littafi nasa ya yi kokarin tabbatar da nuna cewa ziyarar kabarin manzo yana daga cikin abubuwan da aka sallama a cikin fikihu a kan cewa mustahabbi ne. Manyan malaman hadisi da fikhu sun ruwaito hadisai daban-daban a kan kasantuwar ziyar manzo a matsayin mustahabbi, sannan suka ba da fatawa a kan hakan.[19]
Allama Amini wanda yake bincike na wannan zamani kuma mai tsanantawa wajen bincikensa (1320-1390), a cikin babban littafin nan nasa “Algadir” Ya yi kokari wajen cike abin da ya ragu a kan wannan batu na ziyar kabarin manzo, inda ya yi kokari ya zo da ra'ayoyin malamai arbai’n wadanda suka hada da malaman hadisi da na fikhu har ya zuwa malaman zamaninsa. [20]
Wannan marubuci shi ma ya yi kokari ya samo wasu daga fatwoyin da ba su zo ba a cikin wadancan littattafan guda biyu da muka ambata. Ta yadda ya kawo su a cikin wani karamin littafi da ya rubuta a cikin harshen larabci. Kai har da babban mai fatawar Kasar Sa’udiyya wato sheikh Abdul Aziz bn Baz ya ba da fatwa a kan mustahabancin ziyarar kabarin manzo mai girma.[21]
Kawo dukkan maganganun malamai a kan wannan batu ba zai yiwu ba wannan wuri, saboda haka kawai zamu wadatu da kawo wasu daga ciki ne kawai kamar haka:
1-Abu Abdullaji Jujani Shafi’i (ya rasu a shekara ta 403) Bayan ya yi maganganu a kan girmama manzo sai yake cewa: A matsayin tuanatarwa a yau ziyarar manzo shi ne ziyarar kabarinsa mai albarka.[22]
2-Abu Hasan mawardi (ya rasu a shekara ta 450) Yana rubuta cewa: Jaogoran matafiya zuwa aikin hajji bayan an gama aikin hajji sai ya jagoranci twagarsa zuwa madina domin mahajjata su hada ziyara guda biyu, wato ziyarar dakin ka’aba da ziyarar kabarin manzo. Ta haka ne zasu kiyaye martabar manzo suka kuma bayar da hakkinsa na biyayya gare shi. Ziyarar kabarin manzo ba ya daga cikin farillan ayyukan hajji, amma yana daga cikin mustahabban aikin hajji.[23]
3-Gazali ya yi bayani mai fadi dangane da ziyar manzo (S.A.W), Sannan ya yi bayani a kan ladubban ziyarar manzo Yana cewa: Manzo yace: ziyarata yayin da ba ni da rai duk daya ne da ziyarata a lokacin da nake raye. Sannan duk wanda yake da karfin jiki da dukiya amma bai ziyarce ni ba to ya yi mani tozarci.
Gazali yana karawa da cewa: Duk wanda ya yi nufin ziyarar manzo to ya aika masa da gaisuwa a bisa hanya, sannan a lokacin da idonsa ya hangi itatuwa da bangayen madina sai ya ce: Ya Allah wannan shi ne haramin Manzonka ka sanya shi kariya a gareni daga wuta, Sannan ya zama aminci a gare ni daga azabar wuta da munin hisabi.
Sannan Gazali ya yi tunatarwa dangane da ladubban ziyarar Manzo yana rubuta cewa: Wanda ya ziyarci manzo sai wuce a “Bakiyya” don ya ziyarci kabarin Imam Hasan bn Ali (A.S) Sannan ya yi salla a masallacin Fadima (A.S).[24]
4-Alkali Iyadh maliki (ya rasu a shekara ta 544) yana rubuta cewa: Ziyartar manzo wata Sunna ce wadda kowa ya aminta da ita. Sannan ya ruwaito wasu hadisai dangane da ziyarar kabarin Manzo sannan yana karawa da cewa: Maziyarcin kabarin manzo, to ya kamata ya nemi tabaraki da wurin ibadar manzo (Raudha) Minbarinsa, wurin da yake tsayawa, da shika-shikan da manzo yake jingina a wurinsu da kuma wurin da jibra’il yake saukar wa manzo da wahayi. [25]
5-Ibn Hajjaj Muhammad bn Abdali Kirawani Maliki (ya rasu a shekara ta 738) bayan ya yi magana dangane da ziyarar manzanni da ladubbanta da yadda ake yin kamun kafa (tawassuli) da su da neman biyan bukata daga garesu, sai ya tunatar dangane da ziyarar kamar haka:
“Abin da muka fada dangane da wadansu, a kan abin da ya shafi ziyarar shugaban wadanda suka gabata da wadanda zasu zo kuwa da yadda ake yi masa salla dole ne mu fadi abin da ya wuce hakan. Abin da ya dace shi ne mutum tare da kaskantar da kai ya halarci haramin manzo domin kuwa shi mai ceto wanda ba a mayar da cetonsa. Duk wanda ya tunkare shi ba zai koma ba yana mai yanke kauna ba. Sannan duk wanda ya zo haraminsa yana neman taimakonsa da biyan bukatarsa ba zai rasa abin da yake nema ba”.
Sannan ya cigaba da cewa: Malamammu (Allah ya gafarta musu) Suna cewa abin ya dace shi ne: wanda ya ziyarci manzo ya rika jin cewa kamar manzo yana raye ne ya ziyarce shi. ”[26]
6-Ibn Hajar Haisami Makki Shafi’i (ya rasu shekara ta 973) Ya kasance ya yi riko da dalilin da dukkan malamai suka hadu a kansu wajen kafa hujja a kan kasantuwar mustahabbancin ziyarar manzo. Sannan yana karawa da cewa: Sabawar wani malami guda a kan wandannan dalilai kamar Ibn Taimiyya ba ya cutar da wadannan dalilai da a ka hadu a kan ingancinsu. Domin kuwa malamai da yawa sun bibiyi maganganunsa kuma suna tabbatar da rashin ingancinsu.
Daya daga cikinsu kuwa shi ne Izz bn Jama’a, kamar yadda Ibn Hajar yake cewa: “Ibn Taimiyya mutum ne wanda Allah ya batar da shi, Sannan ya sanya masa tufafin kaskanci”. Sannan Sheikh Takiyyuddin Subki wanda dangane da matsayinsa na ilimi kowa ya aminta da shi, littafi na musamman ya rubuta don kalubalantar fatawoyin Ibn Taimiyya.[27]
7-Muhammad bn Abdul wahab yana cewa: Mustahabbi ne ziyayar manzo amma wajibi ne mutum ya yi tafiya zuwa wajen domin ziyara da yin salla a wajen.[28]
8-Abdurrahman Jaziri marubucin littafin nan (Alfikhu Ala Mazahibil Arba’a) Inda ya kawo fatawoyin dukkan malaman mazahaba guda hudu na Sunna, yana cewa: Ziyarar kabarin manzo yana daya daga cikin manyan mustahabbai, sannan hadisai sun zo a kan hakan, sannan ya cigaba da kawo hadisai guda shida da suka yi bayani a kan ziyarar manzo da ladubbanta. [29]
Sakamakon cewa duk shugabannin fikihu guda hudu ba su yi wani karin bayani ba a kan abin da aka ambata a sama ba, yana nuna cewa duk malaman wannan zamani suma sun tafi a kan hakan.
9-Shekh Abdul Aziz bn Baz yana cewa: Duk wanda ya ziyarci manzo mustahabbi ne ya yi salla raka’a biyu a (raudhar Manzo) Sanna ya yi wa manzo sallama, Sannan mustahabbi ne ya je “Bakiyya” domin ya yi sallama ga shahidan da a ka rufe a wajen.[30]
A nan zamu takaita da wannan abin da muka kawo dangane da wannan al’amari mai son karin bayani dangane da haka, sai ya koma zuwa ga “Risalar da muka rubuta a kan haka a cikin harshen larabci. [31]

Ziyarar Kabarin Manzo A Mahangar Kur’ani Da Sunna
A: A Mahangar Kur’ani Maigirma
Kur’ani mai girma yana bai wa al'ummar musulmi umarni da su je wajen manzo su nemi gafararsa sannan su nemi manzo (S.A.W) don ya nema musu gafarar Allah madaukaki: "Duk lokacin da suka zalunci kawunansu (suka yi zunubi) idan suka zo wajen manzo suka nemi gafara kuma Manzon ya nema musu gafara wajen Allah, lallai Allah mai rahama ne kuma mai karbar tuba. "[32]
A wani wurin ciki Kur’ani Allah madaukaki yana zargin munafukai da cewa duk lokacin da aka neme su da su je wajen ma'aiki don ya nema musu gafara sai su ki: "Idan aka ce musu ko zo manzo ya nema muku gafara, sai su juya fusakunsu (don nuna rashin amincewa) zaka ga suna kin maganarka suna masu nuna girman kai. "[33]
Shehin malamin nan kuma Ahlussunna, Takiyyuddin Subki, Ya yi imani da cewa: Msuslmi a wannan lokacin ma tare da amfani da wannan aya suna iya zuwa wajen manzo su nemi gafararsa kuma Allah ya gafarta musu. Ya kara da cewa duk da yake wannan aya ta shafi lokacin da manzo yake a raye ne, amma neman gafara ta hanyarsa bai kebanta da lokacin da yake a raye ba. Saboda wannan wani matsayi ne wanda aka bai wa manzo (S.A.W) don haka sakamakon rabuwarsa da duniya wannan matsayi ba zai kau ba.
Mai yiwuwa a ce: Wannan abin da ya zo a cikin wannan aya da muka ambata a sama, ya kunshi nuna matsayi da daukaka ta manzo ne kawai, amma aiwatar da wannan ya kebanci lokacin rayuwarsa ne kawai, amma ba lokacin da baya duniya ba, ta yadda alakarmu da shi ta yanke.
Amma wannan magana sam ba abin karba ba ce, domin kuwa dalilan da zamu ambata a nan gaba suna bayyana cewa rasuwar manzo sam ba ta da wani tasiri a kan wannan al'amari, don haka mutuwa da rayuwarsa babu wani bambanci duk daya ne:
1-Mutuwa ba tana nuna karshen dan Adam ba ne, mutuwa wata sabuwar kofa ce don shiga wata sabuwar rayuwa kuma duniyar da duk abin da yake a ckinta ya fi abin da yake a duniyar da ta gabata ga rayuwar dan Adam, saboda haka mutum rayayye ne a waccan duniya yana gani kuma yana ji. Musamman shahidai wadanda bayan sun dandana shahada zasu cigaba da karbar ci da sha daga Allah madaukaki, kuma suna cikin jin dadi na musamman ta hanyar ruhinsu. Saboda haka zamu yi bayani a kan wannan a nan gaba a cikin bahasin rayuwar barzahu.[34]
2-Ya zo da yawa a cikin ruwaya cewa: Salatin da musulmi suke yi wa manzo akwai mala'iku na musamman masu isar da wannan salati zuwa ga manzo (S.A.W) don haka duk inda mutum yake idan ya yi wa manzo salati zai isa zuwa ga manzon. Kamar yadda yake cewa: "Ku yi mani salati, salatin yana isa zuwa gare ni daga duk inda kuke".[35]
3-Musulmi a wajen tahiyar salla an umurce su da su yi wa manzo sallama, sannan su yi masa gaisuwa, "Assalamu alaika ayyuhan nabiyu warahamatullahi wa barakatuhu" Wannan gaisuwa ba wai kawai an umurci musulmi ba ne da su yi ta zuwa ga manzo amma shi ba ya jin abin da suke yi, Manzo yana raye kuma yana sauraren mu lokacin da muke yi masa salati.
Wadannan abubuwan da muka fada a sama suna nuna cewa Manzo yana raye a rayuwar barzahu, sannan yana da alaka da mu kuma yana jin abin da muke yi. Sannan yana jin rokonmu kuma yana biya mana bukatunmu a lokacin da ya dace. Saboda haka a nan ya kamata mu ce wadannan ayoyi da muka yi bayani a sama, Suna da ma'ana mai fadi, saboda haka yanzu ma suna kiranmu da ziyarar manzo a kabarinsa kuma mu nemi gafara kuma ya nema mana gafara ga Allah, sannan mu nemi bukatunmu daga gareshi. Saboda haka ya zo a cikin ziyarar manzo da ake karantawa a haraminsa cewa mai ziyara ya nemi gafarar Allah ta hanyar manzon tare da kula da ma'anar ayar da muka yi bayani a sama. Saboda haka ziyarar manzo ba wani abu ba ne sai kawai yin salati ga manzo da kuma neman bukatu da gafarar Allah ta hanyar mazon. Saboda haka wadannan ayoyi na sama suna iya zama sheda a kan inganci da mustahabbancin ziyarar manzo (S.A.W).
Wata sheda kuma a kan wannan batu shi ne, bayan rasuwar Manzo wani balarabe ya shigo Madina yana karanta wannan aya da muka ambata, sai ya ce: "Na zo wajenka ina mai neman gafara daga zunubaina kuma ina mai neman ceto gareka zuwa ga Ubangijina".[36]
Sannan muhimmin abu kamar yadda Subki yake cewa: Kiran al'ummar musulmi da su ziyarci manzo kuma su nemi gafara da bukatunsu daga gareshi wata alama ce ta karrama manzo da girmama shi. Kuma tabbas wannan girmamawa ba ta kebanci lokacin rayuwarsa ba, saboda girma da mukamin ruhinsa a wajen Allah wani abu ne wanda ba mai shakku a kansa kuma madawwami ne, saboda haka bai kebanta da wani zamani ba sabanin waninsa.
Saboda haka ne malaman Tafisri suka tafi a kan cewa, girmama manzo bai kebanci lokacin rayuwarsa ba, saboda haka dole ne a kiyaye shi har bayan rasuwarsa. Har ma ayar da ke umurta musulmi da su rika magana a hanakali a gaban manzo, tana nan a matsayinta, inda Allah yake cewa: "Ya ku wadanda kuka yi Imani kada ku daga muryarku saman muryar Annabi[37]".
Saboda haka bai kamata mutum ya rika magana da karfi a cikin haramin mazon mai tsaira ba. Sannan wannan aya an rubuta ta a kan kabarin manzo, wanda duk ya je wannan wuri ya gane wa idonsa hakan.

B: A Mahangar Sunna
Mun ga hukunci da matsayin Kur’ani a kan wannan al'amri, yanzu abin da ya rage shi ne ku ga kuma me Sunnar manzo ke cewa a kan hakan..
Ruwayoyi da dama sun zo akan wannan batu na ziyarar kabarin manzo, kuma malamai sun yi kokarin tattara su da kuma tabbatar da danganensu. Saboda haka a nan a matsayin misali zamu kawo wasu daga cikinsu kamar haka:
1-Takiyyuddin subki (ya yi wafati a shekara ta756h) a cikin littafinsa "Shifa'us sikam" ya ruwaito hadisi tare da sanadi ingantacce. [38]
2-Nuruddin Ali bn sahmudi (ya yi wafati 911H) ya ruwaito ruwaya 17 akan wannan batu, a cikin littafinsa na tarihin Madina sannan kuma ya inganta sanadinsa.[39]
3-Muhammad fukki daya daga cikin Malam Azahar tare da shafe sanadi ya ruwaito matanin ruwayoyi 22 a kan ziyarar manzo.[40]
4-Allama Amini tare da tare da bin diddigi wanda ya ci a yaba masa, ya tattara ruwayoyi da dama a kan ziyarar manzo (S.A.W) saboda haka a nan kawai zamu yi nuni da daya daga cikin ruwayoyi da ya samo daga littafi 41 da a ka ruwaito a kan hakan. Al-Gadir
Saboda haka kawo dukkan ruwayoyin da danganensu ba zai yiwu ba a nan, saboda haka kawai a nan zamu takaita ne da kawo wasu kawai daga cikinsu. Wadanda suke son karin bayani sai su koma zuwa littafin da aka ambata a sama.
Hadisi na farko: "Wanda duk ya ziyarci kabarina aljanna ta wajaba a gareshi"[41]. wannan hadisi Allama Amini ya ruwaito shi tare da sanadi daga littafi 41.
Hadisi na biyu: Dabarani a cikin mu'ujamul Kabir, Gazali a cikin ihya'u ulum daga Abdullahi bn umar, Manzo yana cewa: "Duk wanda yazo ziyara kuma saboda kawai ziyarata ya zo, to ya wajaba in cece shi a ranar kiyama. "
Hadisi na uku: Darul Kutni ya ruwaito daga Abdullahi bn umar cewa manzo (S.A.W) ya ce: Duk wanda ya ziyarce ni bayan wafatina a lokacin aikn hajji, to kamar ya ziyarce ni a lokacin da nake a raye. "
Hadisi na hudu: Darul kutni ya ruwaito daga bn Umar cewa manzo (S.A.W) ya ce: "Duk wanda ya ziyarci kabarina kamar ya ziyarce ni a lokacin da nake a raye. " A nan ya kamata mu yi nazarin matsayin ziyara a wajen Imaman Ahlul-bait (A.S)

Ziyar Manzo A Ruwayar Ahlul-Bait (A.S)
1-Imam Bakir (A.S) yana cewa Manzo (S.A.W) yana cewa: "Duk wanda ya ziyarce ni ina raye ko bayan na yi wafati zan kasance mai cetonsa a ranar kiyama"[42]
2-Imam Ali (A.S) yana cewa: "Ku cika hajjinku da manzon Allah a lokacin da kuka fito daga dakin Allah, domin kin ziyartarsa rashin girmamawa ne gare shi, an umurce ku da yin hakan, tare da ziyarar kaburburan da aka umurce ku zaku karashe hajjinku."
3-Imam Sadik (A.S) daga manzon tsira (S.A.W) yana cewa: "Duk wanda ya zo Makka don aikin hajji amma bai ziyarce ni ba, zan banzatar da shi a ranar tashin kiyama, wanda kuwa ya ziyarce ni cetona ya wajaba a garesa, duk wanda cetona ya wajaba a garesa, aljanna ta wajaba a garesa. Saduk: Ilalish shara'i'i