Maganar Malaman Imamiyya Game Da Bada
Wanann shi ne abin da malamai na imamiyya suka karfafa na da da na yanzu, Shaihul Mufid yana cewa: “Fadin imamiyya game da Bada an same shi ne daga ruwaya ba daga hankali ba… ba abin da ake nufi da shi sai bayyanar wani ra’ayi bayan waninsa da kuma bayyanar al’amari bayan ya buya, Ubangiji madaukakin sarki a dukkan ayyukansa bayyanannu ne a cikin halittarsa bayan ta kasance, kuma ayyukansa sanannu ne gunsa cikin abin da bai gushe ba”[12].
Sheikh Tusi yana cewa: “Bada hakikarsa a luga shi ne bayyana saboda haka ne ake cewa katangun gari sun bayyana garemu kuma ra’ayin ya bayyana garemu… amma idan aka raba wannan lafazi zuwa ga Allah (S.W.T), to akwai abin da ya halatta a danganta shi gareshi da kuma abin da bai halatta ba; Amma abin da ya halatta Bada shi ne abin da yake halatta shafe hukuncin shari’a, a kan haka ne kuma ake fassara duk abin da ya zo na daga hadisan Bada wanda ya zo daga imamai (A.S) banda da ma’anar da ba ta halatta ba ga Allah madaukakin sarki na ma’anar samun ilimin da bai sani ba a da”[13].
Sayyid Abdullahi Shubbair ya ce: “Bada tana da ma’anoni masu yawa wasu ana iya siffanta Allah da su wasu kuma ba ya yiwuwa a sifatan shi da su, kuma al’umma ta hadu a kan cewa; ma’anar samuwar ilimi bayan jahilci ba ya halatta ga Allah kuma wanda ya daganta wa imamiyya wannan to ya yi musu kagen karya kuma imamiyya sun barranta da shi”[14].
Sayyid Abdulhusain Sharafuddin ya ce: “Abin da shi’a suke cewa shi ne Allah yana rage rashin lafiya ko ya dada shi, haka nan ma game da lafiya da cuta da dacewa da tabewa da bala’o’i da musibu da imani da kafirci da saurana abubuwa kamar yadda Allah (S.W.T) yake fada: “Yana shafe abin da ya so ya na kuma tabbatarwa kuma a gunsa akwai Ummul kitab”[15].
Wannan shi ne abin da Umar dan Khaddabi ya tafi akansa da dan Mas’ud da Abi Wa’il da Katada kuma Jabir ya rawaito shi daga manzon Allah (S.A.W), haka nan da yawa daga magabata suna addu’a suna kaskan da kai ga Allah da ya sanya su cikin masu arzuta ba masu tabewa ba, kuma hadisai mutawatirai sun zo daga imamanmu (A.S) a cikin addu’i da aka ruwaito, kuma ya zo a cikin littattafan Sunan masu yawa cewa sadaka, da bin iyaye, da aikata kyakkyawa, suna mayar da tabewa ta koma arzuta kuma su dada tsawon rayuwar mutum, kuma ya inganta daga Dan Abbas ya ce: “Daukar mataki ba ya kawar da kaddara sai dai Allah yana shafe abin da ya so na kaddara da addu’a”. Wannan kuma shi ne Bada din da shi’a suka tafi akansa kuma sabaninmu da Ahlussunna a Bada a lafazi ne… abin da shi’a suka fada game da Bada da wannan ma’ana da muka ambata dukkan musulmi sun tafi akansa…”[16].
Shaikh Aga Buzurg ya rubuta yana cewa: “Bada ma’anarsa a lugga shi ne; Bayyanar wani ra’ayi da babu shi a da da kuma canjin wani abu da aka sani bayan da ba a san shi ba. Wannan ita ce fahimtar dukkan mutane sai dai wannan mustahili ne ga Allah (S.W.T) saboda yana lizimtar bayyanar sani da wani abu da da dacan ba a san shi ba, ko kuma gajiya a kan aikata shi wanda Allah ya tsarakaka daga garesu… Bada da imamiyya suke kudurce shi; Shi ne wanda sauran musulmi suke imani da shi da yake sabanin abin da yahudawa suka tafi a kai na cewa; Allah ya riga ya gama komai kuma ba yadda za a yi wani abu ya canja gunsa “Hannun Allah abin yi wa kukumi ne”. Ko kuma idan ka bi maganganun yahudawa zaka ga cewa suna ganin Allah ya samar da dukkan halittu a tashi daya. Babu wani abu da za a samu gunsa sai ya kasance da ma can an same shi tun farko. Ko kuma masu ganin cewa Allah ya halicci mala’ika na farko da sauran rauhanai masu juya falaki kuma ya bar su su aiwatar da abin da su kan tafiyar da al’amuran bayi, shi kuma ya kau da hannunsa wajan tafiyarwa. To wadannan akidoji dole ne ga kowane musulmi ya kore su ya kuma kudurce cewa Allah madaukakin sarki: “Kowace rana shi yana cikin wani sha’ani...[17]”[18].

Muhimmancin Bada Wajan Tarbiyyantarwa Da Ingantacciyar Akida
Ya bayyana kamar yadda ya rigaya cewa; Bada yana da ma’ana da take sananniya gun musulmi gaba daya kuma imamiyya ba su da wata ma’ana da ban da ta sabawa sauran musulmi, sai dai kawai ma’ana ta lugga da lafazi da aka fahimci kuskure ne dangantawa Allah jahilci kuma ya bayyana cewa bai halatta ba danganta wannan ma’ana ga Allah madaukakin sarki. Domin akidun musulmi ana auna su da ma’aunin asasinta na ilimi da kuma dalilanta na hankali ne wani lokacin kuma da sakamakon da take haifarwa, amma game da Bada akwai tambayoyi da zamu iya kawowa da kuma amsar su kamar haka:
*- Idan ya kasance Allah ya riga ya yi hukunci na farko kuma ya san ba shi ne zai yi tasiri ba zai kai ga wurgar da shi ne, to menene amfanin bayar da labarinsa? Menene kuma amfanin da za a samu daga Bada a wannan yanayin?
Amsa: imani da Bada yana da amfani ta bangare biyu masu muhimmanci, bangaren akida da kuma bangaren tarbiyya;
Fuska ta farko: Amma game da akida maganar da Allama majlisi ya kawo ta wadatar yayin da yake cewa: “Imamai (A.S) sun kai matuka wajan fadin Bada domin su yi raddi ga yahudawa da suke cewa Allah ya riga ya gama komai ya gama tsarinsa, da kuma wasu daga mu’utazilawa da suke cewa: Allah ya halitta halittu lokaci daya kamar yadda suke, wanda ya hada da ma’adinai, da shuke-shuke, da dabbobi, da mutane, kuma (suka ce) ba ya gabatar da halitta a kan duk wata halitta, domin gabatarwar tana kasancewa ne a yadda take bayyana ba a faruwarta ba da samar da ita. Wannan kuma sun same shi ne daga maganar malaman falsafa da masu imani da nazarin mala’iku da rauhanai masu juya falaki da su ne ke juya al’amuran bayi, suna ganin Allah ya riga ya bar tafiyar da al’amuran bayi, suna danganta komai zuwa garesu ba zuwa ga Allah ba”[19].
Karfafawar imamai (A.S) a kan Bada ya zo ne domin raddin dukkan wata mahanga da wani ra’ayi da yake iyakance ikon Allah da kudurarsa, da kuma tabbatar da cewa wannan hakika ce tabbatacciya a siffofin Allah cewa yana halitta abin da ya so kamar yadda ya ga dama yana kuma tafiyar da al’amuransu kuma kaddarawarsa ba ta cire masa iko da nufi da zabi.
Kamar yadda Bada ya zo domin ya karfafi zabin mutum da nifinsa ta hanyar bayanin ikon Allah da yake cikin Lauhil mahafuz da ba ya karbar canji da kuma wani lauhin na shafewa da tabbatarwa wanda Allah ya halitta su tun farko cewa abin da aka zartar a cikinsa yana karbar ya canja shi daidai gwargwadon abin da mutum ya yi a wannan duniya na daga ayyuka.
Wato akidar Bada ta zo ne domin ta cika binciken nan na kaddarawar Allah da hukuncinsa saboda a kare wannan akida daga shige gona da iri domin kada a yi mata fahimta da ma’anar da zata cire wa Allah zabi da nufinsa. Saboda haka sai akidar Bada ta zo domin ta tabbatar da cewa kaddarawar Allah ba ta iya cire masa zabi kuma ba ta cire wa shi kansa mutum na sa zabin.
Fuska ta biyu: Ta fuskacin tarbiyya muna iya ganin akidar Bada ta yi tasiri wajan tarbiyyantar da rayuwar mutum. Allama majalisi ya bayyana dalilin da ya sa imamai suke karfafa Bada a cigaban maganarsa yana cewa: “Sai imamai suka kore wannan suka tabbatar da cewa Allah madaukakin sarki kullum yana cikin sha’ani ta hanyar rasarwa da fararwa, da kashewa da rayarwa, da makamantansu, domin kada bayi su bar addu’a da kaskantar da kai ga Allah da kuma rokonsa da binsa da kusanta zuwa gareshi da abin da zai zama maslahar duniya da lahira garesu, kuma domin su nemi yin sadaka ga talakawa da sadar da zumunci da bin iyaye da horo da kyakkyawan aiki da kuma kyautatawa ga abin da aka yi musu alkawarinsa na tsawon rayuwa da dadin arziki”.
Ta wata jihar akidar Bada tana daidai da al’amarin akidar tuba da kuma sharuddan karbarta gun Allah, kamar yadda tuba yake da mfani wajan gina mutane da kuma toshe musu kofar yanke kauna da bude kofar buri da kauna da samar da kumajin canji da kawo gyara haka nan Bada yake da wannan tasiri a rayuwar mutum. Kai Bada yana zama daya daga abubuwan da suke lizimtar tuba da sauran ayyuka, domin dole ne mai tuba ya yi imani da cewa alkalamin Allah bai bushe ba a Allon shafewa da tabbatarwa, Allah yana shafe abin da ya so ya tababatar da abin da ya so ya arzuta wanda ya so ya tabar da wanda ya so daidai yadda bawa ya lizimci kyawawan dabi’u da kyawawan ayyuka ko kuma abin da yake yi na munanan ayyuka. Saboda haka ikon Allah da nufinsa ba haka nan kawai yake ba babu hikima ba, kai da bawa ya tuba ya yi aiki na gari da wajibai ya kuma yi riko da kamewa sai a fitar da shi daga cikin tababbu a sanya shi cikin masu arzuta, haka nan ma akasin hakan.
A kan haka muna iya fahimtar zancen imamai (A.S) cewa: “Ba a bauta wa Allah da wani abu da ya kai (imani da) Bada ba”[20].
A wata ruwayar “ Ba a taba girmama Allah da wani abu da ya kai (imani da) Bada ba”[21].
Da kuma wata ruwaya; “Babu wani annabi da Allah ya aiko sai ya daukar masa alkawarin dabi’a uku; furuci da bautar Allah da kuma sance dukkan gumaka kuma da fadin Allah yana gabatar da abin da ya so ya jinkirta abin da ya so”[22].

Tambayoyi Da Amsa Game Da Imani Da Bada
Akwai tambayoyi da aka yi game da Bada kamar haka;
1- Imani da Bada yana iya kai wa ga wasa ya zo daga Allah (S.W.T) domin tare da ya san cewa za a samu canji a lokacin bayar da labari, ya zama wasa kenan.
Amsa: Wasa yana kasancewa ne idan an kaddara ba wani manufa da amfani da bayar da labarin zai samar, wannan kuma ba zai yiwu a iya tabbatar da shi ba domin akwai yiwuwar samun amfani da manufa da amfanin yana komawa ga bawa ne.
2- Idan annabi ya bayar da labari da faruwar wani abu sannan sai aka sami Bada a labarin farko ba makawa ya zama ya dogara ne da wani abu wajan bayar da labarin farko, kuma yaya annabi ko imami zai yi game da bayar da amsa kan abin da ya fada a baya?.
Amsa: Bari mu bayar da misali; Da wani zai sha guba mai halakarwa da zata kai ga mutuwa tabbas kana iya bayar da labarin mutuwarsa bayan awowi kuma wannan labari gaskiya ne idan an yi la’akari da abin da ya kai ga mutuwar, da mutuwar ba ta faru ba to dole ya zama saboda faruwar wani abu da ya hana afkuwar hakan, kamar zuwan likita da zai yi masa magani da cikakkiyar kwarewa, wancan bayar da labarin ba karya ba ne kuma ba a ganinsa bayar da labari ba dalili, haka nan al’amarin wahayi da yake bayar da labarin abin da zai faru a nan gaba duk gaskiya ne idan an yi la’akari da sababi wanda yake da sharadin rashin faruwar abin da zai hana aukuwar hakan, saboba haka a nan babu wani abin ki da zai lizimci wannan magana sai dai rashin sanin annabi ko imami da faruwar abin da ya hana aukuwar hakan, muna iya cewa Allah yana iya ba wa annabi labari da faruwar abin amma ya ki ba shi labari da abin da zai hana afkuwarsa saboda wata maslaha da take ga bayi[23].
3- Faruwar Bada yana iya kaiwa ga tuhumar annabi ko imami da karya?.
Amsa: Tuhumar annabi ko imami da karya zunubin yana kan wanda ya yi haka ne, domin tuhumar idan ta zo daga kafiri to wannan ba mamaki domin da ma ya ki duk imani da Allah da annabta da makoma, idan kuma ya zo daga mumini to imaninsa zai hana shi, idan kuwa bai hana shi ba to wannan mai raunin imani ne.
Muhimmi a nan shi ne Bada ba dalili ne na hankali ba da zai sa tuhuma da karya, da yawa ma Bada yana bayar da yakini ne kamar a kissar Annabi Ibrahim (A.S) da aka umarta ya yanka dansa, fansar dan da wani abu yana bayar da yakini ne na farko da yanka dansa Isma’il (A.S). Ba don labarin farko ya zama gaskiya ba da ba a umarce shi da yanka rago ba maimakon dansa, domin fansa a nan tana nufin canji (Bada).

Bayanin Abin Da Ya Gabata A Takaice
Bada da ma’anar samun canjin ra’ayi mustahili ne ga Allah madaukaki kuma imamiyya ba sa imani da shi, wanda ya yi imani da hakan a wajansu kafiri ne kuma dole a barranta daga gareshi[24].
Na’am Bada wanda yake hankali ya yarda da shi kuma wajibi ne a yi imani da shi, shi ne wanda ayar kur’ani mai girma ta yi bayaninsa: “Allah yana shafe abin da ya so yana kuma tabbatar (da abin da ya so) kuma a gunsa akwai Ummul kitabi”. Wannan shafewa da tabbatarwa ga abin da Allah yake bayyanarwa a harshen annabinsa ko waliyyinsa a zahiri yana zama domin maslahar da take cikin bayyanarwar ne, sannan sai ya shafe shi, sai abin da ba shi ne ya bayyanar ba ya faru tare da cewa Allah ya san hakan tun farko.
Bada ya yi kama da shafe shari’ar da suka gabata da shari’ar annabinmu Muhammad (S.A.W), ko kuma shafe wasu hukuce-hukunce da shari’ar ta zo da su da wasu hukunce-hukunce da suke bi musu[25].
Wanda bai yi imani da Bada da wannan ma’ana ba hakika ya kayyade kudurar Allah da nufinsa, kamar yadda kur’ani ya yi nuni da hakan domin raddi ga wasu akidojin yahudawa a fadinsa madaukakin sarki: “Yahudawa suka ce: Hannun Allah abin yi wa kukumi ne, an sanya hannuwansu a cikin kukumi”[26]! [27]”.
Wannan akida ta yahudawa ta shiga cikin akidun wasu daga kungiyoyi da mazhabobin akidu na musulmi ban da mazhabar imamiyya.
Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai


[1] - Bakara: 213.
[2] - Anbiya: 7. Da Nahal: 43.
[3] - Fadir: 43.
[4] - Ahzab: 62.
[5] - Ra’ad: 39.
[6] - Ajwibatu Masa’ili Jarillah: 79.
[7] - Awa’ilul Makalat: 92-93.
[8] - Biharul Anwar: 4\121, H 63.
[9] - Biharul Anwar: 4\111, H 30.
[10] - Ra’ad: 39.
[11] - Arrahaman: 29.
[12] - Tashihul I’itikadatil Imamiyya: 66.
[13] - Iddatul Usul: 2\29.
[14] - Masabihul Anwar: 1\33.
[15] - Arra’ad: 39.
[16] - Ajwibatu Musa Jarullah: 101-103.
[17] - Arrahman: 29.
[18] - Azzari’a: 3\51-53.
[19] - Biharul Anwar: 4\129-130.
[20] - Usulul Kafi: 1\146. Kitabut Tauhid, Babin Bada.
[21] - Usulul Kafi: 1\146. Kitabut Tauhid, Babin Bada.
[22] - Usulul Kafi: 1\147. Kitabut Tauhid, Babin Bada.
[23] - Dubba kissar Annabi Yunus (A.S) da mutanensa wanda ya bar gari yana mai yakini cewa sun halaka bisa sunnar Allah. Hafiz Muhammad.
[24] - Aka’idul Imamiyya: 45.
[25] - Aka’idul Imamiyya: 46.
[26] - Ma’ida: 64.
[27] - Ma’anar hannayen Allah abin yi wa kukumi ne: Baya iya canja wani abu da ya hukunta ba yadda zai yi, wannan kuma shi ne ainihin iyakance iko da kudura na Allah. Ba kamar yadda wasu suka dauka ma’anarta tana nufi rowa ba domin ba wanda ya fi imam Ali (A.S) da Ahlin gidansa sanin ma’anar kur’ani. Kalmar infaki a ayar ba ta zo ba ne a matsayin karina da take nuna ma’anar ciyarwa sai dai ita tana nufin ma’ana mai fadi ta ayyukansa da ba su da iyaka. Ayoyin da suke magana a kan maudu’in da suka biyo bayan ayar suna nuna haka a fili da cewa; da sun yi aiki na gari da Allah ya canja hukuncinsa akansu. Hafiz Muhammad Sa’id.