7-Kamun kafa Da Mutane Tsarkaka Da Mutane Masu Daraja
Bahsin da ya gabata an yi magana ne dangane da kamun kafa da addu'ar mutane masu tsarki da daraja, wato wanda yake da wata bukata yana neman su yi masa addu'a domin Allah ya biya masa bukatarsa, wato addu'arsu zata sanya ya samu kusanci.
Amma abin da muke magana a kansa a cikin wannan Bahasi shi ne yin kamun kafa da su kansu don samun kusanci zuwa ga Allah madaukaki. Wato mai neman biyan bukata ba tare da ya nemi addu'arsu ba domin ya samu biyan bukatarsa, sai ya yi kamun kafa da su domin kasantuwarsu suna da matsayi a wajen Allah, sakamakon haka sai ya nemi abin da yake bukata a wurin Allah madaukaki, ta hanyar wannan matsayi da daukaka da suke da su a wajen Allah, sai Allah ya biya masa bukatarsa. Wannan nau'in kamun kafa kuwa ana yin sa ta hanyoyi daban-daban kamar haka:
Ya Allah don matsayin da suke da shi a wurinka!
Ya Allah don kusancin da Masoyanka waliyyanka suke da shi a wurinka!
Ya Allah albarkacin manzonka da iyalansa tsarkaka!
A cikin dukkan wadannan jumloli shi kan shi mutum wanda yake da matsayi a wurin Allah da siffofinsa masu kyawu su ne zasu sanya a biya wa mutum bukatarsa, bayan shaharar wannan nau'i na kamun kafa, akwai ruwaya ingantacciya da ta zo a kan haka wacce ake kira da "dharir"harda kuwa wadanda suke da sabani a kan wannan al'amari sun tafi a kan ingancin wannan ruwaya. Domin kuwa mun kawo yadda aka kafa hujja da wannan hadisi zamu kawo wannan hadisi a nan kamar haka:
Usman Bn Hanif yana cewa: Wani mutum makaho ya zo wajen Manzo (S.A.W) ya ce ya manzon Allah ka yi mini addua'a Allah ya ba ni waraka. Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Idan kana so zan yi maka addu'a idan kuma zaka yi hakuri shi ne abin da ya fi.
Sai wannan makaho ya ce ka kira Allah ka yi mini addu'a! A wannan lokaci sai Manzo ya ce: ka je ka yi alwala mai kyau, sannan ka yi salla raka biyu ga wata addu'a nan ka karanta.
Ya Allah ina rokonka ina fuskantarka da manzonka Muhammad wanda yake annabin rahama ne ina kamunka kafa da shi a wurinka! Ya manzon Allah ina Kamun kafa da kai a wajen Allah domin ya biya mini bukatata. Sai Manzo ya ce: Ya Ubangiji ka biya masa bukatarsa domin ni.
Ibn Hanif yana cewa: Mun kasance a wajen Manzo ba tare da tsawon lokaci ba sai wannan mutum ya shigo a wajenmu kamar bai taba samun matsalar ido ba. Kafa hujja da wannan hadisi kuwa ya samo asali ne ta hanyar kasantuwar ingancin dangane da kuma ma'anarsa wacce take a fili.
Amma ta bangaren dangane da wannan hadisi kuwa Tirmizi yana cewa: wannan hadisi ne mai kyau kuma ingantacce. Ibn maja shi ma wanda ya ruwaito wannan hadisi yana cewa: wannan hadisi ne ingantacce. Sannan cikin sa'a shi ma Ibn Taimiyya ya tafi a kan ingancin wannan hadisi. Rufa'i wanda yake daya daga cikin marubutan wahabiyawa kuma na wannan zamani yana cewa: Babu shakka a kan kasantuwar ingancin wannan hadisi kuma mashahuri ne.
Saboda haka dangane da sanad ko danganen wannan hadisi babu sauran wani kace-nace. Saboda haka a nan abin da ya yi saura shi ne muyi bincike dangane da ma'anarsa a kan halascin wannan nau'i na kamun kafa.
Domin kuwa bayyana wannan ma'ana zamu tunatar da wasu abubuwa guda biyu kamar haka:
1-Menene makaho ya nema a wajen Manzo?
2-Domin ya samu biyan bukata wane irin Tawassuli ko kamun kafa da Manzo ya koyar da shi? !
Cakuda wadannan abubuwa guda biyu zai sanya a kasa gane gaskiyar al'amarin, babu shakka wannan makaho ya roki addu'a daga Manzo, wato ya yi kamun kafa da addu'ar Manzo, a nan babu sabani a kan hakan.
Magana kuwa tana nan a cikin abin da Manzo ya koyar da wannan makaho, a cikin wannan addu'a da Manzo ya koyar da shi ya nuna masa ne ta yadda zai yi kamun kafa da shi kansa manzon, wato ya sanya Manzo tsakiya a tsakaninsa da Ubangiji, ta yadda sakamakon haka Allah ya biya masa bukatunsa. Sheda kuwa a kan hakan shi ne jumlolin da suka zo a cikin hadisin wadanda suke nuni da hakan. su ne kuwa kamar haka:
1- "Ya Allah ina rokonka ina fuskantarka da annabinka" wato ina rokonka da annabinka kuma ina fuskantarka da annabinka. Wace jumla ce ta fi wannan bayyana a kan cewa mai addu'a yana hada Allah ne da manzonsa wajen neman biyan bukatarsa.
A nan yana nuna ya yi kamun kafa ne da shi kansa manzon sakamakon girmansa a wajen Allah yake neman biyan bukatunsa.
2-jumlar "Muhammad annabin rahama"
Wannan jumla tana nunawa a fili cewa Manzo wanda yake rahamar Ubangiji ce a bayyane, shi ya sanya yake kamun kafa da wannan rahama da Ubangiji zuwa ga Allah.
Abin mamaki a nan shi ne irin wannan al'amari ya sake faruwa a zamanin Usman. Sannan matsalar mutumin da yake neman biyan bukata a wannan lokaci ta warware ne ta hanyar wannan addu'a, amma akwai bambanci kadan cewa wanda ya koyar da wannan addu'a a lokaci na farko shi ne Manzo da kansa, amma alokacin na biyu Usman Bn Hanif ne, a nan zamu kawo cikakken abin da ya faru daga mu'ujamul kabir na Dabarani kamar haka:
Wani mutum a zamanin hukumar Usman ya je wajen Usman domin wata bukata tasa amma bai samu biyan bukata ba, wata rana wannan mutum sai ya hadu da Usman Bn Hanif kuma ya gaya masa abin da yake damunsa, sai ya ce masa: ka je ka yi alwala ka yi salla raka biyu, sannan ka ce:
"Ya Allah ina rokonka kuma ina fuskantarka da manzommu Muhammad annabin rahama, ya Muhammad ina kamun kafa da kai zuwa wajen ubangijinka don a biya mini bukatata".
Sai ya aikata wannan aiki, sannan ya tafi wajen Khalifa sai kuwa ya biya masa bukatarsa, sai ya sake haduwa da Usman Bn Hanif, ya tambaye shi danganen wannan addu'a, sai ya ce masa wata rana mun kasance a wajen Manzo (S.A.W) sai wani mutum mai ciwon ido ya zo wajen Manzo ya nemi ya yi masa addu'a, sai Manzo ya koyar da shi abin da na koyar da kai.
3-Jumlar "Ya Muhammad ina fuskantar Ubangiji da kai".
Wannan lafazi na "da kai"yan nuna kamun kafa ne da shi kansa Manzo din, saboda haka duk da cewa ya roki Manzo addu'a, amma ba shi ne matsayin shedarmu ba a nan. Amma a cikin abin da Manzo ya koyar da shi akwai shi kansa Manzo wanda yake rahamar Allah ne a cikin halitta, kuma shi ne silar biyan bukatar wannan makaho. Sannan jumlar "Ka ba shi lafiya don girmana" ita ma tana nuni ne ga sakamakon girman za a wajen Allah, zai samu biyan bukatarsa.
Wata kila a fahimci cewa wannan jumla ta sama tana nufin cewa; Ya Allah! Ka karbi addu'arsa da na yi masa, amma zahirin wannan hadisi ba ya nuna cewa Manzo ya yi wa wannan makaho addu'a, domin kuwa ya koyar da shi ne addu'ar kamar yadda muka yi bayani a sama. Ballantana Manzo ya bukaci Allah ya amsa addua'r da ya yi masa don girmansa a wajen Allh. Idan kuwa da Manzo ya yi wa wannan makaho addu'a bayan addu'ar da ya kowar da shi, to tabbas da wannan babban sahabi ya ruwaito wannan addu'a ta Manzo.
Bayan wannan ma idan mun dauka cewa bayan addu'ar da Manzo ya koyar da wannan makaho shi ma ya yi wa makahon addu'a, a nan ba zai cutar da kafa hujjar da muka yi ba da wannan hadisi, domin kuwa ba muna magana ne ba a kan addu'ar da Manzo ya yi masa. Domin kuwa muna kafa hujja ne a kan addu'ar da Manzo ya koyar da makaho ta yadda ya koyar da shi yadda zai yi kamun kafa da shi kansa Manzo sakamakon matsayi da daukaka da yake da shi a wajen Allah.
Idan da zaka bai wa wani masanin harshe wannan hadisi wanda ba shi da wata masaniya a kan haka, babu abin da zai fahimta bayan kamun kafa da Manzo (S.A.W) a wajen Allah madaukaki.
Ibn Taimiyya da mabiyansa lokacin da suka fuskanci wannan hadisi sun yi kokari su kawo matsala dangane da ma'anar wannan hadisi dangane da jumlolin da suke nuni a kan kamun kafa da Manzo a fili, sai su ce yana nufin addu'a ne, suna cewa:
Jumlar da take cewa: "Ina fuskantarka da manzonka" sai su ce wai ina fuskantarka da addu'ar manzonka.
A wannan akwai wani abin da ba a fada ba wannan kuwa shi ne sun yi hukunci ne sakamakon akidar da suke da ita tun da farko na haramcin kamun kafa da waliyyan Allah, amma wannan tawili nasu sam bai dace ba da jumlolin da muka ambata dangane da hakan.
Idan kuwa gaskiya ne makaho ya yi kamun kafa ne da addu'ar Manzo, to me ya sa Manzo ya ce masa ka ce: "Muhammad annabin rahama" sannan ya ce masa ka ce: "Ya Muhammad lallai ina fuskantarka"
Bayan wannan idan muka dauka ma'anar wannan yana nufin addu'a ne, to wannan zai bata tsarin jumlar.
Alusi Bagdadi (ya rasu 1270) wanda ya kasance daya daga cikin wadanda suka yada wahabiyanci a nan yana mika wuya zuwa ga gaskiya, inda ya tafi a kan cewa kamun kafa da waliyyan Allah Manzo ne ko waninsa ba shi da wani laifi, da sharadin cewa mu dauka wannan mutumin yana da matsayi ne a wajen Allah .

Tarihin Kamun kafa Da Bayin Allah Tsarkaka
Tarihi a bayyane yana nuna cewa tun kafin zuwan musulunci mutane masu kadaita Allah sun kasance suna Kamun kafa da wadanda suke ganin suna da matsayi a wurin Allah, sannan kuma sakamakon tsarkin fidirarsu su suna ganin wannan aiki wani aiki ne wanda yake mai kyau. A nan zamu yi nuni da wasu daga cikinsu:
1-Abdul Mutallib da kamun kafa da Muhammad (S.A.W) a lokacin da yake shan nono, tsananin fari ya mamaye Makka da kewayenta, sai Abdul mutallib ya dauki jikansa mai shan nono ya daga sama, sannan ya roki Allah ruwan sama, har ana cewa mashahuriyar wakar Abu Dalib ya yi ta ne dangane da haka wacce take cewa: Fuska mai haske wacce gizagizai suka yi ruwa dominta, wacce sakamakon haka ne marayu da mata gwagware suka samu mafaka.
2-Abu Dalib da kamun kafa da Manzo a lokacin da yake saurayi
Kamar abin da ya faru lokacin Abdul mutallib a lokacin shugabancin Abu Dalib ma ya sake faruwa, sakamakon haka ne sai kuraishawa suka zo wajensa suka kawo masa kuka a kan fari da rashin ruwa da ake ciki, Sai Abu Dalib ya yanke shawara a inda ya roki Allah da ya saukar musu da ruwa tare da kamun kafa da dan dan'uwansa Muhammad wanda yake karamin yaro ne a wannan lokaci. Sai ya kama hannun Manzo ya jingina bayansa ga dakin ka'aba, wani lokaci yana nuni da wannan yaro wani lokaci kuwa yana nuni da sama, wato Ubangiji albarkacin wannan yaro ka saukar mana da rahamarka. Ba tare da tsawaita lokaci ba, sai hadari ya mamaye garin Makka da kewayanta, sai koramu da tabkuna suka cika makil da ruwa .
3-Sallar rokon ruwa tare dakananan yara da tsofaffi
A cikin ladubban sallar rokon ruwa ana cewa ya fi dacewa masu sallar rokon ruwa su fita tare dakananan yara da tsofi, har wasu ma suna cewa a tafi tare da dabbobi ma wajen wannan sallar rokon ruwa. Manufar kuwa zuwa dakananan yara marasa laifi da tsofaffi raunana da dabbobi wadanda ba su magana shi ne, domin suna cewa idan su ba su cancanci rahamar Ubangiji ba sakamakon zunubbansu .
Ya Ubangiji wadannan kananan yara mararsa laifi, da tsofaffi raunana, da dabbobi wadanda ba su iya magana, sun cancanci rahamarka.
Ya Ubangiji albarkacinsu ka aiko mana da rahamarka!
Ya uabngiji! Mai lambu saboda itaciya guda daya yake ban ruwa, amma sakamakon haka sai ciyawu ma su samu!
Wannan yana nuna mana cewa tun kafin zuwan musulunci mutane a dabi'ance sun kasance suna kamun kafa da abubuwan da suka cancanci rahamar Allah, don neman biyan bukatunsu, kuma da musulunci ya zo ya tabbatar musu da hakan.
4-Khalifa na biyu yana kamun kafa da Ammin Manzo (S.A.W)
Bukhari a cikin sahih dinsa yana ruwaito cewa Umar Bn khattab a lokacin fari da tsananin rashin ruwan sama ya kasance yana kamun kafa da Abbas dan Abdul Mutallib domin su samu ruwan sama, ga abin da yake cewa: Ya Allah muna muna rokonka albarkacin annabimmu ka shayar da mu ruwa, ya Allah muna kamun kafa zuwa gareka da ammin annabimmu ka shayar da mu sai su sha!
Dangane da danganen wannan hadisi kuwa babu sauran wata magana domin kuwa sahih bukhari karbabbe ne a wajen 'yan Sunna, saboda haka magana kawai ta rage wajen ma'anarsa.
Duk lokacin da aka bai wa wani balarabe wannan hadisi wanda a cikin zuciyarsa bai hadu da wani sabani ba zai ce: Khalifa na biyu ya kasance yana kamun kafa ne da ammin Manzo domin Allah madaukaki ta albarkacinsa ya aiko da ruwan sama ya shayar da su saura su samu.
Wannan addu'a kuwa tana nufin cewa ya Allah idan harm u ba mu cancanci ka yi ruwa saboda mu ba, to albarkacin ammin Manzo domin alakar da suke da ita a tsakaninsu ka aiko mana da ruwan sama.
Saboda haka idan a nan ana nufin kamun kafa da wani mutum ne, to kamun kafa da Manzo ya fi komai dacewa, domin kuwa Abbas ya samu darajarsa ne daga Manzo (S.A.W) saboda haka me ya sa a nan ya bar Manzo ya yi kamun kafa da Abbas, wannan shi ne abin tambaya a nan?
Amsar wannan kuwa shi ne a wajen rokon ruwa ana kamun kafa ne da wadanda masu rokon ruwa suke daya da shi wajen bukatr ruwan, kamar kananan yara da tsofaffi, ta yadda zasu motsa rahamar Ubangiji, su ce ya Allah idan mu ba mu cancanci wannan ba to wadannan kananan yara da tsofi sun cancanta ka aiko saboda su.
Saboda haka wannan ya cancanta ga ammin Manzo wanda ya kasance yana raye a wannan lokaci, ba wai Manzo ba domin kuwa shi a wannan lokaci ya bar duniya kuma halin da suke ciki ya bambanta.
Wadanda suke sabani a kan halascin kamun kafa ko tawassuli da manyan bayin Allah suna fito-na-fito ne da wannan hadisi, saboda haka ko ta halin kaka suna kokari ne suga sun karkatar da ma'anarsa, suna cewa abin da khalifa yake nufi a nan yana kamun kafa ne da addu'ar Abbas, ba wai yana kamun kafa ba ne da shi kansa Abbas ko wani matsayi na shi. Wannan tawili kuwa ta fuskoki daban-daban ba zai inganta ba:
Na farko: Sallar rokon ruwa da addu'ar, umar ne ya gabatar da su ba Abbas ba, saboda haka a nan babu magana a kan addu'ar Abbas.
Abin da kuwa yake tabbatar mana da cewa wannan addu'a umar ne ya yi ta ba Abbas ba, lafazin da ya zo a cikin addu'ar kamar haka: Ya Allah mun kasance muna kamun kafa da Manzo ka shayar da mu, yanzu muna kamun kafa da ammin Manzo ka shayar da mu, a wannan lokaci sai ruwa ya sauka aka shayar da su.
Saboda haka wannan yana nuna cewa wanda ya gabatar da wannan shiri tun daga farko har karshe khalifa ne, ba wai Abbas ammin Manzo ba, ballantana Umar ya yi kamun kafa da addu'arsa.
Na biyu: Dalili na biyu shi ne a cikin babin da wannan addu'a ta zo yana magana ne a kan neman mutane daga shigaba don ya roka musu ruwan sama yayin da aka samu fari da rashin ruwan sama.
Wannan yana nuna cewa mutane su ne suka nemi khalifa da ya roka musu ruwan sama, shi kuma ya amsa musu rokn da suka yi masa.
Saboda haka a cikin wannan al'amari matsayin Abbas shi ne lokacin da umar yake addu'a ya yi nuni da shi inda yake cewa: "Ya Allah muna kamun kafa da ammin Manzo ka shayar da mu"
Na uku: Ibn Asir ya yi bayani yadda aka gabatar da wannan salla da addu'ar rokon ruwa, yana cewa Umar ya kasance yana nuni da Abbas yana cewa: "Wallahi wannan shi ne tsani zuwa ga Allah kuma mai tsayi a wurinsa" . Ya kasance yana rokon Allah ruwa a cikin wannan hali. Don haka kamun kafa ya kasance da shi kansa Abbas ne ba da addu'arsa ba.
Ibn Hajar Askalani (ya rasu 852) a wajen sharhin wannan hadisi yana rubuta cewa: dangane da abin da ya faru da Abbas yana nuna mana yadda ya halatta mutum ya yi kamun kafa da mutanen kwarai da iyalan gidan Manzo don samu ruwan sama .
A karshen wannan Bahasi zamu yi tunatarwa da cewa, Tawassuli ko kamun kafa da addu'a wacce take kowa ya aminta da wannan, wani nau'i ne na kamun kafa da wanda yake addu'a sakamakon matsayi da girma da yake da shi a wajen Allah. Domin kuwa idan da mai yin addu'ar ba shi da wani matsayin na musamman a kan abin da ya shafi tsarkin ruhi, sam addu'arsa ba zata iya zama mai tasiri ba.

Kamun kafar Masu Tsarki Da Matsayi A Cikin Ruwaya
Ya zo a cikin ruwayoyi da dama na AhlusSunna dangane da kamun kafa da manyan bayin Allah tsarkaka, amma abin mamaki a nan shi ne masu sabani da wannan abu duk da cewa suna ganin wadannan ruwayoyi har yanzu suna ci gaba da wannan fito na fito nasu, a nan masu wannan akida suna koyi ne da Ibn Taimiyya ba suna koyi da gaskiya ba ne, idan da ba suna yanke hukunci ba ne tun kafin su ga dalilai tabbas da ba zasu dage ba a kan wannan akida tasu ba.
A nan zamu kawo wasu daga cikinsu:
1-Atiyya Aufi ya ruwaito daga Abu Sa'idul Kudri yana cewamanzo ya ce: duk wanda ya fito daga gidansa da nufin zai je masallaci ya yi salla idan ya karanta wannan addu'ar rahamar Ubangiji zata lullube shi, sannan mala'iku da yawa zasu yi masa addu'a su nema masa gafara a wajen Allah. Wannan addu'a kuwa ita ce: "Allahumma inni as'aluka bi hakkis Sa'ilina alaika, wa as'aluka bihakki mashai haza, Fa inni lam akhruj ashran wala batran wala rayyan wala sum'a, innama kharajtu itka'a saktik wabtiga'a mardhatika, an tu'izani minan nar, wa an tagfira zunubi, innahu la yagfiruz zunuba illa ant"
Wato, ya Ubangiji! Ina rokonka don matsayin masu rokonka, ina rokonka da matsayin wannan tafiya tawa, kuma ban fito ba don jin dadi ko saboda riya in nuna wa wasu mutane, ya Allah na fito ne domin tserewa fushinka da azabarka da neman yardarka, ya Allah ka tseratar da ni daga wuta, kuma ka gafarta mini zunubbaina don babu mai gafarta zunubbai sai kai.
Wannan hadisi dangane da ma'anar a kan abin da muke magana a kan shi na kamun kafa da masu matsayi da tsarki a fili yake. Sannan sanad ko danganen wannan hadisi ingantacce ne domin kuwa dukkan maruwaitan wannan hadisi an amince da su, sai kawai mutum guda wanda dole mu yi bayani a kansa, wannan kuwa shi ne Atiyya Aufi.
Masana ruwaya sun yi hukuncin da ya dace a kansa:
Abu Hatim yana rubuta cewa: Ana iya rubuta hadisinsa.
Ibn Mu'in yana cewa: Mutumin kirki ne.
Ibn Hajar yana cewa: Mai gaskiya ne.
Ibn Adi yana cewa: Ya kasance yana ruwaito hadisi daga mutanen kirki.
Ibn Sa'ad yana cewa: Hajaj ya rubuta wa wani daga cikin hakimansa mai suna Muhammad Bn Kasim takarda cewa: Ka kama Atiyya, sannan ka bijiro masa da zagin Ali ya kara da cewa shi mutum ne amintacce sannan hadisansa ingantattu ne.
Idan har ma wasu sun kasance suna sukarsa laifinsa bai wuce shi'anci ba, shi'an da ma'anarsa shi ne son Ali da 'ya'yansa (A.S)
Sannan yanayin wannan hadisi yana tabbatar mana cewa maganar ma'asumi ce, sannan makamantan wannan hadisi suna da yawa a musulunci.