4-Kamun kafa Da Adu'ar Manzo (S.A.W)
Manzo (S.A.W) mutum ne wanda yake ya fi kowa girma da daukaka a cikin dukkan halittar da Allah ya yi, Ayoyin Kur'ani sun yi nuni da haka a wurare da dama, saboda haka ba zai yiwu ba mu kawo dukkansu a wannan wuri.
Dangane da darajar Manzo ya wadatar da mu a kan cewa yana matsayin mai kare al'umma daga azabar Allah, Allah yana bayyanarwa a cikin Kur'ani cewa, matukar Manzo yana a cikin al'umma to Allah ba zai kama wannan al'ummar ba da azaba ba, kamar yadda yake cewa: Allah bai kasance zai azabtar da su ba matukar kanacikinsu, sannan Allah ba zai azabtar da sub a matukar suna neman gafara".
Sannan ya wadatar da mu a kan girman Manzo inda Allah madaukaki ya sanya sunan Manzo a gefen sunansa, sannan ya sanya biyayya ga Manzo tare da biyayya ga Allah, a kan haka Allah yana cewe: "Duk wanda ya bi Allah ya bi Manzo, lallai ya samu babban rabo".
Wadannan ayoyi da masu kama da su suna bayyanar da dajara da karama ta Manzo (S.A.W) matsayi da darajar da babu wani a cikin halitta wanda yake da shi, sakamakon wannan matsayin da daukaka da Manzo yake da shi a wajen Allah duk abin da yaroka za a biya masa bukatarsa. Don haka ne aka bai wa masu laifuka da zunubbai umurnin cewa, su nemi Manzo daya nema musu gafara a wajen Allah, inda Allah madaukaki yake cewa: "Da wadanda suka zalunci kawunansu zasu zo maka suna masu neman gafara a wajen Allah, kuma Manzo ya nema musu gafara, da sun samu Allah yana mai gafara kuma mai karbar tuba".
Sannan zamu iya fahimta daga wasu ayoyi cewa, sakamakon matsayi da daukaka manzanni sun kasance ana iya kamun kafa da su a wajen Allah kamar yadda zamu gani dangane da 'ya'yan annabi Yakub (A.S) lokacin da kuskuransu ya bayyana a fili, sai suka cewa mahaifinsu: "Ya babanmu ka nema mana gafara lallai mun kasance masu kuskure. Sai ya ce musu zan nema muku gafara a wajen ubangijina, kuma lallai shi mai gafara ne mai rahama".
Dangane da halascin wannan nau'i na kamun kafa babu wani shakku a cikinsa, domin kuwa babu sabani a kan haka. Abin da yake da muhimmanci a nan shi ne, sanin dalilin da ya sa nya ake karbar addu'ar annabawa.
Babu shakka tushen abin da ya sanya ake karbar addu'ar annabi ya samo asali ne daga tsarkin ruhinsa, sannan da kusancinsa ga Allah madaukaki. Don haka sakamakon wannan girma da daukaka ne na ruhi ya sanya Allah yake karbar addu'arsu.
Babu shakka addu'ar da ta taso daga ruhi mai tsarki wanda yake cike da soyayyar Ubangiji, ba tare da wani bata lokaci ba zata samu karbuwa a wajen Allah madaukaki.
Idan har akwai wata magana a kan halascin wannan kamun kafa kuwa, zai kasance ne dangane da kamun kafa da annabawa yayin da suka rasu wato lokacin da ba su raye a duniya. Tare da kula da abin da muka fada a wajen ziyarar kabari, mun yi bayani kan cewa babu wani bambanci tsakanin lokacin da annabawa suke a raye da lokacin da ba su raye a duniya, domin kuwa Manzo a cikin wadannan hali guda biyu yana iya nema wa mutum gafara a wajen Allah. Zamu yi cikakken bayani a kan wannan a cikin nau'in kamun kafa na shida insha Allah.

5-Kamun kafa Da Addu'ar Dan'uwa Mumini
Kur'ani yana bayyanar da cewa mala'iku suna yi wa masu imani addu'a, kamar haka:
"Wadanda suke daukar al'arshi da na gefensa, suna tasbihi da godiyar ubangijinsu, kuma suna masu imani da shi, sannan suna neman gafara ga wadanda suka yi imani" .
Wannan ba yana nuna cewa ba mala'iku ne kawai suke yi wa masu imani addu'a. Domin kuwa Kur'ani a fifli yana bayar da labarin yadda muminai suke wa junansu addu'ga abin da Kur'ani yake cewa: "Wadanda suka zo a bayansu, suna cewa, ya ubangijinmu! Ka yi mana gafara da 'yan'uwammu wadanda suka riga mu da imani, ya Allah kada ka sanya jin zafin a cikin zukatanmu dangane da wadanda suka yi imani, ya Allah kai ne mai rangwame mai rahama".
A cikin ayoyin da muka ambata a sama zamu iya fahimtar cewa, addu'ar mala'iku masu daukar al'arshi da kuma addu'ar muminai a kan 'yan'uwansu ta cancanci karbuwa. Saboda haka wannan aya tana nuna mana cewa mutum yana iya neman addu'a daga mala'ku da kuma sauran 'yan'uwansa masu imani.
Dangane da karbar adduar mumini kuwa, ya wadatar da mu inda Manzo (S.A.W) yake neman muminai su yi masa addu'a, inda yake cewa: Ku nema mini tsani a wajen Allah domin kuwa matsayi ne a cikin aljanna, babu kuwa wanda zai samu wannan matsayin sai wasu da suka cancanta daga cikin bayinsa, ina fata in zama nine, don haka duk wanda ya nemi kamun kafa da ni, cetona ya halasta gare shi". Kasantuwar wannan kamun kafar ya karbu a wajen dukkan musulmi ba tare da wani sabani ba, muna iya wadatuwa da wannan.

6-Kamun kafa Da Addu'ar Manzo Bayan Rasuwarsa
Bahsin da ya gabata ya tabbatar mana yadda kofofin rahama suka kasance a bude ga masu laifuka, ta yadda zasu iya kamun kafa da Manzo kamar yadda aya take nuni da hakan (da wadanda suka zalunci kawunansu sun…) wato suka nemi Manzo da ya neman musu gafara a wajen Allah. Sakamakon haka ne Kur'ani yake zargin munafukai domin kasantuwarsu sun rasa wannan falalar mai dimbin yawa. Ga abin da yake cewa: "Duk lokacin da aka ce musu, ku tafi zuwa Manzo domin ya nema muku gafara sai su kawar da kansu".
A nan akwai abin tambaya: shin sakamakon tafiyar Manzo zuwa ga rahamar Ubangiji wannan kofar gafarar da jin kai shi kenan ta kulle, ta yadda babu wani musulmi da zai je wajen Manzo ya roke shi da ya nema masa gafara a wajen Allah, ko kuwa wannan kofar albarka tananan bude kamar lokacin da yana raye? Wato musulmi har yanzu idan suka je haraminsa suna iya neman addu'arsa, ta yadda wannan ayar da muka ambata; "Da wadanda suka zalunci kansu sun zo wajenka suka neme ka da nema musu gafarar..". tana amfani a dukkan lokuta guda biyu, wato zamanin raywarsa da kuma bayan wafatinsa?
A wajen bayar da wannan masa dole ne a ce: Musulmi daga sahabbai da tabi'ai har zuwa yanzu sun kasance a aikace suna daukar wannan kofa a bude take, sannan musulmai a lokacin da suka ziyarci raudhar Manzo bayan yi wa manzon tsira sallama sukan karanta wannan ayar da muka ambata, tare da neman gafara daga Allah kuma suna rokon Manzo da ya nema musu gafara a wajen Allah madaukaki, saboda haka duk lokacin da mutum ya je ziyarar Manzo zai ga wannan al'amari daga al'ummar musulmi.
Bayan abin da tarihi yake nunawa ta hanyar ayyukan al'ummar musulmi danagane da neman addu'ar Manzo, addu'ar ziyarar Manzo ma wacce sunna da Shi'a suka ruwaito wannan addu'a tana tabbatar da wannan magana ta neman addu'ar Manzo. Domin jan hankalin masu karatu kuma suka kara natsuwa da abin da muke magana a kai, zamu kawo wassu daga cikin maganganunsu, ta yadda zai bayyanar mana yadda manyan malamai tun tsawon zamani suke neman kamun kafa da Manzo wajen yi musu addu'a:
1-Zakariya Muhyiddin Nawawi (631-676) Yana rubuta cewa: Mai ziyara yakan fuskanci Manzo ya yi kamun kafa da Manzo a kan abin da yake bukata kuma ta hanyarsa ya nemi ceto daga Allah, yana daga abu mafi kyau kasantuwar Mawardi, Alkali Abu Tayyib da wasu daga cikin manyan malamai suka ruwaito daga Utba tare da yabo suna cewa:
Utba yana cewa: Na kasance a wajen Manzo (S.A.W) wani mutum daga daji ya zo wajen Manzo ya ce "Assalamu alaika ya rasulullah, na ji Allah yana cewa: "Da wadanda suka zalunci kansu sun zo wajenka suka nemi gafara, kuma Manzo ya nema musu gafara, da sun samu Allah yana mai karbar tuba kuma mai jin kai"Lallai na zo wajenka ina mai neman gafara daga zunubaina sannan mai neman ceto a wajen Allah tare da kamun kafa da kai".
Kada mu yi tunanin cewa Nawawi ne kawai da malamansa suka tafi a kan ingancin kamun kafa da neman ceto daga Manzo. Malaman fikhu da na hadisi da dama sun kawo wannan a cikin littafansu na ziyara.
2-Kuddama Hambali (ya rasu shekara ta 620) a cikin ladubban ziyarar kabarin Manzo inda yake kawo maganar cewa"Mustahabbi ne ziyarar Manzo" Yaruwaito daga Abu Huraira yana cewa Manzo (S.A.W) ya ce: Duk wanda ya yi mini sallama, zan amsa masa sallamarsa. Sannan sai ya ruwaito daga Utba abin da muka ambata a baya kadan cikin hadisin Nawawi. Ya ce manufarsa wajen kawo wannan hadisi shi ne, don ya nuna cewa ana gabatar da ziyarar Manzo kamar haka:
3-Samhudi a cikin littafin "Mustau'ab" wanda Muhammad Bn Abdullah Samiri Hambali ya rubuta, yana ruwaito yadda ake ziyarar Manzo kamar haka:
Assalamu Alaika ya Rasulallah, assalamu alaika ya Nabiyyallah! Ya Allah kai ne ka fada a cikin littafinka ga annabinka cewa: "Da wadanda suka zalunci kawunansu…Ya Allah ga ni na zo wajen manzonka (S.A.W) ina mai neman gafara, ya Allah ina rokonka a kan ka wajabta mini rahamarka, kamar yadda ka wajabta ga wanda ya zo wajensa yayin da yake a raye, ya Allah ina ina kamun kafa da annabinka zuwa gare ka".
4- Gazali (ya rasu 505) Dangane da falalar ziyarar Madina da yadda ake ziyarar Manzo ya ruwaito a bayyane yana cewa: Bayan mutum ya gama sallama ga Manzo, sai ya dubi kabarin Manzo yana tsaye, sannan ya yi godiya ga Allah da yabonsa, sai ya aika gaisuwa mai yawa zuwa ga Manzo, sannan ya karanta wannna ayar da take cewa: Da wadanda suka zalunci kawunansu sun zo, sannan ya ce ya Allah mun ji kiran ka kuma mun amsa umurninka, sannan mun yi kamun kafa da manzonka muna neman cetonka daga zunubbammu, lallai zunubbai masu nauyi sun yi mana yawa…"
5- Sheikh Hasan Bn Ammar sharanbalani a cikin littafinsa "Murakil falah" yana ruwaito ziyarar Manzo kamar haka:
"Amincin Allah ya tabbata gareka ya kai shugabana ya manzon Allah, Amincin Allah ya tabbata a gareka ya annabin Allah! Lallai kurakurai sun karya mana kashin baya, sannan nauyin zunubban ya yi mana yawa a kan kafadummu. Kai ne mai ceto kuma wanda ake karbar cetonsa. Allah madaukaki ya yi maka alkawarin ceto da matsayi mai girma kuma abin yabo a wurinsa, sannan yana cewa: "Duk lokacin da suka zalunci kawunansu sannan suka zo wajenka suna masu neman gafarar Allah sannan Manzo ya nema musu gafara a wajen Allah, zamu samu Allah mai karbar tuba kuma mai jin kai.
Mun kasance mun zalunci kawunammu ga mu mun zo wajenka sannan muna neman gafara dangane da zunubbammu, ka nema mana gafara a wajen Allah".
6- Sayyid Ibn Dawus (ya rasu 664) ya ruwaito yadda ake ziyarar Manzo daga Imam Sadik (A.S) ga abin da yake cewa: Ya Ubangiji kai ne ka ce wa manzonka duk lokacin da suka zalunci kawunansu kuma suka zo wajenka suna neman gafarar Allah, sannan Manzo yanema musu gafara, zasu samu Allah yana mai karbar tuba kuma mai jin kai"
Ya Ubangiji ban kasance ina rayuwa a zamanin Manzo ba, amma yanzu na zo ziyararsa, kuma ina mai tuba daga munanan ayyukana, kuma ina neman gafara daga zunubbaina kuma ina mai ikrari a kan aikata su".
Mun kawo wasu daga cikin misalai dangane da yadda ake ziyarar Manzo, sannan mun ga yadda suka hadu a kan karanta wannan aya ga mai ziyara. A hakikanin gaskiya wannan aya wani nauyi ne aka aza wa mai ziyara aka kuma aza wa Manzo:
Amma nauyin da aka aza wa mai ziyara shi ne, mutum ya je wajen Manzo ya nemi gafarar zubbansa, sannan nauyin da ya hau kan Manzo shi ne ya neman wa mai ziyara gafara a wajen Allah.
Dukkan wadannan ladubban ziyara suna nuna mana yadda mai ziyara yake neman ceto daga Manzo a yayin da ba shi duniya, babu bambanci da lokacin da yake raye ta yadda mutum zai yi kamun kafa da shi.

Ibn Taimiyya Da Mabiyansa
Ibn Taimiyya da mabiyansa suna cewa: Neman addu'a daga Manzo ya kebanta ne da zamanin rayuwarsa ne a duniya kawai, don haka wannan ba ya halatta bayan wafatin Manzo! Haka ne zai yiwu mutum ya ziyarci Manzo, sannan ya yi addu'a a gefen kabarinsa sannan ya nemi abin da yake so a wajen Allah.
Dangane da amsar wannan magana kuwa zamu yi fadakarwa a kan cewa, dole ne a fahimci matsayi da darajar Manzo a wajen Allah, wato matsayin da zai sanya al'ummar musulmi masu zunubi su zo wajensa domin ya nema musu gafarar Ubangiji ta yadda addu'arsa karbabba ce.
Shin wannan matsayi da daraja ta Manzo ya samu asali ne daga jikinsa ko kuwa wani abu wanda ya shafi rayuwar duniya, ta yadda sakamakon wafatinsa zai kawo karshe, ko kuwa wannan matsayin sakamakon tsarki da daukakar ruhinsa ne?
Ra'ayi na farko kuwa ya saba wa hankali da shari'a, domin kuwa kamar yadda muka yi bayani a cikin bahsin rayuwar barzahu mun ga yadda ya kasance cewa; hakikanin mutum ruhinsa ne ba jikinsa ba. Sannan mun ga cewa ruhin mutum bayan rasuwarsa zai ci gaba da rayuwa a rayuwar barzahu, wato mutuwa ba yana nufin karshen rayuwa ba ne, ci gaba ne da rayuwa a wata duniyar ta daban. Don haka matsayi da daukakar Manzo ta samo asali ne daga girma da daukaka na ruhinsa, don haka bayan wafatinsa wannan matsayi yananan kamar yadda yake lokacin da yake a raye.
Sannan a bahsimmu da ya gabata mun tabbatar da kasantuwar alakarmu da wadanda suka riga mu gidan gaskiya, ta yadda suna jin duk abin da muke fada.
Tare da kula da abin da muka ambata, ayar da muka ambata a baya ba ta kebanta da lokacin rayuwar Manzo ba, kuma riko da hakan wani abu ne marar dalili. Sannan zamu tambayi wadanda suke inkarin kamun kafa da Manzo da cewa: me ya sanya bai halatta a yi kamun kafa da Manzo bayan wafatinsa ba? Shin don ya kasance ne duk wani girma da daukaka da kusanci ya samu ne a gare shi sakamakon yanayin jikinsa ne, ta yadda sakamakon rasuwarsa wannan matsayin da kusancinsa a wurin Allah zai kawo karshe?! Shin mutuwa shi ne karshen rayuwar mutum ta yadda Manzo bayan wafatinsa ba shi da sauran rayuwa?!
Shin sakamakon wafatin Manzo shi kenan ba mu da sauran wata alaka da shi?!
Amsar dukkan wannan tambayoyi kuwa ita ce; a 'a, don haka dole ne mu amince da cewa kamun kafa da Manzo a dukkan lokuta guda biyu (rayuwa da rasuwarsa) babu bambanci.
Daga karshe zamu yi tunatarwa da cewa, Sheikh Khalil Ahmad saharnafuri ya tattara fatawowin malaman AhlusSunna 75 dangane da halascin kamun kafa da Manzo.
A cikin wannan littafi da muka ambata a sama, an yi Karin bayani da cewa: A nazarimmu da manyan malamammu shi ne, ziyarar kabarin Manzo yana daya daga cikin manyan hanyoyi wajen neman kusanci zuwa ga Allah madaukaki, sannan yana daya daga cikin muhimman ayyuka masu lada kuma wata hanya ce domin samun matsayi da daraja madaukakiya. Wannan kuwa wani umarni ne wanda yake kusa na wajibi da farillai na shari'a, madamar isa zuwa ga hakan ba zai janyo tsanani ko asarar rayuwarka ba. Kamun kafa kuwa da annabawa da waliyyai da manyan bayin Allah, shahidai da siddikai, a cikin addu'a a lokacin rayuwarsu ne ko kuwa bayan rayuwarsu ya halatta.

Tambayoyi Da Amsoshi
Dalilai a kan halascin kamun kafa da Manzo bayan wafatinsa wani abu ne wanda ya bayyanar mana. Amma dangane da hakan akwai wasu tambayoyi wadanda dole ne mu bayar da amsarsu.

Tambaya ta farko: Shin neman addu'a daga mamaci shirka ne?
Wasu suna tunanin cewa neman addu'a daga wanda yake raye, wato yana iya yin addu'ar wani abu ne wanda ya halasta, amma yin haka ga mamaci shirka ne. Amma shin wannan tunani daidai ne?
Abin da ake nufi da shirka kuwa a cikin wannan tambaya da tagabata shi ne shirka a cikin ibada, (hadallah da wani a cikin bauta) wato neman addu'a daga mamaci yana nufin yi masa bauta kenan.
Wannan tunani na sama sam ba ya inganta, saboda:
Na farko: Idan neman addu'a ga mamaci yana nufin yi masa bauta, to wannan ya nuna cewa neman addua'a daga mutumin da yake a raye shi ma yi masa bauta ne domin kuwa babu bambanci, domin kuwa neman addu'a ne tare da kaskantar da kai, don haka wadanda suke ganin neman addu'a daga wanda yake raye ba ya nufin bauta masa ba ne, don haka dole ne su amince da cewa yin hakan bayan rasuwa ma ba yana nufin bauta ba ne, ballantana ya zama shirka ko sabanin tauhidi.
Na biyu: A cikin fasali na hudu na wannan littafi mun bayani a kan ma'anar ibada bisa dalilai na hankali, ta yadda muka nuna cewa ba duk neman wani abu ko addu'a ko makamancinsa ba ne ibada. Abin da ake nufi da ibada shi ne wani nau'i ne na girmamata musamman wacce take tare da wata akida ta musamman, wato mutum ya dauki wanda yake kaskantar da kansa a gare shi a matsayin Allah, wa'iyazu billah, ko kuma mutum ya dauka cewa wani abin halitta ne yake tafiyar da wasu daga cikin ayyukan Allah kamar yadda masu bautar gumaka suke dauka.
Amma girmamawa da kaskantar da kai wanda ya koru daga wannan akida marar tushe, ta yadda mutum yana ganin wanda yake girmamawa a matsayin wani bawan Allah ne, kuma wanda yake da kusanci zuwa ga Allah, sakamakon haka ne yake kamun kafa da shi yana neman addu'arsa, sam ba a kiran wannan bauta, ballantana ya zama shirka da Allah.

Tambaya ta biyu: Shin neman addu'a daga mamaci ba shi da wani amfani?
Daya daga cikin abin da masu inkarin wannan al'amari suke kawowa shi ne, mutumin da ya mutu sam ba shi da ikon da zai iya biya wa mutum bukatarsa. Saboda haka neman wani abu daga wanda ya mutu sam wani abu ne marar amfani.
Amsa: Tushen wannan tamabaya yana komawa ga yadda mutum yake ganin duniya, wato kamar cewa wannan duniyar da muke gani ita kawai ce duniya bayan wannan babu wani abu, wdan da suke kuma ganin cewa mutum da zarar ya mutu shi kenan babu sauran wata rayuwa, don haka wadanda suka gabata sama ba su da wata rayuwa, don haka neman wani abu daga gare su wani abu ne marar amfani.
Amma tare da kula da ka'idojin da muka ambata a sama, amsar wannan tambaya a fili yake, haka ne mutum da ya mutu ba shi da rayuwa irinta duniya, amma yana da wata rayuwar ta lahira, sannan tare da izinin Ubangiji yana iya amsa na bukatocinmu.

Tambaya ta uku: Shin tsakanimmu da wadanda suka rasu akwai wani shamaki wanda zai hana su jin maganarmu?
Wadanda suke da wannan tunani suna ganin tsakaninmu da wadanda suka rasu akwai wani abu wanda ya kare tsakanimmu, wanda Kur'ani yake ambata da barzahu. "A bayansu a kwai barzahu, har zuwa ranar tashin kiyama". Don haka kirammu ba zai isa zuwa gare su ba.
Amsa: Barzakh a harshen larabci ba tana nufin shamaki ko hijabi ba, wato ana nufin shamaki wanda yake hana su dawowa zuwa rayuwar wannan duniya, ba wai abin da zai hana su alaka da wadanda suke a raye ba. tare da kula da ayar da take da alaka da barzahu muna iya fahimtar wannan al'amari kamar yadda Kur'ani yake cewa:
"Zuwa lokacin da mutuwa zata zo wa daya daga cikinsu, zai ce: Ubangiji ka mai da ni zuwa duniya, domin kuwa zanyi aiki mai kyau a cikin abin ya ragu gare ni, sam ba haka ba ne kawai magana ce wacce mai yin ta yake fada".
Tare da kula da abin da mamaci yake fada shi ne Kur'ani yake ba shi amsa da cewa: "A bayansu akwai abin da ya kare su ta yadda ba zasu koma ba har zuwa ranar kiyama". Saboda haka wannan shamaki na hana dawowa a duniya ne, ba wanda zai hana wadanda suka rasu ba su yi alaka da wadanda suke a raye.

Tambaya ta hudu: Shin Manzo yana jin maganarmu?
Kur'ani yana kamanta yadda mushirikai suke da matattu, manufarsa kuwa da wannan shi ne, kamar yadda matacce ba ya jin magana, masu shirka suma haka suke, a kan haka ne yake cewa: "Lallai kai ba ka iya jiyar da matattu" "sannan ba ka iya jiyar da wadanda suke cikin kabari" Dangane da kamanta mushirikai da matattu dangane da rashin jin magana, muna iya cewa wani abu ne wanda babu shakku a cikinsa cewa an kamanta mushirikai da matattu.
Amsa: Babu shakka a cikin kowace kamantawa ko misaltawa a kwai wata fuska da abu guda biyu a kan kamanta su, misali lokacin da za a ce Ali kamar zaki yake, tabbas a nan an dauki fuskar jarunta ne aka siffanta Ali da zaki domin kuwa duka guda biyun suna da wannan siffa. Saboda haka a nan zamu ga menene fuskar da ta sanya a kamanta matacce da mushiriki?
Tabbas babu yadda za a ce ta fuskar cewa sam ba su ji ko kadan, domin kuwa idan muka dauki hakan cewa mamaci ba ya ji, to shi ma mushiriki zai rasa wannan halitta ta ji ke nan, ga shi kuwa mushiriki yana jin maganar Manzo da ma ta sauran al'umma.
Saboda haka wannan kama da ta sanya aka kamanta su da wani abu daban, wannan kuwa shi ne rashin sauraren magana mai amfani. Wato kamar yada kiran wanda ya mutu zuwa ga aiki mai kyau ba shi da amfani, domin kuwa lokacin aikin ya riga ya gabata, haka nan kiran mushrikai zuwa ga aiki mai kyau ba shi da wani amfani, domin kuwa sam ba su da niyyar amsa wannan kira, tare da lura da ayoyin da suke magana a kan rayuwar barzahu zamu iya fahimtar wannan hakika.
Saboda haka magana guda a nan ita ce, kiran mushrikai zuwa ga imani kamar kiran wadanda suka mutu ne zuwa ga aiki mai kyau. Don haka kiran wadannan gungu guda biyu (Mushrikai da matattu) sam ba zai samu wata riba ba. Mushiriki yana ji amma ba shi niyyar karbar gaskiya, mamaci shi ma yana ji amma lokacin aiki ya riga ya wuce yanzu lokacin sakayya ne ga abin da mutum ya aikata ne.
Abin burgewa a nan shi ne almajirin Ibn Taimiyya wato Ibn Jauziyya, shi ma a cikin littafinsa (Arruh) ya fassara wannan aya da ake tambaya a kanta kamar yadda muka fassara. Yarda da wannan tafsiri da Ibn jauziyya ya yi, yana nuna kaucewa daga ra'ayin malaminsa Ibn Taimiyya a kan wannan magana.